← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 56

Sashe 37

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~22~*

*Wannan Page ɗin sadaukar wa ne ga ɗaukacin WRITERS ɗin Golden Pen, Allah ya ƙara mana ɗauka ka, basira, da zaƙin hannu, Allah kuma ya bamu ikon rubuta Abunda zai amfani Al'umma baki ɗaya. AMEEN*

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Ban dena ja da baya ba ina yarfe hannu, haka shima bai dena matsowa inda nake ba, har saida na dangane da bangon ɗakin, ba arziƙi na ja tsaya ina ta ƙwalalo idanuwa kaman uwar da yaranta suka ɓata.

Daf dani ya ja ya tsaya, har ina iya shaƙo ƙamshi turaren da ke jikin shi, saurin sadda kaina ƙasa nayi, yanda ƙjrji na ke bugawa, har ina jin kaman zuciya ta zata tsago ƙirjina ta fito tsabar yanda take bugawa.

Bai ce man ƙala ba, nima bance mashi ba, sai ma nake ganin dukkan abunda zan faɗa don kare kaina ba yarda zai yi ba, tinda tin farko ya nuna man baya buƙatar hakan.

Hannun shi ya sanya a aljihu wandon nashi gami da ɗauko waren ɗan kunnen nawa da yake ta walwali cikin hasken farin ƙwan dake ɗakin yana ta sheƙi da walwali.

Miƙo man yayi, kaman wadda ƙwai ya fashe mawa a ciki na sanya hannu gami da amsa, duk da yanda zuciya ta ke bugawa, hakan bai sanya murna da farin cikin da nake ciki sun ɓoyu ba daga fuska ta, murmushi na saki, har saida siririyar wushirya ta ta bayyana, fararen haƙora na da suke jere reras ya bi da kallo, lokaci guda yana mai ɗauke idanun shi gami da juyawa yana nufar ƙofar fita cikin salon takun tafiyar shi.

Kaman ance ya tsaya, ya kuwa ja ya tsaya, gami da juyowa, Allah sarki, ta kuwa ƙure warin ɗan kunnen wanda yake cikin tafin hannun ta da idanu, ga dukkan alamu dai taji daɗin ganin abun kunnen, kuma ko babu komai ya ameen ya gane dalilin bincika mashi ɗaki da ya tadda ta take yi.

"Sai ki gyara man É—aki na tsaf, kaman yanda kika tadda shi" Abunda ya faÉ—a kenan gami da juyawa ya idasa ficewa zuwa falon.

Da kallo na bishi, zuciya ta na raya man, wai in gyara mashi kaman yanda na tadda, kaman ba nice na gyara ɗin ba😠

Cikin sanɗa ma shiga bin shi a baya, bayan na maƙala ɗan kunnen nawa a mazaunin shi watau kunne na.

Leƙawa nayi falon a hankali, hango shi nayi zaune bisa kujera mai cin mutum biyu, gaban shi da laptop yana ƙoƙarin kunna wa, ga dukkan alamu aiki zai yi cikin ta.

Rufe ɗakin nayi, gami da murza mashi key, a hankali ya ɗago jin ƙarar sanya key a ƙofar, ɗan murmushi ya saki na gefen baki, yana girgiza kai bayan ya kauda idanun shi daga ƙofar ɗakin zuwa laptop ɗin.

Nikau dalili na nayin hakan, ba zan juri in gyara mashi É—aki harda gado ba, alhali yana cikin sashen kuma mu biyu da gani sai shi, ina ai ba zai yuwu ba.

Gyaran da nayi ma yafi na farko wanda nayi, saboda wannan karon ɗakin ya samu canje canje da nayi, hatta gadon na canza mashi mazauni, da ba a saitin taga yake ba, gashi muna yanayi na zafi, wannan ce ta sanya na maida kan gadon saitin taga, yanda fresh air zata ringa shigowa, zai samu sauƙi kunna ac ɗin da yake yi, wanda kowa ya sani tana da illa ga lafiya ɗan adam.

Ina gamawa, ban jira komai ba, na fito da niyyar ficewa, yanzun ma ban tanka mashi ba, shima bai ko ɗago ya kalle ni ba, duk da yaga gittawa ta, Amman ƴan maganar basa kusa, koma suna kusa me zai ce mata? Yarinyar da ƙiri ƙiri ya nuna bata yadda da shi ba a zahiri.

Ina daf da ficewa na tsinkayi muryar shi yana cewa "Ki kira man Hafsat in kin fita" & an waiwayowa nayi ina cewa to gami da idasa ficewa gabaki É—aya a part É—in.

Fita ta ne yayi daidai da fitowar maree daga babban sashen gidan, direct ɗakin Ya Ameen ɗin ta nufa, Nikau da idanu na shiga binta, wasu irin kaya ne ta sanya matsattsu, dinkin ya kama ta sosai, bayan nan kau an wawashe kusan rabi, haka ma gaban rigar, kai abun dai babu kyaun gani, ɗan gyale ne ta yafa wanda dashi gara babu, takalman ta masu tsinci ne, wannan tasanya duk takon da tayi sai ya bada sauti "ƙwas"

Itama bata yi sanya ba ta bini da kallo, mamaki fal a cikin ranta, me naje yowa sashen Yayan ne? Gashi kuma ni kaɗai ta gani, wani wulaƙantaccen kallo ta shiga jefo man, tanayi tana tauna chewin gum tana ƙas ƙas dashi tana farfara idanu tana wata yatsina, ni wallahi sai ma ta bani dariya.

