← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 56

Sashe 52

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gida yayi tsit tin bayan da aka tashi sallar isha'in
Yo kowa ya gaji wasu ma har sun fara bacci, har yanzu zuciya ta a cunkushe take na kasa gane kaina, Alfarmar su Hafsat ɗin na roƙa akan su barni inje in kwana tare da ummata ko Naji sauƙi.

Basu hanani ba, saidai sunce su ba zasu rakani ba, a haka na ratso tsakiyar gidan zuwa sahen namu, ummata har ta kwanta na kwankwasa mata ta buÉ—e na shiga.

Da kallon ke lafiya kuwa ta bini, yi nayi kaman ban kula da ita ba, kai tsaye na haye katifar na kwanta, yayin da itama ƙalau bata ce mani ba ta hawo itama tare da kwanciya.

Saidai me? Bacci Sam yayi mani ƙaura, idanun a kaman an soya, saboda rashin baccin har wani raɗaɗi suke yi mani. Saidai in juya in sake juyawa, idan na tinank kaɗan sai in ɗan ja tsoki kaɗan in sake juyawa.

Ƙwaƙwalwa ta fa har yanzu a cunkushe take, ina buƙatar wanda zai yi mani fashi baƙi dalla dalla fa, saidai wanene shi?

Wayata ce ta ɗauki haske alamar saƙo ya shigo, da hanzari na jawo ta gami da buɗewa, banyi mamakin sunan shi da nagani ɓaro ɓaro kan screan ɗin a, saidai Abunda saƙon ya ƙunsa shi ne ya bani mamaki.

Ummata wadda bansan da ta tashi zaune ba, kwatsam saidai Naji muryar ta tana mai ceman

"Mamana na kula dake fa tin da rana, ga dukkan alamu akwai Abunda yake damunki, Amman in kinga ɓkyemun shine Abunda yafi ɗin, sai ince Allah ya sanya hakan ne, domin bana so kizo kiyi danasani akan dukkan Al'amurranki, idan kuma kin yanke shawarar faɗa mani tau ina saurarenki"

Cikin ƴar razana bakina na rawa na tura wayar tawa ƙarƙashin follow, bansan lokacin da na shiga ce mata "umma fa ba komai, kawai na gaji ne, kuma gashi kaman ba ɗan jin daɗi ne..."

Na ƙarashe cikin in ina wadda take alamta ba gaskiya a cikin maganar tawa, wanda ni kaina bansan dalilin nawa na ɓoyema umman tawa ba, da duk duniya bani da abokiyar shawarar da ta wuce man ita.

Gyaɗa kai kawai tayi, bata sake ce mani komai ba ta koma ta kwanta, tana fatan Abunda na faɗa ɗin ya kasance gaskiya, duk da bata taɓa kamani da laifin yi mata ƙarya ba.

*_"ki dena yawo cikin dare, sannan ki shirya fuskantar duk wani ƙalubale da ka iya tunkaro mu"_*

Abunda ya rubuta mani kenan, ban iya bashi amsa ba, duk kuwa da karanta saƙon da nayi sau ba adadi.

Ni ya ma ƙara sanya ni cikin wani duhun wallahi, wai ni shin me yake nufi dani ne? So yake ne ya tarwatsa mani ƙwaƙwalwa ne ko kuma me?

~Oum-Deedat ce~

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

A haka dai na kwana juye juye, zan mabiya cewa ko baccin kirki ban samu nayi ba, umman tawa duk tana kula da dukkan motsi na Amman ƙala bata ce mani ba.

Washegari kuwa tin dasafe aka tashi aka hau shirye shiryen walima da za'a gabatar itama dai a farfajiyar gidan, wannan karon harda dangin anguna duk zasu halarta, daganan ne za'ayi buÉ—ar kai, bayan an gama sai a basu amaryar su su tafi da ita.

