← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 56

Sashe 35

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigar shi kenan part ɗin nashi, a matuƙar gajiye yake, waya kawai yayi ma Nihal ta kawo mashi snacs yunwa yake ji, kai tsaye ɗakin shi ya faɗa ya shiga kwaɓe kayanshi, wanka yake son yi ko zaiji sauƙi gajiyar dake nuƙurƙusar shi, gashi part ɗin nashi yayi matuƙar dauɗa, rabon da ya samu kyakkyawa n gyara tin wanda Suhan ɗin tayi mashi.

Bayan ya gama wankan ne, ya shirya cikin pajmas na maza, saboda sauƙin nauyin su, gashi yana so ya kwanta ya ɗan huta, sallama yaji ta baƙuwa murya daga cen falin nashi, a hankali ya miƙe gami da fita domin ganin wake sallama, kaman muryar mace yake iya jiyowa.

Maree ce tsaye, hannun ta ɗauke da farar roba mai garai garai, kana iya hango Abunda ke ciki, a tsakiyar falin ya iske ta tsaye tana ƙare ma sashe nashi kallo, ita asali ma bata taɓa shigowa cikin shi ba, saidai kawai ta hango shi daga nesa, duk da a zahiri kasan zubin nashi dama zai yi kyau, saidai ya zarta yanda take tunani.

Ƙamshin turare ne, ya alamta mata lallai akwai wani tsaye kusa da ita, ɗan zabura tayi kaɗan tana cewa "Yallaɓai barka da hutawa, gashi inji Aunty Nihal tace in kawo maka" ta faɗa tana miƙa mashi robar cikin ƴar rissinawa tana wani far-far da idanu, ko kallon ta baiyi ba, ya nuna mata stool dake gefen kujera ajiye, alamar ta ajiye bisa, gami da juyawa da niyyar komawa cikin ɗakin yana cewa "Ki turo mun Nihal ɗin"

Da kallo ta bishi ta baya har ya shige ɗakin nashi, ajiyar zuciya ta sauke, dama haka Al'ameen ɗin yake? Lallai dole ne ta sake taku, wannan ai kalar nasu ne, ko ba zai aure ta ba, lallai dole ne ta ɗanɗana zumar shi, zata san yanda tayi ta jawo hankalin shi gareta, saidai ita kanta ta san da wuya, da wahala, domin a yanda ta ganshi ba zai yi wasa ba ko ya ɗauki wargi, ƙafafunta ta ja gami da barin sashe tana ta saƙa mugun nufi da mugu nƙuduri akan bawan Allah Al'ameen.

Har ɗaki Nihal ɗin ta tadda shi, kwance yake ba bacci yake ba Amman idanun shi a kulle suke, ƙare mata kallo yayi daga sama har ƙasa, sannan ya shiga balbake ta da faɗan, ya sanya tayi mashi abu, ta sanya wata ƙazama cen ta kawo mashi Abunda zai ci, mamakin shi take yi, ai ita a sanin ta yana cin abun hannun ƴan aiki, tinda yana cin na Suhan da mama Maryamar.

Katseta yayi daga tinanin da take yi, "dole ki amshi hukuncin, gobe in Allah ya kai mu ki tabbatas kin gyara mani sashe na tsab, kaman yanda kika ga Suhan nayi mashi, bana son ƙazanta, baƙi zanyi cikin satin nan zaki iya tafiya"

Juyawa tayi tana kumbura baki, har ga Allah in har Yayan nasu na ƙasa yana takura masu, ya sanya sun dawo ƙasar kuma yana neman ya sanya su wahala?

Aikin gyaran wannan sashen ai ba ƙaramar wahala bane, ita da ko toiket ɗinta bata iya wankewa, yanzu saidai ta sanya Maree tayi mata, duk da bawai ta gansu da tsaftar mareen ba kaman suhana, zuciyar ta na raya mata ta sanya Maree ta gyara mashi, wani sashe na zuciyar nan kwabar ta, tabbas zai iya ganewa ba ita tayi ba, inko hakan ta faru ta kaɗe har buzunta, ba zasu rabu ta daɗi ba, ɗan guntun murmushi tayi, mafita da ta samo, ai yace irin yanda Suhan keyi ko? To ba matsala, ai Suhan ɗin ce ma zata yi maka yaya sha kuruminka, tinda aikin nata kake so. Da haka har ta isa sashen nasu, tana labarta ma Saudat ɗin yanda sukayi da yayan nasu, murmushi kawai saudat ɗin tayi gami da cewa "gara ki sanya ta tayi shegiyar, kinga yanzu daga dawowar mu har ta janye Hafsy, ai wannan yarinya wallahi akwai mayya". (😝😝 kunji fa readers ashe sun damu hda hafsat ɗin🤔)

********************

Bacci yake son yi, saidai yunwa ta ishe shi, gashi bai jin zai iya cin abinda yarinya ta kawo mashi, miƙewa yayi a hankali ya isa kitchen ɗin da yake mallakin shi, kaman wata macen, fridge ya buɗe ya ɗauko lemo kwali da ceramic cups ya fito, kai tsaye bedroom ɗin ya koma gefen gado ya zauna, gami da tsiyaya lemon ya sha, kaman wanda aka yi ma dole.

Wayar shi ce tayi tsuwwa, alamar saƙo ya shigo, share ta yayi ya cigaba da shan lemon shi har ya gama, gami da miƙewa ya maida kitchen, ya dawo daƙin gami da saisaita ƙarfin Ac ɗin dake aiki cikin ɗakin.

Gadon nashi ya haye, tare da jan lallausan bargon nashi ya rufe ƙafafun nashi ruf, wayar shi ya jawo gami da maida ta sylent, har zai ajiye sai kuma ya lura da ɗan akwatin saƙo da yake cen sama wayar a maƙale.

