← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 56

Sashe 40

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mun shiga cikin hidimar bikin dumu dumu Dukkanmu, albarkacin Hafsat da mahaifiyar ta, Abunda banyi zaton umman tawa zata lamunta ba, sai gashi ita dakanta ke ƙara gaya man irin halin kirki da karamci irin ma Hajiya zainab ɗin, da gani dai Hafsat ɗin ita ta biyo.

Abunda na kula dashi shine, duk lokacin da zan gifta ko zan wuce ta falon shine shewa da Æ´ar guÉ—a da ake Sanyawa haka ana zunÉ—e na sai kuma ayi tafi a kashe, manyan yara ne masu ji da kansu, ban ma yi tinanin zasu tsaya kula ko zunÉ—ena ba, tinda Nidai bansan me suke mawa ba, bansan me na aikata masu ba da har suke yi man haka. Share su nake yi kaman yanda umman tawa ta umurceni.

"Hahaha, Wannan? Yo me haÉ—aÉ—É—en saurayi kaman wannan zai ci da wannan? Haba Nihla, kisan me kike faÉ—a mana, dubeta fa, kaman alhaja, har koÉ—a take yi, ni anya ma ba sadaukar yalla bace, irin waÉ—annan masu muna bara muna karuwanci bace? Ni wallahi na tsani yarinyar bansan dalilin da ya sanya Dad ya sanya suka dawo nan ba, kishin ta nake ji sosai har cikin raina, bansan dalilin shi na son auren ta ba, bayan gani."

Ɗaya daga cikin ƙawayen su Saudat ɗince ke cewa haka, ban ko kalli inda suke ba nayi saurin wucewa, fatana dai ace ba dani suke ba, yo me ma zai sa inyi tinanin dani suke? Bayan banji sun kama suna ba, kuma ni na san babu wanda yace zai aure ni balle har wata tayi kishina a banza.

Share zancen nayi, ina mai shige wa ɗakin amaren da suke ta shirye shiryen zuwa bridal shiwer ɗin da aka shirya za'a gabatar a yau, duk da ita amaryar tasu tana kwance, tace ba da ita ba, bai hana su cewa wallahi sai sun je ba sun kashe ƙwarƙwatar idanun su.

Harda Afnan aka shirya sunyi shiga ta jar riga da straigh skirt Black, sai hula itama baƙa an ɗaura wani abu mai kyalkyali a hannu shima ja, sunyi kyau ba laifi, Amman a haka wai ƴaƴan musulmai zasu fita, Allah shi kyauta.

Motoci aka kawo aka shiga ɗaukar amaren, dama even ne na mata, wani ƙerarren gida dake ta bayan Layin su aka shirya ma abun, shima ya sha decoration Red and Black, sai amaren da sukayi complet White, ba ƙaramin daɗi suka ji ba da hafsat tace bata yin even ɗin, dama wai suna gudun a cika masu wuri da ƴan ƙauye, Shiyasa suka bata getpass guda biyar kacal.

To ita cewa ma tayi bata zuwa, sai ƙawayenta ne su huɗu suka shirya aka tafi tare dasu, suka saje cikin ƙawayen amaren, saura getpass guda kuwa ajiye shi aka yi baya da wani amfani, gidan fa yayi tsit, duk masu rawar kan an da ƴan ƙaryar na sun kwashe sun tafi, sai Naji dama gidan ya cigaba da zama a haka

Ohh🤔🤔 su suhan da ƙarfin hali ake.

Washegari sukayi arebian night, hall aka kama mai kyau da tsada, acen aka gabatar da shirin, wannan haɗe yake maza da mata, sunyi yadda suke so, da yake ba ya ameen babu mai kwatsa masu, abie ƙanen su ne y bai isa yace gyadda za'ayi ba duk da Aunt Feena na wajen, to itama bata ce ga yadda za'ayi ba, tinda Rayuwar turawa ta shiga kansu da yawa.

Mothers eve, aka shirya washegari, zo Kaga yadda aka ƙawata gidan da yake a haraba gidan za'ayi, anyi ɓarin kuɗi kaman da gayya, makaɗa da mawaƙa sun sha daloli, dole ne asan da bikin ƴaƴan Hajiya kubra Dambulan akeyi, rawa dai da juyi sunyi shi, manyan mata ko kunya basa ji haka suke juyi suna watsi da kuɗi, babu Abunda kake hangowa illa, gwala-gwalai, da ɗanyun lesussuka malam, masu video coverage nayi, masu hotuna nayi.

Duk abun nan da akeyi Ya ameen É—in na tsaye ta window É—in falon nashi yana hango su, hannuwan shi duka soke cikin aljihu wandon bugaggiyar shadda tashi, fuskar nan tashi murtuk, bai san me ke damun mahaifiyar tashi ba, bidi'a da alfahari kawai ne acikin ranta, in banda haka duk wannan watsi da kuÉ—in da akeyi duk na menene? Wa za'a burge? Wa ke bai san suna da kuÉ—in ba? To indai haka ne shi a ganin shi wannan almubazzaranci ne.

Makullan motar shi ya zara gami da ficewa ta ƙofar baya, jin kiɗan dake tashi a cikin gidan zai fasa mashi dodon kunne duk kuwa da girma da faɗin gidan.

Zaune nake kunnuwa na toshe da headphone, ƙira'ar Sheik abdurrahman sudais ce nake saurare. Ina jin daɗin muryar bawan Allahn, a hankali nake bi shi cikin suratul baƙara, nayi nisa cikin bin shi karatun, ɓangaren ɗaya kuma tinani ne barkatai cikin ƙwaƙwalwar ta, a hankali Naji wani abu na bimanta cikin ƙafa, saurara wa nayi, lallai wani abu ne ki bi man jiki dagudu, a zabure na tashi ina kwalla ƙara gami da fara dire dire da ƴan tsale tsale.

