← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 56

Sashe 41

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan juyawa nayi ina mai sake kallon shi, shi ɗin dai ne, Ya Ameen ne yake ta tuƙin shi hankali kwance yake zaroman magana kaman ba shi ba, ashe dama yana magana haka?

Tinani nake ta faman yi, yayin da shi kuma ya sake maida hankalinshi a kan tuƙin shi, ban tashi farfaɗowa daga kogin tinanin da na shiga ba saida naji tsayawar mota alamar dai mun iso inda zamu.

Ɗaga idanuna nayi ina mai ƙare ma wajen kallo, yayin da shi kuma har ya fita gami da kullo ƙofar.

Airport ne muka zo, lallai wajen ya ƙayatar dani, ba ƙaramin ƙaramin kyau wajen yayi mani ba, na saki jiki ina ta more kalle kalle na, tinda na san baya cikin motar, Naji maganan shi kaman daga sama.

"Malama sai ki fito"

Ɗan zabura nayi, kunya duk ta dabaibayeni, domin Sam bansan yana tsaye yana kallo na ba, ashe glass ɗin motar ƙasa yake kaɗan.

Fitowa nayi, zullumi da fargaba duk sun cika man zuciya, na san yanzu umma ta suna cen suna nemana, wayyo Allah na, na san kuma Hafsat zata ce mata bata san inda na tafi ba.

Gaba yayi ina bin shi a baya, sai harÉ—ewa nake ta cikin hijab, yana kallo na kuma bai ce man komai ba, sai nayi kaman zan faÉ—i, sai ya juyo ya É—an kalle ni Amman ba zai ce an komai ba.

Mutane ne ke ta hada hadarsu, ga wajen tar da hasken ƙwan fitilu mashi masifar haske kaman rana.

Wasu da ƴan alluna, an rubuta su aye, ga mutane suna ta fitowa daga wani ɗan ɗaki na glass, tin daga nesa ya hango shi, da ƴar sassarfa ya ƙara so inda muke gefe tsaye Ya Ameen yana ta gabana haka.

Tafasa sukayi lokaci guda suna sakar ma kansu murmushi na tsabar ƙauna irin ta aminai

"Ya dai Friend? Ai ban É—auka zakazo haka da wuri ba, na ÆŠauka sai ka shanya ni kaman yanda ka saba"

ÆŠan murmushi na gefen baki ya sake yi, sannan ya shiga cewa "wallahi ai kasan gidan mutane sun yi yawa, duk an cika gidan da Bidi'o'i sun dameni, suna neman fasa man kunne Shiyasa ma na fito haka da wuri"

Juyawa sukayi suka shiga tafiya suna riƙe da hannayen juna.

Da alama ma ƙila ya manta da wata abu wai ita Suhan a bayan shi tsaye.

Ganin haka nima sai na shiga binsu, mu yi tafiya mai É—an nisa, sannan muka isa ga motar tashi.

Sai sannan ya tina da ita, juyawa yayi a hankali yana kalle kalle alamar yana neman wani abu.

Da yake ina ta gudan ɓarin mota bayan Bilal ɗin sai bai lura dani ba, ganin ya juya alamar zai koma ta inda muka fito ne ya sanya ni cewa "gani nan yaya"

Tsayawa yayi, gami da juyowa, ya sanya key ya buÉ—e motar, Bilal É—inne ya juyo a É—an razabe jin wata irin siririyar muryar mace ta bayan shi.

Kallon tuhuma ya shiga yi ma Al'ameen, yayin da shi kuma ya basar yana mai shige wa motar, bayada zaɓi illa shima ya shiga, zamana cikin motar ne yayi daidai da tashin motar yayi revos ya halba ta bisa titi.

Ba wanda yace uffan har muka yi nisa, ganin shirun tayi yawa ne kowa da Abunda yake saƙawa cikin rai, ya sanya Bilal kauda shirun ta hanyar cewa "Mutumena ya hidimar biki"

"Suna cen suna yi" ya bashi amsa a taƙaice, shiru Bilal ɗin yayi don ya san halin Al'ameen ɗin, tinda ya ji ya fara amsa mashi a gajarce ya san ƴan maganar basa kanshi.

