← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 56

Sashe 26

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da rana ma hakan ce ta kasance, wannan karon free ta fito ta faɗi man cewa an dakatar da bamu abinci a cikin gidan, saboda yanzu mu ba ma'aikata bane, abun ya bamu matuƙar mamaki, me hakan ke nufi ne? Ko dai wani ne ya ja mana wani sharri kuma? Umma ta ce ta bani haƙuri, da unurtata kada in sake komawa amso abinci, har saida suka mula, suka sha iska dan kansu suka bamu.

Ɗan Abunda ke gare mu a ɗaki, shi muka dinga ci ni da ni da umma ta, sai gashi nima na koma cin abunda masu ciwon zuciya suke ci; amman ya zamuyi? Dole mu haƙura, babu, ce da zama ƙarƙashin wani ya ja mana. Amman ace a gida irin wannan ya wuce ace ana irin haka ga masu aiki, sai dai in da wani abu a ƙasa.

****************

Da sallama ya shiga cikin ƙayataccen sashen nata, tana zaune bisa kujera tana waya da ƙawarta Hajiya Laila, cewa tayi ta bata minti biyu zata sake kiran ta, kashe wayar tayi tana mai amsa mashi gaisuwar da yake mata ciki ciki tayi, sannan ta ɗora da faɗin "ya aka yi ne Al'ameen?"

"Mom kiyi haƙuri please, babu kyau iyaye na fushi da ƴaƴansu nazo ne in baki haƙuri" ya faɗa a taƙaice idanun shi na bisa fuskar ta don ganin yanda zatayi

Ɗan guntun murmushi ta saki, cikin duniya ci tace "haba son menene haka? Ai ya riga da ya wuce, na san ba zaka yi Abunda zai ɓata man rai ba, Allah yayi maka Albarka" ina so kaje ka yankar ma su Afnan ticket saboda zuwa anjima zasu wuce, hutun nasu ya ƙare kada su rasa flight"

"OK ya faɗa yana mai miƙewa cikin salon tafiyar shi ya taka ya fice daga part ɗin na mahaifiyar shi, da tin dawowar su bai shige shi ba sai yau, saboda bai san abin da zai je ya tada ba, zuciyar shi cike da wasu wasu, me mahaifiyar tashi take ƙullawa ne? Shi fa yayi mamakin sauri saukowa ta, Amman koma minene zai bita ta ƙarƙashin ƙasa in ta san wata ai bata san wata ba.

Ita kuwa a ɓangaren ta, da murmushi ta bishi tana faɗin "yaro yaro ne, koda kuw ɗan giwa ne, kaman yanda ka bari cikin cikina, Al'ameen ka bar maryam da ɗiyar ta har Abadan abada, hhhhh" ta kyalƙyale da dariya shu'umanci, domin kuwa hajiya Lailan ta bata tabbacin hakan, ita kuma ta yarda da hajiya Lailan ɗari bisa ɗari, in tace zata yi, to fa zata yin ne, koda kuwa sama ce zata haɗe da ƙasan.

~Toh fa! Anya kuwa Hajiya Kubra Alkhairi take ƙullawa kuwa 🤔~

~Ya makoma Suhan da Umman ta a Rayuwar da ake ciki na hana su abincin da zasu ci ma?~

~Al'ameen kuwa ya bar maganar auren suhan É—in? Ko dai irin abun nan yayi mata na yaro bari murna...~

~Oum-Deedat cee~
[9/15, 7:36 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*_Page ~16~_*

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Komawar Bilal ɗinne ya sanya abubuwa suka ƙara yi mashi yawa, ginin shi da kuma kayayyakin su da suka iso, wannan ce ta sanya hankalin shi ɗauke wa daga kan su suhan ɗin, to dama dai taimako ne kawai tsakanin shi dasu acikin ranshi, ba kaman yanda yayi iƙirarin soyayyar ba gaban mahaifan nashi.

