← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 56

Sashe 48

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dad ya gyara zama gami da duban yaron nashi cikin soyayya, farin ciki fal a kan fuskar shi, sannan ya cigaba da cewa"Daga sarkin Katsina ne, haɗin guiwa da sauran sarakunan yankin namu na arewa, saboda yanda kake taimakon matasa ƴan uwanka da basu ayyukan yi, da taimaka masu da jari, da koya masu sana'oi, suka ga ya dace su girmama ka domin suma sauran matasan masu hannu da shuni suyi koyi da kai, sun yanke shawarar naɗa ka sarautar *yariman matasan arewa* kuma suna buƙatar daga yau zuwa gobe ka shirya komai domin a goben ne zasuyi maka naɗin bayan kammala ɗaurin aure, sannan kuma akwai hawan daba bayan kammala lunching ƙarfe biyar na yamma, da fatan zaku je ku shisshirya komai da ake da buƙata, sannan inaso ka aika manyan motoci guda biyu Katsina da zasu kwaso iyayen matar Aleeyu tin da safe idan Allah ya kai mana ranmu sai su juyo dasu, sannan ina so ka tabbatar da cewa an gama tsara komai na wurin da za'ayi lunching ɗin, akwai manyan mutane da zasu halarta harda shugaban ƙasa da sarkin musulmai, sannan muna da baƙi da zasu fara isowa a yau ɗinnan muna so a kama hotel mai kyau da zasu ji daɗin zama saboda mutanen waje ne"

Ya faɗa yana nazarin yaran nashi guda biyu da suke durƙushe gaban shi.

Fara'ar dake fuskar Bilal zamu iya cewa ma tafi ta kan fuskar Ya Ameen É—in, wannan ai wata É—auka ka ce da Allah yayi ma abokin nashi, ko ba komai dai ya san ayyukan Alkhairin da abokin nashi keyi ya zaga dukkan sassan nigeria ba ma arewa kaÉ—ai ba.

Cikin matuƙar jin daɗi suka shiga yin godiya basu fita ba saida dad ɗin nasu ya sallame su, shi fa Al'ameen mamaki kawai yake yi, a ina manyan ƙasar nasu suka san da duk abubuwan da yake yi, bai ƙara sarewa ba saida yaji ana sanarwar naɗin nashi da za'ayi a gobe idan Allah ya kai mu, a hanyar su ta komawa gida.

Sun isa gidan ne, sannan suka kira mudi driver gami da bashi makullin gare jin nasu dake cen gefen gidan gami da umurtar shi da ya fiddo manyan mitocin nan ƙirar homa bomber ya bada a wanke su ɗauki hanyar Katsinan a yanzu nan.

Ficewa suka sake yi daga gidan, saboda gidan ya ƙara ɗinkewa da jama'a ta ko'ina duk mata ne ga wasu manya manyan canofee da ake ta kakkafawa a harabar gidan gefe guda kuma wasu manyan speakers ne aka kakkafa kaman za'a tashi gidan.

"yanzu ina muka dosa ne? Ni fa wallahi duk ma na rasa ta ina zamu fara, kayan da nayi niyyar Sanyawa yanzu dole in cenza su in nemi masu babbar riga, duk yanda kuwa nake gudun ta saboda zafin nan da akeyi"

Al'ameen ya faɗa yana mai kallon Bilal ɗin da hankalin shi yake kan tuƙin da yake yi.

"Ni na san ta ina zamu fara, kai dai kayi kallo kawai" ya faÉ—a da Æ´ar Fara'ar shi, mamakin abun har yanzu bai gama sakinsu ba.

Da kallo ya shiga binnhanyar da suke bi har kawo lokacin da sukayi parking daidai wani tanƙamemen shago an rubuta *Your Choice* a jiki.

Je rawa sukayi har cikin shagon da aka ƙawata shi da farin glassai suna ta ɗaukar idanu.

