← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 56

Sashe 23

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya Auwalu ne ya kamo hannun shi ganin abun na neman kwaɓewa, bai kamata a samu irin wannan saɓanin ba gaban yara, shi kau gogan naku, zaune yake kaman mutum mutumi, me yasa Mahaifiyar tashi take haka ne, mahaifan shi ke saɓani akan shi? Lallai babu wadda tayi mashi, baya kuma jin zai iya auren yarinyar da take nufi, kai shi Sam ma tarbiyyar ta bata yi mashi ba, dama ya kula da yanda take shisshige mashi idan yaje gidan, ashe da biyu ma Mahaifiyar tashi ke aikenshi gidan, itama yarinyar dalilin da yasa take mashi wasu abubuwan kenan? Sai yanzu ma zuciyar shi ta shiga hararo mashi wasu abubuwan, yayi nisa a cikin tunanin yayin da idanu wan shi suke rufe ya tsinkayo maganar wan Mahaifin nashi yana cewa "ya isa Mustapha, Ya isa su ai mata ne, tinanin su ragagge ne, kuma duk wannan abun dake faruwa shi yaron ai gashi gaban ku zaune, har yanzu bai tanka ba, bama mu sani ba shin ko akwai wadda tayi mashi cikin rai? Ko akwai wadda suke tare? A bari aji ta bakinshi tukunna" yayin da ya maida kallon shi ga Al'ameen ɗin sannan ya cigaba da faɗin
"Shin Kai Al'ameen a cikin ranka akwai wadda kake so kuka yi maganar aure da ita? Ko akwai wadda ka yima Alƙawarin aure ne?

Falon yayi tsit, baka jin komai sai ƙarar ac da take ta aikin ta ahankali ahankali, kowa ya maida hankalin shi da natsuwar tashi akan Yaya Al'ameen ɗin, yayin da kanshi yake ƙasa, da yawa daga cikin ƴan matan da suke falon suna so ace sune ya zaɓa a matsayin aboki yar Rayuwar shi, Al'ameen ɗin ɗaya ne tamkar da dubu, komai ya haɗa, kyau, natsuwa, ilimi, gayu, ga uwa uba naira, runtse idanu shi ya sake yi gam, yayin da yake jinjina girman maganar da zata fito daga bakin shi, ahankali ya buɗe idanun nashi ya fara ɗora wa akan kakan nashi, Alhaji Isuhu da shima kaf natsuwar shi na akan jikan nashi, kaka zuwaira ya kalla ta sakar mashi murmushi irin nasu na dattawan da suke cike da natsuwa da kuma dace da ƴaƴa nagari, sannan ya ɗauke kallon shi kacokam ya ɗora shi akan Mahaifiyar tashi da ta cika fam, uwa zata fashe, dan dai wayewa da kuma halin tarin rai irin nata, Sam bata kawo ma ranta cewa yaron nata zai bijire ma buƙata tata ba, na amsar tayin ƴar ɗan uwanta da tayi mashi ba gaban kowa, bata yi tinanin zai watsa mata ƙasa a ido ba.

Kallon shi ya maida kan iyayen nashi maza biyu da suke zaman jiran cewa shi, sake ajiyar zuciya yayi ahankali, yayin da ya gyara zaman shi kan lallausan carpet ɗin da ya malale ilahirin falon, sannan ya nisa ya cigaba da faɗin " Eh ABBA, Akwai wadda muka yi Alƙawarin Aure, sai dai kuyi haƙuri jin ko wacece, Nidai ita nake so, kuma itama tana so na, kuma ina mai roƙon alfarmar da aura man ita, ita na zaɓa a matsayin abokiyar rayuwa ta, uwar ƴaƴa na, tarbiyyar ta tayi mun, komai nata yayi mun, kuma, kuma ina mai roƙon ta yi maku kaman yanda tayi mun"

Ya faɗa cikin salon maganar shi mai kama da ta saraki, sannan ya ƙara she yana duƙar da kai alamar roƙo da girmamawa ga iyayen nashi har dama kakannin nashi da suke zaune a wajen.

Murmushi Alhaji Isuhun ya sake cikin halin dattako ya shiga faɗin " Alhamdulillahi Faɗi kanka tsaye Ameenullah, nan kowa jiran yaji taka zaɓen yake yi, in da hali sai a haɗa da na shi Aleeyu baki ɗaya ma a wuce wurin.

Toh fa! kan kowa da yake zaune a falon ya ƙulle, har da mahaifan shi Al'ameen ɗin watau Hajiya Kubran da Alhaji Mustaphan, Aunty Feena ce ta kalli ƙanen nata cikin wasiwasi da tarabbabi, kada ya janyo masu wani abun kuma, ita ta san bayada wata budurwa da yake so, kuma ta san babu wacce yayi ma Alƙawarin aure, toh fa! Kaman zata ce wani abu sai kuma tayi shiru, ganin Al'ameen ɗin ya fara magana

"Abba Hauwa'u ce ta gidan mu watau Suhaann.. ɗiyar Ma.. Ma Maryama ta ɓangare masu aiki"

Salati Hajiya Kubra ta sake tana mai miƙewa tsaye tana taɓa hannuwa kaman wata sakarai, jin maganar tayi kaman saukar aradu, sakin baki tayi, yayin da su kuma su Nihal suka ƙwalalo idanu, ba su ba har Aunty feenar ma ta shiga komar mamaki, Afnan kuwa murna da farin ciki ne suka mamaye ranta, Aunty Suhan fa! Ko dai kunnen ta ne ke gaya mata ba daidai ba? Nihal ce ta shiga zumɓuro baki tana faɗin wallahi yaya a'a mai aikin mu ce fa?

