← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 56

Sashe 51

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilal ɗin ya sauke ajiyar zuciya mai matuƙar ƙarfi, a hankali shima ya shiga takawa har zuwa gaban gadon, daɓas ya zauna yana mai dafe kanshi da yake sara mashi uwa zai rabe gida biyu, wannan shine dalilin rashin lafiyrr abokin nashi? To indai haka ne munafukan na acikin gidan, lallai tausayin abokin nashi da na yarinyar da ake neman a laƙaba ma sharri bata ji ba bata gani b ya tsira mashi har cikin zuciya.

Sake miƙewa yayi gami da isa ta inda abokin nashi ke tsaye ya haɗe kai da bango yana ta faman maida numfashi yayi, da dukkanin alamu ɓacin ran nashi ya sake komawa sabo fil a cikin zuciyar shi.

Da dukkanin hannuwan shi yayi amfani wajen kamo abokin nashi har zuwa lokacin da ya zaunar dashi bisa gadon nasu, shima zaunawa yayi a hankali, shi ya ma rasa tinanin me zai yi a ranshi, llai abokin nashi na buƙatar wanda zai taya shi wannan yaƙin da ya tunkaro ka, ace wai a wurin aiki baka samu matsala ba sai a cikin gida.

Ummata da take kishigiÉ—e bisa darduma, gama sallar ta kenan ta jawo cesbaha tana ja idanun ta a lumshe, tsulum na faÉ—a É—akin namu ina ta faman haki, ni ban ma san umman tawa na cikin É—akin ba, ai da bari nayi sai na saisaita kaina sannan in shiga.

Da hanzarin ta ta tashi tana mai cewa "ke lafiyar ki kuwa? Ko wani abu ne ya same ki? "

Ganin ban bata amsa ba ya sanya ta ficewa da niyyar zuwa taga menene yake faruwa, saidai bata fahimci komai ba, saboda ko da ta isa wurin mutanen ta tadda wasu suna ta faman cin abinci yayin da wasu ke ta faman É—aukar hoto da Al'ameen É—in. Hakan ce ta sanya ta dawowa zuwa É—akin gami da share ni ta cigaba da laziminta, in na matsu na faÉ—a mata Abunda ya tashi hankalin nawa.

Ban gama warwarewa ba sai ga Hafsat da Afnan sun shigo cikin ɗakin, cewa sukayi in biyo su muje ko suyi mani tonon silili wurin umman tawa. Ba arziƙi na miƙe gami da yafa mayafi na na bi bayan su, ina kula da Afnan wacce take Ƙunshe dariya a cikinta. Da kallo umman tawa ta bimu tana kaɗa kai, koma miye in tayi wari taji.

Masifa da bala'i ba kalar wanda Hajiya Kubran bata sha ba cikin ɗaki, haƙuri suka dinga ɓata, kada ta ɓata taron bikin nan DON Allah, da ita cewa ma tayi aje a sallami kowa tinda an gama cin abincin.

Shawarwari ba kalar wanda ba'a bata ba, daƙyal suka samu tayi haƙurin zuwa dare ayi wacce za'ayi, cikin gidan zata ga mai zaman wani a cikin su ko ita ko su, lallai wannan aikin asiri ne tsab, kenan ma Abunda aka faɗa ɗin ya tabbata gaskiya ne, inko hakane wallahi Sam ba zata saɓu ba bindiga a ruwa.

Abunda ya faru ɗin sai ya sanya ƴan ƙanannn maganganu suka shiga yawo a cikin gidan bikin, duk inda Kaga gungu an haɗa kai maganar akeyi, lallai Hajiya Kubra ta faɗi ƙasa babu nauyi inko har ta bari ɗanɗanta da aka yi ittifaƙin tafi son shi akan dukkanin sauran ƴaƴan nata ya auri talakrr ƴar aikin su.

To dama itama dai Abunda take gudu kenan, kuma tini labarin gulmammakin da akeyi cikin gidan ya isa kunnen ta, domin duk inda ka zaga maganar akeyi.

