← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 56

Sashe 42

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari ansha bacci, yayin da maree da mahaifiyarka mama talatun baccin su ragagge ne, suna ta saƙa yanda zasu yi su mallaki Al'ameen ɗin, domin suna hango ma kansu rayuwa ta jin daɗi da zasu iya fuskanta nan gaba kaɗan ba da jimawa ba, saidai Abunda ya ƙara ɗugunzuma hankalinau shine ganin da mareen tayi ma Suhan ɗin a motar Al'ameen lokacin da suka dawo, haka ta koma fa tayi ta rusa kuka, da gaske son Al'ameen ɗin ya kamata, yayinda ita kuma mama talatun ba ta wannan take ba, abun duniyar kawai take hange, haka kawai ta shiga ce ma mariyar zauna nan abun duniy ya kashe ki, akan waccen kucakar da na san ko kyauta aka bashi ita ba amsa zai yi ba, kawai dai ita ce da uwar ta ke shisshigi mashi, Amman zanyi ma abun tufkar hanci.

Kowa hidima yake yi fafa, gida fa ya kacame, wasu irin garƙama garƙaman tuƙwane ake ɗorawa, bayan abincin da ake yo order ɗinshi daga manyan restourent.

Ƴan kankiya sunyi bajinta ta nan fannin, domin duk wata sanwa da za'ayi suna kamawa, yayinda ƴan uwan Hajiya kubra kejin sun wuce nan, kaman su ba zasu iya fitowa yin girkin hidima ba, rarraba ake da abinci kaman ba'a so.

Kowa sai shirin yin ƙauyawa yake yi yau, da yake duka amaren yau zasu yi, ko wanne ɓangare shiri akeyi, sai shigowa akeyi da dami damin kara, da su goruba, magarya ɗinta, nan cikin gida kuma an sanya ayi lafiyayyen dambu, da zogala ɗanya, ga lafiyayyar fura da amma da taji lafiyayyen nono da yoghurt da madarar ruwa, abun dai gwanin ban sha'awa.

Hajiya Kubra taji haushi wannan event ɗin, saida taga cewa kowa na murna dashi ne sannan ta sake, to muma ta ɓangare namu mun yi murna, saboda yau ne za'a zama ɗaya, da mai ji da kanshi da mara ji da kanshi duk za'a zama ɗaya, matan sunyi shiga irin ta Fulanin usul, musamman suka ɗauko wasu Fulani suka zo sukayi masu kwalliya irin tasu ta filani, an zane masu fuksokinsu ram da kalli baƙi da ɗige ɗige, sai suka ba kansu dariya, kuma suka burge kansu, masalan da suka ji angunan na cewa sunyi kyau.

Banso banso nake cewa, Amman a haka saida Hafsat da afnan suka matsa aka yi man saisa saisa, nima kayan Fulanin na sanya sun matuƙar amsa ta, sun yi man cif cif, dama saida Hafsat ɗin ta zaɓo mana saƙi mai kyau harda jikkarsu ta Fulani.

A haka kowa ya hallara aka fara event, kasancewar da marece ne, da sauran Haske kuma ga maza a tattare guri guda, ya sanya ni takura, gefe na koma gami da zama bisa wani kututture ƙarƙashin bishiyar gwaba, ina ta kallon su ina dariya, hannuna riƙe da ƴar sandarsu ta Fulani ina wasa da ita.

Kwallon su nake tayi, ina tafaman murmusawa, yanda maza ke gatsar rake suna sha suna santi, gefe mata masu ji da kansu su wasu ne, sun dage suna ta gwaguyar goruba duk don su faranta ma amaren rai, gefe wasu gunsu ne suna ta faman afa tambu baka, ga wasu dandalin gefe suna ta faman shan fura cikin ƙorai masu matuƙar kyau da suka sha zanen wuta.

