Sashe 30
Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Riƙe nake da wayar tawa sai jujjuya ta nake yi ina daga tsaye, na kasa kiran shi, gashi lokaci yana daɗa ƙurewa, har takwas saura, shahada nayi na danna ma Layin nashi kira, wannan ne karon farko da hannu na zai soma kiran wani ɗa namiji a rayuwa ta, shi ɗin daban ne, abubuwa da dama shine mai buɗe man ƙofofin yin su.
Na zurfafa a tinani har wayar ta katse ban sani ba, sai dubawa nayi naga ashe ma bai ɗaga ba, ban ƙasa a guiwa ba na sake gwada kira, still dai bai ɗauka ba, haƙura nayi na koma gefen katifa na zauna, ina mai gyara safar dake ƙafa ta da take fara ƙar, sai ɗaukar idanu take yi.
Ci gaba nayi da craming ina mai gyara zaman jikkata a saman kafaɗa ta, idan ka kalle ni kai zaka rantse da Allah ba ɗiyar Hausawa bace, kayan sun matuƙar fidda man shape, skirt ɗin da yabi lafiya ƙuguna ya zauna ɗas kaman a wajen aka ɗinka shi, nayi matuƙar mamakin yanda aka yi har ya gane size ɗin kayan da zasu iya yi mani
Miƙewa nayi ina gyara zaman belt ɗin a saman ƙhgu na da yabi shafaffen cikina, kai kace bana cin abinci, duk da ni ba siririya bace hakan ce ta sanya kayan suka cika ni nayi ɗas ɗas dani.
Waya ta ce ta ɗauki tsuwwa alamar ana kira na, cikin hanzari na ɗaga kasancewar naga har takwas saura minti sha biyar tayi, gashi yace ƙarfe takwas ne ake shiga Jarabawar, sallama kawai nayi ko amsa mani baiyi ba, cikin hanzari yace "Fito" Abunda ya faɗa kenan ya datse kiran
Sallama nayi ma umma, ta shiga bina da addu'a kuwa, gami da gargaɗa ta da in kama kaina, in tsare mutumci na, kasancewar makarantar wadda take haɗe maza da mata, da murmushi na bita, ina jaddada irin ƙaunar da umman tawa take mani, da son kasancewa ta ta gari a duk inda na shiga. Hannu na sanya na ɗauki gogaggiyar zumbuleliyar hijab ɗita da take ajiye gefen katifa nayi, na warware ta na sanya, ba ɓata lokaci na fice daga ɗakin namu addu'a ɗauke a bakina.
Kasancewar safiya ce, babu kowa a harabar gidan, balle Æ´an tsurku su samu na rahoto, ko ba haka ba ma kuma É—aukacin mutanen gidan basa nan, wai sun tafi turkey siyayya, cikin hanzari na isa ga motar da take fake tsakiyar harabar gidan, da gani a cikin ta ne za'a kai ni makarantar.
Baya na buÉ—e zan shiga, har ga Allah na É—auka muÉ—i driver ne zai kai ni, "dawo gaba" muryar shi ta doki dodon kunne na, ba gardama na maida murfin na rufe gami da buÉ—e gidan gaba na shiga. Ko zama ban daidaita ba ya fizgi motar gami da ficewa daga harabar gidan da tuni mai gadi ya wangale mashi gate.
"Kina cen kina shiririta har kin so ki makara" Abunda ya faɗa kenan ya maida bakin shi ya rufe kaman ba shine ya mani magana ba, ɗan ɗagowa nayi gami da ɗan waiwayawa ta gefen da yake zaune yana tuƙi na ɗan kalle shi haka, tuƙin shi yake cikin kwanciyar hankali da kwarewa, sharara gudu yake yi kaman waɗanda zasu bar gari, yayi kyau abun shi, cikin manyan kaya, da dukkan alamu yana son manyan kaya kaman ya san suna matuƙar da cewa dashi, ɗinkin dakakkiyar shadda ce mai masifar kyau da ɗaukar idanu, zamu iya kiran ta da royal blue, hakan ce ta sanya fatar shi haskawa sosai, fatar nan tashi kaman bata shan rana, lumui ga gashi da yake kwance saman ta, hannun shi na ɗauke da zoben azurfa mai kyau da ɗaukar idanu, yayin da agogon shi ƙirar iphone take ta walƙiya cikin hasken ranar da ya riga ya gama hudowa.
