← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 56

Sashe 54

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka firar ta tashi kowa ya nufi sashen nashi, shima yaya Auwalun ya nufi wajen Hajiya Zainab ɗin domin dukkanin ƴan uwanta sun wuce yau bayan kammala tafiya da amaren, jirgi suka hau tinda ana fama da matsalar hanya masalan ma ta Abuja. (Allah ka kawo mana ɗauki, ka bamu zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar tamu)

Baiyi mamakin taddata a sashen nashi ba,ya san hakan ce zata faru dama, kuma yana kyautata zaton maganar yaron nata ce ta kawo ta.

Bai nuna mata ba Sam, sai a wayan cewa da yayi ya shiga zaulayar ta, bata biye mashi ba tinda ita ba wannan ne gabanta ba.

Koda ta fara mashi mitar bai dakatar da ita ba har saida ta gama, shi mamakin ta ma yake yi wallahi, ace mace kaman Hajiya Kubra ta tsaya tana tada jijiyrr wuya akan mutanen da ko abincin da zasu ci basu da, mutanen da suke aiki ƙarƙashin ta abun a tausaya mawa, ita ko ta tara dukiyar da ko mutane dubu zata dinga iya ciyarwa a kulli yaumin har tsawon wasu shekaru ba tare da ta durƙushe ba, saidai da ita Abunda bai sani ba, jinin talakan ne ta tsana, Sam bata so ta haɗa iri dasu kar su goga mata talauci.

Tinda yayi hargagin yayi kuma barazanar bataji ba, ya san kuma aikin abokan shawara ne koma ince mazuga, tau ya san ta inda zai ɓullo ma Al'amarin nata. Lallashinta ya shiga yi gami da nuna mata cewa yana sane fa da zancen kuma zai ɗauki matakin da ya dace Amman ba abu bane ba gaggawa, karfa ta manta duka gidan akwai baƙi, tayi haƙurin zuwa goben idan sun bar gidan sai ayi mai yuwuwa, da haka ya lallaɓa ta, ta fice daga ɗakin tana mita, ita lallai atafau ba zata taɓa lamunta ba.

"mama fa wallahi ya kamata kiyi wani abu, kina gani fa jiya Abunda yayi ma waccen shegiyar yarinyar a cikin jama'a har yana kiran ta matarshi, kuma naji Æ´an uwan Alhajin sunce sun yadda da al'amarin É—azu da ina gyara masu sashen nasu, gaskiya na fara sarewa da dukkan alamu ba zamu samu nasara ba.... "

Mama talatun ce ta buge ma mareen baki, cikin ɓacin rai ta shiga cewa" Kiji ja'irar yarinya ke har baki ma kike mana? Kinsan sharrin da na ja mata kuwa? Ai dolenta ma su bar gidan daga ita har shegiyar uwarta, kuma wallahi ba zata taɓa wankuwa ba a wurin hajiya, Abunda yayi ɗazun ɗin ni ai burgeni ma yayi, bansan ina da sa'a ba sai ɗazu ɗin da ya kamo yarinyar gaban hajiya, wannan shi ke nuna cewa lallai suna aikata baɗalar kenan... "

Mareen ce ta katse mahaifiyar tata cikin zaro idanu

" umma ba dai sharri kika ja masu ba? Kada fa abun ya shafi masoyin nawa kuma mama, gaskiya ki sake dai, kije kice ba haka aka yi ba, yarinyar kawai ke da laifi.. "

" Ke jiman shegiya ƴal banza.. Kina nufin in koma in ƙaryata kaina kenan? Ke wace irin shashasha ce ne? Kinfi son shi a kaina kenan? Tinda gashi har kina neman ki ja mani kora a cikin gidan nan, duk fa Abunda nake yi don ke ne... "

" a'a mama kedai faɗi gaskiya, naira kike so dai kici, Amman ni wallahi banji daɗin Abunda kika yi ba har ga Allah, ai ba zan so ace ya taɓa kusantarta ba wallahi, Allah ma ya kiyaye, insha Allah nice nan zan ɓare Abunda dal a leda"

Rankwashi mama talatun ta sakar mata a tsakiyar kai, ta kuwa dafe da ƙarfi tana cewa "wash, karki kashe ni mama ai gaskiya na faɗa, gaskiya ki canza wani tsarin dai" bata ce mata ƙala ba sai ma juyawa da tayi ta kwanta, sai kuma cen abun ya ɗaɗimo ta ta juyo tana ba ƴar tata amsa.

