← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 56

Sashe 13

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akai Akai yake ɗaga idanu yana kallon kyakkyawa agogon dake hannun shi samfurin Apple, sai kuma kiran da akeyi mashi Akai Akai yana latse wa. Ƙarar buɗe ƙofa ce ta dawo da hankalin mu duka wajen, zabura muka yi mu duka biyun wanda a tare muka isa ga likitan da ya fito daga cikin ward ɗin "likita umma ta ta farfaɗo? Kaddai kace man ta mutu dan Allah" na faɗa ina mai matso wani sabon kwallar, "ummanki lafiya lau ta farfaɗo amman mun yi mata allurar barci saboda ta sake samun hutu, zaki iya shiga ki ganta nan da anjima idan ta farka" ya faɗa man yana mai maida hankalin shi kan yaya ameen ɗin da yake tsaye ta gefen mu, "a'ah yallaɓai ashe baka shiga office ɗin ba? Sai ka zauna waje?" dan guntun murmushi yayi sannan yace ma Ya Ameen ɗin "to muje sai in maka ƙarfin bayani ko" ya wuce gaba Ya Ameen ɗin ya bishi a baya, da idanu na raka su har suka shige office ɗin sannan na sauke ajiyar zuciya lokaci guda ina mai hamdala gami da sanya hijab ɗina na share dukkan ƙwallar dake kan fuskata, muskutawa nayi sannan na maida duba na kan mama Talatu dake tsaye tana binmu da kallo da kuma naɗe dukkanin motsin mu cikin fai-fain ta na gulma, ɗan taɓe baki nayi kaɗan ina mai rayawa a cikin raina "dukkan ku zaku gama ne, zaku gaji ku bari, ai Hajiya Kubra ba'a mata gwaninta.

***************

Likita ne ya zauna a kujerar sa gami da nuna ma Al'ameen ɗin kujerar zaman patient," Bismillah yallaɓai ga wuri zauna" bayan ya Ameen ɗin ya zauna ne sannan ya muƙa mashi hannu suka sake yin musabaha gami da ƴan gaishe gaishe, dama sun san juna don shine family doctor ɗinsu, kuma a asibitin ne suke da file, Dr. Ashafa kenan kwararren likita ta kowanne fanni.

"Yallaɓai garin yaya haka kuka bar matar nan cikin irin wannan hali? Abun yayi tsanani, zuciyar ta ta kusa ta buga, ta daɗe da ciwon zuciya duk da bincike ya nuna tana kan drugs, sai dai ba wasu masu ƙarfi bane, ba zasu yi tasirin hana zuciyar kumbura ba, gaskiya ba dan kunyi gaggawar kawo ta nan ba da abun ya munana, a dinga kulawa pls" ya sauke maganar tare da ɗora dukkanin idanun shi da natsuwarshi akan Al'ameen ɗin don jin amsar da zai bashi.

"Dr wallahi ban san abun yayi worse haka ba, ban ma san wane asibiti suke zuwa ba, na dai san bata da lafiya Amman ban san me ke faruwa da ita ba, yanzu ya jikin nata? Ba zamu iya ganin ta yanzu ba, ina da uzuri ne tin ɗazu ma ake kira na" ya sauke maganar da gani dai cikin hanzari yake don ya ƙagara ya tafi "No babu wani damuwa yanzu mun shawo kan matsalar, sai dai gaskiya a kula, a dena yawan ɓata mata rai, in da hali ma adena bari tana aiki mai yawa da zai iya gajiyar da ita, yanzu ma zaku iya shiga ku ganta, sai dai zaku barta anan ne, ka san tsari asibitin ba'a zaman jinya" ya faɗa yana mai sake miƙa ma Al'ameen ɗin hannu dan musabaha, shima Al'ameen miƙa mashi yayi yana faɗin "Nagode Dr. Ashafa, sai dai alfarma zakuyi mana wannan karon, ita wannan yarinyar ɗiyarta ce, so ko mun koma da ita zata tashi hankalin ta ne, zata damemu da kuka, ku barta ta zauna wajen ta har muga yanda jikin zai yi, ni zan je, idan na taso daga office zan dawo inga yana yin jikin ko da Abunda ake buƙata" "OK shikenan yallaɓai" likitan ya faɗa, sannan suka juyo a tare suka fito domin shiga ɗakin da umman tawa take; ya ameen ɗin ne ya tsaya yana faɗa mana mu shiga muga jikin ta har da mama talatun domin ita zata koma ne gida.

A tare muka shiga ɗakin da shi da mama talatun, likitan ne yake shaida mana banda hayaniya, kada kuma a tada ta har sai dai ita ce ta tashi dan kanta, kuma kada a bata komai taci, akwai sinadari abinci da ake bata ta iskar oxygen ɗin da yake maƙale a hancin ta.

Duk iya rashin imanin mutum sai ya tausaya wa umma ta, kwance take tayi fayau da ita, numfashi take sauke wa a hankali, babu Abunda ke motsi jikin ta, jawo kujera nayi ta roba mai kyau na zauna yayin da na ƙure ta da idanu hawaye na ɗiga ɗis-ɗis saman hijab ɗina.