Kaya ne maƙilbiya kallon ka, shaddoji ne ƴan ubansu an masu ɗinku a irin na manya, sun sha aiki matuƙa, kowacce tare da hula tangaras kalar zaren aikin shaddar, gefe guda kuma ƙananan kaya ne iya kallon ka da hange ka, yayin da sashe guda na shagon kuma bugaggun takalma ne kalar na sarakai da manyan masu kuɗi.

Miƙewa mai shagon yayi gami da tarar su cikin farin ciki, domin ya daɗe da sanin Al'ameen ɗin tin ba yanzu ba, hasali ma Al'ameen ɗin shine ya fara bashi jari a rayuwar shi, bayan ya gama makarantar design da Al'ameen ɗin ya buɗe tin yana ƙasar america.

Gaishesu ya shiga yi cikin girmamawa, basu ɓata lokaci ba Bilal ɗin ya faɗa mashi me yake tafe dasu, da taimakon shi suka zaɓi kayan da suke so.

Shaddoji ne farare ƙal suka ɗ auka, duk da cewa ta Al'ameen tafi haɗuwa, sai ƙamshi take yi da walwali, anyi mata aiki da riyal blue ɗin zare, yayin da hular ma take kalar royal blue ɗin, sai takalmin shi irin na sarauta mai half cover da lanƙwasa ya sha adon farare duwatsu sai ɗaukar idanu yake yi.

Shima Bilal ɗin ya zaɓi masu kyau, saidai shi kuma kalar nashi farar shadda ce da aikin Brown, hakan ne ya sanya shi ɗaukar takalmi Brown masu matuƙar kyau da tsari, sai Abie da suka ɗaukar ma kalar sararin samaniya da aikin bula mai ruwan omo.

Sashen masu haɗewa aka miƙa kayan, daidai jikin su aka auna sannan aka haɗe, Al'ameen ɗinne mai cewa a maida mashi babbar rigar fitted yayin da Bilal ɗin ke cewa a ƙyale shi ayi mashi yanda zata yi kyau.

Su sha mamaki matuƙa lokacin da suka zo biyan kuɗin yace ba zai amsa ba, ba yanda ba suyi ba yace Sam Allah ya sauwaƙe ya amshi kuɗin su, ganin ba zasu yarda ba ya sanya shi faɗin bari ya gaya masu dalilin shi na ƙin amsar kuɗin nasu.

Tiryan Tiryan ya basu labarin Alkhairin da Al'ameen ɗin yayi mashi, sannan ya ƙara da faɗin "Haba yallaɓai, ni wane irin butulu ne kuwa da har zan iya amsar kuɗin kaya a hannun ka? Bayan dukkan shagon nan da yanda na zama a rayuwa kai ne sila, yanzu haka ƙanena yana aiki a kamfanin ka na sarrafa hatsi a Lagos, dama ban daɗe da gama sauraren radio ba, Naji irin gagarumin naɗin da za'ayi maka a goben idan Allah ya kai mu, bansan zaka zo ba i da har gida zan kawo maka da kaina, Amman ko yanzu bata ɓaci ba, insha Allah kuwa zan halarta harda iyali na baki ɗaya, Mungode Mungode Allah ya shirya maka zuri'abyasa ka gama da iyayen ka lafiya"

Ko ba komai wannan kaɗai ya isa ya ƙara sanya shi farin ciki, ashe dai shi alkhairi ko ya yake baya da kaɗan kuma daɗi ke gareshi, gashi Alkhairin da yayi ma mata san a lokacin da aka yaye su, har shi ya girbi abinda ya shuka.

Sun mashi godiya matuƙa, yayin da Al'ameen ɗin ya bashi ƙaton shi, gami da cewa bayan hidima ta kwaranye ya neme shi su sake gaisa wa sosai, har bakin motar su ya raka su, yana mai ɗaga masu hannu har suka fice daga plazar, sannan ya juya da maɗaukakin farin ciki, dama tini ya daɗe yana addu' ar Allah ya haɗa shi da Al'ameen ɗin ko a hanya ne ya ƙara mashi godiya, domin ya san ba lallai bane in ya neme shi ya same shi.

