Sashe 53
Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har aka tafi kaisu kuma basu ma da alamar kukan saɓanin Hafsat da take ta kuka kuma tana laluben ina zata ga Suhan ɗin Amman ko alama bata hango mai kama da ita ba ma.
Abun ya ɓata mata rai matuƙa, har saida tayi ma Afnan magana, wadda ita Hafsat tace zata bi Alabasshi daga baya zata je gidan ƴan uwan nata.
Motoci ne aka zube bayan wadda su mazajen nasu suka kawo, kowacce amarya kake so kabi akwai mota free da zata kaika ta maido ka, duk da dai galibi wasu acen zasu kwana masalan ƙawayen amaren gashi kuma magariba ta doso ta kawo jiki.
Hatta Hajiya kubran saida taji wani iri rabuwa da yaran nata da zata yi duk da ta san cewa koda yaushe zata iya ganin su matuƙar suna ƙasar.
Bayan kammala komai ne da tafiyar dangin angunan da amaren su, aka hau gyaran gidan
Gidan ya rage Æ´an tsiraru sai masu aiki kaÉ—ai ya rage don sashen Al'ameen ma babu kowa duk an kammala hidimar biki sun wuce masu jirgin gobe kuma sun koma hotel É—in da suka sauka sai a goben zasu wuce.
Kafin isha'i fa tas an gyara ko ina an wanke ko ina, wannan karon harda umman tawa da Hajiya Zainab da wasu daga cikin DANGIN alhaji Mustaphan ne suka sanya hannu aka yi dasu.
Nikau ta ɓangare na, Naji matuƙar daɗin yau, kuma ina cikin farin ciki sosai duk da hayaniyar cen cikin gidan dan loud sleaker da ta dameni kusan ma ince hanani bacci tayi.
Ƴan latse latse na na cigaba da yi ni kaɗai a ɗaki, salla kawai ke ta dani. Ko abinci saidai na sha complax da yake ni ba mai yawan ciye ciye bace ba.
Ina cikin latse latse na a Internet naga alamar kaman an saki Jarabawar mu ta jamb da muka zana kwanaki.
Aikuwa cikin sa'a na tabbatas da gaskiyar Al'amari, wata yarinya da muka zauna kusa da kusa mai suna Samira, ita na kira gami da tambayar ta, cikin farin ciki take sanar dani cin Jarabawar tata, wai ashe ma tin numu'a aka saki ban sani ba.
Roƙonta nayi ko zata je ta dubo mani Alabasshi sai in bata kuɗin scratche card idan na fito, ba gardama ta amsa mani da zata duba mani ma yanzu ba sai na ɓata komai ba, saboda na taimake ta sau ba adadi a yayin zaman namu da ita, nan ne take faɗa man numb ta ce tayi loosing tin bayan canza wayar tata, waccen ta faɗi ne, jajanta mata nayi gami da cewa ina jiran ta sai na jita.
Ko awa uku cikakka ba'a yi ba ta kira ni, tin daga muryar ta na gane kan zancen, ko saurarena ma bata yi ba ta shiga yi mani murna, muryar ta cike take taf da farin ciki ga dukkan alamu har cikin zuciyar ta ne.
"Ƙawata kina da sa'a wallahi, zamana kusa dake ya taimake ni kwarai da gaske, ina alfahari da sanin ki a rayuwa ta, dad da mom duk sunce in miƙa saƙon godiyr su gareki takanas zasu zo har gida suyi ma su mom ɗinki godiya, kuma ina farin cikin sanar dake cewa duk school ɗinmu babu mai highest Mark kamarki insha Allah damun gama zan turo maki score ɗinki ki gani, zan kira ki insha Allah in mun tashi zuwa"
Ko jiran godiyar da zanyi mata batayi ba ta kashe wayar, mamaki na shiga yi wannan wace irin yarinya ce, dama ko da muka zauna kusa da Juna duk da lura da nayi ita ɗin ɗiyar wani ƙusan gwamnati ce, Sam hakan baisa ta ɗauki kanta wani abu ba, tana da yawan dariya ga sauƙin kai don itace ta fara yiman magana ma da roƙon in taimake ta don Allah, wannan ce ta sanya na taimaka mata da iya gaskiya ta tinda ita ta karya kanta ta roƙeni.
Ina hawa WhatsApp kuwa sai ga saƙon ta ya shigo wayar tawa, tayi screanshoot ta turo mani.
Ai bansan lokacin da na miƙe ina sujada ga Mahalicci na ba, Sam ƙarar loudspeaker ɗin bata damuna ta murna ta kawai nake yi, ni kaɗai ace naci 280 Abunda ma wasu 180 suke nema?
Lallai Allah buwayi gagara misali ne, kana taka Allah na tashi, Amman ni kaina in an faÉ—a man naci hakan zan iya musantawa ba don na gani ba. Saidai ada kam nayi mamaki da tace duk nafi kowa maki a duk faÉ—in makarantar da take cike taf da Æ´aÆ´an manya wanda su za'a ma iya bi masu kadin abun, ni kuma da bani da kowa sai Allah gashi ya kwato mani ba don na isa ba.
Kaman in tura mashi saƙo, sai kuma naga ai gani da kai yafi aike, nima tur a mashi nayi kaman yanda ta turo mani, naga ma kaman baya online, kusan ma ince rabon shi da hawa tin kwana biyu da suka wuce, to Allah yasa ma zai gani, gashi banda mail ɗinshi da sai in tura mashi ta cen na san zai fi saurin gani.