"Tinda kince haka shikenan na ƙyale ki, kiyi da kanki, ai ina ce ko kuɗin muka samu tare dake za'a ci.."

"A'a mama, ni da zan aure shi ai saidai ke ince maki za'a ci tare dake, saidai Abunda na wawuro inzo in ɗan lasa maki a baki don ki ƙara ƙaimin nemo magani" ta faɗa hankalin ta a kwance kaman ba mahaifiyarta take faɗa ma haka ba.

(Hmmm Allah shi kyauta, inda akuyar gaba tasha ruwa....)

Zaune yake yana Æ´an latse latsen shi cikin computer, kaman ance ya kunna datar, ya kuwa kunna gami da shiga WhatsApp É—in, sai kuma ya ajiye domin massages É—in su gama shigowa ya gani in da waÉ—anda zai ma reply, domin da yawa wasu abokanan kasuwancin nashi ta online suke magana.

Bilal kuwa yana zaune daga ƙasa bisa carpet ya tankwashe ƙafar shi ɗaya ya miƙe gudar, mug ne a hannun shi yana sipping cofee, ɗan sanyi sanyin Ac ɗin dake aiki ya sanya shi yake jin daɗin cofee ɗin, hannun shi riƙe da remote yana kallon wrestling a tashar MBC Action ɗin, lokaci lokaci yana ma Al'ameen ɗin magana da hankalin shi ya ɗauku ga aikin da yake yi, shima lokaci lokaci yana bashi amsa, duk da sai a daɗe bai tanka mashi ba.

Rufe computer ɗin yayi gami da ɗaukar wayar, sannan ya ɗan zama bisa kujerar ya kishingiɗa, daki daki yakebin saƙon in da aka turo mashi, wasu yana basu amsa daidai da saƙon wasu kuma yana wucewa ko ma karantawa ba yayi masalan ma waɗanda ya san ba masu matuƙar amfani bane.

Har ya wuce number É—inta, sai kuma ya dawo ganin kaman ya san number É—in, domin a wayar da numb É—in tata take ba'a ita yake chat ba.

BuÉ—ewa yayi gami da dubawa

Abunda yaga an rubuta kawai shine

_*Yaya Result É—inmu ya fito*_

Sai kuma wani hoto da yagani daga ƙasan Rubutun, buɗewa yayi gami da dubawa a tsanake.

A hankali ya shiga faÉ—in

"very good Suhan, Allah yasa ma abun albarka"

Bilal É—inne ya É—ago gami da kallon shi alamar magana kake yi.

Baice mashi komai ba sai miƙa mashi wayar da yayi. Amsa yayi gami da dubawa " Wow, wacece wannan?"

"Suhaaan.." ya bashi amsa, saidai shi kanshi bai san dalilin nashi na jan sunan haka ba.

Da kallo Bilal ɗin ya bishi yana cewa "congrat" sannan ya miƙa mashi wayar yana sake faɗin "Gaskiya tayi ƙoƙari, zata iya samun duk course ɗin da take so"

Jinjina mashi kai Al'ameen ɗin yayi yana mai yin typing wani abu ya tura mata, fuskar nan tashi ba alamun dariya fa, duk da yaga cewa tayi ƙoƙari kuma ya jinjina mata, gaskiya za'aje da ita, ga dukkan alamu tanada matuƙar ƙoƙari sosai.

