← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 56

Sashe 49

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tinawa da wulaƙanci da sukayi mani shekaranjiya ne ya sanya ni zamana ba tare da na raya ma raina zuwa ba, har aka gama ma Hafsat ɗin kwalliyarta aka fara ma Afnan da tace lallai sai an fara yi mani ai ina gaba da ita, kuma nice babbar ƙawa, daƙyal dai ta haƙura aka fara mata, ganin yanda nakafe sai an gama mata sannan za'ayi mani.

Ba sallama saidai muka ganta tsulum cikin É—akin.

Da matuƙar fushi ta maida kallon ta a kaina, bayan tabo kowa dake cikin ɗakin da kallon baku isa ba.

"Dame kike taƙama ne da har zamu sanya a kira ki kiƙi zuwa? Ta jefo man tambaya, Afnan ce riƙe da ƙugu ba'i na cin ta cikin zuciya, ko kallon inda take banyi ba, haka in bangon dake ɗakin ya tanka mata tau nima na tanka mata.

Hakan yayi bala'i ƙona mata rai kuwa, cikin hasala tace

"Aikin mu anan gidan shine aikin ki, kuma a ƙarƙashin Alfarmar Ya Ameen kuke zaune acikin gidan nan, sannan ina so ne in faɗa maki cewa ke baki kai matsayi da har mu zamu ce ga Abunda mukeso kiyi mana ba ki ƙiya, kuma ba zaki taɓa kai matsayi ba, kwaɗayayyun banza da wofi, ke da waccen sululu kasa ɗin uwar taki..... "

*" Aunty Nihal ya isa"*

*"Ya Isa Hakanan, in ba haka ba wallahi zanje na faÉ—a ma Ya Ameen É—in"*

Afnan ce take dakatar da ita cikin ƴar tsawa, ranta in ya kai dubu tau ya ɓaci, bata ma san ta ƙwace fuskar taba daga kwalliyar da akeyi mata, ni kau tini fuska ta ta jiƙe da ruwan hawaye, ji nake kaman ƙjrji na zai tsage zuciya ta ta fito.

Wannan cin fuska yayi yawa, gaban ƙawayen Hafsat da basu san ko ni ɗin wacece ba ta biyo ni nan tana ƙasƙantar dani, tini na ruahe da kuka mai sauti, domin ina jin in har banyi ba zuciya ta zata iya bugawa, Hafsat ɗince ta ƙara so wajen da nake zaune bisa gado bansan lokacin da na tashi zaunen ba.

Bubbuga baya na ta shiga yi, ganin haka ne ya sanya ni rungume ta, Allah ma yaso bata kai ga sanya kaya ta ba, da tini zan cukuikuye su, iri. Daƙumar da nayi mata.

Ita kau Nihal jin hakan da tayi ya sanya ta ficewa tana mai saukin maganganu masu zafi a kaina da umma ta, Afnan ɗince ta miƙe gami da ƙarasowa inda nake ta shiga bani haƙuri, gami da cewa "Bari inzo, ai sai na faɗa ma Yayan tinda su dai basa son zaman lafiya"

Nice na riƙo hannun ta ina mai girgiza mata kai cikin kuka, fasawa tayi gami da shiga lallashi na, daƙyar suka samu nayi shiru, babu wanda bai tausaya man ba a cikin ɗakin Allah wadai suka shiga yi ma Nihal ɗin Afnan na jinsu ƙala bata ce ba, to me zata ce ai halinka shi ake faɗi ko bayan ba ranka kuwa.

Manyan kuloli ne aka shiga shigowa dasu cikin gidan, rumfa guda aka ware da aka jejjera abinciccikan, sai ma'aikata masu serving da aka zube saidai Abunda mutum yake da buƙata a kai mashi, babu kalar nau'ikan abincin da babu acikin gidan nan, har ma da na gargajiya ga masu buƙata, kama daga su Alkubua, fankaso, waina, dambun shinkafa lafiyayye da ya sha zkgala da kayan lambu, to dama dai kowa ya san Katsina wa da wannan cimaka kuma bikin nasu ne, wannan ce ta sanya basu yada al'adar tasu ba.

