← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 56

Sashe 27

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mudi ne ya shiga kallon ubangidan nashi ta gefen ido, dafe yake da kanshi dake sara mashi, kaman zai faÉ—o, gyaran murya yayi sannan ya shiga faÉ—in "ranka ya daÉ—e ko dai asibiti zamu fara zuwa ne?"
Girgiza mashi kai Al'Ameen ɗin ya shiga yi cikin rashin son Magana irin tashi, sannan ya buɗe baki daƙyar yana faɗin "Naje jiya mudi, na sha magani ma ai" ɗan guntun murmushi mudin yayi kasancewar ya san ubangidan nashi yanda yake tsoron asibiti da Allura tin ba yanzu ba, idan akwai Abunda ya tsana baifi ace za'ayi mashi Allura ba
Sake nisawa yayi cikin san gulma, "ummmmm yallaɓai nace, dama...... Uhm" ya faɗa yana mai ɗan haɗiye miyau cikin in-ina, "Ina jinka" ya tsinkayi muryar Al'Ameen ɗin yana faɗa a hankali.
"Yallaɓai ka gafarce ni, na san in bani ba, babu mai zarafin gaya maka wannan maganar, dama ina ta son samun dama, ayyuka ne da naga sun yi maka yawa ne yasa ban tinkare ka ba"
Ya isa mudi, kawai ka gaya man meke faruwa ne? " ya faÉ—a har yanzu idanun shi na a lumshe, hannun shi har yanzu yana a bisa kanshi, ya to kare shi da murfin motar
" Maganar su Suhana ce Yallaɓai, yarinyar nan da suke zaune ita da mahaifiyar ta, da aka dakatar dasu daga aikin gidan..... "
Cikin hanzari ya buɗe idanun shi, da suka kaɗa sukayi ɗan ja, hakan ce ta sanya suka ƙara shanye wa.
Kallon muÉ—i É—in yake yi cikin alama ta son jin meke faruwa dasu ne kuma?
Baice ƙala ba, hakan ce taba mudi tabbacin yana sauraren shi kenan
"Yanzu fa ba'a basu abinci a gidan nan, bama asan halin da suke ciki ba, gashi har yanzu lokacin albashi baiyi ba, nima a bakin saude mai dafa abincin naji, kasan su da ƙananan maganganu, kuma wai........

" Ya salam" ya furta cikin tsananin firgita, sauke hannun shi yayi bisa cinyoyin shi, hakan yayi daidai da ƙarasawar tasu bakin gate ɗin tanƙamemen company ɗin, mudi na shirin danna kan motar cikin gate ɗin da tini an riga an buɗe masu

"Mudi"

"Na'am Yallaɓai"

"Mu koma gida, muyi gaggawar komawa gida, me ya sanya baka faÉ—a man ba tini? Wanene ya bada wannan damar ta hana a basu abinci?"
Ya jefa ma mudi tambaya cikin ɓacin rai, "Magana nake yi maka mudi"
Cikin sanyin jiki, da nadamar gaya mashi zancen da yayi muɗi ya duƙar da kanshi ƙasa yana faɗin "Allah ya huci zuciyar ka yallaɓai, Amman Hajiya Babba ce ta hana tin waccen tafiyar da kuka yi, mu kuma muna tsoron gaya maka a samu matsala, hajiya ta gane daga bakin mu maganar ta fito"
Ya faÉ—a a sanyaye yana mai juya akalar motar zuwa inda suka fito.

"Haƙiƙanin gaskiya raina ya ɓaci mudi, menene laifin yarinyar da mahaifiyar ta? Aikin ai basu ne suka ce basa yi ba, wannan ɗaukar alhakin yayi yawa mudi, ya kamata ka dinga sanar dani abubuwan dake faruwa a gidan, saboda na kula munafunci yayi yawa a tsakanin mata ma'aikatan gidan nan"
Mudi ne ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya, yana faɗin "haka ne yallaɓai, Allah ya kyauta gaba, kayi haƙuri idan irin hakan ta ƙara faruwa, za'ayi gaggawar sanar da kai"
Shiru ne ya biyo baya cikin motar har zuwa lokacin da suka isa zuwa ga gidan, ko daidaita tsayuwar motar mudin baiyi ba, Al'Ameen ɗin ya ɓalle murfin motar, cikin sauri da azama ya isa zuwa ga sashen na masu aiki.
Cikin sallama yake ratsa sashen namu har zuwa bakin ƙofar ɗakin namu
Kwance nake nayi matashi da cinyar ummata da take zaune gefen katifa tana ƙara man karatun umdatul ahkam,
Nikam har ga Allah bana gane karatun Sam, yunwa ce kawai ke cina, ko motsin kirki na kasa yi, sauraren ta kawai nake ba tare da gane abunda take faÉ—i nake ba
Ita ɗin ma ƙarfin hali take, rabon da mu sanya abinci acikin cikin mu anfi sati, kullum saidai farau farau wanda tin jiya ma furar tamu ta ƙare
Sallamar shi ce ta dakatar damu daga karatun da mukeyi, banyi yunƙurin tashi ba, haka ma umman tawa bata matsa man ba, saboda ta san halin da nake ciki, ita ce ta yunƙura dakyal ta miƙe, bayan ta zame kaina daga saman tata cinyar.
Ɗakin da yake sakaye ta buɗe, da ɗan murmushi a kan fuskar ta, sannan ta shiga faɗin " a'ah Muhammad ne? Shigo mana, ka tsaya daga bakin ƙofa?"
Jiki a sanyaye ya sanya kai cikin ɗakin yayin da ummata ke shimfiɗa mashi yalwata ciyar dadduma a gefen ta katifar daga ƙasan tiles ɗin
Zama yayi yana mai gaida umman tawa, cikin natsuwa da girmamawa, haka itama umman tawa ta shiga amsawa da ɗan murmushi a kan fuskanta, kai daga gani ka san na yaƙe ne.
Nikau dakyal na É—aga na zauna gami da ja na jingina jikin bangon É—akin
"Ina kwana?" na faÉ—a a hankali, murya ta har bata fita sosai, kallona yayi cikin ido sosai yana mai amsawa, ya É—auke kanshi zuwa ga umman tawa.
"umma nazo ne in baki haƙuri, a bisa Abunda yake faruwa acikin gidan nan" ya nisa sannan ya ɗora da faɗin
"Sam bansan me ke wakana ba, sai yanzu ne mudi driver ke faÉ—a mani, umma menene ya sanya in irin haka ta faru ba kwa sanar dani da gaggawa? Idan an dakatar daku aiki, ai ba hakan yana nufin ba kwa cikin gidan bane, kuna nan kaman yanda kuke a da"
Ya tsagaita yana kallon umman tawa da kanta yake ɗan duƙe tana murmushi, dame zata saka ma Al'Ameen ɗin? Lallai yaro ne ɗan albarka da bai biyo halin mahaifiyar tashi ba Sam, murmusawa tayi ta shiga faɗin
"kai haba babu komai ai Al'Ameen, Hajiya bata yi komai ba, ni ban ma so muɗi ya faɗa maka maganar ba, bana so hakan ya kawo saɓani tsakanin ka da mahaifiyar ka Muhammad, don Allah ina so ka bar zancen nan, Mungode da alkhairi ka gare mu, Allah yasa ka gama da iyayen ka Lafiya, ka cigaba da yi masu biyayya, insha Allah zaka ga haske a rayuwarka"

