← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 56

Sashe 4

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"OK ki jira mu gama ki tattara wurin" ta fad'a tana mai faracin abinci, "to Hajiya na fad'a ina mai dan rissinawa irin na biyayya sannan na juya na wuce babbanb falo domin jiran su gama din tinani fal araina, " Saudat had'a man Lipton din" naji ya fad'a daidai lokacin da nake idasa ficewa daga dining area din.

Sun shafe awa biyu kafin duk suka tashi tareda yima juna sallama hajiya ta haye sama inda abi ya shige sashenshi suma su nihal suka shige nasu sashen sai kuma Allah ya kaimu.

Tattara plates din nayi nakai kitchen na juya zan koma dauko sauran, naga ya shigo da wasu bance komai ba saima dukar da kai danayi na jaye na bashi hanya ya wuce cikin kitchen din nima na fice dan dauko wasu, ahaka ya tayani kwashe kayan dukda hankalina bai kwantaba saidai nasan cewa hajiya na iya saukowa taganshi aiko da na kade har buzu na, bansan me yasanya shi aikata hakan ba yau lokutta dadama naga ko kallo ban isheshi in ka cire 'yan kwanakin nan da yake yawan bina da ido, shima na dauka hakan na da nasaba da tausaya wa duk wani mai aiki ne na gidan daidai da masu sharar lambu, nikau ta bangarenta baisan wata irin kacha bace yake sanya wa yana daure illahirin jiki da jijiyoyon jikina ba,ba bazai hantareni ba amman ko kallo ban isheshi ba, babu fuskan tambayan yasanya naja bakina na tsuke, na isa wajen sinc din ina dauraye abun da suka b'ata naji maganar shi a bayana don har ga Allah na dauka ya fita.

Wannan tasanyani zabura na juyo mamaki fal a raina wanda har saida ta bayyana fuskana

Wace irin mai sa'a ce yau ni?🤩 ni suhan ce yau YaAmeen ke cewa zaiyi magana dani? Tau wacece irin magana? Kodai wani laifin nayi mashi? Kodai bai hakura ba dazu dana tureshi? Ko dai........"Ko baakijii ba ne? Nace inaso muyi magana"
ya fada hankali kwance da maganar nan tashi ta rowa da muryarshi mai kama da goge a cikin kunnen 'yanmata

"Too yaya"
na fada a ahankali cikin dardar tareda juyowa na fuskanceshi zuciyata kaman za tayo tsalle ta fito waje, saboda tsabar kad'uwa

Guntun murmushi yayi iya lebo shi aganinshi nan ya k'okarta hakan sai tasanya kyaun shi ya k'ara fitowa afili kasancewar ba halinshi bane ko da murmushin amman ko baiyi ba kyaun shi na d'aya daga cikin abunda ke fizgar yanmata. Kallona yayi na tsawon second biyu, gamida gyara jinginar da yayi da cabinet ya motsa bakinshi ahankali kaman mai maganar saidawa ya fara da cewa.........

~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:20 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*

*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)

*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)

*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.

*Page* ~4~

°^^^^^^^^^^^^°

"Ajinki nawa a makaranta?" Ya jefa man tambayar bazata.

A d'an firgice na dago ina kallon shi, gami da ɗan zaro idanu na, da sau da dama na sha jin ana cewa kaman na mai jin barci amman suna da girma sosai,tambayar ce ta zo man a bazata, ko da alama ban taɓa kawo tinanin magana makamanciyar irin wannan zata iya shiga tsakaninmu ba;

"na'am, ni?" Na Maida mashi da tambaya a É—an firgice kuma cikin sigar mamaki,

Shiru yayi na wani lokaci, kaman ma baya da alamar sake tanka mani, nikuma alokaci guda tambayoyi suka ziyarci kwanyata, har banma san mun shafe kusan minti biyu a haka ba, Yayinda shikuma ya kafeni da idanunshi masu kama da na wanda soyayya taci ta cinye😜
"Banjin akwai wani da nake magana dashi a kitchen dinnan da ya wuce ke; Ai ina tinanin mu biyune kadai a nan ko?"

Ya faÉ—a a gajiye kaman, wanda akeyi ma dole, "Na gama makaranta. "

Na fada a gajiye ciki-ciki ina mai gyara tsayuwata, Tare da janyo hijabi na, na rufe gefen fuska ta, saboda kallon da yake yi man yana distracting din attention dina;

Jina nakeyi kaman a gaban miliyoyin mutane, kai gara ma ace a kotu nake, da sainafi sake wa, Da ace a gaban mutum nake kaman YaAmeen muna magana dashi one on one.

'Yar guntuwar dariya yayi, "Wow kina fadin har kinyi degree da masters, A hakan nan yanda kike yar mitsitsiya?"

Ya fada yana mai nuna ni da duk kan hannun shi yana sama da ƙasa da su saitin Inda nake tsaye, Da wani yanayi, wanda nidai nakasa ganeshi; don bazance zaulaya ba don nasan ba halinshi bane yin hakan.

Sai a lokacin nagane kuskuren danayi,dan zaro idanu nayi alamar wayyo Allah, Gami da Jan sauran hijab dina, na ruge fuska ta ruf, ina dan mai sakin É—an k'aramin murmushi;

A hankali nace, "am sorry secondary nake nufi yaya"

"OK good " ya fada a gajarce, Yana mai ƙara nazarinta, ko buƙatar da yake da ita zata samu karb'uwa awajenta?