Na mashi uziri ne tinda na san yana Cikin hidima da jama'a gashi kuma Naji kaman ance bayada lafiya rannan a bakin Hajiya Kubra duk da Nidai banga alamun hakan ba a jiya da ya bani kunya a gaban mutane, har yanzu saƙon shi na jiya yana kai kawo acikin ƙwaƙwalwa ta, saidai na Gaza gano mai yake nufi duk kuwa da kwana laluben da nayi.
Umman tawa bata shigo sashen namu ba sai bayan isha'i bayan sun kammala gyara ko ina, a bakin ta ne naji tana cewa su Hajiya Zainab É—in gobe zasu wuce, tace wallahi gidan ta zata koma, saboda gidan duk ya isheta dan ma Æ´an kankiyar na nan ko ba komai tana jin É—uriyar waÉ—anda ta sani.
Sannan ta shiga yiman faɗan rakiyar Hafsat ɗin da banje nayi ba, tace tana jin Hafsat ɗin ta kira maman tasu tana mata tsogumi, kuma da gaskiyar ta "lallai kinyi laifi mamanta, ai kin san dai ba zan hana ki raka Hafsat ɗakin miji ba, yarinyar da ta fifita ki akan kowa na gidan nan har su ƴan uwan nata, to maza idan Allah ya kai mu kiyi sammakon shiryawa ki kira ta tayi maki kwatance kije mata ki gano ɗaki, Naji ance wucewa zasuyi ita da mijin cen ƙasar da yake aiki"
To nace mata, ni yau fa zuciya ta fes, duk da umman tawa ta lura, ita fa harma ta fara zargn anya yarinyar tata lafiya take kuwa, yau farin ciki gobe akasinshi? Kaman ba ita ce ba jiya ta kasa barci, yau kuma ta kasa shiga jama'a, koma dai miye zata zuba ido ta gani.
Ita Abunda ma yafi ɗaure mata kai, wasu ƴan maganganu da taji suna tashi daga bakin ƴan bikin masalan dangin Alhaji Mustaphan, har kaka zuwaira na cewa ita ce wannan? Lokacin da taje gaida ta dayi mata saida safe, sai gashi har tana bata saƙon gaisuwa zuwa wajen Suhan ɗin da tace mata yau bata ga giccinta ba, Allah dai yasa lafiya.
Dariya tayi, zuciyar ta cike da wasi-wasin Abunda taji ɗin, harda wata taji tana cewa "ance fa ƴar aikin gidan ce, amman sun naniƙe ma Al'ameen ɗin" gabanta ya tsananta faɗuwa kaddai tinanin ta ya kasance gaskiya, domin maganganun sunyi yawa kuma ta fahimci duk akan ƴar tata ce, tinda ba kowa ya san ita ɗin wacece ba a wurin suhan ɗin, Shiyasa wasu ma a gabanta suke gulmar.
Sheda mata nayi naci Jarabawa gami da nuna mata sakamakon a cikin wayata, tayi murna matuƙa Amman fa jikin ta yayi laƙwas, to ko shine dalilin da nima na kasa bacci jiya, kuma dai gashi taji ban tunkareta da maganar ba, saidai bata kyautata zaton haka ne, ƙila dai ƴan maganganu ne da gulmace gulmace irin na gidan biki da kuma jama'a
Hakan ce ta sanya ta share wa da batun, sai a take tambaya ta ko na tura ma Yayan namu? Amsa mata nayi da cewa na tura mashi saidai ƙila bai gani ba, tinda har yanzu bai ce komai ba.
A haka muka kwanta tinani fal zuciyar ummata yayin da ni kuma yau nasha bacci na harda saleɓa.
A sashen Hajiya kubran kuwa dangin ta kawai suka rage sai ita kanta, duk da wasu suna cen gidan yaran nata, suma kusan duk gobe zasu wuce, su Hajiya Sa'a ɗinne dai sai bayan isha'i suka tafi suna mai kwantar mata da hankalin cewa tasha kurumin ta, zata ga me zai faru bada jimawa ba, ta yarda da hakan tinda ta san hatsabibancin ƙawayen nata, wannan ce ma ta sanya suke juya akalar mazajen nasu, sun zama hotiho a cikin gidan, tini itama suka so su rinjayeta Amman ita tana tsoron shirka, kuma ko ba haka ba in Alhajin nata yaji zai yi mata bore ne sosai kuma ta san halin shi.
Bayan kammala shiryawarta ce da daddare ta doshi ɗakin mai gidan nata, so take taje ayi wacce za'ayi, tana so ayi ta ta ƙare su tattara su bar mata gidan ta, lallai tabbas ta yarda da maganar ta mama talatun cewa sun saba taɓa juna, in ba haka ba harma wani yafa mata gyale yake yi a bainar jama'a kuma yake kuranta matarshi, ko a gidan ubanwa ta zama matar tashi,? Ita zata ga yanda wannan al'amarin zai kaya, ko da kuwa zatabar duniyar ne ta kwammace indai ba zata haɗa jini da waɗancen maƙasƙantan Talakawan ba.
Saidai Takawa take yi zuwa sashen zuciyar ta taf da wasu wasin ko zai amshi maganar tata, bata ma ko tadda shi a sashen nashi ba, yana cen suna fira dasu kaka zuwaira da Alhaji Auwalu ya sauran Æ´an uwansu matan, suna jin damuwoyinsu, saidai Abunda hajiya Kubran bata sani ba kaka zuwaira tazo da maganar Al'ameen da Suhan É—in kuma duk kansu sunyi na'am da zancen, shi kuma shi da yaya Auwalun sunce abar lamarin a hannun su tukunna har sai sun kammala bincike.