Sashe 19
Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sake shigowa naga sunyi shi da likitan, watau sai da ya kira likitan kenan? Haka na cigaba da rayawa a rai ina mai janye idanu a ga barin kallon su, bakin gadon suka ja suka tsaya, hakan yayi daidai da farfaÉ—owar umman tawa.
"Ƴan mata zo ki taimaka ma umman ki ta tashi zaune kinji, zamu auna ta ne" likitan ya faɗa yana mai waiwayowa ya kalle ni da nake zaune ina aikin binsu da idanu da nayi nayi ga barin kallon su Amman na kasa, Ya Ameen ɗin yayi kyau, wani abu ke taso man cen ƙasa rai duk lokacin da ya bayyana inda nake, tasowa nayi a hankali na kama umman tawa ta zauna sosai, shi kau gogan ko kallo na ma bai yi ba, kaman ma bai san ina ta wurin ba, ya koma mani Yaya Al'ameen ɗin da na sani tin cen baya, da baya ɗaukar wargi, fuskar shi Sam babu walwala saɓanin yanda ya fita ba daɗewa.
Aune aunen su na likitoci ya shiga yi, sannan ya É—ago yana mai faÉ—a ma Ya Ameen É—in komai normal, za ta iya cin komai, kuma ta kula da shan maganin ta akan lokaci, zamu iya tafiya gida, Amman nan da sati É—aya mu dawo a sake gwada ta a gani, dokoki sosai aka shinfiÉ—a ma umman tawa, sannan aka hana ta cin wasu abubuwa da dama; wayyo likita, bai san ma abincin sai wanda aka ga dama aka bamu ba, in kace ba zaka ci ba sai yunwa ta kashe ka babu mai sani.
A haka na kama umman tawa muka fito, bayan motar na saka ta, ta É—an kwanta na koma na kwaso sauran kayan da suke mallakin mu, har da take away É—in da yayo mana da ko kallon shi banyi ba, balle in buÉ—a inga Abunda ke ciki.
Har zan shiga bayan ya tsattsare ni da idanun nan nashi masu rikita dani, sannan ya mani alama da in shiga gaba, haka kuwa aka yi shiga nayi na takure, masalan ma ga umma ta acikin motar kuma idanun ta biyu ba bacci take yi ba.
Kai tsaye naga mun nufi hanyar kasuwa, ban da hurumin tanka wa balle in tambaya me zamu yo a kasuwa, ƙila uzirin shi ne zai kai shi; parking yayi bakin tanƙamemen suoer market ɗin da yake bakin kasuwar, fita yayi ya shiga ba dadewa sai gashi ya fito yaron shagon na biye dashi a baya, hannun shi niƙi niƙi da kaya, but ya buɗe mashi tare da Sanyawa ya rufe, ya zagayo ya tada motar muka shiga cikin kasuwar, nan ma soyayya yayi sosai, cikin ni da umma ta babu mai tankawa, kowa da abunda yake saƙawa cikin rai.
Gida muka nufa kai tsaye, yayin da yake parking ya yafito mai gadi da hannu, cikin hanzari ya iso inda muke ƙoƙarin fitowa daga cikin motar; umarni yayi mashi da ya kira mama talatin a sashe namu na masu aiki, aiko ya ruga cikin hanzari, sai gashi da mama talatun ta taho cikin sauri, umarni yayi mata da ta kama man umman tawa mu kai ta ɗaki mu kwantar, yayin da ya kirayi mai gadin da isa da yake tsaye yana gyaran flowers da suka taimaka wajen ƙayata gidan, kayan yace su kwashe su shigar mana dashi cikin ɗakin mu, yayin da ya ja motar shi yana mai barin gidan.
Kai tsaye ɗakin namu muka nufa da umman tawa da take ɗan iya taka wa a hankali a hankali, kwantar da ita muka yi, yayin da su isa suka shisshigo mana da kayan namu suka fice suna ma umman tawa sannu da Allah ya kyauta, ina kallon mama talatun tana jinjina kai tana mai ƙare ma niƙi niƙinbkayan da ta gani tare da mu, ta dai san wannan aikin Alhaji ƙarami ne, wato dama ya ƙi bin su Hajiya Babba ne domin ya tsaya bauta mana kenan ko? Wai menene haɗin shi da mu ne? Su dai basu ga wata alama da ke alamta masu akwai wani abu tsakanin Suhana ba da Alhaji ƙarami ɗin balle ace dan ita yake yi? Koma minene zata yi ƙoƙarin sanar da hajiya ɗin, me hakan ke nufi ne? Ya kamata hajiyar tayi wani yunƙuri akai wallahi, ita ta ma ga sanyar Hajiyar wannan karon akan yanda ta santa da in ta ƙi abu duk yanda zata yi akan taga bai faru ba ta sani, tana cike da tsantsar mulki da kuɗi, naira shegiya ce, mai maida tsoho yaro ta maida yaro babba.