Murmushi Alhaji Mustaphan yayi, ko babu komai ya san dalilin yaron nashi na yin hakan, tabbas ya jinjina ma yaron nashi, yayi na'am kuma da buƙatar tashi, sannan kuma ya bashi goyon baya ɗari bisa ɗari, jinjina kai ya shiga yi yana faɗin "Masha Allah, haka ake so Al'ameen yarinya tayi, kuma ina tare da kai, insha Allah zan shige maka gaba wajen ganin komai ya daidaita" yayin da Hajiya Kubran ta koma ta zauna bisa kujera inda ta tashi tana faɗin "kai shashasha ne Ameenu? Ashe baka da hankali? Me zaka ci da wannan yarinyar? To bari kaji ban yadda ba ka auri yarinyar da bata da asali koda kuwa ace mata sun ƙare ne a duniya, Ban yadda ba Sam, idan ba haka ba kuwa zaka gamu da fushi na, au ashe dama munafintata kake yi? Kana cen kana soyayya da wannan ƴar jariri yar abun? Sam ban lamunta ba, Alhaji har kana faɗin ka yarda, tau bari kuji ni Sam ban yarda Bako sama da ƙasa zasu haɗe bazan lamunci wannan auren ba"

Alhaji Auwalu ne ya shiga kwantar mata da hankali yana faÉ—in "Kai Mustaphan bamu gane yarinyar da yake faÉ—i ba, kar dai ace yarinyar da aka zo da ita a goye gidan ka, É—iyar wannan mai aikin?"

Jinjina mashi kai Alhaji Mustaphan yayi cikin son bashi tabbaci, yaya Auwalun ne ya shiga faɗin ai ko hajiya ta yadda mu ba zamu yadda da wannan abun ba har sai an nemo asalin ita yarinyar, kai Ameenu ka bamu lokaci zamuyi ƙwaƙƙwaran bincike akai, kuma bamu ce ka cigaba da neman yarinyar ba har sai mun samu cikakke bayani akan ta,

Alhaji Mustaphan ne ya shiga faɗin hakan yayi daidai, zamu bincika bayan wannan yarinyar bata da wani abun da za'a ce an kasa auren ta, kasancewar ta ɗiyar mai aiki, wannan ba hujja bace, ni na yarda da yarinyar da kuma tarbiyyar ta, Allah yayi maka albarka Al'ameen kayi Abunda ake so, ina alfahari da kai da wannan tausayi da jin ƙai da kake tare dashi, Allah ya ƙara ma Rayuwar ka Albarka duniya da lahira"

Da ameen kowa ya amsa, yayin da Hajiya Kubra ta miƙe ta fice daga falon kaman zata fashe, da kallo kowa ya bita yayin da wasu suka shiga jinjina kai, shi kau Al'ameen ɗin duƙar da kanshi ya sake yi ya maida idanu shi ya kulle, me ya sanya shi yin hakan? Me ya janyo mashi? Yana so ne Mahaifiyar tashi ta canza halin ta akan masu aiki, yana so ne ta gane mecece duniya da Abunda ke cikin ta, Suhan ɗin alkhairi ce duk da kasancewar irin taƙaddamar dake cikin auren, ba soyayya tsakanin shi da yarinya Sam, bata ma san wainar da ake toyawa ba, kuma da wanne ido ma zai kalle ta yace mata ita ce ya zaɓa a matsayin wadda zai aura? Ta yaya zata kalli abun? Ta yaya ummanta zata fassara abun? Baya tinanin idan har umman bata yadda ba ko ta bada goyon baya ba abun idan zai yuwu.

*Wacece Suhan É—in???*

Tambayar da ya shiga yi ma kanshi kenan

Nisawa yayi yana mai sakin ajiyar zuciya ahankali ahankali, yayin da ya kai kallon shi kan sauran ƴan uwa nashi, tashin hankali da ƙyara ƙarara ya hango cikin idanu saudat da Nihal ɗin tau sai dai shi ba tasu yaje yi ba, yana hango Abunda zai faru ne nan gaba, da irin ƙalubalen da zai fuskanta nan gaba wajen Mahaifiyar tashi, gashi har ta fusata ma tabar falon, dama ya san hakan ce zata kasance, kuma shi baya jin idan zai iya janye maganar shi, hakan ma wata dama ce da yarinyar zata iya tantance wacece ita.

Alhaji Auwalun ne ya shiga kwantar mashi da hankali, yana faɗin ba zamu ƙi amince maka ba, muddin muka ga babu abun ƙi tattare da asalin yarinyar, sannan muna mai baka shawara ka koma ku sasanta da Mahaifiyar ka, saboda abun yayi maka albarka, idan babu mai magana zamu rufe taro da addu'a da kuma sanya ran cewa manema auren saudat da Nihal ɗin zasu zo gobe idan Allah ya kai mu.

Babu wanda yace komai, kowa da Abunda yake saƙawa acikin ran ta, abie ma ba zamu iya tantance halin da yake ciki ba, mutum ne mai zurfi ciki, kusan ma yaso yafi Al'ameen ɗin, tau sai dai shi ɗan ɓangare Hajiya Kubran ne, sai abin da tace, ko ta zartar, saɓanin Al'ameen ɗin da komin yake biyayya yaga za'a kauce ma gaskiya baya bin wannan ayarin.

A haka aka kulle taro da addu'a yayin da iyayen nasu maza suka cigaba da zama wannan karon har da mama zuwaira ɗin domin su ƙara tattaunawa
Chapter 23 · 0% Book details