Daganan suka zarce kasuwa, inda suka shiga neman kayan kwalliyar doki, da ƙyar suka samu, domin har Al'ameen ya gaji har ya fara faɗin su koma gida hakanan shi fa ya fara gajiya da wannan wahalar sannan suna da sauran ayyukan da zasu aiwatar da yawa kafin zuwan daren.

Kalar kayansu kowa ya ɗauka, sun kwaso kayan kwalliya doki sosai, bayan da Bilal ɗin ya tambayi abokin nashi dokin da zai hau, "Farar Goɗiyar" ya bashi amsa a taƙaice cikin gajiyawa.

ÆŠan murmushi yayi shi kuma yana faÉ—in "sai in hau gwaska ni, shi kuma Abie ya hau kule"

Bai tanka mashi ba har suka iso gidan, Barde mai tsaron barar suka kira gami da bashi kayan dokin suna faÉ—in ya shirya su goben bayan gama cin abincin É—aurin auren, sannan suka faÉ—a mashi dawaman da zasuyi amfani dasu a cikin dawakan dake gidan.

Saida suka ajiye kayan sannan suka watsa ruwa gami da cenza kayan jikin su zuwa ƙananan kaya sannan suka fice daga cikin gidan bayan sun ajiye motar suka cenza wata.

Ganin yau bamu da aikin komai, ya sanya mu kwanciya muka huta bayan mun ware duk Abunda muka san zamuyi amfani dashi gobe, to bamu da yawa dama, mu bakwai ne harda amaryar sai mai kwalliyar mu da suka taho ta ita tinda ga Katsinan yasa muka kama mu takwas, ɗaki ne tanƙameme da toilet, bamu takura ba sosai komai namu tsaf yake, kaka zuwaira kaɗai muka fita muka gaida yau sai hafsat ɗin da taje Sashen mamanta, cen ta tadda ummata har take tambayar ta ina ina? Take ce mata ina ɗaki lafiya ta lau.

Washegari tin da asubar fari aka farka kusan ince dukka gidan, bayan gama sallah ne aka shiga É—ora Abunda za'a karya, tinda dugu-dugu aka yi break fast, sai kuma aka shiga hidima wanka, masu girka abinci nayi masu sake shirya harabar gida inda za'ayi zaman cin abinci nayi.

Mu dai bamu tashi ba sai wajen ƙarfe takwas na safe, mun tadda an kawo mana kayan karin mu, hakan yasa saida muka gama wanka duka sannan muka zauna zaman karyawa, amarya aka fara shirya mawa, mai kwalliya ta hau aikin ta na cakare amaryar, yayi da muku a muka hau gyara ɗakin namu tsaf.

Tin da aka fara hidimar biki banga afnan É—in taje sashen nasu ba, Sam ta fita harkar su kaman ba Æ´an uwanta ba, koda yake hali ya bambanta Shiyasa basa shiri, Amman da yake halin na Saudat da Nihal É—in É—aya ne gashi nan kansu a haÉ—e yake kaman Æ´an biyu, saidai wani lokacin aunty Feena kan aiko mata da Nasreem da Ayan masalan ma in tana wata hidimar da yake ita a É—aki ta ta sauka da yake cikin babban sashen gidan inda aka sauki Æ´an uwa Hajiya Kubran.

Dama tini ta maido kayan ta kaf da ta san zata yi amfani dasu cikin hidimar bikin.

Mun gama gyaran kenan muna hutawa wata ƴar matashiya budurwa tayi sallama, yaran dangin hajiya kubran ne, da suke cike da jiji da kai da tinƙahon su ɗin wasu ne, babu wanda ta gaida ta shiga faɗin "wacece suhan wai? To taje Aunty Saudat na kiranta a ɗakin nasu" tana gama faɗar haka ta fice daga ɗakin ba tare da ta tsaya jin me za'a faɗa ba.
Chapter 48 · 0% Book details