"Friend inaso muyi wata magana Pls, Amman inaso ka fahimce ni nima in fahimce ka"

Bilal É—in ya faÉ—a bayan ya koma ya jingina bayan shi jikin kujerar da Al'ameen É—in yake kai.

"gyara zama yayi alamar ina jinka, domin ya san duk lokacin da Bilal É—in yayi mashi haka tau fa magana ce mai amfani.

Ganin bai tanka ba kuma ya tattara dukkanin natsuwarshi a kanshi ya sanya bai damu ba da rashin tankawar tinda ya san hali, ya fara magana.

"Bro bawai nace ka sauka akan bakanka ba ko kuma niyyar auren yarinyar cen don ka fidda su a halin da suke ciki ba, a'a na san kai mai biyayya ne ga iyayen ka, ka sani sarai mom ɗinka tana matuƙar sonka kuma tana ji da kai fiye da dukkanin sauran ƴaƴan ta, kuma tana son dukkanin Abunda kai kake so koda bata nuna maka ba, sai nake ganin wannan al'amarin tinda ta nuna bata so kuma bata goyon baya, mai zai hana ka dakata kagani har zuwa lokacin da zata yarda don kanta ta amince maka? Babba babba ne kuma yaro yaro ne koda kuwa ɗan giwa ne, bamu san Abunda ta hango ba, ba kuma kusan Abunda take hararo maka ba zuwa nan gaba, kuma inaso ka sani yarinyar nan dai ahe's innocent bata san komai ba, dukkanin Abunda ke faruwa ma in ka kalli fuskar ta zaka gane ba wai ta fahimta bane, in banda jiya da kayi Abunda kayi, yau kaga koda giccinta ne? Na tabbata wannan saƙon ma da tayo maka, bata da yanda zata yi ne, baka tinanin zata yi maka kallon mugun mai son raba su da inda suke cin abinci? Me mahaifiyarta zata ɗauka, wanne irin kallo kake so tayi maka? Baka tinanin zasuyi maka kallon kafi ƙarfin su ƙila dai kana da wani buri ne a kansu? Ka taɓa zama kayi tinanin haka? Yeah for sure na san kaman yanda mahaifiyarka ɗin take faɗa, lallai fa kafi ƙarfin wannan yarinyar, kafi ƙarfin aure ta ita ba sa'ar auren ka bace. Kasan baka buƙatar sai na tina maka kalar ƴan matan dake rubibi a kanka, Nidai shawara ta anan ka dakata da dukkanin yaƙin nan daka ɗauko ka saurari mahaifiyarka, lallai zaka ga nasara, Amman ba wai nace karka aure ta bane, saidai inaso tin wuri tin kana wasa, kada abun yazo ya kasance ya zama da gaske ka fara son yarinyar nan a ranka, abun sai yafi rashin daɗi" ya ƙarashe yana waiwaya wa ya kalli cikin ƙwayar idanun abokin nashi.

Lallai ko Bilal É—in bai faÉ—a ba zantukan nashi sun ratsa zuciyar abokin kuma aminin nashi, shiru yayi yana sauraren maganar da zata fito daga bakin shi.

Nisawa Ya Ameen É—in yayi yana Sauke wata gagarumar ajiyar zuciya, saidai ya kasa buÉ—e bakin shi balle yace wani abu.

Lumshe idanu yayi a karo na biyu yana sake sauke ajiyar zuciyar sannan ya sauko ƙasa ya zauna yana fuskantar abokin nashi cikin ɗaki ya irin ta maza ya fara magana kaman baya so

"Na fahimce ka abokina kuma nima na daɗe ina nazarn hakan, saidai zuciya ta ba zata iya jure ganin su cikin wani hali ba, su ɗin mutane ne masu tawakkali Amman inaso kayi mani wata Alfarma guda ɗaya" ya ƙarashe yana kamo hannuwan abokin nashi duka. Sannan ya ɗora da faɗin
Chapter 54 · 0% Book details