← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 56

Sashe 45

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba tace ƙala ba a lokacin sai faman share kwalla take yi da gefen gyalenta, to me zata ce? Ai kuma yanzu ta lafiyar shi akeyi, amman fa ita tasha alwashin ɗaukar ma abun mataki, ta san mama talatun ba zata yi mata ƙarya ba, gudun kada Alhaji yace bata ji maganar shi ba, zata yi nata binciken itama ta ƙarƙashin ƙasa, ba zata taɓa lamunta yaron nata mai ji da kyau, ilimi, kwarjini, da wadata ya ɓige ga auren maƙasƙanciyar mai aikinsu ba, ɗiyar mai aiki, kai ina ba zata yuwu ba, tasha Alwashin ko dukkan Abunda ta mallaka zai ƙare sai ta raba yaron nata da waccen shegiyar yarinyar, yo shegiya mana, in banda haka duk duniya wanene ya isa ya nuna wani yace ga ubanta? Yarinyar da ko asali bata dashi balle ma uba.

Cikin dare misalin uku saura ya farka, lokacin duk an bar su sun shiga ɗakin, shi dai alhajin kujera ya nema ta gefe mai cin mutum ukku ya zauna shi da Abie, ita kau Hajiya kubran kujera taja irin ta silver mai soso da mugun taushi, gefen gadon ta ajiye ta gami da zama ta tura ma yaron nata idanu, ita kanta ta yarda yaron nata ya rame fara ɗaya, a hankali yake sauke numfashi, ya sake yin fari ƙwal kaman ba jini, Amman fuskar tayi jawur kaman an gaggaura mashi maruka, Bilal ma kasa zama yayi ya koma ta gefe guda kusa da kan Al'ameen ɗin yaja ya tsaya, abokin nashi yake kallo da duk ya fita hayyacinshi lokaci guda, kuma ya san duk akan yarinyar nan ne, a yanda ya fahimta Alhajin na ma hajiya magana, in ko haka ne, Soyayya na ɗawainiya da abokin nashi, ba zai yadda bane kawai, ai in har taimako ne ba zaka yarda ka dinga shiga irin waɗan nan haɗarurrukan ba, ba tare da ka sallama wannan taimakon ba.

Ganin da sukayi ya farka ne yana neman tashi lokaci guda gami da ƙoƙarin buɗe ido ya sanya Abie rugawa office ɗin likitocin domin ya kira su, ita kau Hajiya miƙewa tayi gami da kamo hannun Ameen ɗin ɗaya mai ɗauke da canula ta riƙe gam tana "Son buɗe idanun ka mune nan wurin da Alhajinka da Abokin ka Bilal🤣, don Allah ka tashi Son karka mutu ka barni". A hankali ya shig buɗe idanun nashi ya wara su akan mahaifiyar tashi, saurin maida idon yayi ya kulle, sai da Bilal ɗin yayi mashi magana ne ya sake buɗe idanun ya ɗora su kan Bilal ɗin da ya zagayo ta ɗaya ɓarin shima gami da ranƙwafowa sosai kusa da Al'ameen ɗin, hannu ya miƙa ma Bilal ɗin a hankali, shima ya kama gami da sakar mashi murmushin ƙarfafa guiwa, Soyayyar abokan guda biyu, abun burgewa ce da ban sha'awa, hakan ba ƙaramin ƙona ran hajiya kubra yayi ba, duk yanda tayi akan yaron nata ya kalle ta yaƙi kallon ta.

Alhaji Mustapha da yake gefe cen zaune, yana kallon duk Abunda ke faruwa, hamdala yayi ga Allah, domin ya san dole ne ta fuskanci hakan ga ɗanɗan nata, tinda har zata iya yarda da ƙazafin neman mata da aka laƙaba mashi kuma ta hau ta zauna akai, hakan ce ta sanya sai bai taso ba bai kuma tanka ba, har saida yaga shigowar likita cikin ɗakin.

Dudduba shi yayi gami da yi mashi Æ´an aune aune, sannan ya É—aura mashi ruwa gami da tsira Allura cikin ruwan, a hankali baccin ya sake É—auke shi, to dama dai ya kulle idanun nashi gam, duk da sun san cewa ba bacci yake ba, Amman akwai Abunda ke kai kawo a zuciyar shi da har yake sa baya son kallon su.

Jikin Hajiya kubra yayi sanyi matuƙa, gashi da ta kai kallon ta kan Alhaji ya kan auna mata harara har sai ta ji ba daɗi ta janye idon nata, Abie fa har yanzu kanshi a kulle yake saidai da yake shi ɗinma halin shi daban, baya shiga Abunda babu ruwa shi duk da sangartar shi, bakin shi yaja ya kulle gami da kishinhiɗawa kusa da alhajin tinda ance ya samu lafiya daya farfaɗo za'a basu sallama,tini bacci ya kwashe shi shima, tau an sha ƙauyawa day an gaji matuƙa, ga rashin barci, shi kau har yanzu Bilal ya kasa koda zama ne, duk da ƙafafun shi da sukayi matuƙar sanyi, baya jin zai iya zama har sai yaga farkawa Al'ameen ɗin.

Har aka yi kiran salla suna nan zugum, ganin za'a tada sallah ne ya sanya Bilal tashin Abie suka nufi masallacin dake cikin asibitin, a daidai lokacin kuma Al'ameen ɗin ya sake farkawa, ganin mahaifiyar tashi a kusa dashi ne ya sashi saurin maida ido ya kulle, magiya ta shiga yi mashi akan ya buɗe idanun koda sau ɗaya ne ya kalle ta, hakan ce ta sanya shi buɗe idanun da suka koma ƴan ƙanana ya shiga kallon ta.

