← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 56

Sashe 22

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan karin, Al'ameen ɗin ne ya kalli Bilal ɗin ido cikin ido sannan ya shiga faɗin "Oho mata, ita wannan haka take, ban cika kula da al'amurran ta ba, Amman zan iya ce maka irin tarbiyyar da mahaifiyar tata ta bata kenan, bata saki jiki da kowa in ba mahaifiyar tata ba, hakan ya samo asali ne daga wariya da ƙyara daga sauran ƴan uwan nasu ma'aikata" ya faɗa yana mai ɗan taɓe bakin shi, sannan ya juya ya gyara kwanciyar shi gami da karanta addu'ar barci.

Ganin haka da Bilal ɗin yayi, ya san ba zai ƙara tankawa ba kenan ya kuma wuce da maganar kenan.

Shiru yayi shima yana mai hangen bayan kan Al'ameen É—in da suma ta kwanta mashi luf abinshi, abun ka da farar fata sai yayi kaman wani ba'indiye, ta cikin haske dumlight É—in da suka sanya mai É—an duhu sosai kalar shuÉ—iya.

Shiru ɗakin yayi in banda ac dake aikin ta a hankali a hankali, sai kuma Bilal ɗin dake ta saƙa da warwara, idanun shi ƙyam akan murɗaɗɗen abokin nashi, da tini bacci yayi awon gaba dashi, yana ta sauke numfashi a hankali, a hankali.

Shima dai a haka baccin ya kwashe shi, washe gari duk suka haÉ—u a nan cikin gidan Alhaji Isuhun da duka nan suke karyawa da iyalan Æ´aÆ´an nasu guda biyu watau Yaya Auwalu da Alhaji Mustapha Dambulan

Sai da kowa ya gama karyawa, har da Bilal ɗin kuwa sannan aka koma babban falon domin sake sabuwar gaisuwa ga iyayen nasu guda biyu da kuma sanya lokacin da za'a zauna meeting da ƙarfe biyu rana, wannan karo harda ƴan uwan nasu mata,watau Gwaggo Aisha da kuma Gwaggo Fatima dake aure nan cikin kankiya da kuma kannen su mata watau Hassana da Hussaina suma duk an masu waya, saboda irin wannan taron babban taro ne da yake ƙara haɗin zumunci da ɗabbaƙa shi, hatta da yaran su matan an kikkira su a waya, tinda ƴan uwan nasu duk sun zo har da waɗanda ke ma'aura ya kamata kowa yazo a gana a kuma ƙara sanin juna.

To sai mu ce Allah yasa ayi taro lafiya a kuma tashi lafiya Alhaji Isuhu family

~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:24 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~14~*

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Zama ne da akan yi duk lokacin da É—aukacin family É—in suke nan, wannan ma karon kowa ya hallara, Alhaji Isuhu ne tare da Æ´aÆ´an shi maza suka fara zama, sun tattauna abubuwa masu mihimmanci wanda mafi akasari Yaya Auwalun ne ke zartar da hukuncin, kasancewar shi babba namiji, sai da suka kammala tattauna war su sannan aka umurci kowa da ya hallara a babban falon sashen Alhaji Isuhun, kowa ya zazzauna Amman banda gogan naku, hakan ce ta sanya Alhaji mustapha É—aukar wayar shi ya kirawo shi tare da umurtar shi da yazo sashen iyayen nasu.

Taro ne da aka buɗe da addu'a bayan zuwan Yaya Ameen ɗin, inda aka gabatar da gaishe gaishe da kuma ƙara sani ga juna duk da dai kowa ya riga ya san kowa.

Alhaji Auwalu ne ya fara da godiya ga Allah subhanahu wa ta'ala, sannan ya ɗora da faɗin, "Ba dan komai muka tara ku anan ba sai dan kuji maƙasudin tara ku anan da hukumci da tsarin da muka zartar, kasancewar kowa ya san ba shawara muke tambayar ku ba, amman dai hakan ba zai hana mu jin naku ra'ayin ba, idan mun gama sanar daku Abunda muka tattauna da shi Alhaji gashi nan" ya faɗa yana mai nuna farin tsohon da yake zaune bisa kujera irin ta alfarma yana ta faman murmusawa da kallon jikokin nashi har ma da surukkan nashi guda biyu watau Hajiya Kubra da Mama Zainab dake zaune ɓangare guda, duk da kasancewar Mama Zainab ɗin babba ga hajiya Kubran, Amman kai kace ita ce babba, saboda jin daɗin da gogewar kai harma da suturar ba ɗaya ba.

