← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 56

Sashe 11

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Look afnan✋🏻" ya katse ta daga inda indar da take yi, sannan ya ɗora da faɗin "Na riga nayi duk iyakar ƙoƙarin da zan iya yi akan issue ɗin karatun yarinyar nan, tin ma kafin ke kizo, saboda haka bana jin zan iya maida kaina acikin al'amurran su, tinda har mahaifiyar ta bata son al'amarin karatun nata, zai fi kyau muma mu dakata hakanan, mu barta tayi ma mahaifiyar ta biyayya Allah ya sani mun riga mun yi iyakar iyawarmu" ya ƙarashe maganar cikin wani yanayi na ƙunar rai lokaci guda yana ɗan ƙutawa gami da janyo laptop ɗin tashi ya buɗe, ga duk kan alamu yana nufin ya gama magana kenan.

Shiru falon yayi, in baya ga ƙarar Ac da take bada sanyi ƙaɗan-kaɗan baka jin komai, ita kanta Afnan ɗin shiru tayi kaman ruwa ya cinye ta, ta rasa minene tinanin umman suhan ɗin akan ɗiyar tata, amman dai koma minene ita bazata bar lamarin haka nan ba, za tayi iya yi ta tinda ta kula babban burin suhan ɗin kenan, don dai Allah yayi ta da kawaici da biyayya ga na gaba da ita.

Muskutawa ta sake yi ba don ta gaji ba, sannan ta marairaice dama abunka da auta an saba shagwaba "Na sani wlh yaya na, sai dai ba zamu bi ta kan umman ba, ita ba sanin daɗin abun tayi ba, Yaya Pls, don Allah ba don ni ba, ka taimaka mani, bana so ma ta gane da sa hannuna" shiru yayi mata na wasu daƙiƙai, sannan ya nisa tare da faɗin "Toh Naji, yanzu ya kike so ayi?" tini fara'ar fuskar ta ta dawo, afnan kenan baiwar Allah, yarinya da kyakkyawa zuciya.

"Yauwa Big boo" ta fada cike da jin daɗi sannan ta kamo hannuwa shi ta riƙe su gam, sana ta ɗora da faɗin " Dady, Dady zaka yi ma magana, shine kaɗai zai iya sawa umman suhan ta yarda, ba tare da samun wata matsala ba, Pls my Lovely yaya" shiru yayi sai daga bisani ya nisa gami da faɗin "Is OK dear, Consider it done, kar ki damu ina so ki bar maganar nan a hannuna zamu san yanda zamuyi, ni kaina ina tausayin Rayuwar su, mutane ne da suka cancanci a tausaya masu don ga duk kan alamu sun fi sauran ma'aikatan shiga halin damuwa, masalan ita umman suhan ɗin" ya faɗa cike da basarwa kai kace ma bashi ne yayi maganar ba, saboda bazaka taɓa kawo ma ranka cewa miskilancinshi ma zai bar shi fahimtar wani abu ba.

Miƙewa tayi tsaye, gami da yin wani ɗan tsale cike da annashuwa, "Nagode Yaya, na gode Allah ya saka da Alkhairi ya bar ƙauna, I love u sooo much, Good night Swt Yaya" ta faɗa tana mai nufar ƙofa domin fita, saboda dare yayi, da murmushi ya bita, wannan zuciya ta Afnan da kyau take, tabbas shi ya san ko ba daɗe ko ba jima sai sun yi alfahari da yarinyar

"Ameen" ya furta a hankali cikin salon san kauda tinanin abun a ranshi, domin aikin da yake yi Afnan É—in ta shigo, mai muhimmanci ne.

×××××××××××××××××××××××

Washegari bayan mun kammala aikin mu, mun dawo sashen mu munyi wanka wajen ƙarfe biyu na rana, aiken Hajiya Kubra ya iske mu, ni da umma ta wai tana neman mu, har ga Allah gaba na sai da ya faɗi, domin har jin daɗi nake inje in kammala aiki na tana sashen Alhajin ta yanda ma babu abin da zai haɗa ni da ita, sai dai wajen zuba abinci. Ummana ce ta amsa da cewa gamunan zuwa, lokacin da ƴar saƙon ta fita ne ta juyo da kallon ta gare ni da nayi fiƙi fiƙi da idanu, ina ta tinanin laifin me kuma muka aikata yau, saboda duk idan aka yi mana irin wannan kiran to fa ba lafiya ba.

"ki kwantar da hankalin ki mama na, insha Allah lafiya lau, babu abin da zai faru sai alkhairi" da to na bita domin in kwantar mata da hankali saboda yanzu umman tawa sai a hankali ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, don ko jiya dakyar muka yi bacci, ciwon zuciyar ta ne ya kusan tashi. Hijabi na na ɗauko na sanya gami da wucewa gaba umman tawa na biye a baya na, babu mai cewa ƙala har muka isa babban sashen gidan, ta bangare guda kuma zuciya ta na luguden duka, domin na san rashin mutucin Hajiya Kubra sosai, fata na dai kada al'amarin ya shafi umma ta, ko minene dai ya tsaya iya kaina.

