Sashe 17
Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasaƙe yayi yana ta kallon uwa da ɗiyar tata cikin tausaya wa ta ɓangare guda kuma yana mai sakin Sirrin murmushi har dimple ɗinshi ya loɓa, Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaga umman ta samu bacci, ko ba komai zai samu sauƙi da zuciyar shi take yi mashi na kukan da afnan ɗin take yi, ya tsani kuka, ya tsani kuka masalan na mace mai rauni, yanzu zai ruɗe ya rasa inda zai sanya kanshi.
Tasowa yayi a hankali,, ya tako har zuwa gaban gadon da ya koma ya zauna bayan da yaga ɗiya da uwa suna magana cikin shauƙin so, ledar da Nihal ta ajiye ce ƙasa gaban gadon umman tawa ya shiga buɗewa, kayan ciki ya shiga fiddowa a hankali a hankali, yana jera su bisa kyakkyawa locar da take ajiye gefen gadon, kayan tea ne, sai ruwan gora, da plax sai mug na shan tea, sai kayan marmari da su cake da sauran kayan ciye ciye da marar lafiyar zai iya buƙata.
Da gani dai wannan siyayyar ta abban shi ce, dan ko kusa ya san halin mom É—in tashi ba zata iya tsayawa yima Æ´an aiki soyayya ba.
Sai da ya tabbatar da ba zasu buƙaci komai ba sannan yayi mata sallama a gajarce ya fice yana mai ja masu ƙofar, da idanu na bishi har ya wuce, tabɗi Ya Ameen Matarka zata sha miskilanci na raya a rai na ina mai miƙewa domin komawa inda ya tashi dan in samu in miƙe ƙafa ta, da kallo na shiga bin wajen da ya tashin, kaman yana wajen zaune, ƙamshin turaren shi yana nan liƙe kaman nan ya fesa shi, ajiyar zuciya na shiga sauke wa a hankali a hankali ina mai furta Alhamdulillahi!
******************************
Bai shiga babban part É—in ba saida ya koma nashi yayi wanka ya kintsa sannan ya nufi part É—in hajiyar cikin takon shi kaman na saraki; Sallama yayi ya shiga, duk sun hallara a dining table suna cin abincin da sai dai aka yi ma mama Talatu umarni da ta girka shi ita da mama uwani, kujera ya ja guda É—aya ya zauna saitin abban nashi, Mug ya É—auka gami da haÉ—a cofee, domin bai jin zai iya cin komai a wajen, tsaftar umman Suhan É—in ce kawai ya yarda da ita.
A hankali ya ke shan cofee ɗin yayin da Alhaji yayi gyaran murya duk suka maida hankali su akan shi, " Gobe idan Allah ya kai mu zamu tafi kankiya, kaman yanda muka saba in mun yi haɗuwa irin wannan, Hajiya ki rubuta list ɗin abubuwan da za'a buƙata da wanda za'a kai ma su Baba ɗin, sannan ku Saudat da Nihal sanin kanku ne cewa idan muka je sai anyi maku maganar fidda mazaje, idan kuna da tsayayyu ku tura su cen kankiya su gaida kakannin naku kafin mu taho, zan yi ma yaya Auwalu magana sai yazo su gaishe su tare, sannan kai kuma Al'ameen idan an amshi list ɗin ka tabbatar ka haɗa komai cikin daren nan dan ina kyautata zaton da safe zamu wuce don na riga nasa anyi booking flight. Ina fatan babu mai magana ko?" ya faɗa yana mai maida kallon shi kan Hajiya Kubran da take zaune tana ta cika tana batsewa,"
Alhaji shi Al'ameen É—in baka ce ya fidda mata ba, don na gaji da ganin shi zaune haka nan, tsararrakin shi har sun yi aure, wasu ma harda Æ´aÆ´a, don haka shima yayi gaggawa fidda wadda yake so, in mun duba munga cancantar ta, sai a haÉ—a bikin da na su Saudat kawai"
Ɗan murmushi Alhajin yayi yana mai maida kallon shi kan Al'ameen ɗin da ya kafe mom ɗin tashi da idanu yana ɗan murmusawa, shi da ya gano ta, watau tana gudun ya so yarinyar cen dake asibiti tare da maman ta, humm Hajiya kenan, yana fatan Allah ya shirya da mom ɗin tashi ta gane annabi ya faku, koma dai minene shi dai ai ba za'ayi mashi auren dole ba, ba kuma za'a ƙayyade mashi lokacin auren shi ba, duk tsiya dai sai ya samu wadda tayi mashi, kuma har yanzu baya tinanin ya dace, duk cikin ƴan matan da suke cewa suna so shi, shi fa ba suyi mashi ba, bai yarda da natsuwa da inganci shi ba, don duk irin ƴaƴan hamshaƙan masu kuɗi ne, masu ɗabi'a irin ta mom ɗin tashi watau wulaƙanta na ƙasa dasu, Sam basu san babu ba basu kuma san daraja ɗan adam ba, abin da umman tashi bata sani ba shine, duk wacce ya auro cikin su ya kawo mata ba zasu taɓa daidaitawa ba, saboda halin su ɗaya ne, isa, taƙama, izza da son mulki, wa zai bi wani? Murmushi ya ƙara saki daidai lokacin da yaji Dad ɗin nashi na faɗin
"Tau kaji fa Son, Mom ɗin ka na nuƙatar suruka" "Amman sai inga ai shi namiji ne ya kwantar da hankalin shi ya zaɓo wadda tayi daidai da ra'ayin shi, kada ya je yayo zaɓen tumu dare, kinsan matan yanzu ɗin yanda suke" ya faɗa yana mai maida kallon shi kan Hajiya Kubran.