Kaman yanda aka jejjera abinci cika da lemuka kala kala, haka ma acen tanƙameme hall ɗin da yake mallakin Alhaji Mustapha inda za'ayi walimar cin abincin aka har haɗa komai da taimakon su Al'ameen ɗin da Bilal, basu bar wurin ba hr saida suka ga komai ya kammala, kuma an ware ma manya iyayen ƙasa nasu ɓangaren ta inda babu ma mai ganin su, sannan suka wuce gidan domin shiryawa

Ƙarfe ɗaya ƴan Katsinan suk iso iyayen khadeejar Yaya Aleeyun da yake ma harda shi aka je ɗauko suruka nashi, ya sanya shima saidai abokanan shi ne suka taimaka mashi har haɗa komai.

Har zuwa ƙarfe ɗayan ban yadda anyi mani kwalliya ba, yo ni kwalliyar ma me zanyi? Saida Afnan da Hafsat ɗin suka matsa ne gami da tsoratar dani zasu gaya ma Ya Ameen ɗin Abunda ya faru to, sannan na yarda aka yi mani ƴar Light ba mai yawa ba, duk da haka nayi kyau ba laifi kam.

Kowa na ɗakin namu ya haɗe cikin ƴar ubansun ashoben yinin da ta kasance ƴar ubansu atamfa, fara ce tas sai ƴan pattern na dark blue da Orange, atamfar bata da hayaniya, hakan ce ta sanya tayi matuƙar kyau da haskawa gashi zanenta ba mai irin yawan nan bane jefi jefi ne.

Haka muka shirya cikin atamfar, Nidai kasa tashi ma nayi saboda Hafsat ce ta bada mana ɗinkin da aka yi mana, kasancewa ƴar ƙibar dake gareni ya sanya skirt ɗin kama ni tsam, duk nabi na tsargu kaina, yayin da su kuma sauran suka ruɗe da ganin ƙirar da Allah yayi mni suna cewa dama su.

Gyalena da takalma na masu tsinci duk blue ne, yayin da siririyar sarƙar dake wuya na ta kasance fari tar ɗin duwatsu da kar ta Orange, lallai munyi kyau, kaman yanda vail ɗina yake blue haka na kowa dake ɗakin namu ya kasance, banda Hafsat da ita kalar golden ne gabaɗaya jikin ta hatta sarƙar gold ɗin dake wuyan ta da Sadeeq ɗin ya zubo mata su cikin lefe kaman ba kuɗi ne ya siya ba.

Masu aiki ne suka leƙo sashen namu gami da faɗa mana mu fito za'a fara cin abincin kaman yanda aka tsara.

Tin daga nesa ake kallonmu, domin dai yau duk hassadar ka ba zaka kushe mu ba haka ma amaryar tamu, runfuna ne guda bakwai kaman yanda aka tanada, Hajiya Kubra, Hajiya Zainab, Kaka Zuwaira da tawagarta, sai ta Saudat, Nihal Da Hafsat É—in. Kowa da tawagar shi yake zaune.

Hajiya Kubra ce na fara hangowa, saboda wani irin kwarjini da cika idanu da take yi, ta kame ɗaya daga cikin kujerun Alfarmar dake ƙarƙashin haɗaɗɗiyar rumfar tata da taji ado da silkin yadi da balam balam.

Sanye take cikin wani ɗanyen pink ɗin lace anyi mata ɗinkin bubu, wuyan nan nata babu Abunda yake yi in banda walƙiya, haka ma kunnuwan ta da hannayen ta da suke cike taf da zobuna da abun hannuwa na gold

Yau ko gyalen ma babu a wuyan ta, sai ƴan fadan ta da suke zaune kujerun da suke gefen nata, sauran kuma duk kansu kujerun ƙarfe ne anyi masu ado da fararen ƙyalle in ka cire na kaka zuwaira da na Hajiya zainab, sai na amare da suke royal chairs kaman na kamu haka.