Maimakon in bashi ansa, sai na kauda zancen da cewa "Yaya Ina kwana?"
Bai bani amsa ba, sai ma ɗagawa da yake yi yana kallon agogon dake maƙale a hannun nashi, yana sarkin ɗan siririn tsaki.
Daidai bakin gaye É—in makarantar yayi parking, yana mai waiwayo wa ta inda nake zaune yake faÉ—in "Ki tabbatar kin cire wannan hijabin kafin ki shiga makarantar nan, doka ne gashi nan rutuce a jikin gate"da" to" na bashi amsa ina mai ficewa
Tsayawa nayi tinanin ta ina ma zan fara cire wannan hijab É—in ni na ma rasa ta yanda zan ratsa tsakiyar mazan dake ta wucewa zuwa cikin makarantar ga dukkan alamu dai mun soma makara.
Ban aune ba Naji muryar shi ta baya na yana cewa "ba zaki hanzarta ba sai sun rufe shiga? Bani hijab ɗin nan, ba zasu bari ki wuce da ita haka ba, zasu ga kaman exam malpractics zakiyi da ita, bana son ƙauyanci" ya faɗa yana mai ƙara sowa ta inda nake tsaye
ÆŠan waiwaya wa nayi ina mai kallon shi cikin É—an marairaice fuskar da babu komai samanta, daga hoda sai kwallo da lip balm,
Miƙoman hannu yayi alamar in cire na bashi.
Soma kiciniyar cire wa nake yi Naji yana faÉ—in "ai bake kaÉ—ai bace a haka, haka dokar makarantar take, su a kamarantar su ake rubuta jamb É—in, student É—insu basa zuwa ko ina, kiyi maza ki shiga bana so a samu wata matsala"
Miƙa mashi na yi, gami da juyawa na fara taka wa a hankali zuwa ga shiga makarantar da duk na tsargu, gani nake kaman kowa ni yake kallo, Amman a zahiri ba haka bane, wasu ɗaliban ma harda ɗan gudun su, zuwa cikin makarantar hankalin su duk baya jikin su, tafiya nake yi ina ɗan ƙara jan skirt ɗina ƙasa har ga Allah a takure nake.
Daf da zan shiga makarantar ne na ɗan juyo haka, yana nan dai tsaye inda na bar shi, ni yake bi da kallo duk wani taku na ɗaya akan idanun shi suke, wuf na faɗa cikin gate ɗin gami da ƙara ɗaga ƙafa cikin sauri na doshi babban hal ɗin makarantar da naga kowa na nufa.
Ɗan jingina bayan shi yayi da jikin motar yana mai sauke ajiyar zuciya, tabbas sai yanzu ne yake na damar menene ya zaɓa mata wannan makarantar da uniform ɗinta suke haka? Kayan sun matse ta da yawa, yanzu a haka kowa zai ta kallon ta? Amman baya da yanda zai yi, makarantar ita ce makaranta mafi girma da kyau da ƙayatuwa a duk faɗin garin na Abuja, makaranta ce da aka yi recomending akan irin ƙoƙarin ta da hazaƙarta, ɗaliban makarantar basa faɗuwa exam duk wahalar ta, saboda suna follow-up da kuma jajircewa wajen ganin ɗaliban nasu sun kai ga gaci.
A hankali ya shiga taka wa har zuwa ga motar murfin motar ya buÉ—e gami da zama, tada motar yayi yana mai ajiye hijab É—in kujerar da shan É—in ta tashi.