"Haka ne Alhaji, sai ya duba cikin lokaci, in bai yi yanzu ba, sai yaushe? Ko so yake ayi mashi tare da Afnan ne? "
Ta faɗa tana mai goge baki da soft tissue dake ajiye gefe da gefen dining table ɗin, miƙewa tayi tare da faɗin Al'ameen ɗin ya biyo ta domin su rubuta Abunda za'a buƙata tare, gami da ficewa ta haye sama nata.
Al'ameen ɗin ne ya bita a baya, tare suka isa falon yayin da ta wuce bedroom ta ɗauki wata jotter mai kyau ta zauna ta shiga zana abubuwan da za'a buƙata cikin isa da taƙama, yayin da suka baro Alhaji Mustapha ɗin da sauran ƴaƴan nashi yana jin damuwoyin su, domin shi mutum ne mai yawan jiɓintar Al'aamarin iyalan nashi, dama kuma haka ake so, haka ya kamata ace ko wanne mai gida yana ma iyalanshi, komin girman shi kuma komin matsayin shi.
Bayan Hajiyar ta gama rubuta komai ne ta miƙa mashi, gami da cewa ya duba in da wani abu sai a ƙara, dubawa ya shiga yi cikin halin ko in kula da isar da mahaifiya tashi take ta zubawa, babu komai ya faɗa mata gami da miƙewa don barin ɗakin.
Dakatar dashi tayi, tare da ce mashi ya zauna zasu yi wata magana ne, zaunawa yayi bisa sofar dake kusa da tata ya bata dukkain natsuwar shi, domin shi mutum ne mai biyayya da son gamawa da iyayen nashi lafiya, shiru ne ya biyo baya na ƴan dakiƙu, domin ta san abun da zata zo ma ɗan ɗan nata ba lallai ya ɗauka ba domin ita ta haife shi, ta san halin shi sarai.
"Al'ameen watau na lura ka fiye shiga Al'ameen Suhan da maman ta, bana so fa raini ya shiga tsakanin ku, kuma da me suka fi sauran ma'aikatan gidan nan ne da kafi basu cikakkiyar kulawa, ko dan Kaga mahaifi ka ya ɗaure maka wutsiya ne? Tau fa ka sani ni bazan lamunta ba, tinda Alhaji ya ce a ƙyale su da aikin gidan, da ta samu lafiya ka faɗa masu su tattara su koma cen inda suka fito tinda ba zata faɗi ainahin daga ina take ba ita daƴar tata, kuma ina so ka samo mana kuku cikin ma'aikatan company ɗinka guda biyu, wanda ka san sun ƙware sosai, saboda Sam girkin talatun nan baya man daɗi" ta faɗa cikin muryar ta, da ta koma ta mulki gaba ɗayanta.
"Mahaifiyar tashi ya tsura ma idanu har saida ta kai aya, ba tare da ya katse ta ba, sannan ya muskuta ya gyara zama," Mom ina so ki sani, ni duk cikin ma'aikatan nan babu wanda na fifita, duka matsayi su ɗaya ne a wuri na, mom rashin lafiya tafi gaban komai, kuma ko da sun bar aiki, bana da hurumin korar su, kin manta ne dad yace gidan shi ne? Kuma ya basu izinin zama har zuwa lokacin da suke so, ko kuma suka gaji dan kansu, babu wanda zai hana su tafiya, so mom ina ganin wannan maganar yafi da cewa ku tattauna ta da dad, duk hukuncin da ya yanke a kansu is better" ya faɗa kan shi tsaye, domin Al'ameen ɗin mutum ne da yake kai tsaye, watau babu munafunci ko ɓoye-ɓoye a al'amurran shi.
Sannan ya cigaba da faɗin "maganar kuku kuma zan magana cikin ma'aikatan sai a turo su ko zuwa da safe ne" ya furta cikin salon miskilanci shi, tare da miƙewa ya bar ɗakin ranshi a cunkushe, bai san sai yaushe ne mom ɗin tashi zata bar halin ta ba, bai koma gidan ba ma ga baki ɗaya sai da ya tabbatar ya haɗa komai da aka bashi list, sannan ya kai ma Aunty Feena, domin yin packaging ɗinsu ko wajen mom ɗin tashi bai koma ba ya wuce part ɗinshi kai tsaye.
Yana kai kafaɗar shi bisa gadon nashi, tinanin su yayi mashi sallama, kenan umman tata ta bata dama domin tayi karatun? To ko Dad ɗin yayi mata magana ne? Allah sarki umma baiwar Allah, har yanda take ma ba cikin hayyacin ta ba, maganar ta Suhan ɗin tabi iyayen shi, abun da shi kuma Mahaifiyar tashi ta gaza fahimta, me suka tsare mata? Menene ɓata fi su dashi ba? Koda yake ya lura akwai ƴan zuga cikin Al'amarin, dole ya taka masu burki, dole ya gargaɗe su indai suna son zama cikin gidan, ba zai lamunci munafunci da haɗa husuma ba, hakanan su sanya ma bayin Allah karan zuƙa ba tare da sunyi masu wani abu ba daidai ba.