← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 56

Sashe 12

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fashewa tayi da kuka gami da barin part ɗin ma gaba ɗaya, cikin gudu ta sashen yayan nata, ta tarad dashi dawowar shi kenan daga office, don ko takalma ma bai cire ba, faɗa mashi tayi cikin kuka mai fidda zallan ɓacin rai, cikin tashin hankali ya janyo ta gami da rungume ta ya shiga shafa mata baya, cikin sanyin shi mai haɗe da miskilanci yake faɗin " Is OK Lil, is OK, tell me what is happening ne, me ya same ki? Ina ke maki ciwo?" cikin wani sabon kukan ta zayyana mashi komai dake faruwa da Abunda mom ɗin tasu tayi, zaunar da ita yayi yana mai faɗin "is OK Afnan, kinsan halin mom sarai, no, bai ma kamata ki ɓata ma kanki rai ba hakanan, ko ni da kika ga ina gaya mata gaskiya ba saurarena take yi ba a times, sai muyi mata addu'a insha Allah zata gyara halin ta, kiyi shiru babu inda zaku koma sai hutun ku ya ƙare, Amman ina so kema ki ɗan ja baya da su, saboda kada ki dinga ja masu ɓacin rai wajen mom ɗin, kin gane ko? Gyaɗa mashi kai tayi tana mai faɗin "na gane Yaya, amman wlh maman Suhana ba lafiya gareta ba, ina gudun ɓacin rai ya sanya wani abu ya same ta, gashi na baro Phone ɗita ɗaki balle in kira su na basu haƙuri" ta ƙarashe faɗi tana goge kwalla da ke saman fuskanta kwance shaɓe shaɓe.

Is OK, kwanta nan ki huta,bari in shiga in watsa ruwa, sai in fito mu san abun yi,; ya faÉ—a mata haka ne don ya san rikicin Afnan, tana iya cewa zata kuma zuwa sashen nasu, kuma shi ba zai so hakan ba, gara ace ta É—an ja bayan dasu, ta bar mashi komai a hannun shi insha Allah shi zai daidaita komai.

Ni kau muna fita na kama umma ta muka nufi sashen namu, ina kallon mama Talatu murna fal cikin ranta, ga duk kan alamu ma laɓe tayi mana, domin taji Abunda Hajiyan zata faɗa, dama ita ta kai mata gulmar, kuma tayi ta zuzuta Hajiyar tana ƙara ma labarin gishiri, har cewa tayi Afnan ɗin sai ta kai ƙarfe sha biyu a ɗakinmu, kuma wai kuɗi take kashe mana sosai muke yi mata wayau, kuma yanzu na fara jin kaina daidai da su Nihal, saboda irin sutura da afnan ɗin wai ta siyo mun daga cen ƙasar wajen.

Lafiya muka isa ɗaki, duk da umman tawa na ƙoƙarin dannewa, tinda ta lura da kwallar da nake share wa akai, akai, Amman hakan bai hana ta kwantawa ba, ba tare da ta furta ko uffan ba, nima bazan tada maganar ba, saboda maganganu ne marasa daɗin ji, to kenan ma tana nufin ƙilan bama da asalin kenan?, me umma ta ke nufi da ɓoye mana salainmu da take yi? Me hakan ke nufi,?

Ganin ta samu barci ne, ya sanya nima komawa gefen ta na kwanta ƙasa, nayi matashi da katifar tamu, ina fata in ta farka komai ya wuce guri ta, ina fata kada ta tashi da :a in rai, domin kafin ta kwanta saida na ɓalli maganin ta na bata, na ƙudurce a raina zan nisanci Afnan ɗin, ba tare da na bari ta zargi wani abu ba, sai dai don mu tsira da mutumcin mu.

Afnan ɗin ce ta roƙi Yaya Al'ameen ɗin da ya ara mata wayarshi ta kirani, sai kuma ta manta bata riƙe number ɗin wayata ba, dole ta sanya ta haƙura da niyyar in mun haɗu cikin gida zata sake bamu haƙuri dangane da Abunda mom ɗin tata tayi mana.

Ta ɓangaren Hajiya kuwa, ko da ta tuntuɓi Aunty feena da maganar komawa, cewa tayi gaskiya ita ba yanzu ba, duka ma yaushe tazo? Kuma wannan dalilin ma bai kai Abunda za'a ce an koma saboda shi ba, ai tinda an ja kunnen Afnan ɗin shikenan bazata kuma maimaitawa ba,; su kuwa su Aunty saudat da sauran ma'aikatan gidan daɗi suka ji, wai ko ba komai an nesa ta ni da afnan, dama ƙaryar tawa ta Afnan ɗin ce (oh🤔 wai ko ma yaushe Afnan ɗin ta dawo, duka duka?)

Haka Ya Ameen ya ta lallaɓa Lovely sister ɗin tashi har ya samu sukayi kwana uku da faruwa Al'amari, dama Alhaji mustapha yayi tafiya, duk wainar da ake toyawa bai sani ba acikin gidan, wannan ce ta sanya bayan ya dawo Al'ameen ɗin ya kuduri niyyar tunkararshi da maganar karatun suhan ɗin, a ganin shi wannan ce kawai damar da zai yi amfani da ita wajen ceto suhan ɗin da mahaifiyarka a halin taskun da suke ciki.