Cikin jin daɗin addu'ar da umman tawa tayi mashi ya murmusa yana faɗin "Ameen Umma, nagode kwarai da addu'ar ki, ina mai ƙara baku haƙuri insha Allah komai yazo ƙarshe, ina so komai ya tsaya iya mu ne dake nan, ku siyo abubuwan buƙata da Abunda zakuyi girki iyakar naku, ku dinga cin abinci, duk abinda kuke buƙata kuma insha Allah ku tuntuɓeni kai tsaye ina tare daku. Kuyi haƙuri da halin mahaifiya ta, ina mata Addu'a Allah yasa ta gane gaskiya"

Miƙewa yayi tsaye gami da ajiye mana kuɗi masu yawa sosai, gami da complement card ɗinshi da yake ɗauke d suna da number tashi ta waya, sai kuma matsayi shi na MD Dambulan And CEO Dambulan Estate and More, sai Address ɗin Office ɗin nashi.
Murmushi umman tawa tayi tana mai Cewa "a'a Muhammad ba zamu karɓa ba gaskiya, abun yayi yawa, ai ana hidima damu, kwarai da gaske, Allah ya ƙara buɗi"
Ameen ya amsa yana daga tsaye, yake faɗin "Umma ki amsa Alkhairin da nayi maku, ba kowa ya sanya ni ba, ni na sanya kaina, ba roƙona kuma kuka yi ba, ni ne naga dacewar hakan, indai kin ɗauke ni ɗanɗan ki da kika haifa, ki amsa ki sanya man Albarka umma" yana gama faɗar haka ya juya ya fice cikin azama, har yanzu kan nashi na sara mashi matuƙa gaya
Da kallo nabi bayan shi har ya idasa ficewa gaba ɗaya daga ɗakin namu, ajiyar zuciya na sauke a hankali ina mai zamewa na kwanta lamo abubuwa da dama na man kai kawo cikin ƙwaƙwalwa game da wannan cukurkuɗaɗɗiyar rayuwa da muke yi.

Watau ni na ma rasa gane kan wannan mutum wallahi, Ya Ameen daban yake cikin mutane, kallona na maida kan uban damin kuÉ—in da ya ajiye, in ba gizo idanuna keyi man ba, raper ce ta Æ´an dubu É—aya har guda biyu, sai katinshi da ke bisa kuÉ—in ajiye,
Ba ɓala lokaci na mirgina ina mai wawurar kuɗin, na sanya hannu na zaro masu ɗan yawa ina Miƙewa kaman zan faɗi
Mun daɗe bamu da ko sisi a daƙin, me zamu tsaya jira tinda ga dama tazo ta iske mu har inda muke? Ban bi ta kan ummata ba, na zari hijab ɗina ina mai ɗaura wa bisa kayan dake jikina na atamfa ɗinkin doguwa riga bubu dake jikina
"Umma me zan fara siyo mana muci kafin mu nemi mafita?" na furta daga tsaye ga dukkan alamu ma ba sauraren cewa da take yi "ke suhan menene haka?" nake yi ba

ÆŠan murmushi tayi cikin tausaya war mahaifiya ga yaron ta ta shiga faÉ—in "Ko me kika nemo mana suhan zanci"
"To umma"
Na faɗa ina mai ficewa a daƙin, da zallan kallon tausayi ta bini dashi hawaye na biyo kuncin ta suna silalowa, "Allah yayi maki Albarka Hauwa'u ya ƙara shirya man ke, ya baki miji nagari, mai tausaya ma maraici ki, Allah ya ƙwato maki haƙƙin ki, ya kuma saka ma zalumcin da aka yi maki Ameen.
Ta daɗe zaune tana kuka tana share wa, gami da jera ma gudar tilon ɗiyar tata adduo'i na alkhairi da take fatan su bita ko bayan babu Rayuwar ta, sannan ta miƙe gami da kauda sauran ragowar kuɗin da kantin kada ƴan bani na iya su leƙo su gani, ɓalli ya tashi,
Chapter 27 · 0% Book details