Tin da safen kuwa sai ga su Afnan wai sun zo ƙara tafiya dani, aikuwa fir naƙi binsu, ba irin magiyar da basu yi mani ba, Amman na ƙiya, bana so in koma wurin ne a sake samun matsala gashi naga ga dukkan alamu ummata tana shirin zuwa wurin ne.

Kwanciya ta nayi ko bayan fitar su, har itama umman tawa ta kammala shirin ta ta fice, gyara kwanciya ta nayi gami da jan abun lulluɓa domin baccin da ban samu nayi ba a daren jiyan.

An ƙawata wurin fiye da na jiya, tini dangin angunan sun iso tin wajen ƙarfe goma na safiya.

A sashen Hajiya kubran aka yi masu masauki, saidai dangin sadeeq É—inne suka ce a nuna masu wajen surukar yaron nasu acen ne zasu zauna.

Ba musu aka nuna masu, ganin su manyan mutane kowacce cikin shiga ta alfarma.

Hajiya Zainab É—in bata yi tinanin haka ba, Shiyasa ba'a shirya masu tarba ba dukkanin kayan tarbar suna cen sashen Hajiya Kubra. Nan fa ta shiga ina taka saka su.

Lura da sukayi ne ya sanya suka ce karta damu kanta, ba wannan ce ta kawo su ba, su yarinya kawai suke so a basu.

Rumfuna bakwai aka kafa ayau, sunsha deciration kuwa, rumfa ta farko ta hajiya kubra ce, sai ta kaka zuwaira, sai ta Hajiya Zainab, sai ta dangin anguna guda uku, gefe kuma ta anguna ce da abokaninsu maza

An zagaye farfajiyar gabaki É—aya illa iyaka hanyar da za'a bi a wuce.

Ƙatuwar darduma aka shimfiɗa tsakiya inda gefe aka jera amaren kowacce tasha lulluɓi da kalar nata kayan da sukayi masu matuƙar kyau, gefe guda kuma aka jera ƙawayen amaren a yau babu bambanci duk kansu wuri guda suke zaune, cikin atamfar su english, kalar ta yarbawa yellow ne da ɗige ɗigen ja a jikin ta. anyi masu ɗinkin buba duk kansu, hakan ce suka sanya jan gyale da sarƙar murjani a wuyan su ɗaurin zanen ma bisa riga aka yi shi, hannuwan su riƙe da ɗan mafici mai ƴar bazar gashi gashi haka.

Kowa ya hallara, nan fa aka fara gabatar da jawabai da kuma gabatar da kai.

Kowa ka kalla yana cikin farin ciki, banda hajiya kubra da fuskar nan take ba yabo ba fallasa masalan ma data kula dangin iyayen mijin Hafsat É—in sun zarce na yaran ta gabaki É—aya a komai kuma.

An kira kowanne ango yazo ya nuna amaryar shi, gami da kama hannun ta zuwa gaban dangin shi ta kai gaisuwa, sannan sauran mutanen, haka suma angunan amaren suka kama su har gaban nasu iyayen suka gaida su. Kaka zuwaira ce duk wanda yaje kusa da ita sai ta zaulayeshi tace ita ba sadaki take so ba na goro take so, haka suka babbata kuÉ—i gami da komawa suka zauna.

Bayan ƴan abubuwa da aka gabatar aka buƙaci iyayen anguna da su kawo kayan aure.

Nan fa idanun mutane ya shiga buɗewa ganin iyayen kaya na ƙarya da kuma kuɗi da ake ɓari kaman wanda ba'a so.

Ba'a sha mamaki ba saida iyayen mijin na Hafsat suka taso, nan fa wuri ya hau tafi da sowa, ganin irin iyayen kuɗin da suka ajiye gabanta, daloli ne iya kallon ka, tare da sarƙar gwal da abun hannunta da zobunan ta wasu irin manya ne ko daga ina kake zaka iya hango su, tare da makullan mota guda biyu, ita ɗaya mahaifiyarta ɗaya, sai makullin tanƙamemen gida da yake nan cikin abujar da suka mallaka ma mahaifin Hafsat ɗin.