Har muka isa gidan ba wanda ya kuma tankawa, an tashi daga mothers eve ɗin da ya tashi daga evening ya koma night, sai aje ayi ta faman ƙara'in salloli kuma.

Da kwai sauran mutane, Amman jefi jefi, har cikin gidan ya shiga gami dayin parking, dama abunda nake jira kenan, nayi saurin ɓalle murfin motar gami da ficewa, kai tsaye sashen amaren na nufa da yanzu cen ɗakinsu Hafsat nake kwana.

Duk agaji anyi tuɓus, wasu ma duk sun kwakkwanta, hakan ce ta sanya ba kowa ne ya lura dani ba, Hafsat ce kawai zaune tana waya da angonta, ita kau Afnan ta shiga watsa ruwa toilet.

Lallaɓawa nayi gami da kwanciya kafin Hafsat da take tsaye bakin window ta ganni.

"Tashi Tashi na ganki wallahi, gaya man daga ina kuke?" Abunda Naji hafsat ɗin ta faɗa kenan, bansan ma lokacin da ta katse wayar ba, sai ganin ta nayi har ta ƙara so inda nake kwance bisa katifa.

Tashi nayi duk borin kunya ya kama ni, cire hijab É—in na shiga yi, ina cewa" uhmm wai daga ina muke? Ko dai daga ina nake, ko kin ganni da wani ne da zaki ce daga ina muke?"

" Eh" ta bani amsa kai tsaye, sannan ta É—ora da cewa "ke da Yaya Al'ameen da Yaya Bilal da ganku kun dawo yanzun nan"

Ɗan zaro idanu nayi, kaman ƙasa ta tsage in shige nake ji uwa wadda tayi wa sarki ƙarya.

"Kinga fa wallahi shine ya......" fitowa afnan ce daga toilet É—in É—aure da towel ya katse man maganar da nayi niyyar faÉ—a ma hafsat É—in.

"Humm" kawai afnan ɗin tace tana ɗan murmusawa, da alama duk taji zancen da mukeyi, saidai ƙala bata ce ba.

Lura da ita ne da Hafsat ɗin tayi ya sanya ta basar da zancen itama, tana mai miƙewa zuwa toilet ɗin.

Duk ina zaune ina saƙawa da warwarewa, har afnan ɗin ta gama shirin kwanciya, lokacin ne Hafsat ta fito da alama itama wanka tayo, "Ki tashi ki bar tinanin hakanan Aunty Suhan kije kiyo wankan kema" Abunda afnan ɗin tace man kenan, ta sake gyara kwanciyar ta gami da juyawa tana murmushi.

Duk fa na bi na tsargu kaina, kaman wadda kwai ya fashemawa haka na miƙe ina jan ƙafafun nawa har na shige toilet ɗin. Da murmushi itama Hafsat ɗin ta bini, tana fatan Abunda take zargi ya tabbata, da tafi kowa jin ɗaɗi, kuma taga ƙarshen Hajiya Kubra da ta ɗauki son duniya da burin duniya ta aza shi akan yaron nata.

Makullin sashen kawai ya miƙa mashi, yana mai cewa "bari in nemo mana Abunda zamu ci" Amsa Bilal ɗin yayi gami da juyawa ya nufi sashen aminin nashi, yayin da shi kuma Al'ameen ɗin ya kaɗa kan motar gami da sake ficewa daga cikin gidan.

A bisa kujera 3seater ya zube, gajiya fal a cikin jikin shi, Amman ba ita ce tafi damun shi ba, ganin aminin nashi da yayi da yarinyar da yake iƙirarin auren ta, kar dai ace da gaske abokin nashi yake akan zancen yarinyar, saidai lura da yayi da yanda ya gansu, da kuma irin zaman da aka yi cikin motar har kawo dawowar su gidan babu wata alama dake nuna maka cewa su ɗin soyayya suke, Amman in ko haka ne, menene dalilin Al'ameen ɗin na yawo da ita cikin mota da daddare haka?