Wasu kuma suna zaune gefe wasu kuma a tsaye suna zance da samarin su, kai abun dai kaman a ƙauye, sai abun ya burgeni, hannuna riƙe da taura guda ɗaya ina ta faman jujjuya ta, ina so inci ina jin kunyar ɗimbin maza, abokan anguna da suke ta wajen.

"Allah kuwa Friend ina son leƙa wa wurin cen fa, Naji kiɗan mu na gargajiya na tashi fa a wajen, har ma na ƙagara inje," Bilal ne da yake tsaye bisa kan Ya ameen ɗin, shi kuma yana kishingiɗe yana latsa waya yake bashi amsa

"To kaje mana, ai ni dama ban hana ka ba, Nidai na gaya maka, hidimar yara ce ba zan shiga ba."

Ɗan murmushi yayi, son zuwa wajen na ƙara tsuma shi, "Pls Pls Al'ameen Dont do that to me please i beg u Friend"

Ɗan tsaki yaja a hankali yana mai miƙewa "Muje na lura kai in maye ne ya kama mutum sai ya lashe mashi kurwa tas wallahi"

"Eah Naji ba komai shege, tinda fa ba kai kayi niyya ba, ai komai ma zaka iya faÉ—a"

Je rawa sukayi suna ci gaba da tafiya, har zuwa tafkeken lambun nasu da ya wadatu da mutane da ɓawon rake da wasu suke gefe suna ta fama n fere bayan suna rage mashi baƙi.

Da ƙafar dama Bilal ɗin ya shiga wurin, domin yana saka ƙafa ya hango one of his colique a cikin abokan ango, ya ja area cen gefe yana ta zuƙar zaƙin rake, hannun Al'ameen ɗin yaja suka isa har inda yake zaune bisa wani dutsi shida abokan shi.

Ji yai an taɓo shi ta baya, ai waigawar da zai yi sai suka haɗa ido da Bilal ɗin, a sukwabe ya tashi yana ihu, "Wow wa nake gani nan kaman Bilal Musaddiƙ ja?" ya faɗa cikin murna, yanayi yana murza ido da gudan hannun da bai riƙe karan ba.

"Nine son Ubanka Mubin, long time not see, ka ɓace ɓat fa baba, ya rayuwa?" y a faɗa yana mai kamo hannun Bilal ɗin.

"bikin wa kazo nan?" Wanda aka kira da Mubin ɗinne ke tambayar Bilal, dariya Bilal ɗin yayi gami da cewa "Kai zan tambaya Mubin ai ni nan gidan mu ne, duka amaren ƙannai ma ne, wannan shine Abokina Moh'd Almustapha Dambulan da kuke jin labarin shi" ya faɗa yana mai juyawa gami da nuna Al'ameen ɗin da yake tsaye yana ta faman doka murmushi.

Su kansu miƙewa sukayi gami da miƙa ma Al'ameen ɗin hannu suna mai girmamawa, "Nyc to meet you our gallant Yaya" suka faɗa cikin barkwanci, har yanzu basu bar shan ka ransu ba.

"Bikin fa Sadeeq Mufti akeyi angon Hafsat, ai mu so mu gayyace ka shi sadeeq É—in ya hana a cewarshi ayyuka sunyi maka yawa, da wahala ka shigo Nija withing this Period of time"

Mubeen É—in ya faÉ—a cikin jin daÉ—in ganin abokin nashi.

"Braboo, ai banga ta zama ba, muje ka nuna man shegen surukin namu" ya faÉ—a yana kamo hannun Al'ameen.

Sun gaggaisa sosai, nan suka shiga firar yaushe rabo, shi dai Al'ameen É—in sai faman murmushi yake, mutane sai zuwa suke gaida shi, da waÉ—anda suka sanshi a zahiri da waÉ—anda ma sunanshi kaÉ—ai suke ji, nan da nan fa aka shiga kallon Moh'd Al'ameen É—in gami da nuna shi, waÉ—anda ma basu san shi ba yau duk sun sanshi kuma sun ganshi.