Cikin kasala ya buɗe, yayi mamakin ganin sunan ta ɓaro ɓaro a wayar, bai ƙara shan mamaki ba har saida ya karanta Abunda saƙon ya ƙunsa, karantawa yayi ya sake maimaitawa, ita ɗin ce kuwa? Zaune ya miƙe bisa gadon, gami da jan bayan shi ya jingina shi jikin lallausan tissue foam ɗin dake jikin wood ɗin gadon. Sake dai maimaitawa yayi, lallai ita ce ta turo idanun shi ba gizo suke yi mashi ba.

Hannu ya sanya gami da ɗan yin typing a hankali ya maida mata reply, unlight ɗin wayar yayi, gami da tura ta ƙarƙashin fillow.

Zamewa yayi ya kwanta idanun shi a lumshe, zuciyar shi na ta kai komon karanta saƙon nata, su kansu idanun nashi sun gaza dena nuno mashi hoton Rubutun, tiryan tiryan yake karanta shi cikin idanun shi, kaman yana kallon scream ɗin wayar ne, a hankali bacci mai nauyi ya kwashe shi.

Niko da muke cen ɗakin mu mun bararraje muna ta fira da Hafsy, ko ba komai dai Naji sauƙin kaɗai ci yau, na samu aboki yar fira, tana ta bani labarin tafiyar su, ina ji daman nice ace yau na ganni a ƙasashe ƙetare, mu biyu ne cikin ɗaki, domin umma ta ta fice ƙofar ɗaki gami da shimfiɗa tabarma ta zauna tana yanke farce.

Sabuwar waya ta ce ta ɗauki tsuwwa, alamar shigowar saƙo, hannu na sanya gmi da jawo wayar, na buɗa. Cikin ƙwalalo idanu nake kallon wayar, hakan ce ta jawo hankalin hafsat ta tashi zaune tana tambaya ta ko lafiya?

"ina fa lafiya Hafsy?" na faÉ—a bayan na gama karanta Abunda ta ta tura da shi kuma wanda ya turo.

"To menene a ciki Suhan? Naga ai godiya kawai nayi ba wani abu ba, menene na damuwa, shima ko kinji yace wani abu ne?" ta faÉ—a bayan ta amshi wayar ta karanta reply É—in da yayo.

"A'a Amman ni kin sa har na fara jin kunya, waÉ—annan kalama ai irin naku ne na masoya hafsat, kada fa ki sanya yayi tsammnin wani abu" na faÉ—a hankali na aÉ—an tashe, har ga Allah kunya duk tabi ta baibaye ni, kaman ina gaban shi, sai yanzu nayi na damar barin ta ta tura Abunda ta rubuta ba tare da na amsa na karanta ba.

"kinga karki wani damu kanki Suhanan umma, ki kwantar da hankalin ki Yayan namu wayayye ne ba zai kawo ma ranshi komai ba akasin Abunda aka rubuta"

Ta faɗa cikin son ƙarfafa man guiwa, Nidai lafewa nayi jikin bango ina sauke ƴar ƙaramar ajiyar zuciya, gami da ce mata "To Hafsat Allah ya sanya"

~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~21~*

*Ina ma É—aukacin Al'ummar musulmi barka da shigowa sabuwar shekara a musulunci, Albarka dake ciki Allah ya sada mu da ita, sharri da tsautsayin da yake ciki, Allah yayi mana tsari dashi Albarkacin fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.*

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

_Assalamu Alaikum, Yaya ina yini, ya gida da aiki? Ya fama da jama'a? Ina fatan komai lafiya, na rubuto in maka godiya da abun arziƙi da alkhairi da kaman, bani da bakin godiya a gareka, irin kyakkyawar kulawa da kake bani, i do appreciate Yaya, Allah ya ƙara arziƙi da wadata_

Ya kai sau biyu kenan ina ƙara maimaita karanta saƙon da Hafsat ɗin ta rubuta ta tura mashi, ina hango rashin dacewar kalaman, idanun a kaman zasu faɗo ƙasa saboda yanda na ƙura ma scream ɗin idanu, kunya tana baibaye dani, gashi dai tini hafsat ɗin ta fice taje ta kwaso kayan ta, Amman duk kina nake yi wani iri, a hankali idanun a suka kai ƙasa kan nashi saƙon da ya maido tin bayan tura saƙon da mintoci kaɗan

_OK ba damuwa, Ameen_

Iya abunda ya rubuta kenan, sai nake ƙara ganin rashin dacewar hakan, fata na dai ace baiyi mani wata fahimta daban da.

Tare da Hafsat ɗin muka kwana a ɗakin mu, wanda saidai umma ta shimfiɗa tabarma gefe cen ƙasa tiles ta kwanta, ta bar mana katifar.

Yau mun hutar da umman tawa, ni da hafsat muka yi komai muka kammala har abun kari, sannan muka yi wanke wanke a cen gefen ƙofar ɗakin namu, kallo ake ta binmu dashi sauran ma'aikatan wasu na zunɗen mu da baki, mu dai bamu damu ba, harkar gabanmu kawai mukeyi.

Hafsat É—in na kula dasu, shaye da mamaki ta kalle ni lokacin da muka gama wanka muka zauna zaman shafa, "Suhan wai dama haka ma'aikatan gidan nan suke yi maku ke da umma?" ta faÉ—a mamaki fal a fuskar ta. "Eh nace, ina mai basar da zancen, saboda umma ta bata so ake zancen su. Girgiza kai kawai tayi gami da cewa" Allah shi kyauta" daga haka itama ta ja bakin ta ta kulle lura da tayi Suhan bata son maganar tasu.
Chapter 35 · 0% Book details