Wucewa nayi ina mai waiwaye ta, lallai kuwa ɗakin ta ke da niyyar shiga, Amman taja ta tsaya tana ƙara gyara zaman riga da skirt ɗin a jikin ta, ikon Allah, yau ina kallon abu, to me zata je yowa sashen nashi a haka?

Har ga Allah dai na san duk da ba'a shedar É—an mutun, na san shi ya Ameen É—in bai da wannan É—abi'ar, kuma ma dai na san ko neman matan zai yi, ba zai tsaya ma wannan ballagazar ba, wanda ko jirin kirki da kyaun kirki bata da.

Ban aune ba naga har na isa ɗakin namu, sallama nayi na shiga, naki yi sa'a umman tawa bata nan ta fita, Hafsat kawai na tadda a zaune tana ta faman yin waya da wanda zata aura, murmushi tayi gami da cewa "Laa gata nan ma muna maganar ta" miƙoman wayar tayi tana faɗin "gata ku gaisa ma"

Amsa nayi ina mai ɗan harararta cikin wasa, alamar ban shirya ba haka kawai ta dunguno man wayar tana dariya shaƙiyyanci.

Ba laifi mun gaisa cikin raha, harda ɗan wasa haka, yana tambaya ta "ya shirye shirye biki, tace yau zaku fara ko?" da eah na bishi don bansan ta kan zancen ba, muka yi sallama yake faɗa man ya kusa shigowa ƙasar zai zo mu ƙara tattauna wa.

Itama ɗin sallama tayi dashi, bayan na miƙa mata, ta ƙagara taji ina na samo ɗan kunnen da ta hanga a kunne na bayan na cire hijab ɗin dake wuya na.

Aikau na kwashe komai na faɗa mata, na ƙara she da faɗa mata saƙon na yayan namu.

Me ko zata yi in ba dariya ba, nan ta shiga zaulaya ta, ta miƙe tana cewa bari inje inji kiran da yayan namu yake yi mani, in kaji kiran shi ai samu ne wallahi, kiyi maza ki shirya lokacin fitar tamu ya ƙarato.

Sallama tayi cikin shaƙaƙƙiyar murya, ga dukkan alamu ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba wajen siranta muryar tata, bai ko ɗago ya kalle ta ba, shi duk a zaton shi hafsat ce, gashi kuma yaga ana nufo inda yake zaune ba tare da ɗar ko wani shayi ba, tin daga ƙafafun nata yake bi da kallo, sun kuwa sha mai sunyi da bare da bare abun su🤣🤣 sai sheƙi suke yi cikin man da ta shafa.

Aiko cikin hanzari ya ɗago yana bin sauran jikin nata da kallo, har zuwa kan fuskar ta, runtse idanu yayi gami da juyar da kanshi, ko babu komai dai yayi mugun gani, domin kuwa kusan rabin nonuwan ta a waje suke, show me your breast kenan🤔

"Keeee" ya miƙe a fusace yana mai daka mata tsawa, sannan ya ɗora da faɗin "me ya kawo ki nan? Wani abu kike buƙata? Ko wani ne ya kira ki? Ya faɗa cikin fushi da matuƙar ɓacin rai.

Rau-rau da idanu tayi alamar tausayi, wanda hakan da tayi ne ya ƙara ƙular dashi ma, sannan ta shiga faɗin" Suhan ce ta ce inzo wai kana nema na" ta faɗa cikin yanko ƙarya tana mai lailaya mashi.

"Get out from here" ya faɗa yana nuna mata ƙofar fita, ba ke nace ta kira mani ba, Hafsat nace, ke me zan maki in nace ta kira mani ke? Ko ni kike ma aiki ne?" ya faɗa yana mai jefo mata tambaya kaman zai make ta.

Girgiza mashi kai ta shiga yi, har ga Allah jikin ta yayi sanyi, domin ko kafin tazo nan saida ta shisshirya, hatta wankan da tayi da ruwan magani tayi shi, tayi matse matse da dama, domin tana tinanin Al'ameen É—in kanwan lasa ne, da har zata jawo hankali shi ta ruwan sanyi haka.

"A'a yaya, kayi haƙuri" ta faɗa kaman wata baiwar Allah, sannan ta juya tana wata irin karairaya har zuwa ficewa ta a ɗakin. Da kallo ya raka ta yana mai jan wani irin tsoki, baya son wulaƙanta mutum masalan ma wanda yake ƙarƙashin shi, Amman wannan dole ce ta sanya, in banda tana sakarya ma ya za'ayi ta yi irin wannan shigar sannan tazo gaban shi tana karairaya kaman zata faɗo mashi?

Sallamar Hafsat ɗin ce ta katse mashi dogon tinanin da ya shiga, zama yayi yana mai amsawa a hankali, rufe laptop ɗin yayi yana mai kurɓar ruwan tatattun ƴaƴan itatuwa masu sanyi da suke gaban shi yayi.

ÆŠan nesa da shi kaÉ—an ta samu ta zauna tana mai cewa "yaya gani Suhan tace kana nema na"

Da idanu ya bita yana mai ƙirƙiro murmushi dole cikin son kauda ɓacin rai da yake ciki, kenan waccen Yarinyar da ta fita yanzu ƙarya take ma Suhan da tace ita ce tace tazo yana neman ta?

Sake kauda tinanin yayi cikin ranshi, yana mai gyara zama ya fuskanci hafsat ɗin sosai, tambayar ta ya shiga yi shirye shirye da sauran abubuwan da take buƙata wanda bata idasa ba, yana gargaɗar ta da kiran nasu gidan domin neman wani abu, duk Abunda take so yana iya yi mata, ta tunkare shi kai tsaye kawai.
Chapter 37 · 0% Book details