← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 56

Sashe 16

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Horn yayi mai gadi da fitowarshi kenan daga makewayi, ya rugo da gudu ya shiga wangale tangaman gate ɗin, lokaci guda yana mai ɗaga ma uban ɗakin nashi hannu, ( da yake Al'Ameen ɗin mutumin shi ne sosai da sosai) shima mamaki fal cikin ranshi, ganin suhan ɗin a gaban motar Alhaji ƙarami da mama Talatu a baya sai wata mata da take kwance da bai iya tantance wacece ba bayan motar kaman matatta, Allah dai yasa lafiya ya faɗa yana mai furzar da dattin asuwaki daga bakin shi sannan ya shiga rufe ƙyauren gate ɗin da take turawa da ƙarfi saboda nauyin shi.

Motar ya harba bisa titi, yayin da ya ƙara speed ɗin motar, mu da muke cikin motar gani muke tamkar baya gudu, Amman a zahiri gaskiya gudu yake wanda ya wuce ƙa'ida ma, hakan ce tasa nake ganin nawar tashi kaman in ƙwace tuƙin nake ji.

Lokaci lokaci yakan juyo ya ɗan kalle ni da nake ta sharar kwalla gami da jan majina a hankali, tin kafin mu isa asibiti yayi masu waya gashi da patien emergency, aikuwa muna isa aka turo ɗan gadon ɗaukar marasa lafiya tare da gungura ta zuwa emergency ward, ɗaga ƙafa nayi da niyyar bin bayan su suka dakatar dani ta hanyar ɗaga man hannu, wannan ne ya sanya hankali na ya ƙara tashi fiye na da baya, ganin umman tawa kaman gawa sai yanda aka yi da ita, sake durƙushe wa nayi wurin ina mai sakin wani tsumammen kuka da ya karaɗe ilahirin reception ɗin, Ya ilahi, na shiga furta wa a fili ina faɗin "Ya Rab sa'idnee ya Allah" mama Talatu bata yi yunƙurin zuwa inda nake ba, kaman yanda shi ma gogan naku bai yi yunƙurin hana ni ba, sai ma waje da ya samu ya zauna ya tsura man idanu yana mai ƙara nazari na, lokaci guda ya miƙe tare da nufi inda nake durƙushen cikin sakon tafiyar shi mai kama da ta saraki.....

*Fans Kuzo kuci cake É—in deedat, fa u are All invited*

~_Oum-Deedat ce_~
[8/5, 8:24 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~11~*

**********'*********************

Kusan yini afnan tayi mana ita dasu Ayan, tafiya tayi wajen ƙarfe shidda saura, bayan ta sake bani haƙuri, na nuna mata haba ya wuce ai babu komai.

Ya Ameen bai dawo ba har misalin ƙarfe shidda da wani abu kuma umma ta bata farfaɗo ba, hankali na ne ya tashi, office ɗin likitan na koma ya ƙara kwantar man da hankali, cewa yayi lafiya lau idan ta farka zata samu ƙarfi sosai, da wannan ne na samu naji ɗan sauƙi, babu abin da ke tadani kusa da umman tawa sai salla, ko abincin da afnan ta sanya ni inci, kaɗan na ɗan tsakura, ita ma da taga ba zan iya ci bane sai ta haƙura ta ƙyale ni.

Ƙarfe bakwai daidai ya shigo bakin shi ɗauke da siririyar sallama da ni ƙaɗai na jiyo shi, kaina da yake duƙe bisa gadon umman tawa na ɗago a hankali na ɗora idanu na akan shi, idanun mu ne suka sarƙe cikin na juna nayi sauri janye nawa, kujerar da nake zaune kai na miƙe gami da tura mashi domin ya zauna.

Dakatar dani yayi ta hanyar ɗaga man hannu da na lura sana'ar shi ce, watau maganar ma wahala take bashi, da ido nake bin shi har ya zauna kan sofar dake ɗakin ƙwara ɗaya tal doguwa 3seater, "ya jikin umman? Har yanzu bata farka ba?" na tsinkayi muryarshi yana jefo man tambaya cikin muryarshi mai daɗin saurare, ɗaga mashi kai kawai nayi, domin har ga Allah kwarjinn shi na hana ni sukuni, ƙamshin turaren shi duk yabi ya cika man hanci." OK" ya faɗa cen iya leaɓɓa, zaro wayar shi yayi ya cigaba da latsawa kaman ma baya cikin ɗakin.

Sallama aka yi, gami da shigowa baki ɗaya, Alhaji Mustapha ne da iyalanshi baki ɗaya suka iso ta ƙarƙashin jagorancin Afnan da tace ta san ɗakin, miƙewa nayi cikin hanzari tare da masu barka da zuwa na ba Alhaji Mustapha kujerar da nake zaune, Gaishe su na shiga yi su da Hajiya kubra da take tsaye gefen Alhaji cikin isa da taƙama, "lafiya" Hajiyar ta amsa mani tana mai nufar kujerar da Ya Ameen yake kai ta zauna, tana mai sakar mashi murmushi yaƙeda wani irin kallo mai cike da ma'ano ni daban daban;

Shi kau Alhajin amsawa yayi cikin sarkin fuska, yana mai tambaya ta jikin umman tawa, amsa mashi nayi ina mai É—an murmushi iya fuska ta.