Juyawa suka yi suka fita har mama Talatu da Ya ameen ya yafito da hannu, kuɗin taci ya bata tare da mata godiya sosai yace ta koma gida sai ya dawo, dawowa yayi ɗakin tare da kira na domin shi wucewa zai yi, a baya na bishi zarai-zarai har muka fita harabar asibitin da har mama Talatu ta samu abun hawa, ina kallon ta tana leƙowa taga shin ina zamu, sai dai ta makaro dan mai motar ma har yaja sunyi gaba, naso nayi mata godiya Amman ba komai ai bana ma fatan mu daɗe asibitin, zan yi mata idan mun koma gida.

"Is OK Suuhaaan" ya faɗa a hankali bayan ya daidaita tsayuwarshi bakin motar sannan ya juya ya jingina da ita sosai, "Comon goge wannan hawayen naki, kukan ya isa hakanan, ki yi mata addu'a sannan ki guji ɓacin ran ta, a mamadin mahaifiya ta ina mai ƙara baku haƙuri, na san ita ce sanadi, Amman insha Allah komai ba zai ƙara faruwa ba" ya faɗa yana mai ƙoƙarin haɗa idanu dani, ni kau sauke kaina nayi ƙasa ina mai bin umarnin nashi na share fuskar tawa gami da jan majina a hankali na shiga faɗin "Mungode Yaya babu komai wallahi, dama umma ta tana da wannan ciwon, nima dashi na taso na ganta, ba Hajiya bace sila, Mungode da karamci Allah ya saka da Alkhairi" na faɗa ina mai ƙosawa da tsayuwar, ba zan iya jure tsayuwa wuri ɗaya dashi ba, kwarjini yake man, gani nake duk ya cika wajen, Al'ameen ɗin daban ne, akwai kamala da haiba tattare dashi, komai nashi da yake yi cikin hankali da natsuwa yake yin shi, daidai da magana kaman baya son yi, muryar shi, ƙamshin turaren shi na ƙara rikitar dani, bana son irin yanayin da nake shiga a duk lokacin da muka kasance mu biyu a wuri ɗaya, kula yayi da irin yanda duk nabi na takura, motsa bakin shi yayi a hankali ya shiga faɗin "ki koma wurin umman, zan je aiki in dawo tin ɗazu ake jira na babu Abunda zaku buƙata, akwai komai a ɗakin kuma akwai drinks a fridge zan sa a kawo maki break fast ki tabbata kunci don na san baki ci komai ba, sai na dawo" Ya faɗa, bai jira cewa ta ba ya faɗa mota gami da yi mata key, janyewa nayi na bashi hanya, ya zo yawuce bai ko kalli inda nake tsaye ba (hoooo Al'ameen miskilanci)

*******************************

Mama Talatu kuwa na isa gidan sashen Hajiya kubran tayi, ta iske bata tashi ba Amman don tsabar san gulma sai da ta jira ta, bayan ta fito ne take tambayar ta ya bata ganni ba? Ban shigo aiki ba,me yake faruwa, "yo Hajiya ina ko zaki ganta? Ai bama su gidan gaba daya" cikin isa take kallon talatun, "ke Talatu bana son munafunci, faɗa man gaskiya me yake faruwa ne a gidan? Ta faɗa cikin gadara lokaci guda tana mai zama kan ɗaya daga cikin sofa na alfarma da sukayi ma falon ƙawanya, sanye take cikin wani ɗanyen lace mai azabar kyau, dama hajiya Kubra ba dai kyau ba, naira ta kwanta mata ta ko ina sai sheƙi take yi da walwali, nan mama Talatu ta kwashe ƙarya da gaskiya har faɗa mata take yi cen ta baro Al'ameen ɗin ai muna tare.

Ranta ko in yayi dubu ya ɓaci, au ta hana taraiya da afnan shine muka koma ma Al'ameen? Al'ameen ɗin nata da take ji dashi tamkar tsoka ɗaya a miya, me hakan ke nufi? Dakatar da mama talatun tayi gami da miƙewa cikin takon isassu ta fita daga sashen zuwa sashen Alhaji da take barowa da sanyi safiya, Afnan ce ta fito tana kallon mama Talatu, ashe ta zo fitowa taji suna magana shine ta koma da baya take jin duk abubuwan da mama talatun ta faɗi ma mom ɗin tasu "mama kiji tsoron Allah fa, ashe ke ke hadda sa fitina tsakanin hajiya da masu aikin gidan nan? Kina shugaba baki so a zauna lafiya, to wallahi kema ba zaki ci gaba da zaman gidan nan ba muddin kika yi sanadiyyar barin su suhan ɗin gidan nan". Tana kaiwa aya bata jira cewar mama talatun ba ta koma ɗakin nata da gudu tana mai rarumar wayar tata gami da kiran Ya Ameen ɗin, tsaf ta kwashe komai ta faɗa ma gayan nata yanda taji mama Talatu na faɗa ma Hajiya, tare da faɗa mashi yanzu zata bar gidan zuwa asibitin ta taya ni zama, koma minene ya faru ai su ne sila; Dakatar da ita yayi gami da cewa ta bari sai ya dawo baya son wata matsala kuma, shi zai jawo hankalin hajiyar ta bar zancen bari ma ya faɗa ma Alhaji komai kafin Hajiyar ta isa.
Chapter 13 · 0% Book details