Sashe 43
Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Afnan ce ta kalli Hafsat gami da cewa "Aunty Hafsat ya kamata ki koma wajen baƙi, kinga ke amarya ce, ba kin baro mutane kizo ki zauna nan ba, gashi ba'a tashi daga event ɗin ba, ga kuma angonki da baƙin shi"
Miƙewa hafsat ɗin tayi gami da cewa "bari inje in sallama kowa, ni na tashi hakanan" girgiza mata kai Afnan ɗin tayi, kiyi haƙuri, Aunty Suhan ta samu lafiya, kinga ma bacci take yi, kar kiyi haka, kije nima gani nan zuwa"
Hafsat ɗince ta shiga gyaɗa kai, sannan ta juya gami da fita itama, a falo ta taddasu zazzaune ba mai ce a ɗan uwanshi kanzil, gara ma Bilal da yake ta fama latsa waya, ganin fitowar ta ne ya sanya Sadeeq ɗin shima miƙewa yana cewa "ya jikin ta ne?"
"Ta samu bacci ne, kasan Suhan da mugun tsoro, ita fa abu kaɗan ma kan firgita ta balle wannan ƙaton ƙadangaren"
"Haka ne kam, gaskiya dole ta firgita, Allah ya bata lafiya" binta yayi suka fice tare gami da komawa wajen baƙin nasu.
Sun tadda an cigaba da hidima kaman ba Abunda ya faru, baƙin nasu dai ne sai a hankali, ganin yanda amaryar tasu ta firgita ya nuna masu cewa lallai itama ƴar gidan ce, hakan ce ta sanya jikin su yayi sanyi, saida suka ga dawowar su sana suka saki jiki aka yi ta kwasar gara da nishaɗi, su kau dama su Saudat ɗin taɓe baki sukayi, gnai da cewa Allah ya bata lafiya, suka koma wajen ƙawayen su aka cigaba da shagali, domin Suhan ɗin bata kai wadda zasu tashi hankalin su a kanta ba, ko mutuwa tayi balle ta ruguza masu farin cikin da suke ciki.
Har aka tashi Afnan bata dawo ba, ita kau Hafsat dama tinda ta koma bata saki jiki ba, ƙawayenta sai bata haƙuri suke yi gami da ban bakin ƙawar tata zata samu lafiya.
Cikin hanzari ta nufi sashen na Yayan nasu bayan duk ta sallama baƙi masu komawa, na cikin gidan kuma ta raka su sashen nasu na amare, gami da ɗaukar excuse ɗin cewa zata je ta dawo.
Miƙa nayi, salati ɗauke a bakina, sannan na karanto addu'ar tashi daga bacci, wara idanu nayi, gami da saurin yaye bargon da aka lulluɓeni dashi.
Nazarin ɗakin na shiga yi, ba ɗakin umma ta bane, ba kuma ɗakin Hafsat bane, ba kuma asibiti bane, to ina ne nan aka kawo ni, har bisa gado harda kuma lulluɓeni?
Zumbur nayi na tashi, ina mai ƙoƙarin sauka daga kan gadon, dafe da kaina dake saramun alamun ciwo.
Afnan ce ta shigo ɗakin da saurin ta jin alamun motsi, kamfani tayi gami da taimaka man na zauna, ƙafafu a a ƙasa.
Bin ɗakin na shiga yi da kallo, ɗakin Ya ameen😳 bisa gadon shi🤠ni Suhan???
Aikau a sukwane na miƙe har ina harɗewa da zanin gadon da ya maƙale man a ƙafa.
"Yi a hankali Aunty Suhan" Abunda afnan É—in ke cewa kenan
"Afnan nan kaman É—akin Ya Ameen? Wa ya kawo ni nan? Me yasa?" na shiga jero mata tambayoyi a firgice ina mai jiran amsar ta.
ÆŠan murmushi tayi gami da jan numfashi, "to miye? Ai ya ameen É—in ne ma da kansa ya É—auko ki ya kawo ki nan kuma......."
