Sashe 44
Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Salati Hajiya Kubra ta rafka, tana mai miƙewa ta shiga tafa hannuwa, ɗanta? Ɗanta ne ya lalace haka? Yaro ma kaman Al'ameen?
Baya san lokacin da ta zari hijabi ba, ta tsallake mama talatun da take durƙushe tana ta fama hakin ƙaryar da ta shirga, ita kanta ta san da gaskiya zata bayyana, babu Abunda zai hana ta barin gidan, don idan kowa ya barta ta sani Al'ameen ba barin ta zai yi ba.
Sashen Alhaji ta nufa kai tsaye, yayi mamaki da ya buɗe yaga ita ce, tin kafin yace komai ta fasa kuka, salati ya sanya cikin ruɗewa yake tambayar ta menene? Kuka take fafa, ta ma ƙi ta tsaya ta bashi bayani, waya ya ɗauka gami da kiran Al'ameen ɗin yace ya same shi sashen shi, ga Hajiya na ta kuka taƙi magana.
A firgice ya zabura, gami da zura jallabiyar shi, Bilal É—in na tambayar shi bai tsaya bashi amsa ba, kawai dai yace Alhaji ne ke kiran shi.
Ko da ya isa, ya tadda tana kuka, haƙuri shima ya shiga bata, yana cewa tayi masu bayanin me ke faruwa.
Ko da ta shiga koro bayani, irin wanda mama talatun ta kai mata gulma, shiru Al'ameen É—in yayi yana ta faman kallonta, Alhaji ne ya shiga jifan shi da wani irin kallo na tuhuma, shi ya ma kasa buÉ—e baki balle ya kare kanshi.
"Ka bamu kunya Moh'd, ina tarbiyyar da muka baka? Abunda zaka yi mana kenan ka lalata ma ƴar yarinya tarbiyya, me ka nema ka rasa? Mene baka mallaka ba? In ma mata huɗu kace kana so a aura maka, wallahi ina mai tabbatar maka zamu aura maka su, kuma zaka iya riƙe su, me kake nema wajen waccen ƴar tatsitsiyar yarinya? Kucaka ƴar aiki, marar galihu? Wallahi *kafi ƙarfinta* nayi matuƙar baƙin ciki, nayi nadamar sanina dasu a rayuwa, yau ba zasu kwantar mani a gida ba, zasu bar gidan nan koma wace duniya zasu bana da damuwa, domin cece ɗana, domin in ceceka daga halin da kake ƙoƙarin jefa kanka, babu abinda ba zan iya yi ba.
Alhaji mustapha da yake tsaye, ya gaza gazgata gaskiya ko akasinta, domin dai ga moh'd ameen zaune Amman ya kasa musantawa ko ƙaryata Abunda mahaifiyar tashi take faɗa da bakin ta, illa iyaka ma dai miƙewa da suka ga yayi ya nufi ƙofar domin fita daga ɗakin.
"ka gani ko Alhaji, ka gani ko? Yana aikatawa, ya gama bada kanshi gareta, sunci galaba kanshi, ashirin da suke yayi tasiri kan yaro na, ina gab da rasa shi, Alhaji kayi wani abu"
Daf da bakin ƙofa ne suka ga y a yanke jiki ya faɗi, babu alamun rai a tare dashi.
Da gudu suka zabura inda yake kwance, rige rigen taɓa shi suka shiga yi, Alhaji ne yayi da dabarar kiran Bilal da abie yace su fidda mota Al'ameen ba lafiya, ita ko mom kuka ta ƙara ruahewa dashi, ba zata juri rasa ɗan nata ba akan wata banza yarinya, saidai ayi ɗaya cikin biyu.
Bilal ybatashi a firgice, yaga fa lafiya lau abokin nashi ya bar ɗakin, kuma Alhaji ne ya kira shi, gashi kuma ya sake kira yace baya lafiya, baiyi wata wata ba ya tashi a hanzarce ya zura kayanshi, gami da ɗaukar ma ƙullin mota babba da suke zube kanbstool ɗin falo, ko tsaya kulle sashen baiyi ba ya fice gami da juya mota.
Daidai nan Alhaji da Abie suka fito ɗauke dashi babu fa alamun rai a jikin shi, babu ɓata lokaci suka saka shi cikin motar gami da shiga, mai gadi ya wangale gate suka fice cikin matsananci Gud. Shima hankalin shi a tashe ya kulle gidan yana fatan dai lafiya uban ɗakin nasu yake.
Wata private hospital da tafi kusa suka kai shi, da gudu nurses suka zo suka tura shi bisa gadon É—aukar marasa lafiya, har yanzu Hajiya Kuba kwalla take mataewa, shi kau ABBA sai binta da kallo yake yi, duk laifin na kanta ya É—ora shi, baima yadda da Abunda tazo mashi dashi ba tin asali, da ya san wannan shashashar maganar zata kawo mashi da bayyi ma gigin kiran Al'ameen É—inba.
Tin a hanya suka maƙala mashi oxygen, Abunda ya ƙara firgita su kenan, suka sare da Al'amarin, su kau Bilal da abie tambayoyi ne fal a ransu Amman babu wanda zasu yi mawa, basu sare ba saida suka ga ana goga wani abu kaman dutse guda ana man nawa a ƙirjin Al'ameen ɗin, shi kau sai ya yunƙuro kaman zai tashi sai ya koma, duk cikin son samo numfashinshi ne, dukan su ba wanda idanun shi ba suyi ja ba, Abie da har ya fara kuka, Bilal ɗin ya shiga bashi baki, duk da shima zuciyar shi kaman zata fito saboda tsabar ƙuna.
