Sashe 7
Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuwan su yayi daidai da gama shiryawa ta, kiran Hajiya Kubra ne ya shigo waya ta, tare da bani umarnin zuwa sashen na baƙin domin taya su zuba abincin.
A falon muka haɗu da Alhaji Mustapha ɗin da na kwashe watanni ban sanya shi a idanuna ba domin baya yawan zama; Durƙusawa nayi har ƙasa na gaida shi, yayin da ya amsa man cikin fara'a da sakin fuska, tare da tambayar umma na ko muna cikin ƙoshin lafiya.
A ɗarare nake zuba masu abincin domin harda Hajiya Kubra zaune a wajen saboda baƙi ne abokan hulɗarsu na kasuwanci kuma ita ma tanada share a ciki, wannan ce tasa nake yi a hankali domin kada inyi laifi wajen Hajiyan.
Gama zuba masu abincin yayi daidai da wanzuwar daɗaɗɗen ƙamshi, lokaci guda mamallakin ƙamshin ya bayyana fuskar shi ɗauke da maɗaukakin murmushin da ban taɓa ganin yayi irin shi ba; Sanye yake da lallausan farin tissue yard har kana iya hangen fara ƙal ɗin singlet dake jikin shi, kanshi babu hula hakan ya bayyana kwantaccen sumarshi luf da ita bisa kanshi har sheƙi take yi, hakan ya ba gyaran fuskar shi damar ƙawata fuskar shi da take ɗauke da madaidaici saje, ƙafar shi na Sanye cikin wani cover ɗin takalmi ɗan ƙasar italy sai sheƙi da walwali yake yi.
Cikin hanzari yake takowa cike da kwarjinin shi, lokaci guda yana fadin "am so sorry wallahi na samu tsaikon jirgi ne" ya faÉ—a daidai lokacin da ya isa gare su yana mai jan daya daga cikin kujerun ya zauna.
Da hannu Hajiya tayi man nuni da in serving ɗinshi, aiko ba ɓata lokaci na duƙa daidai saitin inda zai iya jin me make faɗa, saboda bana so in damesu saboda har wasu sun fara cin abincin;
"Me za'a zuba maka Yaya?"
Na faÉ—a ba tare da na bari mun haÉ—a idanu ba, "fried chicken with mixed fruit" ya faÉ—a shima yana kauda kai gefe cikin salon shi na miskilanci wanda ni na kula ma kwata-kwata shi haka halinshi yake;
Ban ƙasa a guiwa ba kuwa nayi maza na zuba mashi, nuni yayi mani da ido da na bar wajen daidai lokacin da nake miƙa plate ɗin gaba shi, na daga ƙafa cikin sauri na bar falon domin wasu daga cikin baƙin sun fara tsare ni da idanu, ina tunanin shima abunda ya kula dashi kenan.
*******************************
Bansan ya suka ƙare da baƙi ba, domin ni na fita batun su tinda dai na gama masu abin da zan masu, hutu aka bamu cikin gidan na kwana biyu domin family ɗin zasu yi wata tafiya da mu kanmu yan cikin gidan bamu san ina zasu ba, saƙon Alhaji Mustapha ne ya iso mana, dama duk in zasu yi tafiya koda ta yini ɗaya ce ya kan mamu alkhairi irin nashi da ya saba. Kudi ne masu yawa ya bayar a rarraba mana koda zamu buƙaci wani abu baya nan.
"Allah sarki, Allah ya saka ma Alhaji da alkhairi ya ƙara buɗi na Alkhairi" umma ta ta faɗa lokacin da saƙon namu ya iso gare mu, su kau sauran ma'aikatan ƙananan maganganu suka hau yi, wai sun fi so Ya Ameen ya basu kyauta saboda shi bai Iya kyauta ba da yawa yake bayarwa. Kaji butulci irin na ɗan adam, mu dai bamu damu ba ai ance ma raina kaɗan ɓarawo ne, kuma ko ba haka ba umma ta tana da wadatar zuci abu kaɗan ke isar ta a rayuwa hakan ce tasa nima na tashi da irin wannan tarbiyyar.
*******************************
Sun shafe kwana biyar babu su a cikin gidan hakan ce tasa muka samu sauƙin tsangwama da walwala acikin gidan, dama ba mu ke aikin abincin ma'aikata ba iyaka ayi mukai kwano in mun gama ci mu dauraye, iyakarmu gyaran dakinmu sai ko umma ta da take share tsakar gida, domin ita bata son ƙazanta Sam bata iya zama cikin ta, yayin da su kau sauran basu damu ba kitchen ɗin girki kawai suke share wa.
Wani lokaci nakan shiga lambun gidan insha iska ko in katso gwaba ko Apple in ci idan nayi marmarin hakan, umma ta bata hanani domin ta san ko babu komai ba kullum muke samun irin wannan damar ba, hanani sake wa da sauran ma'aikatan kawai ta hanani shima mafi yawancin mazan ne, nima ban damu ba saboda da irin wannan tarbiyyar na taso ta rashin sake wa da maza.
Shugabar ma'aikata mata ce ta leqo ɗakin namu, lokacin ina toilet wankan ƙa'ida na idan na tashi baccin rana ƙarfe uku wanda sake wa yanzu ya zame man kaman nafila cikin ƴan kwanakin nan da sukayi basa nan.
" Maman Suhana Hajiya ce tayo waya, tace a faɗa maku ku gyara masu sashen su duka, Suhana ta gyara na Alhaji ƙarami da na Abie domin dukkan su gobe suna hanya idan Allah ya kai mu"
Dam!! Naji gaba na ya ruguje ya faɗi, daidai lokacin da na fito ina goge kai da towel ɗina na wanka, shi kenan zasu dawo, shi kenan walwala zata ragu, Abunda zuciya ta ke ƙissima man.