Katse mata hanzari nayi daga amso shin da take bani, " me? Ya ɗauko ni fa kika ce? Au shine ma ya ɗauko ni ya kawo ni nan?" na faɗa ina ɗan jinjina kai gaba jiran ƙarin bayani.
" To miye ne? Kaji aunty Suhan da wani zance, ke ba ƙanwar sa bace? Kuma ai nan yafi kusa akan cen cikin gida, hankalin mu fa duk ya tashi wallahi, masalan ma shi, mu ai mun ɗauka abun yafi haka, ashe razana ce kawai"
Gaba nayi ina mai cewa "ai na warke, wajen umma ta zanje ni" jawo hannuwana ta shiga yi, ki bari su dawo yaje siyo maki maganin zazzaɓi, kar yazo ya tadda baƙya nan inda ya ajiyeki"
Girgiza mata kai na shiga yi, kayan kunya iri iri ina shan shi ƴan kwanaki nan, kaji fa wai shine ma ya ɗauko ni da kansa, kaman wata baby, kuma wai kar yazo ya tadda bana nan inda ya ajiye ni, kaman wata kayansa😗
"ya baki ki kawo mani, ina sashen mu" Abunda nace kenan ina mai ficewa daga sashen, kai tsaye É—akin namu na tura na shiga, umma ta da bata nan kuma bata kulle É—akin ba, hakan ce ta sanya ni kwanciya dafe da kaina da yake ta sara man kaman zai faÉ—o.
Ɗan murmushi Afnan ɗin tayi, gami da gyara gadon, ta nayi tana zancen zuci, "lallai ya Ameen da gaske yake, kaji fa yanda ya ruɗe, ko mune dai bama lafiya ai iyakar ruɗewa da zai yi kenan" 😉☺
Bilal ne da yake zaune kujerar mai zaman banza, ya kalli abokin nashi gami da muskutawa ya gyara zama.
"Abokina it seems fa labari yana neman ya cenza, naga fa ka damu da lamarin yarinyar nan over, wai whats going on ne? Yayi maganar in a serious tone.
Ɗan kallon shi Al'ameen yayi yana mai maida hankalin shi kan tuƙi, baya da Abunda zai ce ma Bilal ɗin, ba zai fahimta ba, shi ba zai gane tsabar tausayin da yarinya take bashi ba, halin da suke ciki ita da mahaifiyarta kaɗai abun dubawa ne.
"Oh ba ma da amsa ko" ya faÉ—a cikin son kauda shirun da Al'ameen É—in yayi mashi.
Ya fara ƙule shi da waɗan nan maganganu nashi, ashe shi ba mai bashi goyon baya ne ba kan taimakon da yake son yi.
"Idan Kaga kare na shinshinar takalmi...."
"ɗauka zai yi" Bilal ɗin ya ƙara sa mashi yana ɗan murmushi.
Gefen damtse hannun shi ya kaima bugu, "watau shege tini ka fito kayi man bayanin Abunda ke faruwa ka tsaya sai kwana kwana kake yi, nima ai na fara gundura da zaman naka hakan a babu mashinshiniya, saidai fa kasan ka É—auko dala ba gammo, ka É—ebo ruwan dafa kanka mutumena, ina tsoron Allah ina tsoron Hajiya, bana son Abunda zai baka matsala, kuma hakan ba yana nuna bana tare da kai bane, aa am 100% with you abokina"
ÆŠan guntun murmushi na gefen baki Al'ameen É—in yaja, ga dukkan alamu ya zama al'ada shi.
"Tinda haka kake so kaji, na faÉ—a hankalinka sai ya kwanta, banza magulmaci"
Dariya Bilal É—in ya saki, saida yayi mai isar shi sannan ya tsagaita. "Kana nufin don inji daÉ—i kenan ka faÉ—a ba gaskiya bane"
"Duk yanda ka É—auka, naga babu haramci a ciki inma cewa nayi ina so"
"ai ba cewa aka yi haramun bane Alhaji, ana so ne dai a nuna maka matsayi ka yafi gaban ace wannan yarinya kake so da aure, shi fa aure ba abun wasa bane, abu ne for life, zama ne na dindindin"
"Naji malam bilalu, ai sai ka faÉ—a man yanda yake tinda kayi kaji yanda yake" ya faÉ—a cikin É—aure fuska da gundura da zancen.