Aunty feena ce ta ja kujerar da na bama Alhaji domin ya zauna sai bai zauna ɗin ba, gaishe ta nayi itama ina mai sa hannu na ɗauki Nasreem da take saɓe a kafaɗarta, ta ko wangale man baki tana wasa da hijabin jikina, Amsawa tayi cikin sakin fuska da har saida ta bani mamaki, (Lallai mai ɗa wawa inji Hausawa) jikin umman tawa ta tambaya na amsa mata kaina duƙe ina ɗan yaƙe, Allah ya bata lafiya, da Allah ya kyauta ta shiga yi man, Ameen mun gode na shiga jerawa

Afnan da Ayan ne suka nufi wajen Yayan nasu tin shigowar su, dama ita ta hannun daman shi ce, Nihal ce ta dire wata ƙatuwar ledar da suka shigo da ita a hannu suna ta cin magani ko tanka man ba suyi ba, balle kuma in samu arziƙi tambayar jikin umman tawa,

Angode na shiga faɗi lokacin da Alhajin ya ke faɗa man su zasu wuce Allah ya bata sauƙi. Da ameen na bishi ina mai masu rakiya har bakin ƙofar motar da suka zo da ita, wata danƙareriyar mota ce duk yawan su ta kwashe su tsaf, gaskiya motar ta haɗu iya haɗuwa, Nidai ba zance ga sunan motar ba, Amman Alhajin ne da kanshi ke tuƙawa.

Hajiya Kubra ce ta kalli ɗan nata cikin wani yanayi na ɓacin rai Amman tana ƙoƙarin dannewa ne saboda kada Alhaji ya gane "Son ko zaka zo muje ne? Zamu yi ma su Hajiya siyayya ne gobe insha Allah zamu tafi cen mu duka muyi masu week end" ta faɗa tana mai gyara zama ta cikin motar,

"No mom ina da uziri yanzu gaskiya, akwai inda zanje mai muhimmanci, zamu haÉ—u gida wajen dinner kawai" ya faÉ—a a dake cikin miskalancin shi, lokaci guda yana latsa wayar shi kaman ma ba da mom É—in tashi yake magana ba; saboda ya kula da hajiyar ko jikin umman tawa bata tambaya ba, hakan bai mashi daÉ—i ba kuma ya kula ko Alhajin nasu ma hankalin shi bai kai wajen ba.

"OK Al'ameen kayi ƙoƙari dai ka dawo kafin diner ɗin saboda zamu tattauna yanda tafiyar zata kaya" aAbban nashi ya faɗa cikin murmushi yana mai tada motar tashi, Saboda ya ji daɗin yanda ya iske Al'ameen ɗin a asibitn, ko babu komai ya san zasu samu kulawa da ta dace, kuma ya san tausaya war ɗanɗan nashi ga na ƙasa dashi.

Juyawa muka yi ni da Ya Ameen É—in muka shige asibiti n akan idon Hajiya Kubran,

Cikin ɓacin rai da hajiyar ta kasa dannewa ta shiga faɗa tana faɗin "Amman Ahaji hakan ya dace ace kaman Al'ameen yana zaune suna jinyar ƴar aiki tare wannan yarinyar? Haba Alhaji, ya kake maida mu baya ne? Gaskiya Sam banji daɗi ba, iske shi fa nayi zaune hankalin shi kwance, shi ko iskar da take tasowa daga jikin su ma bai ji gurɓatacciya ce" Alhajin ne ya Dakatar da ita cikin ɗan ɓacin rai da yake ɗan taso mashi na halin Hajiyar "Ya isa Hajiya, kibar wannan maganar, wannan shine abun da ya dace kowanne shugaba yayi, na tsayawa tsayin daka ya tabbatar da lafiyar duk wani da yake aiki ƙarƙashin shi, ina Alfahri da Ameenun yana abunda yake dacewa" ƙutawa tayi cikin ɓacin rai da ƙudurce ɗaukar mataki akan al'amarin.

Afnan da take cen baya sai zumɓura baki take yi tana ƙunƙuni, Saudat ɗin ce ta hamɓare ta gami da cewa "village gal, ai dama ke kullum kina bayansu kullum" Aunty Feena ce ta dalla mata harara gami da cewa a hankali "kedai kin cika baƙin hali Saudat"

Shigarmu ɗakin yayi daidai da farfaɗowar umman tawa ta shiga motsa hannun ta gami da ƙoƙarin buɗe idanun ta.

Cikin hanzari muka isa bakin gadon a tare, gami da furta sannu umma, lafiyar ki ƙlau? "Jiddah! Jiddah, kina ina? Matso nan Suhan, hannuna na saka cikin nata ina mai murmushin farin ciki da ke taho wa da ƴar kwalla ta," Gani umma, gani kusa da ke" na shiga faɗi ina mai durƙusa wa na ranƙwafa daidai kan ta ina mai rungumo ta cikin jikina

"Hauwa'u ki yafe man kinji, na hana ki cikar burin ki, ki kira Alhaji ƙarami ki ce mashi na yarda da karatun ki, kiyi haƙuri da sannu kuma zaki san su wanene dangina, ahalina kuma, kiyi ma su Hajiya biyayya su ɗin iyayen ki ne, amanar ki na hannun su ko da bani da rai" ta ke faɗa cikin zafin ciwo idanu ta na a kulle har yanzu

Kuka na fashe dashi ina mai furta "umma ni zaki yafe mawa, nice sanadin tashin ciwon nan naki umma, kiyi haƙuri umma, na dena tambayar ki komai wallahi insha Allah"

Runtse hannuwa na tayi cikin nata tayi shiru a hankali tana mai sauke numfashi a hankali a hankali da gani bacci ne ta samu.
Chapter 16 · 0% Book details