← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 56

Sashe 28

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abundant bata sani ba, tin bayan shigar Al'Ameen ɗin sashen ma'aikatan, mama uwani, da mama Talatu sun gashi, suna laɓe bayan ƙofar ɗakin su suna hangensu, saidai basa iya jiyo me yake faɗa ko kuma me yake wakana acikin ɗakin, fitowarshi, da kuma fitowar suhan ɗin ba jimawa da fitar Al'Ameen ɗin duk sun gani,
Cikin sauri mama uwani ta fito ta bi bayan Suhan É—in, saidai cikin rashin sa'a ta tadda Al'Ameen É—in ya fice cikin motar shi, da matsananci gudu yayin da ita kuma suhan É—in tabi ta gefen titi tna tafiya alamar ma tafiyar tasu bata zo É—aya ba, tinda su a tinanin su ko Al'Ameen É—inne zai É—auki suhan É—in su tafi tare da ita.
Abinda duk basu sani ba shine, Al'Ameen É—in dukan su tara su yake yi, lokaci yake jira yazo da dukkan su zai shayar dasu Madarar mamaki.

_Masu karatu kada fa ku manta har yanzu fa a cikin ma'aikatan gidan, babu wanda ya san da maganar auren Suhan É—in da Al'Ameen ya bijiro da ita, har ita kanta suhan É—in da umman ta_

~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:36 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~17~*

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Tini rahoto ya isa kunnen Hajiya kubra, wannan ne ya sanya ta wakilta mama talatun da ta kai mata tsogumin zuwa É—akin namu ta duba mata me ke wakana, domin dai ita dakanta ba zata iya taka sashen masu aikin ba.

Cikin sa'a kuwa, ko da ta isa ta tadda umman tawa zaune bakin katifa tana jan carbinta a hankali yayin da idon ta yake kulle haka ta jingina bayan ta da jikin bangon ɗakin, bata yi sallama ba har saida ta isa tsakiyar ɗakin tana mai ƙare ma dukkanin lungu da saƙo dake cikin ɗakin kallo, cikin matuƙar mamaki umman tawa ta buɗe idanun ta tana mai bin mama talatun da kallo wadda har ta samu gefen katifa ta zauna, Amman duk da haka bata bar bin loko loko na ɗakin da kallo ba, ko zata hango wata leda ko wani abu.

"A'a Talatu ce yau a É—akin namu? Sannu da zuwa" umman tawa ta faÉ—a cikin É—an murmushi haka kaÉ—an a fuskar ta, domin dai ta san me ya kawo mama talatun É—akin namu

"Eh wallahi kuwa Maryama, nazo duba jikin naki ne, ya ƙarfin jiki?" ta faɗa cikin ɗan ruɗewa kaɗan kama ta da umman tawa tayi tana mata kalle kalle a ɗaki.

"Aikuwa Naji sauƙi sosai Alhamdulillah wallahi Talatu, kinga kaman ba ni ba Naji ƙarfin jiki na, Allah dai ya saka da Alkhairin sa"

Umman tawa ta faɗa tana mai komawa ta jingina da bangon, daga haka ta ja bakin ta ta tsuke, hakan da mama talatun ta fahimta ne ya sanya ta cewa "Madalla Madalla, Allah ya ƙaro afuwa" ta miƙe cikin hanzari zata fice yayin da umman tawa ta bita da ameen tana mai kallon bayan ta, gami da girgiza kai a hankali a hankali

Daidai bakin ƙofa muka haɗu da ita, gaida ta nake yi ma, Amman Sam hankalin ta na ga ƙatuwar ledar da na ciko mana ita taf da siyayyar abinci da zamu ci kafin muyi tinanin mafita.

Har na gitta ta na shige ɗakin tana tsaye tana bin ledar da kallo, domin sanin menene ciki, niko ba ta ita nake yi ba, sanin halin ta da nayi, sai ma na tsinci kaina da baƙin cikin shiga ɗakin namu da tayi, koda yake ba zuwan kanta bane turo ta aka yi.

Jiki a matuƙar sanyaye ta wuce direct zuwa sashen hajiya Kubran ta zauna zaman jiran ta fito, domin taji ba'asin aiken da tayi mata.

Ta ɓangaren mu kuwa ba ma ta ita mukeyi ba, abincin mu muka ci cikin jin daɗi, da sanya ma Ya Ameen albarka, ko babu komai ya zo mana a lokacin da muke buƙatar shi, mu bamu damu da halin mahaifiyar shi ba, ko ma me zata yi ai yunwa bata da hankali.

Ƙarya da gaskiya ta shiga zayyane ma Hajiya Kubran, yayin da ita kuma take zaune hakimce tana sauraren ta, take gyaɗa kai a hankali, lokaci guda ta sallami talatun da take faɗa mata ƙarya da gaskiya gami da kiran hajiya Laila aminiyar ta, kuma maganin kukan ta.

****************

Washegari tin da sassafe sai ga mudi driver ya mana sallama, gami da miƙo man fararen takaddu ƙal dasu, yake shaida man Alhaji ƙarami yace in cike zai aiko shi ya amsa anjima

Amsa nayi gami da mashi godiya, na koma cikin ɗaki fuska ta fal da annashuwa, farin ciki nake yi sosai matuƙa, domin dai ko ba komai na fahimci ya danganci karatu na ne, umma ta na shiga nuna mawa, itama tayi murna sosai, gami da ƙara gode ma Al'ameen ɗin da ya tsaya ma Al'amarin mu kai da fata.