"To Talatu, insha Allah yanzu zamuje mu gyara, Amman gyaran zai kai goben tun da kinga yanzu marece ya riga ya kawo jiki" Ummata ta faÉ—a tana mai kallon Talatun, Talatun ta amsa mata da cewa "To shi kenan Maman Suhana ai ba damuwa gaskiya aikin da yawa, ku fara É—in zuwa da safen kwa idasa" ta faÉ—a tana mai ficewa a É—akin, da kallo na bita, matar kam kaman ta Allah to sai dai fa fuska biyu gareta, domin ita ce ta gaban goshin Hajiya babba a gidan Amman bata bari a sani,; nima na san hakan ne ta dalilin a cikin gidan nake nawa aikin kuma harda É—akin Hajiyar nice ke gyarawa.
Haka kau aka yi tuƙuru muka hau gyaran cikin gidan, ko ina yayi ƙal, ya rage gyaran ɗakin Abie ne da ya Al'Ameen ya rage, shima idan aka yi Magriba zanje na gyara na Abie, na Ya Ameen ne sai goben Saboda na san halin wannan sarkin ƴan tsaftan, tsaf zan gyara Amman yana zuwa zai ce baiyi ba.
::::::::::
Washe gari tin da duƙu-duƙu na tashi gami da shiryawa na leƙa ɗakin Shugabar ma'aikata na amso makulli, an ma ci sa'a domin bai barin makullin ɗakin shi a hannun kowa wannan sarkin ƴan tsarin.
Yanda yake na daban, haka ma part din nashi yake, komai dake shashen daban yake da sauran abunda ke cikin gidan, ba wasu tarkace amman an narka dukiya wajen;saitin kujeru ne a falon farare ƙal masu kwalliyar golden haka jefi jefi a jikin su, golden tiles ne malale a falon da ya ƙawatu da wani makeken chinese carpet da ya lashe fin rabin falon bayan su babu komai sai center table na zallan glass fari tar dashi mai haɗe da tumtum irin na gidan sarauta guda biyu tsakiyar falon, akwai stools suma kwara biyu tsakanin kujerun, sai saitin kayan kallo ƴan kamfani Samsung haɗe da Italian Tv stand, up White ne fentin falon yayin da ya dace da cottons masu matuƙar kauri suma kalar golden, sai na'urar sanyaya ɗaki da water dispenser dake maƙale a saƙo guda na falon. Kai kanka in ka kalla sai ka sake kallo, iya tafiya da imani falon ya tafi da nawa.
Corridor ne gefe guda daga bangon hagu da ke falon, idan ka bishi shi zai sadaka da ɗaki ɗaya tal acikin shashen da yake mamallakin shashen, sai ƙofar ɗan ƙaramin kitchen da yake ta cen ƙuryar Corridor ɗin da yake ɗauke da madaidaicin dining area a ciki, kitchen din ya tsaru kaman na wata macen komai na aikin gida akwai shi ciki, sabo da Ya Ameen ya iya girki, in ƴan miskilancin nashi suka taso shi ke girkawa da kanshi yaci abun shi ko kuma in yayi baƙin shi yakan dafa masu abinci simple kuma ya wanke dishes ɗin da kanshi.
Yanda falon ya tsaru sai naga ma kaman bedroom ɗin yafi ƙayatuwa, shima komai upwhite ne da kwalliyar golden, saɓanin toilet ɗin da yake kalar sararin samaniya da fitilu farare, sai ya zamana abun burgewa da ban sha'awa.
Zagewa nayi na gyara ko ina na ƙalƙale, shi tas na kunna boner ta ruwan ƙamshi, take part ɗin ya ɗauki ƙamshi mai sanyaya rai, sannan na kunna na'urar sanya ɗaki domin ƙamshin ya kama ko'ina,bayan na gama na kashe komai na janyo part din na kulle gami da mayar ma da Mama Talatu makullin.
*******************************
Ƙarfe biyar sakaliyya suka iso gidan, yayin da dukka mu ma'aikata muka fita taro su da yi masu barka da zuwa, harda umma ta baiwar Allah da take sanye cikin zurmemen hijab ɗinta, wanda bata ma lafiya kwance take zazzaɓi ne rau a jikin ta, Amman hakan bai hana ta fitowa ba, tinda haka aka saba kafin su shiga part ɗin nasu sai an gaggaisa da kowa tare da jin lafiyar kowa, wannan doka ce daga Alhaji mustaphan wanda a haka dole suke tsayawa suna zuzzunɓura baki suna aika mana da harara su sun dawo a gajiye amman baza'a bar su su shiga ciki su huta ba. Hakan baya damun Alhajin domin ya saba da halinsu tsaf halin mahaifiyarsu ne hakan ta saba masu dashi, halinta ne tin kafin ya aure ta kyamar talaka, masu aiki, sai dai yana tausaya masu har faɗa yana masu a lokutta da dama yakan ce "ku shiga taitayinku kuma ku natsu kusan inda yake maku ciwo, faɗi baya dauwama, haka ma wuya, kuma aure zakuyi ba kuma kusan gidan wanda zakuje ba" Hajiyar kan amshe da cewa "a'a alhaji ka rinƙa faɗar alkhairi a bakinka fa, yaran nan fa kai ka haife su"
Wannan karon da Afan mutuniyata aka dawo, sai aunty Feena da yaran ta guda biyu É—an shekara shidda mai suna Ayan sai Æ´ar karama da ba zata fi shekara biyu ba Nasreem.