"Oho dai, ai ko banyi ba ina kan hanya, kuma na fika tinda ina da gurin yi"
"Nima ai ina da burin yi É—in, tinda gashi na samo"
Tsoki Bilal ɗin yaja cikinbƙuluwabyake cewa "kai dai Kwallon ɗan iska ne wallahi, ana cewa ga ruwa kana ga wuta"
"Eh Naji a barni in faɗa wutar in ƙone ba shikenan ba, kowa ya huta, tsuntsu dayaja ruwa ai shi ruwa kan doka" ya faɗa yana mai ficewa daga motar da tini ya isa gidan.
Afnan ya shiga kira a wayar shi, tazo ta amsar mata maganin, tinda shi tinanin shi har yanzu suna sashe nashi, Shiyasa bai shiga ba.
Bayan ta amsa ne ma take faÉ—a mashi cewa ai ta koma É—aki su, wai ba zata iya zama ba kunya take ji.
Bajce komai ba ya nufi sashen nashi Bilal É—in na biye dashi, "Kudai tabbatar tasha maganin, kinga dare yayi, ciwon daren ake gudu" da to ta amsa mashi tana mai nufar sashen su Suhan É—in.
Umman tawa ma a haka ta tadda ni, ban gaya mata me ya faru ba, illa dai iyaka nace mata kaina ne yake É—an man ciwo.
Sannu tayi man tana cewa hayaniya ce.
Saida na sha maganin da Afnan É—in ta kawo man sannan na kwanta, dama ina fashin sallah ne.
Sannu Afnan ɗin tayi man, bayan tayi tayi dani muje cen ɗakin nasu na ƙiya, a haka ta fice tana ƙara man sannu, gami da cewa Hafsat ɗin na gaida ni, baƙi ne sukayi mata yawa.
Duk yanda mama talatin taso ta danne gulmar tata abun yaci tura, gani take yi abun na ƙara gaba, ga maree sai tazo ta sanya ta gaba tana ta mata koke koke, idan har taga Al'ameen ɗin da Suhan ɗin, masalan ma yau da kan idon ta Al'ameen ɗin ya sunkuci Suhan ɗin kaman matarshi ko kuma wata ƴar baby, ai ko daƙin nasu bata gama shiga ba ta fasa kuka, ba yanda mama talatun bata yi ba akan tayi shiru ta kasa. Hakan ce ta sanya ta miƙewa ta doshi sashen hajiyar da yake cike da baƙi, a haka ta kutsa har zuwa ɗakin hajiyar.
Taci sa'a ba kowa, domin tin isha'i ta shiga ta huta, duk ƴan baran dan nata suna ɗakunan su, balle da yanzu kusan ƙarfe goman dare ne.
Ƙwanƙwasawa tayi, daga ciki hajiyar ta buɗe, tana mai cewa "a'a Talatu, kece cikin daren nan, ba mu gama magana ba, ta shirye shirye da za'ayi gobe"
"Eah hajiya, ba wannan ce tafe dani ba, labari na kawo maki" dakin ƙofar hajiya tayi gami da juyawa ta isa ga tanƙamemen gadon nata ta zauna.
Maida ƙofar mama talatun tayi ta rufe, tana mai bin bayan hajiyar har gaban gadon zan nan ta zube ƙasa, gami da tanƙwashe ƙafafun ta cikin salon koro gulma da munafurci.
Ƙarya da gaskiya ta shiga koro ma hajiyar, harda cewa yanzu ma Suhan ɗin har tallar kanta take kaima Al'ameen ɗin har ɗaki shi, ko ɗazu ma da kanshi ya ɗauke ta cikin bainar jama'a ya shiga da ita sashen nashi ya kullo, alamar sun fara cin galaba kenan a kanshi.