Bamu kaɗai yake ma haka ba, kowa a cikin gidan yana taimaka mashi, muddin abun ya sha kai, domin kwanaki ma sai da ya biya maƙudan kuɗi aka yi ma yarinyar mama saude mai girki aiki, muma cikin gida ne muke ta jin raɗe raɗi, da irin taimakon da yake ma ma'aikatan baya ga albashin su.

Cikewa na shiga yi, da gani dai kaman Jarabawa ce zan rubuta watau Jamb, inda naga ban gane ba sai in tsallake, a haka har na gama na maida cikin folder É—in na ajiye jiran mudi yazo ya amsa.

Wannan ce ta bani damar yin aikace aikace na cikin jin daɗi, lallai ina dab da cika buri na, abun ya matuƙar ƙarfafa man guiwa, saidai na nazo wajen zaɓen choice na Abunda zan karanta tsallakewa nayi, na bar mashi ya zaɓa man, duk abinda ya zaɓa man daidai ne.

Zuwa azahar na gama komai, har list ɗin abinda zanje in sissiyo mana na buƙata nayi, wanka nayi cikin shiri na simple ba mai ɗaukar lokaci ba, doguwa riga ta material ce jiki na, Afnan ce ta bani ita cikin kayan da ta kawo mani kafin ta koma, da gani ma bata taɓa sanya ta ba, ta amshe ni matuƙa, gyale na ɗauko zan yafa, umma tayi man wani irin kallo, ba arziƙi na ajiye ina ƙumshe dariya a ciki na, oh umma bata so taga nayi gayu, ita har kullum gani take yi ba'a matsayin kowa muke ba, in ana ganin ka ƙwas-ƙwas ma sai ayi ta gulmar ka acikin gidan, dama ga shi ga irin zaman da mukeyi acikin gidan.

Sallamar mudi ce ta katse man dariya da nake yi a zuciya, ɗauko takaddun nayi na miƙa mashi ina ƙara mashi godiya, amsa yayi yana dariya tare da ƙara ma umma ta ya jiki, saboda ɗazu da yazo basu gaisa ba.

Sai da na gama kitsawa sosai, sannan na ɗauki ƴar jikka ta gami da takadda ta list ɗin abubuwan buƙatar, sallama nayi ma umma gami da ficewa daga ɗakin namu kai tsaye zuwa ga barin gidan cikin salon tafiyata da lokutta da dama umma ta kace Allah yayi mani nawar tafiya, su kuma sauran ma'aikatan kance ya ga ce, kai ba kowa kowa ba Galadima kashi🤣

Tin daga nesa na hango shi tsaye jingine jikin motar shi, mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, baƙa ce wuluk sosai, saidai gilassan ta masu sauƙi duhu ne, ni ban ma taɓa ganin shi a cikin wannan motar ba, da gani dai sabuwar siye ce, to abu da masu abunsu

Sanye yake cikin riga ƴar shara, da wando dogo har ƙasa, kanshi babu hula saidai baƙin gashin shi da akoda yaushe yake kwance luf bisa fatar kanshi, hannun shi na riƙe da makullan mota da takaddun nawa a hannun shi yana dubawa,

Baƙin sun glass ɗin da ya sanya ma idanun shi, su ke katange ka daga kallon cikin ƙwayar idanun shi, kaman kullum dai yana tsaye cikin kwarjini shi, da kamalar shi, Al'ameen mutum ne da idan ka kalle shi sai ka ƙara kallon shi

Duk da ba ni yake kallo ba hakan saida ya jaza mani harharɗewa, cikin son gyara tafiyar tawa na isa daidai saitin inda suke tsaye shi da mudi driver "Ahaf, yallaɓai ai gama ta nan tafe" mudi ya shiga faɗa mashi, ga dukkan alamu magana suke yi ko kuma aika mudin yayi ya kirawo ni.

"OK ce mata tazo ina kiran ta" Abunda ya faÉ—a kenan, har yanzu idanun shi na kan takaddun ko sau É—aya bai É—ago ya kalle ni ba,

Kwala man kira mudin yayi "Ke Suhana, kizo yallaɓai na kiran ki" chak naja na tsaya, da ɗan ɓacin rai a fuskanta, in ma kiran ne ai sai ya isa inda nake ba ya kwala man kira ba haka gatsau kowa na saurare.

A hankali na juya akalar tafiyar tawa daga nhfar gate É—in zuwa wurin su inda suke tsaye, da sallama a bakina na isa lokaci guda ina mai gaida shi "Yaya ina wuni?" bai É—ago ba har yanzu idanun shi na kan takaddun yana nazari su ya amsa mani da "Lafiya" a gajarce

Gyara tsayuwa ta nayi duk a takure nake wallahi, kwarjini shi kan ƙara ruɗani, ɗan guntun murmushi naga ya saki, yana mai juyawa kai tsaye zuwa ga bakin motar tashi ya sanya makullan da suke hannun shi ya buɗe tare da ɗauko wasu biruka guda biyu ya dawo inda nake tsaye

Still bai kalle ni ba, ya shiga man tambayoyi wasu ina bashi amsa, wasu ina yin shiru dan ban sani ba.

Choice É—ina ya tambaya na Abunda zan karanta, nan ma shiru nayi mashi, murya ta har rawa take idan zan bashi amsa da ya kula, inda Allah ya taimake ni mudi da yake tsaye ta gefen mu yana sauraren mu.
Chapter 28 · 0% Book details