Nan fa ƙaryar iyayen su Nihal ta ƙare masalan dangin Hajiya Kubran, saidai ita ce tayi ƙarfin hali ita kuma taba dangin mijin ƴaƴan nata motoci da kujerar Makka a matsaynn tukuicin kayan auren da aka kawo masu.

Hajiya zainab bata san da wannan al'adar ba, hakan ce ta sanya bata tanaji komai ba, gashi kuma mijin nata baya kusa.

Shiru aka yi, kowa naso yaga me su Hajiya Zainab É—in zasu bada tukuicin wannan babbar kyauta da aka yi masu.

Takawa ya shiga yi har gaban iyayen mijin Hafsat ɗin ya ajiye check gami da wata takadda ya koma ya zauna, Ya ameen ne da yake zaune cikin rumfar abokan angunan, tini kuwa kallo ya koma kanshi, Hajiya Kubra tsabar ƙuluwa kaman idanun ta zasu sauka kan Al'ameen ɗin.

Mai jawabi ne ya taka har gaban iyayen mijin Hafsat ɗin ya sanya hannu gami da ɗaukar check ɗin da kuma farar takardar da take ƙar babu komai akai sai Rubutun Al'ameen ɗin jiki da ya gaji da ƙayatuwa.

"Masha Allah, Alhaji Moh'd Al'ameen Almustapha Dambulan ya bada tukuicin Zunzurutun kuɗi Naira Million Biyar tare da kujerar hajji ta kimanin mutane biyar da kuma upper ta ɗaukar matasa aiki a cikin Zuriyar angon Hafsat ɗin ƙarƙashin jagorancin kamfanin, suma kimanin mutane Ashirin"

Tafi aka saki, gefe guda wata zabiya ta saki guÉ—a, babu Abunda kake ji a wurin illa iyaka hayaniyar mutane data kauraye wurin kowa na faÉ—in Albarkacin bakin shi.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Hajiya Zainab ɗin ta sauke, ganin cewa yaron nasu ya fidda su kunya, duk da ta san cewa ba da son ran hajiya kubran da take zaune cen cikin mutanen ta tana ta sakin yaƙen dole bane, Amman ko ba komai ta san Al'ameen ɗin mutum ne mai alkhairi da zai yi ma daman shi ba tare da hagun shi ta sani ba.

Mutum ne mai hangen nesa da kuma kakkaifan tunani, baya buƙatar in zai fidda family ɗin nashi kunya sai ya jira shawara da wani.

Ta ɓangaren Al'ameen ɗin kuwa idanu sukayi mashi yawa, ilahirin ɗaukacin mazan dake rumfar nan ya matuƙar burge su harda mazajen ƙannan nashi kuwa, wannan ta sanya suka ƙara gane B ƙaramin gida sukayi aure ba.

Bayan kammala wasu Al'adun ne aka yi addu'a tare da ƙarin godiya, sai kuma aka fara shirye shiryen miƙa amaren ga dangin mazajen nasu bayan yi masu huɗuba mai ratsa jiki da Alhaji Auwalun da Alhaji Mustaphan sukayi.

Hafsat tasha kuka, da kyar aka ɓanɓareta jikin mahaifiyr tata, babu wanda bata ba tausayi ba, yayin da su kau sauran ƙemadagas iyayen su ne ma suka sanya su mota babu wacce take kuka cikin su.

To a ganin su dai auren so ne, kuma na wayayyu, auren ma sunan anyi ne, Amman suna da Æ´ancin da zasuyi komai a sadda suka so, kuma a lokacin da suka so.

Kkwacce cikin su an mallaka mata jibgegiyar mota harda Hafsat É—in kuwa, wannan kuma kyauta ce daga hannun Alhaji Mustaphan bayan gama masu huÉ—uba da sukayi.
Chapter 52 · 0% Book details