Hakan ce ta sanya bata ƙara fitowa harabrr gidan ba, duk wanda yazo saidai a shiga dashi sashen nata, shima ɗin saidai in manya ne, inko jigari jigari ne iyakar su babban falo a basu abinci suci ba ta gudunmuwar da suka kawo take yi ba, Alla Alla take yi dare yayi domin ayi wacce za'ayi.

Kusan ma zamu iya cewa bikin sai ya koma sashen hajiya zainab da kaka zuwaira, dama su ta fannin su abun yayi masu 100% sun yaba da yarinyar da kuma tarbiyyar ta, alwashi dai sun sha shi indai da gaske Al'ameen É—in yake yi yana son yarinyar itama tana son shi to fa babu makawa da izinin Allah sai abun ya tabbata, tinda sun san yaron nasu ba irin raggwayen mazan nan bane.

Haka har suka sake shiryawa suka fice dogarawanshi na biye dasu a baya suna mashi kirari da wasa shi wannan karon harda ce mashi Angon Hauwa'u sai dubu ta taru.
Domin duk akan idon su Abunda ya faru ya faru.

ÆŠaki suka sanya ni gami da titsiyeni suna tambaya ta wai in faÉ—a masu lokacin da muka fara soyewa da yayan nasu basu sani ba.

Ba kalar rantsuwrr da banyi masu ba, Amman fir suka ƙi yarda, dole naka bakina nayi masu gum, ina jinsu suka cigaba da zaulaya ta. Afnan ɗince mai cewa

"Ni fa tin lokacin da yaya yazo da maganar auren aunty suhan É—in na yarda dashi, dama na daÉ—e ina addu'ar hakan a zuciya ta..."

Hafsat ta amshe da cewa "Kedai bari Afnan, kuma ke fa don ma baki nan, baki ga yanda yake kulawa da al'amarin ta ba ke dakin gani ma kinsan ba banza ba wlh"

"Welcoee to our Family Aunty Suhan" Afnan É—in ta faÉ—a tana mai rungumi ni zuwa jikin ta.

Nan suka shantake suna ta zaro fira, ni wani abun ma in sun faÉ—a saidai in kwalalo idanu, gani nake yi kaman sharrinsu ne kawai Al'ameen É—in ba zai iya yin hakan ba.

Sauran ƙawayen Hafsat ɗin duk sun dawo ɗaki, nan fa aka buɗe sabuwar fira, cikin su ma har akwai wadda tayi man congrat gami da faɗin "Lallai kunyi matuƙar da cewa, ku duka kun iya zaɓen abokin rayuwa" dariya kawai aka sanya maganar gaskiya zukatn Afnan ɗin da hafsat ɗin cike suke taf da farin ciki marar misaltuwa, yayin da ni kuma ta ɓangareaa na ma rasa kalar tinanin da zanyi, har yanzu ba wai na gaskata bane, gani nake yi kaman mafarki nake yi ko kuma yaudara ce irin ta ɗa namiji akwai Abunda yake son cimma wa.

" ba zata taɓa saɓuwa ba wallahi, ashe yaya bai bar zancen nan ba har yanzu, gaskiya ya zubda mana aji at All wallahi, duk da yau ta kasance ranar farin ciki a gare mu ta wani ɓangaren ranar tazo da akasi"

Nihal ɗin ta faɗa tana mai faɗa wa kan jibgegen gadon nasu inda Saudat da sauran ƙawayen nasu suke ana ta maida yanda akayi

"menene ba zai faru ba? Ai ya riga ya faru saidai Allah ya kyauta gaba kawai, Amman ke kina kallon cikin idanun yaya wallahi kinsan har cikin zuciyar shi ne sonta yake da gaske"

