← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 56

Sashe 56

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Maganar ta maƙale daidai lokacin da na fito ina ta matse matsen jiki da dukkan alamu ni kaina kunyar kayan nawa nake ji.

Idanunmu suka sarƙe cikin na juna, ya kai kusan second biyar yana kallon a, lokaci guda ya janye idanun nashi ga barin kallon nawa, daidai lokacin ni kuma na kai zaune bisa kujera ina gaida su.

A gaggauce suka amsa gami da tambaya ta lafiyar mu lau dai ko? Lafiya na amsa mashi, bilal ɗinne ke ƙara mani congrat na Jarabawa lokacin da Al'ameen ɗin ya kai kallon shi kaina yana mai cewa

"Tafiya ta kama ni, ga Bilal nan ko me kenan sai ki tuntuɓe shi, zai gama maki komai insha Allah" yana gama faɗar haka ya miƙe yana shirin ficewa.

Hafsat ɗince ta fito riƙe da wata jikkar kwali mai kyau a hannuwan ta, ta ƙara sa ga Al'ameen ɗin gami da miƙa mashi tana mashi fatan Allah ya tsare ya kiyaye hanya.

Bilal ne ya maida kallon shi kaina shima yana mai miƙewa gami da ce mani "Ya bani number ɗinki insha Allah zan kira ki" ya ƙara sa shima yana mai juyawa ya fice.

Har gaban danƙareriyar motar tashi da his excelency ya bashi ta raka su tana mai waving ɗinsu har suka fita a harabrr gidan da mai gadi ta wangale masu gate. Domin gidan na Hafsat duk yace ma na sauran ban wuri a kyau da haɗuwa.

Hatta kayan da aka yi ma hafsat É—in saida sadeeq É—in ya cire su ya cenza mata wasu sabbi dal masu masifar kyau ba tare kuma da dangin shi kun sani ba gudun Æ´an tsogunguma.

A falin ta iskeni zaune jikina sanyi ƙalau, to me ke shirin faruwa ne? Nidai na san Al'ameen ɗin ba haka yake yi mani ba, na kula ma ko kallon a baya son yi a yau, ko na bashi haushi ne rannan dana ruga ɗaki? Ko dai banyi ƙoƙari bane......

"Ke Suhan lafiyarki ƙlau kuwa? Naga jikin ki yayi sanyi, da ɗina dake wallahi wani lokaci ke baƙauya ce, ko irin ƴar rakiyar nan ma baki Iya ba"

Firgigit nayi ina mai binta da ido bansan lokacin da na samu kaina da tambayar ta ba "wai da gaske Ya Ameen tafiya zai yi?"

"eah mana Suhan, waike da kina nufin baki sani ba? Bai gaya maki ba?"

"Huh..." Na sauke ajiyar zuciya lokaci guda ina mai ce mata "wallahi ban sani ba Hafsat"

Mamaki ta shiga yi, har tana zaulayar ta wai wannan wace irin soyayya ce?banza nayi mata ban tanka mata ba, Amman fa gaskiya zan faÉ—a jikina ya mutu murus wallahi.

Su kansu Æ´an kankiyan sunyi mamakin tafiyar, Amman da yake sun san yana yin aikin nashi sai sukayi mashi fatan alkhairi, sun É—auka zuwan na aje a dawo ne.

Ƙarfe biyar bilal ɗin ya kai shi airport ɗin, ba ɓata lokaci jirgin nasu ya ɗaga zuwa america.....

#cying

Wash gaskiya na gaji fans gashi nan nayi maku na kwana uku.
~Oum-Deedat ce~
Chapter 56 · 0% Book details