Kukan da Hajiya Kubra keyi ne, ya sanya nurses É—in zagyowa suka ce don Allah a janye ta, suna kan aikin su ne, dole tasanya suka janye ta gami da komawa reception suka zauna
Kusan ƙarfe goman dare na farka a firgice, umma ta dake gefe na kwance ce tayi azamar tashi gami da kamo ni, har nayi hanyar fita daga ɗakin, lafiya, ta shiga tambaya ta, ba zance komai ba, mafarki nayi mai ban tsoro, saidai ba zance ga Abunda na gani ba a mafarki, saidai naga fuskar Ya Ameen a ciki, addu'a tayi man gami da maidani ta kwanta.
Lamo nayi ina mai sauraren ta tana ta tofa an adduo'i, abun ya dameni, menene nawa na mafarki shi? Kuma fa kaman yana cikin wani hali ne, Allahu a'alamu.
Runtse idanun a nayi, Amman fa har yanzu shi nake gani cikin mawuyancin hali ya na miƙo mani hannu alamar in fiddo shi, miƙewa nayi gami da shiga tiolet na ɗauro alwala, gami da zuwa na kabbara sallah, ina addu'ar Allah ya sanya dai lafiya, domin ban taɓa yin irin haka ba
Itama umman tawa ganin sallah na tada sai ta rabu dani ta koma ta kwanta, Amman ta kasa runtsawa, tinani take yi me ya samu ɗiyar tata da tin ɗazu ta ganta wani iri, Amman taƙi bayyana mata halin da take ciki.
*koma dai miye tana fatan ya kasance lafiya ko kuma yazo da sauƙi*
_To sai mu ce dai Ameen Mama Maryam_
~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~âœðŸ½âœðŸ½GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONâœðŸ½âœðŸ½~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden penâœ,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~26~*
Kyautar Page gareki Safiyya, na cika AlÆ™awari, na baki shi halak malak, ina sonki fiye da yanda kike son littafin nan, Allah ya bar mu tare. ðŸ¤ðŸ»ðŸ˜
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, lokaci guda yana mai ƙoƙarin buɗe idanun shi, likita da nurses ɗin dake kanshi duka suka maida dubansu a kanshi, tini fara'a ta bayyana a fuskokin su suka fara cema juna congratulation, sanin shi ɗin wanene da sukayi, da ceto Rayuwar shi da sukayi, taimaka mashi suka cigaba da yi, har numfashinshi ya daidaita, sannan suka ɗan ƙara mashi allurar barci, lamo yayi yana sauraren su har dai nannauyan barci yayi awon gaba dashi.
Hajiya Kubra da tini tabar kuka, saidai ajiyar zuciya da take sauke wa, to dama dai Bilal da Abie ɗinne masu lallashi ta, shi kau Alhaji tsabar ɓacin rai da Abunda taja masu ya sanya ko kallon ta ma ya dena yi, ba yanda likitocin ba suyi ba akan su shiga office ɗinsu su zauna, Amman hakan ya gagara.
Bilal da yake ta safa da marwa hannuwan shi goye a bayan shi, fuskar nan tashi ba annuri Sam, ya san ba ƙaramar matsala bace yin hakan ga Al'ameen, ya sani duk lokacin da aka faɗa mashi wata magana ne ta ɓacin rai ko mummunan abu ne yakanyi haka tin yarintar su, likitocin cen ƙasar sun sha gargaɗin a dena ɓata mashi rai irin haka, amman dai hajiyar bata ji, tinda zai iya cewa ya lura kaman ita ce sanadi a yanda yaji Alhaji na cewa
"hankalin ki ya kwanta, ke har abada ba zaki dena ɗaukar jita jita ba, ba bincike ba komai kin laƙaba ma ɗanki ƙazafin da aka yi mashi, to inaso ki sani, ni ban yadda da Abunda kika zo dashi ba, ba kuma zan yarda ba har abada, ko daga baya kika ƙara tada zancen nan, ko su Maryamar kika yi mawa ban yafe maki ba, kuma wallahi kika yi sanadin da yarona ya mutu sai nayi shari'a dake, tinda Nidai tini nace ƙibar maganar, da yake bakya jin magana kika yi kunnen uwar shegu, su masu kawo maki gulmar ai gashi sun zura ki zaki kashe ɗanki da kanki, in ke kin lamunta ni Sam ba zan iya lamunta ba, dole ne in aka gama bikin nan in yi bincike da kaina, duk wanda na samu da hannu cikin Al'amarin nan zai sha mamaki na wallahi, ashe ni ina cen ina ta yadda zamu samu rufin asiri, ke kina nan kina fama da magulmata munafukai a cikin gida da ma wajen gidan, kin kasa riƙe gida kina cen kina ta zuba mulki da isa, in ma hakan ta faru wanene keda sila? Ai kece tinda saida yace a aura mashi ita, atafau ke kika ce ba haka ba, kin manta ƴaƴan yanzu duk yanda suke maka biyayya, zasu iya bari akan Abunda suke so, kuma hukuncin Allah rubutacce ne"
Yana gama faɗar haka ya koma gefe ya zauna, hannayen shi harɗe cikin na juna, sai karkaɗa ƙafa yake yi ƙasa, ita zata iya cewa tinda take duniya ma bata taɓa ganin ɓacin ran Alhaji haka ba, shi mutum ne mai sauƙi, duk da yadda yake tsaye akan al'amarin gidan shi, dawowar Al'ameen ɗinne ma ya samu sauƙi ya janye ya bar mashi wasu al'amurran.