(Humm🤔🤔 Ya Allah kayi mana tsari da Hassada, Æ™yashi, ganin gari da munafunci ameen ya Rab🤲ðŸ»)
Bayan duk sun fita ne, na gyara komai a ɗakin na adama komai inda ya kamata, kayan ciye ciye ne da basu da illa ga masu ciwon zuciya irin wanda likita ya bada umarnin aci, su ne ya kwaso mana su sosai da sauran kayan buƙatu har da kayan marmari ma da zasu yi ma mai rashin lafiya daɗin ci, gyaran ɗakin nayi nayo wanka na shirya kaina cikin baƙar doguwar riga mara nauyi na tattara gashi na na ƙulle cikin ribom sannan na ɗaura ɗan kwalin rigar a bisa kai na, nayi kyau daidai misali, sannan na ɗauko ledar take away ɗin da yayo mana tin asibiti na buɗe da niyyar zuba mana muci ni da umma ta, lafiyayyen chips ne da plantain, sai soyayyen ƙwai da miyar kayan ciki, sai ƙamshi take har yanzu da sauran zafin shi, saboda mazubin na glass ne, da gani dai abincin zai yi tsada, sai dai baya cuwuwa ga umma ta saboda farin mai da aka yi using wurin suyar, kaina kaɗai na zuba mawa na fidda sauran ga ƴan uwa na ma'aikata da har yanzu sun gagara shigowa yi mana koda sannu saboda tsabar hassada, Abunda na san zata iya ci wanda likita bai hana ta ci ba na zuba mata, saida na tabbatas taci na ɓalli maganin ta na bata tasha sannan na gyara mata kwanciyar ta, na koma gefen katifa na zauna ina ya ƙunar abincin ahankali
Fira mukeyi jefi jefi da umman tawa da take bina da kallon tsantsar ƙauna ga ɗiyar tata, addu'a dai kam Al'ameen ya sha ta daga bakin umman tawa, godiya take jerawa wanda hakan ne ta sanya ni ɗan murmusawa a hankali dai ina ci gaba da cin abinci na; Sallama yayi daga bakin ƙofar ɗakin yayin da umma ta ta bashi izinin da ya shiga daga ciki, lokaci ɗaya tana mai umartata da shinfiɗa mashi darduma.
Kasa tashi nayi, domin jikina babu hijabi babu gyale, gashi rigar mai bin jiki ce ta fidda duk surar jikin dake Sanye da ita, kuma a zahiri bai kamata ya ganni haka ba, saboda shi É—in ba muharrami na bane, hakan ce ta sanya na shiga bin ko ina na jikina da kallo kaman mai son gano wani abu.
"Hauwa'u dake fa nake magana fa, nace ki shinfiɗa mashi darduma ya zauna kin bar shi tsaye" umman tawa ta faɗa tana mai yunƙuri tashi, a haka ta samu ta zauna daidai domin Nidai na gagara koda motsi balle in taimaka mata har ma nayi mashi shimfiɗar
Hankalin shi ya maida kanta da take ajiye plate ɗin abincin kaman mai tausayin ƙasar, ta shiga miƙewa a hankali, lura da yayi da Abunda take ɓoyo ko ji ma kunya ne ya sanya shi kauda kanshi gefe, ya maida hankalin shi kan umman tawa yana mai ɗan sakin guntun murmushi iya laɓɓa, ko me take ɓoyo? Wannan mitsitsiyar yarinyar ma, da yake kyautata zaton garin jiki ne ya kwashe ta, ita har tana ganin ma ta cika ta kai mace, ƙara murmusawa yayi daidai lokacin da take shinfiɗa dardumar ɗan nesa kaɗan da katifa tasu.
"Nagode" ya faɗa iya maƙoshi maganar tana mashi wahala, yana mai zama ya tanƙwashe ƙafafun shi irin zaman salla, lokaci guda yana mai gaida umman tawa, cikin sakin fuska ta amsa mashi, sannan ya ƙara mata ya jiki da Allah ya sauwaƙe.
Godiya ta shiga jera mashi da kuma fatan nasara da cigaba a rayuwa, harma da iyayen shi, hakan ce ta sanya shi jin daɗi, yana mai ƙara ƙaunar matar da son taimaka mata da duk ahalinta.
Ikon Allah, abikan aikin mu da tin ɗazu suka kasa leƙowa su ga jikin umman tawa su gaida ta, sai gashi ɗaya bayan ɗaya yanzu da suka ga shigar Ya Ameen ɗin ɗakinmu suna shigowa gaida ta da ganin ƙwam, kowa ya fita kuma sai ya ƙara da abin da ya gani gaba.
Sake natsuwa yayi yana mai ɗan yin gyaran murya a hankali, sai da ya maido kallon shi inda nake rakuɓe bisa katifa gefen umman tawa, sannan ya saki wani ƙayataccen murmushi ganin ta sanya hijabi da shi bai ma kula da lokacin da ta ɗauko shi ba, haƙuri ya shiga ba umman tawa, da mata Alƙawarin hakan ba zata sake faruwa ba, ya faɗa mata afnan ce ta sanar dashi komai; ɗan faɗa umman tawa ta shiga yi tana faɗin hajiyar ta isa ne ya sanya tayi masu faɗa, ai ba wani abu bane, gyara ne take so ayi, kuma mun ɗauka insha Allah.
Haƙuri ya ƙara bata sannan ya shigo mata da maganar makarantar tawa, ta bacin yardar ta ta ƙara bashi, sai dai tana mai shawartar shi da yayi komai a hankali kada ran hajiyar ya ɓaci, ya alƙawarta mata komai ya wuce kuma babu abin da zia faru insha Allah.
Maida kallon shi yayi yana mai cewa "Ki ɗauko man takaddun naki in gani ko, don mu san ta yanda zamu ɓullo ma al'amarin" ya faɗa yana mai kauda idanun shi daga kaina kaman ma ba dani yake magana ba.
Miƙewa nayi cikin ɗan sanyi gami da nufar wardroop ɗin tawa, gami da janyo ƴar ƙaramar folder da takaddun tawa suke na miƙa mashi.