Ta ɓangaren mu kuwa, komai yayi tsanani, rashin abinci ai ba ƙaramar barazana bace ga ɗan adam.
Idan hankalina yaso ya tashi umman tawa ce ke taɓo ni, da nasiha da wa'azoji da dama, dole ne in daure in maida komai ba komai ba, gudun ɓacin ran nata.
Bamu da wani aiki a yanzu sai sallah, wanka da kuma bacci, mu kan share tsawon yini biyu bamu ci komai ba, saidai ruwa da kuma É—an farau farau É—in da muke kaÉ—awa mu sha, saboda rashin kuÉ—i a hannun mu, sai umma ta ce ta bani Æ´an abunda suka rage a hannun ta na siyo mana fura cen cikin gari, muka dama muka ajiye in munji yunwa mu É—iba mu tsiyaya ruwa mu kwankwaÉ—e, da haka har muka kwashe tsawon yini biyu
Idan ma fita muka yi tsakar gida haka zamu dinga fuskantar ƙananan maganganu da habaice habaice daga sauran ƴan uwan namu ma'aikata, hakan ce ta sanya umma ta hanani fita, idan ba aike ba to fa mun gwammace muyi zaman mu a ɗaki umma tayi ta ƙara man karatu in mun gaji mu kwanta
Ko wanki a banɗakin ɗakin namu nake yi mana, iyaka shanya ce zanyi a tsakar gida, sai sharar ɗakin namu da ƙofar ɗakin.
Mun zama bare na ƙarfi da yaji a cikin gidan, gashi shi wanda ke ɗan tausaya mana ɗin ma ya ɗauke ƙafar shi ɗaf daga gare mu, afnan kuma sun riga sun koma tini, saidai kafin tafiyar tata, tayi dabara zuwa sashen mu, duk da ba kuɗi ta kawo mana ba, abubuwa ne masu yawa nata ta tattara ta bani, irin su kaya da kayan kwalliya.

Ta ɓangaren su hajiya Kubra kuwa, komai ya mata yanda take so, magana ta mutu murus, su ɗin da ta tsana ko jin ɗuriyar su yanzu bata yi, lallai Hajiya Laila ƙawar tata hatsabibiya ce, gashi ko Alhajin ma ta dena jin zancen auren Al'Ameen ɗin a bakin shi, gashi ya sake mata sun koma kaman da cen yanda suke
To dama dai ita É—in wannan ne kawai burin ta, tini Al'Ameen É—in ya samo masu kuku har biyu suna masu aikin abinci,
Wannan ce ta sanya ta ci gaba da harkokinta cikin kwanciyar hankali, ta ci gaba da zuba mulki da isa da ikon ta kaman yanda take so
Likafa ta ci gaba, yanzu bata ko zama sosai a gidan, tanƙamemen shagon kayan ƙyale-ƙyale da make-up ta buɗe, irin na manyan mata da riƙaƙƙun yara masu tashe da watayawa a faɗin Nigeria.
Yara ta ɗiba kyawawa ta zuba suke aikin, wannan ce ta sanya wurin haɓaka, duk wata mace da ta amsa sunan ta a faɗin garin na Abuja shagon take zuwa ayi mata gyaran jiki, da kuma siyan kayan ƙyale-ƙyale da take yo order ɗinsu daga ƙasashe mabanbanta
To shima Alhajin baiyi yunƙurin hana ta ba, asali ma, shi ma ɗin ba mazauni bane, gara ma Al'Ameen ɗin, yafi zama a gida Nigeria, yana kula da sauran ma'aikatan nasu da suke ma'aikata da kamfanoni daban daban.
Duk da cewa ya fara jan Abie yana koya mashi abubuwan da suka danganci kasuwancin, shi kaɗai ba zai iya ba, ina zai kasu? Gashi yanzu amana tayi ƙaranci a wajen jama'a.

*********

Duk wannan abubuwan dake faruwa, Al'Ameen ɗin bai san dasu ba, tsarin da aka ɓullo dashi a gidan na hana mu abinci,
Yana iyakar ƙoƙarin shi ganin cewa babu wani ma'aikaci acikin gidan dake fuskantar matsala,
Wannan ce ta sanya ya shafa'a Sam damu da al'amarin namu, gashi yanzu ko a hanya bama haɗuwa dashi, saboda babu inda nake zuwa, haka umman tawa, kullum tana ɗaki tana karatun ta, kuma tana iya bakin ƙoƙarin ta, wajen kauda tinanin komai, gudun sake tashin ciwon ta.

Tafe yake cikin takunshi mai ɗaukar hankali, sanye yake cikin fari ƙal ɗin wandon jeans da riga ƙirar polo mai ruwan makuba.
Cikin sauri ya kwala ma mudi driver kira, da É—an gudun shi ya iso wurin, yana mai russunawa cikin girmamawa ga uban É—akin nasu yake faÉ—in "Gani Alhaji"
"Mudi gashi" ya miƙa mashi ƴan makullayen motar, "yau bana jin daɗi sosai, so bazan iya driving ba, ina so ne ka kai ni office, aikin gaggawa ya taso mani, da bazan ma iya fita ba" mudin ne yayi saurin amsar makullin, yana mai ƙara russunawa yake faɗin "Angama ranka ya daɗe"

Buɗe mashi ƙofa yayi, ta mai zaman banza ya zauna sannan ya sake zagaya wa ya shiga yayi ma mota key, tare da danna horn ga mai gadi, cikin daƙiƙa da basu Gaza biyu ba ya wangale masu gate, yayin da mudi ya harba motar bisa titi, yana mai sake danne ma mai gadi horn alamar sai sun dawo, shi kuma ya shiga ɗaga masu hannu yana mai washe haƙora.
Chapter 26 · 0% Book details