Ya rasa dalilin shi na damuwa da halin da yaga suhan ɗin ta shiga na tsarguwa da kanta, ya san tarbiyyar ta ce haka, shi in ba yau ba ma zai iya cewa bai taɓa ganin ta da ko gyale ba ma balle kayan da suka matse ta haka ba, ɗan runtse idanun shi yayi yana buɗewa gami da ɗan bugun sitiyarin motar, ji yake kaman yaje ya maida mata hijabin ta ta ɗora saman waccen da ita da babu duk ɗaya ne.
A haka har ya isa office ɗin nashi tinanin bai bar shi ba, yaji duk ya rasa sukuni, bai san menene haka ya tsaya ya to kare mashi zuciya da maƙoshi haka ba.
To ko bayan ya shiga office ɗin kasa taɓuka komai yayi, sai jujjuya kujera yake yi idanun shi a rufe ya ɗaga kanshi sama, duk da ya rasa tinanin da zai yi, ƴar ƙaramar ajiyar zuciya yayi yana mai jawo wayar shi ya latsa kiran lambar Bilal domin yaji ya shirye shirye nashi bikin ke tafiya.
***************
Cikin ikon Allah, ba zance banji wahalar exam ɗin ba, saidai zan iya cewa ta zo man Da sauƙi ba kaman yanda na zata ba, karatun da nayi ya matuƙar taimaka mani, inda na ɗan samu matsala kaɗai cumputer ɗin da ban san yanda ake amfani da ita ba, inda Allah ya taimake ni an nunnuna mana yanda duk zamuyi, sai gashi kafin lokaci ya cika ma na gama duka, ina dai ta addu'a cikin zuciya, saboda Jarabawa dace ce, ba ƙoƙarin ka ko hazaƙarka ke baka ba, iko ne kawai na Allah.
Bayan mun futo ne, ina jingine jikin bangon hall ɗin tsaye rataye da ƴar jikka ta, wayata tayi tsuwwa. Ina ɗauko wa naga Afnan ce, cikin hanzari na amsa, gaisa wa muka yi cikin mutu ta juna da ƙaunar juna ta shiga zaulaya ta, tana ceman ya exam ta kira yayan ta yace mata ina cikin exam, kuma ga lokacin da zan fito shine tace bari ta kira taji ya wasa kwalwa, cikin dariya nace mata "haba ai wlh ba wani wasa kwalwa, komai masha Allah, sai fatan fitowar ta lafiya" itama dariya tayi ta ɗaya ɓangaren tana mai cewa "kai aunty na, ko dai yayan nawa ya samo maki satar amsa ne? Baya so ki wahalar mashi da kanki?
ÆŠan sororo nayi ina mai sauraren ta, to me hakan ke nufi? Me maganar tata take nufi ne? ÆŠan murmushi nayi ina cewa" Haba afnan wace irin magana kike haka? Kaman ya in wahalar mashi da kaina? Wai tsaya ma yaushe ne na zama auntyn taki?
Cikin kwalalo idanu afnan ɗin tace "wai sorry" ɗif ta datse kiran tana mai maida numfashi da ajiyar zuciya ta maida kallon ta ga aunty feena dake zaune tana tsefe ma Nasreem kai, murmushi aunty feenar tayi nata cewa "Ah to uwar surutu, ina tinanin fa yarinyar da mahaifiyar ta basu san menene ke faruwa ba a gidan nan, gashi ke kin kira zaki gwangwaɗa mata, ke da Al'ameen ai, indai yaji katoɓarar da kika aikata mashi" cikin ƴar shagwaba irin wacce suka saba ta shiga diddire ƙafafu, Allah kuwa aunty ba zai ji ba, saidai in kece kika faɗa mashi, kinga ita suhan ba surutu ke gareta ba, hasali ma ban taɓa ganin suna magana da yaya ba, wallahi shaf na manta ance a bar maganar na ɗauka Mom ta amince ne"