Sallama muka yi daga bakin ƙofa, Mama Talatu ce ta amsa mana daga ciki tare da faɗin "ku shigo mana, kuka tokare daga bakin ƙofa kaman wasu baƙi" shiga muka yi, ina gaba Ummana na baya; zaune muka iske ta bisa ɗaya daga cikin sofar da suka yi ma falon ƙawanya, gefe na samu da niyyar zama ƙasa ta dakatar dani, "a'a Suhana, ku shiga dai daga cikin falon Hajiyan, tana daga ciki tana jiran ku" "Toh Talatu" Ummana ta amsa mata.

Kai tsaye falon muka shiga tare da sallama, waeh Aljannar duniya kenan, tsayawa fasalta kyaun falon da dukiyar da aka narkar ma ɓata lokaci ne, kawai ka fasalta shi da duk falo mafi kyawo da ka taɓa gani a Rayuwar ka. Zaune take, hakimce cikin isa, izza da taƙama (Hajiya Kubra ba dai ji da kai ba) ko amsa mana sallamar da muka yi bata yi ba, sai ma cen gefe ɗan nesa da tayi mana nuni saman carpet din da ya lashe fin rabin falon tayi, bamuyi ƙasa a guiwa ba muka zauna, muna mai gaisheta cikin ƙan-ƙan da kai, shima bata amsa ba, sai ma shiru da ya biyo bayan hakan na tsawon wucin gadi, sannan ta nisa cike da gadara ta fara faɗin "ina so ku nisanci ɗiyata Afnan, domin duk abubuwan da suke faruwa cikin gidan nan tin zuwanta a kunne na suke, na hana ta taƙi bari, ina so ku sa ta tayi nesa daku, domin ko alama bana son zuwa sashen masu aikin nan da take yi, kuma na san ɗiyarki ke janta" ta faɗa tana maida duban ta kan umma ta da kanta ke sunkuye, sannan ta cigaba "kunsan ko alama ba da son raina kuke zaune a gidan nan ba, saboda har yanzu kin ƙi ki faɗa mana asalin daga inda kuke, daga ke har ɗiyar taki bamu san asalin ku ba, sannan ki shirya bayyana mana komai da ya shafe ku idan ba haka ba, ba jin zaman ku a gidan nan zai cigaba da ɗorewa, bazan lamunci a mallake man ƴaƴa ba idan kunne yaji...... " ta ƙarashe tana mai ajiye maganar cike da gadara, ko ɗar bata ji ba, duk cin mutumcin da tayi mana bata gani ba, wannan ai tozarci ne, ko ba'a faɗa ba, na san mama Talatu da uwani ne suka kawo wannan gulmar, watau ita dai duniya haka take kana barci ana maka mun shari, idan da sabo ma mun saba jin ire-iren wannan tozarci daga gurin Hajiya kubran, muryar Hajiyan ce ta katse man tinanin da na Lula "Kuna iya tafiya Maryama, Amman kada ki manta da buƙata ta a gare ki"

Cikin mutuwar jiki muka taso muka fito, tabbas idan raina yayi dubu ya ɓaci, a bakin ƙofa muka haɗu da afnan ɗin, tana yi man magana amman ni Sam hankali na ma baya kanta, murmushi kawai nayi mata na raɓa ta na wuce, juyowa tayi da niyyar binmu, na sanya hannu na dakatar da ita gami da girgiza mata kai, sannan na sanya ƙafa cikin sauri na bi umma ta da har ta kusa ficewa a babban falon.

Wucewa Afnan ɗin tayi zuwa cikin falon Hajiyan, tare da zama cikin tashin hankali don ta san halin mom ɗin tata sarai "Mom me kika yi masu? For God sake me kika faɗa masu?" ta faɗa kaman zata yi kuka, "ke dallah saka rai shashasha, me kika gani jikin waɗancen faƙiran da har kika liƙe masu, har kina ɗaukarta kuje siyayya tare? Su fa ƴan aikin mu ne, ko kusa ba tsararki bace, bata da wani amfani wajenn mu in ba tayi mana aiki ba mu biya ta, ko kaya sai mun sanya mun cire sana muke basu su sanya, Amman wai kece yau kike haɗa kanki dasu, har kike zuwa ɗakinsu ki zauna, to ahir ɗinki wlh in ba haka ba zan saɓa maki fiye da tinaninki wallahi" ta ƙarashe tana mai nuna zallan ɓacin ranta ga autar tata "mom, ni fa banfisu da komai ba, in fact ma, babu Wanda yafi wani wurin Allah sai wanda yafi tsoron shi, so ni gaskiya momy baki kyauta mani ba, ai su ɗin ma ƴan adam ne, wanda ya halicce mu ya bamu, suma shi ya halicce su, kuma bai manta dasu ba" ta ƙarashe cikin matsanancin ɓacin rai, domin ga alama mom ɗin tata magana marar daɗi ta faɗa masu, kuma akan ta ne, mom ɗin ce ta amshe da cewa "au haka kika ce? Ashe ba zaki dena ba kenan? Maza ki shirya kayan ki, in kin fita ki kirawo man Nafeesa kuzo ku koma inda kuka fito domin bazan lamunci wannan iskancin naki ba wallahi, kada in saɓa maki"
Chapter 11 · 0% Book details