Ya daɗe nan kwance yana saƙawa da warwarewa har Al'ameen ɗin ya dawo, nan ya tada shi kwance yayi zurfi a tinani, ɗan dukan shi yayi a cinya yana "tashi yallaɓai, ba dai bacci kake yi ba haka, ko wanka ba kayi ba balle kaci abinci"

Tashi yayi yana murje ido, yayin da Al'ameen É—in ya wuce kitchen É—auko spoons da plate da lemo da ruwan sha, a haka ya dawo ya tada abokin nashi zaune yana narai narai da idanu.

Zuba masu abincin yayi, yayin da ya jawo stool ya ɗora masu akai, Al'ameen ya san darajar baƙo, duk da kasancewar Bilal ɗin ɗan gida kuma aminin shi, haka yake in yaso har ruwan wanka yana haɗa mashi in ya kawo mashi ziyara.

Har suka gama cin abincin, Bilal na ma Al'ameennÉ—in kallon tuhuma, to abunka da aminai, tini Al'ameen É—in ya É—ago shi, murmushi yayi yana mai goge baki da tissue

"Bari in gaya maka Abunda kake son tambaya ta tin kafin ka tambaya, yarinyar da ka ganni É—azu ya ita, na san dai ka santa kasan komai a kanta, kuma har yanzu ina kan baka na a kanta, saidai ita bana tsammani ntasan komai, dalilin da ya sanya kuma ka ganni tare da ita, shine....... " nan ya kwashe komai ya faÉ—a mashi a gajarce.

Murmushi yayi yana faɗin" Mugu, watau har kasan Abunda nake son tambayar ka ko? To ai shikenan Allah ya zaɓa mafi alkhairi a cikin Al'amarin, Amman dai ka kula gudun ja ma yarinyar matsala ko a wajen mahaifiyarka, kadai ga yanda take iya ƙoƙari wajen bata tarbiyya" yana faɗin haka shima ya ajiye spoon ɗin dake hannun shi ya tashi gami da shige wa bedroom domin yin wanka da rama salloli dake kanshi, sannan ya kwanta, shi kau oga Al'ameen, maida komai yayi kitchen, gami da wanke na wankewa, ya gyara komai tsaf, dama haka yake, baya son ƙazanta ko kaɗan, duk wani abu da ya san zai yi na tsabta baya jira ayi mashi shi keyi da kanshi, saidai Abunda ya san zai ɓata masa lokaci ne. Hatta da girki ba Abunda bai iya dafawa ba, saboda shi ba abincin kowa yake iya ci ba, ko zaman da yayi ƙasashe waje shi keyi a kanshi abinci, matuƙar bai yadda da wanda aka kawo mashi daga cikin hotel ɗin ba.

Sun daÉ—e suna fira kafin su kwanta, yayin da ni kuma har bayan na kwanta É—in juye juye kawai nake yi, hafsat É—in na kula dani, har yanzu bata gaji da wayar ba haka, tinani nake yi na abubuwa da dama, Amman tinanin nawa yafi karkata ma ga Jarabawa da na rubuta kusan kwanaki da dama baya.

Sai daga baya ne tinanin Al'ameen É—in ya faÉ—o mani, lallai ni bansan ma me zan kira Abunda yayi mani dashi ba

Gashi in akula har yaja hafsat ta fara mana wata fassara ta daban, ɗan guntun tsaki naja ina mai sake gyara kwanciya ta gami da karanto addu'oin barci, banga dalilin ma ɓata lokaci yin tinanin abun ban haushi ba, ko in kalle shi inji me? Ko ya ɗauka nima ina cikin ƴan matan da suke rububinshin ne oha? 🤷🏻‍♀
Chapter 41 · 0% Book details