Wata daga cikin ƙawayen nasu ce da ta kasance ƴar uwarsu ta fannin Hajiya Kubra ke faɗin haka, ta bala'n so shi itama a da, ganin ba kula ta yake yi ba, hasali ma ba ta ita yake yi ba, duk iya yin da take dashi da fi'ili lokutta da dama gwasale ta yake yi ko kuma yayi ma kaman bai san ta nayi ba, ya sanya ta dole ta watsrr da makaman soyayyrr nata rabi wani sarkin.
Wata daga cikin ƙawayen ce ta sake amshe zancen da cewa "dalla bari wannan maganar khairi, ai ke kinsan wallahi Ya Ameen ya wuce da ajin wannan ƴar aikin, ni ina gani ko dai asiri sukayi mashi ya aikata a cikin jama'a ba tare da ya san ya aikata ba"
"Confirm cewrr Saudat da take kishigiɗe sai lokacin ta tashi zaune, gaskiya Yaya bai kyauta mana ba Sam, haba ina shi ina wannan kucakar? Duk tarin ƴan matan da suke rububinshi ace bai hango kowa ba sai wannan ruɓusar, ke kiga jikin ta ma fa ko ina a sake take ko irin slimming ɗinnan ma ita bata iyawa saboda duhun kai anfj so a zauna tuɓs ko ina tsoka"

Shewa suka sanya suna faÉ—in Amman fa Saudat baki da dama wallahi, "Amman fa ni kinsan ina tsoron irin wannan jikin, komai fa suka sanya zama yake das yayi masu kyau daidai jikin su"

Cewar ɗaya daga cikin ƙawayen nasu da suka zo masu hidimar bikin tin daga ƙasar ta ta America.

Nan fa aka buÉ—e sabon babin yin zancen suhan É—in duk kusan rabin firar aibantawa yafi yawa a ciki

(Hmmm Allah shi kyauta, Hassada ga mai rabo taki)

Ana gama sallar la'asar aka fara shirin hawan dabar, bayan an ci an sha, anyi hani'an. Sarakunan jihohin namu na arewa suna nan sai washegari zasu koma gruruwan nasu, inda aka yi masu masauki a fadar shugaban ƙasar namu ta nigeria.

Hawan daba fa ya ƙayatar, tashohin gidan talabijin suna ta ɗauka live, matsa dai an gansu a wurin, kowa yayi mamakin irin yanda dawakai suka yalwata a wurin kaman dama an san da naɗin sarautar.

Ƙarfe shida suka gama zagaya duk inda zasu zagaya, manyan namu suka samu suka koma masaukin nasu domin su huta, yayin da cikin gidan yake ɗinke da jama'a gefe guda ga masu kiɗin ƙwarya suna ta chashewa ana masu ɓarin kuɗi, abinci kuwa har kawo yanzu shigowa akeyi da sababbi, duk Abunda kayi sha'awrr ci akwai shi.

Gudun sake tada gulmammaki ya sanya Hajiya Kubran ta dage ta cije, Amman fa har kawo yanzu da magariba ta kawo jiki bata saki jikinta ba, walwalarta har yanzu ragaggiya ce, don ma su Hajiy Lailan na bata baki da shawarwari akan yanda za'a ɓullo ma 'amarin.

Hajiya sa' ar ce tayi mata alwashin ta bar komai a hannun ta nan da kwana uku zata ga Abunda zai faru a cikin gidan. To da haka ne fa ta samu ta lalubo walwala ta yafa a kan fuskar ta Amman ba don har cikin zuciyar ta haka yake ba.

Wannan karon sashen na Al'ameen cike yake da baƙi, abokanan shi da suka zo mashi ɗaurin aure da naɗin sarautar tashi, da yawa ma daga cikin abokan yanzu sunan shi ya tashi daga Ameen ko Dambulan da suke kiran shi dashi ya Koma Yariman Matasa, duk da baya so Amman a haka yake amsawa, saidai kowa ya kula da rashin walwalar tashi, Amman sun mashi uzuri akan cewa hayaniya da jama'a ne.
Chapter 51 · 0% Book details