Duk abubuwan dake faruwa ina zaune gefe ina kallo, nayi mamakin yanda sunan Al'ameen ɗin ya buɗe wajen cikin ɗannƙanƙanin lokaci, koda yake shi ɗin mai yi ne, na matsa ne, domin kafin ka samu matashi kaman shi da yake da kishin matsa da samar masu da ayyukan yi sai ka tona.

Wani ƙadangare ne da bansan da tahowa shi ba, ga dukkan alamu ma faɗa suke yi, irin manyan nan ne masu jan kai da bindi.

*Jiffff*

Ƙarar fadowar ƙadangare ne bisa kaina ya zabura dani daga faman murmushi da nake yi, ƙara na ƙwalla gami da daka tsalle, bai sauka ba ma, sai ƙara maƙalƙaleni a yayi yana neman shige wa cikin riga ta.

Wata razananniyar ƙara na kuma saki da saida ta karaɗe illahirin lambun nan baki ɗaya, lokaci guda na saki ajiyar zuciya ina mai sulale wa ƙasa sumammiya.

Rige rigen isa inda nake yaushe suka shiga yi, Al'ameen ne, da Bilal sai Hafsat da afnan, tini suka ƙaraso inda nake kwance a sume, Afnan ce ta tallafi kaina tana sakin wani tsumammen kuka, lokacin da ƙadangaren ya sauka daga bisa jikina ya sulale abin shi yanayi yana gyaɗa kai.

"ta suma Yaya ta suma ka taimaka mata" Abunda afnan ɗin ke faɗi kenan, daidai lokacin da su Saudat da Nihal suka iso wurin su da tawagar ƙawayen nasu, da sauran angunan nasu.

Baiyi wata wata ba ya sun kuce ta, hankalinshi a tashe ya nufi cikin gidan da ita, har yanzu bata ko motsi bata san inda kanta yake ba.

Sakin baki sukayi gami da bin shi da kallo, tini ƴan maganganu suka baibaye wurin, wasu na cewa ƙanwar shi ce, wasu na cewa budurwar shi ce.

*To koma dai miye ku biyo alƙalamin ~Oum-Deedat~ domin jin yanda zata kaya*

~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~25~*

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Rasa inda zai nufa yayi da ita, daya kalle ta yaga yanda take sake a hannun shi, sai ya ƙara ɗaga ƙafa, sashen shi da yafi kusa da lambun ya nufa da ita kai tsaye.

Bai ajiye ta a ko'ina ba sai bisa gadon shi, Bilal Sadeeq Afnan da Hafsat amarya da suke biye dashi, cikin su babu wanda baiyi mamakin shi ba, to saidai shi É—in ba tasu yake yi ba.

Ruwa yace Afnan ta ɗauko masu sanyi, miƙewa yayi daga bisa gadon yace Afnan ɗin ta shafa mata a fuska.

Ajiyar zuciya na sauke, jin saukar ruwan a fuska ta, har saida ƙirjina ya ɗaga sosai, ƙoƙarin miƙewa nake yi afnan ɗin ta sanya hannu ta maidani kwance.

Lamo nayi ina sauke ajiye zuciya a hankali a hankali, har yanzu jikina rawa yajeyi, tsoro gami da firgici har yanzu bai sake ni ba.

A hankali zazzaɓi mai zafi ya lulluɓeni, ganin ina rawar sanyi ne ya sanya ta jawo bargo ta lulluɓeni ruf, ga tashin bargo ga laushi katifa, uwa uba wani daɗaɗɗen ƙamshi da nake shaƙa suka taru suka sanya nayi luf abuna.

Juyawa Ya Ameen É—in yayi gami da fita daga É—akin, ganin haka ne Sadeeq É—in da Bilal suka mara mashi baya wajen ficewa su bamu wuri.
Chapter 42 · 0% Book details