"kai Aliyu, munsan buƙatar ka na anema maka auren Khadeeja, wanda mun yanke hukuncin nan ba da jimawa ba zamu je a nema maka auren" ya faɗa yana mai kallon babban ɗanɗan nashi namiji da ya sunkuyar da kai yana ɗan murmusawa, Yaya Auwalun ne ya cigaba da faɗin "sannan ku kuma Saudatu, da Nihal sai Hafsat (Ɗiya ga yaya Auwalun ta uku domin ta biyun mai suna Amina itama tayi aure har ma da ƴaƴan ta guda biyu, kuma itama tana zaune ne a wurin) kuma muna da buƙatar ku turo mana da manema aurenku zuwa gobe ko jibi domin mu tattauna dasu kuma mu basu izini" gabaki ɗaya sunkuyar da kai sukayi yayin da saudat ta zumɓuro baki ita fa bata shirya yin aure yanzu ba, dama Nihal ɗince mai saurayi, sannan ita hafsat dama tana da maneman ta masha Allah kasancewar ta nutsattsiyar yarinya ga kunya da girmama na gaba da ita, kyakkyawa ce masha Allah, domin su Nihal ɗin babu abin da zasu nuna mata.

Dakatawa yayi yana murmusawa tare da cewa idan Alhaji mustapha yana da magana yayi yana sauraren shi, to shi É—inma cewa yayi babu sauran wani abu sai dai ko a cikin yayyen nasu mata idan da mai magana.

Goggo Aisha ce ta shigo da buƙatar tallafin karatun ƴaƴan nata maza da suka gama makarantar secondry yayin da Goggo Fatima tace ita kam babu abin da take buƙata, duk buƙatocin nata ƙannen nata sun gama mata komai sai Sam barka, tau suma ɗin dai haka Aunty Hassan a da hussainar babu abin da suka buƙata, sai godiya da suka shiga yi.

Yayin da aka tambayi su Hajiya Kubran dake Zaune gefe, Hajiya Zainab dai cewa tayi babu komai, yayin da Hajiya Kubra ta buɗe baki cikin isa, ta shiga faɗin "Maganar Al'ameen fa? Banji kunce komai ba dangane dashi, shima ya kamata ya fiddo mata cikin wannan lokacin, in ba haka ba zan zaɓo mashi da kaina cikin family ɗin ƴan uwa na ko kuma cikin ƴaƴan ƙawaye na" Alhaji mustapha ne ya shiga kallon ta cikin ɗaure fuska yayin da Yaya Auwalun ya shiga girgiza kai a hankali yana ɗan murmushi, kasancewar duk sun san halin ta ne ya sanya abun bai basu mamaki ba.

Shi kau Ya Ameen bazan iya fasalta yana yin da ya shiga ba, "wai me yasanya Mahaifiyar tashi take haka ne? Me yasanya idan zata yi abu bata tinani akai? Me yasanya, me ya sanya?" haka ya shiga furta wa cikin zuciyar shi da take ta kai komo, bugun zuciyar shi ya ƙaru, idan ko haka ne zai rufe bakin ta, zai bata mamaki, yana so ya cenza mata tinani, yana so ya cenza mata kallon da take yi ma kowa na bai isa ba sai ita kawai, yana son Mahaifiyar shi, ba zai so yana kallon ta tana tafiya bisa turbar da ba ita bace kuma ya sanya mata idanu ba.

Hajiya zuwaira ce ta sanya baki a karo na farko, tin zaman da aka fara kusan awa guda kenan da suka shuɗe, ita ɗin ma murmusawa tayi, yayin da ta kalli Hajiya Kubran ta shiga faɗin "Ke kau Kubura me yasanya kika sanya ma wannan mijin nawa ido ne wai? Mai mata kaman ni har a ce ya fiddo da aboki yar rayuwa, ko ba haka ba ma ai shi Ameenun baki ga yanda yake ba, wannan ma mai tsoron matan? Ina ce ma ni ban taɓa ganin ya tsaya kula ƴan mata ba ko jin labari" kowa sai da ya murmusa banda Hajiya Kubran da take zaune hakim ce gefe guda yayin da Hajiya Zainab mata ga yaya Auwalun ta ɗora da faɗin " wannan gaskiya ne Mama, kamata yayi a bashi lokaci ya fiddo a tsanake, kaman yanda Aleeyu yayi, gashinan abokanan shi har da masu mata biyu Amman shi sai yanzu ya samu ya lalubo, zaɓen aboki yar rayuwa ai abune mai wahala sai an bincika sosai.

Kowa yayi na'am da wannan maganar yayin da Hajiya Kubran ta Sake ɗaure fuska tana faɗin "Akwai ɗiyar Abokin wasa na Sen. Abubakar ɗan Malam, yarinya ce mai natsuwa, duk abin da ake buƙata mace da shi itama tana dashi, ta fito daga babban gida babban Family na yardar mashi yaje ya neme ta ni zan shige mashi gaba wajen aiwatar da komai" toh fa, Hajiya Kubra kenan, ita a ganin ta dukiyar ta arziƙin ta ya kai ta aiwatar da duk abin da take so, ta manta itama a ƙarƙashin wani take.

Wannan karon cikin ɗan zafin rai Alhaji Mustapha ya shiga faɗin "Babu wanda zai sanya in ma yaro na auren haɗi, bamu taso munga ana yi mana shi ba anan gidan, kuma duk mu muka zaɓo ku, haka su Yaya Aisha duk su suka kawo mazajen aure, in ma haɗin ne ai muna da yaran da suka taso gaban mu a cikin family ɗin gasu nan duk sun isa aure, Meyasa bamu ce ya zaɓa a ciki ba?"
Chapter 22 · 0% Book details