Rumfar da babu kowa sai kujeru muka nufa gami da zama idanun kowaa kammu masalan ma ni da bani da alama da ƴar aiki ayau, ba wata wata ma'aikata suka fara serving ɗin mutane, baka jin komai sai ƙarar chokulla, ni kau na kasa cin ma abincin sai juya cokali nake ta faman yi.

Da na ɗaga idanu na kuwa sai su faɗa cikin na Hajiya Kubra, data ƙure ni da kallo tana so ta gano Abunda yaja hankalin yaron nata a jikina, saidai duk iya kallon nata bata gano komai ba, domin in hasken fata ne ko hanci babu kalar wanda yaron nata bai gani ba har cen ƙasashen ƙetaren

Da mun haɗa idanu kuwa zan saurin sadda kaina ƙasa saboda irin kallon tsanar da take bina dashi, sa'a ta ɗaya ummata bata wurin domin dukka ƴan aiki acen sashen nasu suke in abincin, hakan ce ta sanya su zama sashen namu, ita kau ummata ma ɗaki ta shiga gami da kwanciya saboda ta gaji gashi har juwa take ji..

Ƙarfe biyu daidai dubban mutane suka shaida ɗaurin auren Saudat Almustapha da Kamal jamu, akan sadaki naira dubu Hamsin, sai Zuwaira (Nihal) da Nuradden Baffa itama akan sadaki naira dubu hamsin, sannan Hafsat Auwalu da Abubakar Sadeeq Muftee itama akan sadaki naira dubu Hamsin ɗin Sannan na Aleeyj Auwalu da Khadeeja Ibrahim akan sadaki Naira dubu ɗari domin su ne suke da alhakin sanya ma ɗiyar tasu sadaki ba Alhaji Auwalu ba, tinda su cewa sukayi ba kuɗin ke gaban su ba albarka auren da ɗorewa shi suke so.

Bayan kammala É—aurin auren ne, haka dubban jama'ar suka shaida naÉ—in ya Ameen É—in a matsayi *Yariman Matasan Arewa*

Bayan kammala naɗa mashi rawani ne da miƙa mashi sanar girma sai aka lulluɓa mashi alkyabba fara ƙal da surkin royal blue

Tini fa Yariman namu ya Faso, cikin salon tafiyar shi ta ƙasaita, yau kam tafiya ta tabbata, shi ba gadon sarauta ba Allah ya ci dashi, bayan ya kai gaisuwa ne ga dukkanin sarakunan dake wajen mai girma shugaban ƙasa ya mallaka mashi makullin dunƙulalliyar mota ƙirar royce - royce 2019 da lambogini 2019 collection a matsayi kyautar shi shi kuma, nan fa aka yi ta mashi kyaututtuka, fadawan da aka mallaka mashi suna mashi godiya, a haka ya nufo cikin gidan Bilal ɗin na take mashi baya domin zuwa kaima tashi mahaifiyar gaisuwa.

Matasa kuwa ya gansu kowa so yake ya gaida shi, don ma fadawan na buÉ—e mashi hanya, a haka ya ratso dimbin mutanen nan har zuwa cikin gidan nasu.

Tin daga nesa mahaifiyar tashi ta hango shi, Miƙewa tayi gami da isa wajen shi, baiyi wata wata ba kuwa ya sunkuya ya kai gaisuwa gareta, itama bata yi wata wata ba ta sunkuya gami da rungumo shi cikin ƙirjinta ta miƙe tsaye dashi, sowa aka ɗauka da tafi kowa sun burge shi, yanyameshi aka shiga yi ana ta kai gaisuwa, abokan wasa na yankar shi, hatta da kaka zuwairan da take tafiya daƙyar saida ta taso ta iso gareshi.

Sa hannu yayi ya rungumo ta gami da É—ora mata peck a tsakiyar kai, dungureshi tayi tana mai cewa "ja'iri girma ya hau kanka yanzu saura mata"

Haka yabi yana rungume ƙannen nashi amare da suka kai gareshi Hafsat ce kawai bai runguma ba, saidai ya kamo mata hannu yana mai cewa "Congrat ƙanwa ta" da murmushi ta bishi tana mai cewa " Same Yaya"
Chapter 49 · 0% Book details