Bai aune ba yaji an kai mashi cakuma, zuwan shi kenan ta wurin yaji ihun mace, ni kau da dai Naji na samu wanda zan kama sai na kuma ƙwaƙume shi ina ta kurma ihu da tsalle tsalle, duk na cukuikuye hijabi na da fuska ta, wayata datayi tsallen baɗake gefe ta faɗi har headphone ɗin ya zare, karatun ta take ci gaba da rerawa a hankali a hankali.

Ƙoƙarin raba ni yake da jikinshi, ni kau sai ƙara ƙwaƙumeshi nake yi cikin murya ta mai cike da tsoro nake faɗin "wani abu na bina, ƙila kunama ce, a taimakeni"

"Ke ke wai meye haka ne, ya isa babu abinda ke binki, ba kunama bace, gidan nan babu kunama, ana yin feshi ki natsu"

Ban ko saurare shi ba, har saida na cire hijabi na wurgar da ita ta gefe, kama zanin nayi da niyyar kwance wa ya daka man wata irin tsawa, ba azziƙi na dawo cikin hankali na.

Sai sannan ne wata irin kunya ta kama ni, ganin Abunda nake shirin aikatawa, gani tsaye ko hula babu a kaina balle É—an kwali, duk nayi wurgi dasu harda hijab É—in.

Kaina kuwa kaman wata sabuwar mahaukaciya, dama ɗazu muka je akayo mana saloon, babu wanda baiyi santin kyawon da kaina yayi ba da tsawon da yayi har kusan tsakiyar baya, dama ban taɓa yi ba wannan ne yina na farko, duk da cika da yawan da gashin nawa yake dashi haɗi da tsawo.

Tattara gashin nawa na fara yi, na maida baya, sannan na wawuro hijab ɗita na sanya gami da ɗaukar wayar tawa da har yanzu sautin ƙira'ar malamin ke tashi.

Juyawa nayi da niyyar barin gurin ina mai cewa "Yi haƙuri yaya" dakatar dani yayi fuskar na tashi murtuk

"Ko kin koma cikin gidan basu gama kaÉ—e kaÉ—en nasu ba, zo muje"

Yana gama faɗar haka ya juya ya cigaba da tafiya, zuwa ga ƙofar da zata sadaka da bayan gidan, wanda sai kayi doguwar tafiya kafin ka shawo kwana zuwa bakin Gates.

Mamaki ne cike da raina, in bishi muje ina cikin wannan daren, ko ba ma haka ba, in ummata ta ganni ince mata me? Ko idan wani ya ganni yaje ya faÉ—a mata fa?

Ganin yaja ya tsaya ne gami da ɗan waigowa ya sanya ni ɗaga ƙafa cikin sauri na shiga binshi, juyawa yayi gami da cigaba da tafiya, duk da ɗan hasken farin wata da fitilu jefi jefi dake bayan gidan, da naga zai yi man nisa na kan ɗaga ƙafa a sukwane in bishi, har muka ɓulla ta fuskar gidan.

Hamdala nayi ganin mutane jefi jefi a ƙofar gidan da alama ma wasu zance sukeyi, bugun zuciya ta ne ya ƙaru, ganin ya nufi motar shi dake fake gefe guda ya kunna ya shiga, alama yayi man da in zagaya in shiga nima.

Ba musu, dole na buÉ—e gidan gaba na shiga shiga na zauna, É—an kwali na a hannu, sai raba idanu nake yi.

Tada motar yayi gami da ficewa daga Layin, bai tanka mani ba haka nima ban ce mashi ƙala ba, kowa na fama da ƴan miskilancin shi a kai, ni gani ma nake yi ya cika ƙarfin hali, haka kawai sai yasa ni in shiga motar shi ya ɗauki hanya dani alhali bansan inda zai kai ni ba?

"Sai daki zanyi" Abunda yace kenan ya ja bakinshi yayi shiru, ɗan zaro idanu nayi, bansan zancen zuci ya fito fili ba, ɗan waiwaya wa nayi na kalle shi, ina mai sadda kaina ƙasa, "kayi haƙuri, ummata bata san na fito ba Kaga dare yayi, Shiyasa nake jin tsoro"

Maimakon ya bani amsa, sai shiru da yayi yana mai maida hankali shi kan tuƙin da yake yi, shiru ne ya biyo baya acikin motar kaman ma ba zai tanka ba, sai kuma cen Naji yace

*"Kallon me kike yi mani rannan??? "*

~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~24~*

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Shiru nayi mashi ban tanka mashi ba, har yanzu fa ni a tsorace nake, yo naga muna ta sharara uban gudu hanyar ba kowa, bansan ina muka nufa ba, sai aikin murza yatsu nake, ganin ban bashi amsa ba na É—auka ya bar zancen kenan.

*"Kallon me kike man rannan?*

Tambayar ta ƙara zo man a bazata, bayan duk tsawon lokacin da muka ɗauka ban tanka ba.

Shahada nayi wajen cewa" kayi haƙuri"

"Ba haƙuri na tambaye ki ba, so nak insan dalilin kallon, ko nayi maki kama da wanda kika sani?"

Ya jefo man maganar da banyi tinanin zata iya fitowa a bakin shi ba.

Shiru na sake yi mashi ina sun ne kaina, ni sai ma ya bani Æ´ar dariya, bansan sautin dariyar tawa ya fito ba sai ji nai yana cewa" Dariya ma na baki ko?"
Chapter 40 · 0% Book details