Sashe 38
Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da yake akwai fahimta sosai tsakanin su da ƴar shaƙuwa, yana son hafsat ɗin, ko don sanyin halin ta da kuma girmama na gaba da ita, ba kaman sangartattun ƙannen nashi ba, ta shiga zayyane mashi dukkan abubuwan da take buƙata, take yayi mata trnsfer na kuɗaɗen duk da zasu isheta ta kammala hidima ta har ma tayi saura, sannan ya shiga sanar da ita hukuncin Alhaji na cewa ba zata koma gida ba, har sai an ɗaura auren nata, suma duka sauran mutanen nan ba da daɗewa ba zasu tarkato su taho Abuja acen za'ayi duk wasu shirye shirye da hidima bikin, hatta da su kaka zuwaira duk nan za'a taho dasu domin suma su ɗan shaƙata, zaman wuri ɗayan ya isa hakanan.
Ƴar fira sukayi kaɗan kaɗan, abun ka da wanda bai damu da magana ba, hakan ce ta sanya ta yi mashi godiya gami da miƙewa ta fice harda tukuicin ja mashi ƙofar, wani ɓari na zuciyar ta na tambayar ta me maree taje yi sashen yayan nasu?
*************
Maree da take zaune ɗakin mama talatun da ta kasance ita ce mahaifiya ta, Amman ba kowa ya sani ba, ƙwalla take share wa, cikin ƙunan rai ta shiga zayyane mata Abunda ya Ameen ɗin yayi mata, aiko ashar ta lailayo ta zunduma tana faɗar baƙaken maganganu, "kika ce har Suhan kin gani a sashen nashi?" ta jefa mata tambaya, tana daga tsaye riƙe da ƙugu.
"Eah mama, na ganta lokacin da ta fito, har ma harara ta ta dinga yi.... " ta faɗa cikin ƙunar zuciya, uwar tata ce ta katse mata maganar da take yi "ke dallah ja cen ki ba mutane wuri, ki tabbata duk yanda zakiyi kiyi, ki jawo hankalin yaron nan a gareku, ki tsaya kallon ruwa kwaɗo yayi maki ƙafafu, ki dai san a nan gidan babu wanda ya san nice na haife ki, ko shiga hidimarki kika ga bana yi, bana so kwabar mu tayi ruwa, Amma billahillazee duk yanda zamuyi sai mun mallaki ƙaramin yaron nan attajiri, sai mun mulka da juya gidan nan fiyee ma da yanda Kubra keyi" ta faɗa tana huci da hurtai.
"Kyalesu, na san abun yi, ba dai ke ya wulaƙanta ba,? Zai dawo ne yana neman soyayya ki da roƙon ki, a yayin da zamu juya shi kaman waina a cikin tanada, goge hawayen ki, ki koma bakin aikin ki kada su dawo su tadda baki kammala Abunda suka sanya ki ba, ina so ne ki shiga jiki su, kaman yanda jini yake gudana a jikin nasu, kuma ki tabbatas duk magungunan da na baki kina zuba masu a abincin da suke ci, ki kula fa, kinsan kukun nan basu da mutumci, kinsan ƴan kudun nan, shegu ranakun banza" ta ƙara she tana gyara zaman za in ta da har ya warware tsabar bala'i gab yake da faɗuwa, har ɗan kaman ta kana iya hange.
Da too mareen ta bita, tana mai tashi ta fice daga É—akin, ko da zata gifta ta inda É—akin nasu Suhan yake saida ta wurga mashi harara kaman Suhan É—in ce a ciki.
*******
Kammala shiryawa tawa, yayi daidai da shigowar Hafsat ɗin ɗakin namu tana mai cike da farin ciki, rungume ni tayi tana faɗin "kin gani ko Suhan, kingani dama nace maki kiran yayan Alkhairi ne a gare mu" kuɗin soyayya ya bamu wadda zamuyi har sai mun gaji da kashewa" cikin murmushi na zame jikina daga nata, domin tana niyyar kadan ne, na bita da kallo ina cewa "aiko kin gode wallahi hafsat, don Allah to karki kira gida a ƙara maki wasu tinda waɗannan sun isheki, ko shi Abdul ɗin (sunan saurayi hafsat ɗin wanda zata aura) kar ki amshi masu yawa a wurin shi." da to ta bini, tana mai ƙara gyara fuskar ta, sallama muka yi ma umma da take zaune tsakar gida tana sauraren radio sallama, addu'a tayi mana da sake faɗa mana kar mu kai magribawaje mu dawo da wuri.
Ranshi har yanzu a matuƙar ɓace yake, me Yarinyar ke nufi dashi ne? A cikin gidan nan ma zata dinga yin irin wannan shigar tana matsayi mai aikin gidan da yake wadace da ƴan aiki maza, kama daga masu gadi, drebobin da masu gyaran lambu da ba flowers ruwa da share gida?, miƙewa yayi gami da shigewa ciki domin canja kaya, so yake ya fita ko zai shaƙo iskar da zata sanyaya mashi rai.
Bai ko kula da yanda ta canja ma ɗakin tsari ba, har ya canja kayan ya fice, da yake wardrooo ɗin ta cikin bango ce, mai azabar kyau da ƙayatuwa.
Keys kawai ya zara, gami da kwasar wayoyin shi na hannu, ya fice daga sashen nashi, gami da murza mashi makulli ya rufe😅
Tin daga nesa ya hango su, ya sheda hafsat, Amman gudar ce bai gane ba, har saida ya matsa daf dasu, inda suke tsaye suna jiran driver yazo ya kaisu, saboda yau ba ita kaÉ—ai bace, ita da hafsat ce ya sanya ta yadda zata shiga motar gidan, shima saida suka kai ruwa rana sannan.