**********************

Ƙarfe takwas daidai 08:00pm yayi sallama falon abban nashi, tafiya yake cikin salo shi na cikakke ɗa namiji, duk da yana da sanyi, wannan ce ta ƙara ƙawata tafiyar tashi, murmushi Alhaji mustaphan ke bi shi dashi, har ya ƙara so ya zauna kujerar dake kallon ta Alhaji mustaphan.

Ɗan sunkuyar da kai yayi alamar girmamawa tare da faɗin "ABBA barka da dare" miƙa mashi hannu Alhajin yayi suka yi musabaha, "barka ka dai Son, ya aiki ya jama'a?" Abban ya faɗa fuskar shi cike da annashuwa, "Lafiya ƙalau Abba , an dawo lafiya.?? " ya faɗa cikin girmamawa, "Lafiya ƙalau Son, ina fata dai lafiya? Al'ameen ɗin ne ya amsa da" Lafiya lau Abba, wata magana ce nazo muyi idan ka da lokaci". "To to to, bismilla ina jinka Al'ameen ince dai ko lafiya ko?" Alhajin ya faɗa cikin dattako, lokaci daya yana mai ajiye kofin coffe da yake sha a hankali, ya tattara duk kan natsuwarshi ya ɗora ta kan mafi soyuwa daga cikin ƴaƴan shi.

Natsuwa Ya Ameen ɗin yayi tare da warware mashi komai da ake ciki, dangane da karatun suhan ɗin, sai dai bai faɗi Abunda mahaifiyarshi tayi ba, sannan ya ɗora da faɗin "Abba kuma ina so asamu wasu masu aikin da zasu mayi gurbin su, Kaga dai ita maman yarinyar ba cikakkar lafiya gareta ba, kowa kuma ya sani, sannan idan Allah yayi ita kuma Suhana makaranta zata tafi, Kaga akwai nbuƙatar wasu madadin su, sannan bana so mom ta san da hannuna ko na Afnan a ciki, ka shige mana gaba wajen ganin ka daidaita komai wajen hajiya"

Murmushi Alhaji mustaphan yayi irin nasu na manya, sannan ya ɗora da faɗa ya aka yi ba'a faɗa mashi hakan ba tun farko? Ai da yanzu ma yarinyar tayi nisa a karatu, ko ma ya tura ta cen wajen Aunty feena tayi karatun ita da Afnan ɗin, Amman ko yanzu babu matsala, babu Abunda zai gagara da izinin Allah, wasu ma an temakesu balle waɗan da suke ƙarƙashin su?, shi ɗa ai na kowa ne, kuma baka san mai amfanar ka ba nan gaba.

"Babu komai Al'ameen, ka bar maganar a hannuna insha Allah da kaina zan samu ita mahaifiyarka tata, zan kuma roƙe ta wannan alfarmar in har na isa tayi man" Alhajin ya faɗa cikin son ƙarfafa ma Al'ameen ɗin guiwa ga temakon da yake son yayi, ko bayan ba ranshi, shi ya san ya bar wanda Al'umma zasu amfana dashi, ya san ya bar ma dadi, ko ma yace mafi yi, domin Al'ameen ɗin yaro ne irin wanda kowanne uba yake da burin ace ya mallake shi, a matsayin magaji.

Cikin jin daɗi da godiya yayi ma Abban nashi sallama gami da cewa "bari in barka haka nan Abba, ka huta na san ka gaji, a tashi lafiya, sai da safe" ya faɗa yana Miƙewa da niyyar barin ɗakin, da kallo Alhaji mustaphan ya bishi yana ƙissima wani al'amari da zai faru nan gaba ƙaɗan akan ɗanɗan nashi mai girma, tabbas yana da buri da fatan hasashen nashi ya zamo gaskiya. Murmushi yayi yana mai janyo kofin coffe ɗinshi ya cigaba da kurɓa cikin dattako gami da faɗin
"Allah shi kaimu Son"

_Toh fa Fans, magana ta girmama, lamarin ya kai kotun ƙoli, ko ta yaya Alhajin zai yi domin shawo kan maman Suhana?, Kudai kuci gaba da bin Alƙalamin Oum Deedat domin ta warware maku zare har abawa_

_~Oum-Deedat ce~_
[8/5, 8:23 PM] Aminatu Hassan: 🌹 *_BAN FI ƙARFINTA BA_*🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u nopain✍🏽~*

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Fans ina jin daɗin comment ɗinku, hakan na ƙara man ƙwarin guiwa, nagode akafta*

_*Page ~10~*_

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Takowa ya cigaba da yi a hankali cikin salon tafiyar shi ta ingarman namiji, daf dani ya sunkuyo ta yadda zan iya jiyo shi, sannan ya shiga faɗin "pray for your mom, yanzu ba kukan ki take buƙata ba, sannan ki tashi daga wajen ki koma bisa chair kin tare hanya, wani zai iya bugeki" Abunda ya faɗa kenan a gaggauce ya koma inda yake zaune ya sake zama.

A hankali na tashi ina mai haÉ—a hanya cikin jin juwa da ke neman yin haji-jiya dani, kujerar dake kallon tashi na zauna tare da juyar da kaina daga saitin shi, ta yadda ba ma zamu iya haÉ—a idanu ba.
Chapter 12 · 0% Book details