Ba zai iya jure kallon nata ba ya maida ya kulle, ganin tinani zai dame shi ne ya sanya shi sake buɗewa gami da tashi zaune sosai, ya zare robar ƙarin ruwan da daf yake da ƙarewa, ya jingina bayanshi jikin bango, gami da jawo ƙafafun shi ya soke kanshi ciki.

A haka suka tada su zaune ba mai cewa ƙala, da sauri Bilal ɗin ya isa bisa gadon gami da zama ya kamo hannuwan Al'ameen ɗin duka, shi kau Abie ganin haka sai ya koma zarce wa kiran likita yayin da Alhajin ya ƙara so yana faɗin "son ya ƙarfin jikin? Akwai inda ke maka ciwo?"

Ɗago wa yayi yabi Alhajin nashi da kallo, gami da ɗan murmushin ƙarfin hali a fuskar shi, Amman bai ce kanzil ba, likitan ne ya shigo ya sake duddubawa gami da rubuta magunguna ya sallame su, da gargaɗin abar shi ya sake hutawa, kuma a guji tada mashi zancen da aka yi mashi har ya faɗi.

Da to suka bishi, inda Abie da Bilal suka kama shi har zuwa cikin mota, a haka suka isa gidan babu mai tankawa kowa da Abunda yake saƙawa cikin ranshi.

Har suka isa gidan babu wanda ya fito illa mai gadi da mudi driver, harda muɗi naka kama shi suka isa dashi sashe nashi gami da kwantar dashi suka ja mashi bargo, duk da ba barci yake ji ba, ya sha barci a asibiti hakan baisa ya Musa ba, illa iyaka kwance da yayi yananshaƙar ƙamshin humrar ta da ta bari ɗazu a sama gadon, abubuwa da dama na kai komo a ranshi, shi da yake ɗanɗanta tayi mashi haka ina ga ita baiwar Allah?

Ganin ya juya masu baya ne, ya sanya su ficewa, jiki a sanyaye itama Hajiyar ta fita zuwa sashe nata, gami da yin sallah, kwanciya tayi bata so a dameta ne ya sanya ta kashe wayoyinta gami da kulle É—akin baki É—aya, shima Abie sashe shi ya koma haka Alhajin ma kwanciya yayi domin ya É—an samu yayi bacci tin kafin abokan shi su fara isowa.

Shima Bilal ɗin raɓawa yayi ya kwanta ta bayan Ameen ɗin gami da jan bargo, bacci yake so yayi, ya sha Alwashin ba zai taɓa tada mashi maganar ba in har ba shine yayi mashi ita ba, tinda likita yace a guji yin hakan, da haka har bacci Ɓarawo ya sace shi.

Tin da safe aka fara shigowa ya shanye, da raguna sai kaji da aka kawo mota guda, to dama dai an sallama komai har masu gyara na nan gefe, masu suya kuma basa wahala tinda yau ne daren biki gida ko ina a cike yake, aiki aka hau yi fafa, bayan anyi break fast, dama yau babu wani event da zasu gabatar sai gobe idan an ɗaura aure ne zasuyi dinner, wannan kuma harda iyaye, ko da aka yi ƙoƙarin neman hajiya mama Talatu da Hajiya Laila ne suka hana suka ce tana bacci, su sukayi tsaye wajen komai har Hajiya sa'a ta iso itama suka cigaba da bada command, ita dai Hajiya Zainab da ƴan sashe ta saidai kallo da taimakawa, suma su Goggo Aisha duk sun fito a cewarsu ma ai sune masu tsayawa ayi komai kan idonsu tinda gidan ƙanen su ne, hatta su Goggo Hassana da Hussaina ba'a bar su a baya ba, kowa ta ɗebo zuri'arta kaf zuwa gidan bikin domin Alhaji Mustapha mutum ne na jama'a ba ruwan shi da nuna halin ƙyamar talaka ko mara shi, hakan ce ta sanya kowa ke matuƙar jin daɗin raɓarshi.

Umma ta da domin Hajiya Zainab take yi, ganin itama taja baya sai itama bata je wajen aikin naman ba, duk da ba yanda zasuyi da wannan naman don ma dai akwai ma'aikata da aka ɗauko na musamman aka ƙara dasu mama sauden.

Tin da nayi salla na koma na kwanta, jikina duk a mace yake na rasa dalili, da safe sai ga Afnan da Hafsat sun zo dubani, Naji sauƙi, na kuma ji daɗi sosai, sune ma suka sanya ni tashi har ma na karya gami da yin wanka, a haka suka janki dole ba don naso ba na bisu sashe nasu na amare, itama dai ummata taji daɗin hakan, domin bata son kwanciyar da nake yawan yi, gashi ta kula jikina a sanyaye, in nazauna nan kuma ba abokin fira saidai inta tinani.

Itama wanka tayi ta fice zuwa sashe nasu Hafsat domin ta gani ko da Abunda zata kama.

Wata Æ´ar matashiya yarinya ce tayi sallama É—akin namu, amsawa mukayi mu duka da muke zazzaune ana ta fama fira da bada labarin event É—in da aka yi jiya, "Wacece Suhana a cikin ku?" ta faÉ—a cike da yatsina, nuna ni Hafsat tayi gami da cewa "gata nan lafiya dai ko?" "eh lafiyar kenan, Saudat ce ke kiran ta" tana gama faÉ—ar haka ta juya gami da ficewa.

Afnan ce ta miƙe gudun kada a wulaƙanta ni bayan naje, "muje in raka ki" jerawa mukayi har ɗakin nasu gami da sallama, mun taddasu zazzaune bisa gado wasu a sama carpet, sun yi break oast ko ina gaja gaja, wasu ma duk babu kaya jikin su illa na barci ƴan yalolo.
Chapter 45 · 0% Book details