"Ina so kici gaba da makaranta, domin zaman ki a haka kina wahala ba abune mai dad'i ba; ko babu komai ilimi yanada dadi, zaki taimaki kanki ki taimaki ummanki" Ya tsagaita yana mai zura mata idanu da ke taimakawa wajen ƙara ruɗa ta; Domin yaga yanda zatayi, Nikau bansan lokacin da nabude fuskata ba gabaki daya, ina mai sakin murmushi har siririyar wushiryar dake saman hakora na ta bayyana.

"amman kije ki shawarci ummanki, kuma ina so maganar ta tsaya iyakar ni, da ke, da ita; Don bana so wani ya sani kaf gidan nan, idan ta yarda sai ki kawoman takaddunki, da kuma zabin makarantar dakikeso kiyi da abunda kikeson karantawa, kibar sauran maganar a hannuna. Kome zamu ji, ko zaku gani, Ku kauda idanunku gabaki daya, Babu ruwanku a ciki, Ni nace zan yi, kuma insha Allah zanyi;"

Yana gama fadar haka ya juya, Yana mai barin tanqamemen kitchen din, da kai ka rantse da Allah ba'a Nigeria yake ba.

Dakallo na bishi, a yayin da kwalwa ta ta cunkushe,

"tabbas tabbas mafarkina zai tabbata, tabbas lokaci yayi; Alhmdllh naketa faÉ—a, a cikin raina, saboda na ma rasa tinanin da zanyi, bayan wannan; Juyawa nayi, gami da ci gaba da aiki na.

A gaggauce na gama na rufe kitchen din, gami da barin part din baki daya zuwa namu, Amman zuciya ta cike da tarabbabi, domin nasan halin umma ta, Sannan ni na san kafin in dosheta da maganar, Sai nayi nazarin abunda zance mata tukunna, Don na san ta da gudun duniya da abunda ke cikinta balle wulaqanci irin na hajiya kubra.

Ko da na isa part din namu, Na tadda umma ta, tasha magani amman takasa yin barci, saboda taga na dade har wajen karfe goma da wani abu, Alla Alla take yi, ya kasance lafiya, Gashi ko abinci na ma ban ciba, ina shiga kuwa na taddata zaune bisa sallaya.

Allah sarki umma ta, Mace kamila mai gudun duniya, Mace mai ibada, da rashin hayaniya, Amman dukda wannan halin nata, hakan baisa Hajiya kubra ta É—aga mata ba, Ni gani ma nakeyi kaman babu wad'anda ta tsana irin mu acikin masu aikin dake gidan, Wanda munfi mu goma sha wani abu, ummata ce ta katseman saqa da warwarar da nake tayi cikin zuciya;

"lafiya dai ko mama na?" ta faɗa tana mai miƙewa a hanzarce, sannan ta ci gaba da magana cikin dan firgici kaɗan; "Naga dare yayi sosai, ya kamata ace yanzu kin kwanta ki huta hakanan"

Ta faÉ—a cikin sanyinta, mai sanya ni natsuwa, duk da a É—an firgice take; Kome nake yi, ko ban fad'a ba, son da ummata keman yafi wanda nakeyi mata, Duk da kau a duniya babu wadda tafi soyuwa a raina kamanta, Tinda ita kadai na sani, ita kadai na tashi na gani , ita ce uwata, itace ubana, ita ce yayata, abokiyar shawara ta kuma, ta fanni daya kuma abokiyar wasa ta;

"Ina hankalinki yake ne ummina? Ina ta magana kinyi shiru" ta faɗa tana kamo hannuna, bansani ba ashe har ta nade abun sallar ta iso inda nake tsaye daga bakin ƙofa a tokare.

"Umma saida najira suka gama sannan na wanke kayayyakin kinga gobe in Allah ya kaimu mun rage aikin;" na faÉ—a, ina mai kama mata hannu nima, muka zauna gefen katifar tamu dake yade a tsakiyar dakin.

"ga abincin ki tau, maza kici ki kwanta, kinga karmu makara gobe dasafe in Allah ya kaimu banaso kullum muke b'atawa hajiya rai;" ta faÉ—a tana jawoman kwanon abincin.

Kwanon silver ne amman tsaf yake, kaman sabo sai sheqi da walwali yake yi, kaman yau aka budeshi a leda, Allah sarki ummana akwai tsafta, dakin namu ma sai k'amshi yake yi, an goge tiles dinnan sai daukar ido yake yi, abunka ga fari, dakinmu tsaf yake babu tarkace da karikitai, in ka cire katifarmu, sai labulaye da wani teburi a gefe, inda muke ajiye daddumar sallah tamu, da sauran litattafan addini himili guda, kasancewar ummata tayi karatun addini mai zurfi, sai take k'araman duk bayan sallar subhi, akwai wardrop ta bango a dakin, wannan shi ya tak'aita mana tarkace, tinda ba yaro ke garemu ba, kwata kwata ma babu yaro a gidan, kowa da locar ta inda ni biyuma ke gare ni, kasancewar guda uku ce a dakin, amman ajere suke, sai ummata ta dauki daya, tabar man biyu saboda ni budurwa ce zan fita karikitai.

Abincin naci, naje na daurayo bakina na cenza kaya zuwa kayan bacci, muka kwanta umma tayi mana addua muka shafa kowa ya juya cikeda tinani kala kala.

Nikam ta bangare na banyi bacci ba, amman ummana tayi baccinta saboda maganin da tasha, kuma ko ba hakaba, ita bata kwanciya da damuwa ko haushin wani a ranta, takance ba'asan gawar fari ba hakanan kaje lahira da haushin wani duk abun da gaƙuri bai bayar ba ai rashin shi baya badawa.
Chapter 4 · 0% Book details