Ƙala bai ce masu ba har ya isa ga motar tashi da take gefe tana ta ɗaukar idanu, horn ya danna masu, hafsat ɗin ce ta kula dasu yake kira, ƙara sawa tayi wurin shi, tambayar ta ya shiga yi tsayuwar me suke wurin, sheda mashi tayi driver suke jira ya ƙara so, yace ya kusa isowa gidan. (da yake muɗi sun fita da su Hajiya Kubra da amare)
"Ku shiga in ajiye ku, idan ya ƙaraso sai yaje ya ɗauko ku in kun gama" Abunda ya faɗa kenan yana mai bin agogon hannun nashi da kallo don sanin ko ƙarfe nawa.
Juyawa tayi gami da ya fito ni da hannu, a hankali na shiga taka wa gami da ƙara sawa inda take tsaye bakin motar
Hannu ta sanya gami da buÉ—e man gidan baya, "ki shiga, yaya ne yace zai kai mu, in mun gama mun kira driver É—in ya maidamu"
Ba a son raina ba na shiga, "ya salam" na furta cikin raina, sanyi da ƙamshi motar sun tafi da imani na, ɗan lumshe idanu nayi, lokacin da Naji motar ta daidaita a saman kwalta.
Ta baya nake satar kallon shi, tuƙin ma a natse yake yin shi, yayi kyau cikin riga marar nauyi kamfanin Adidas da baƙin wandon jeans a jikin shi, kai shi duk yadda ya sanya kaya ma kyau suke yi mashi.
Duk yanda naso in hana idanu na kaiwa gare shi, basa jin magana, saidai in samu kaina dumu dumu ina mai ƙare mashi kallo tas, har baƙi siɗik ɗin kwantaccen gashin kanshi.
Wani irin sanyin ni'ima ne gami da gaurayayyen ƙamshi turaren shi ne yake busowa, hakan ce ta sanya ni lafewa daga baya, ina tsura ma kyakkyawar fuskar shi idanu ta cikin madubi, tunanin nika ne masu yawa suke kai komo a zuciya ta, inda na taɓa faɗa mashi a ƙirji, inda na taɓa cakumo shi da umma ta bata lafiya, da kuma a makaranta kwanaki kaɗan da suka wuce.
Ban aune ba na tsinkayo muryar shi daga cen gaba yana cewa " *kallon fa?*"
ÆŠan duburcewa nayi, ina mai faÉ—a a zuciya ta cewa na shiga uku ni Hauwa'u, Ya ameen ya kama ni dumu dumu ina kallon shi, Sam bansan idanuna na kan madubi ba, ban
Kuma kawo ma raina cewa zai iya hango ni ba ta baya, da yake motar na da É—an duhu haka.
Tsaf ya tsare ni da idanu ta cikin madubi yana ɗan cije bakin shi da haƙoran shi kaɗannkaɗan.
Hafsat ce da hankalin ta ya kai kanmu, kuma taji abinda ya tambaya, ɗan juyowa tayi kaɗan tana waywaye na, hakan ce ta sanya ni ɗauke kaina na maida idanuwa na kan glass ɗin da yake gefe na, gami da ƙure titi da idanu, ba tare da ko alamun bayar da amsa ba.
*indai kunya ce, tau nidai yau na riga na shata ni Suhan*
_Share_
_like_
_Comment_
~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~âœðŸ½âœðŸ½GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONâœðŸ½âœðŸ½~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden penâœ,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page~23~*
*Page É—inki ne maman sadeeq, kiyi yanda kike so dashi, asha karatu lfy*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Fuska ta a ɗaure, ko da muka haɗa idanu da hafsat, harara na sakar mata, ita kau juyawa tayi tana ƙunshe dariya a ciki, harda rufe baki, saboda ta fahimci Abunda duk ya faru.
Har yayi parking ƙofar katafaren supermarket ɗin ban ƙara yadda mun haɗa idanu dashi ba, ina ƙoƙarin sauka ne idanun A suka kai kanshi ta madubi, ya ƙureni da kallo ko motsi baya yi, hannun shi duka akan stiyarin motar ya jingina jikin shi da marfin motar ta ɓangaren shi, yayi kyau kaman saraki, saurin ficewa nayi har ina harɗewa da zumbulelen hijab ɗina Allah ma yaso ban kifa ba.
Lumshe idanu yayi, ya sake buÉ—ewa lokacin da yaji duk sun fice hafsat na jero mashi godiya, da kallo ya raka su, a zahiri gaskiya ba ita yake kallo ba, tinanin abinda maree tayi mashi kawai yake yi, ita kau mutuniyar tawa sai ta É—auka still ita yake kallo.
Jan motar yayi a matuƙar fusace ya bar wajen, dole ne ya ɗauki mataki, ba zai lamunci ƙaramin iskanci a cikin gidan nasu ba.
Mun sha soyayya, abinda ke bani mamaki yanda hafsat ta ragargazo mani siyayya sosai da sosai, kayan fitar biki ne masu tsada ta siya man, harda kayan Fulani da za'a sanya ranar tradutional day da za'a gudanar a lambun gidan nasu.
Kwanan mu biyar muna fita siyayya, har É—inkunan mu duk mun amso, saboda kuÉ—in shap-Shap Hafsat É—in ta biya aka yi mana.
Gyaran jiki Hafsat ɗin ta tursasani saida na biye mata aka yi tayi mana tare, wanda a zahirin gaskiya ma gyaran jikin yafi karɓa ta tinda na fita haske sosai.