← Book details Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 65

Sashe 61

Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maman su papa ko ita kawai dena magana ma tayi saidai take ta kallon mutane ko mai za'a mata na farin ciki to baza tayi dariya ba abin yayi ta damun su papa da daddy kullin ina bata labaran dariya amma abun ba sauki haka mukaci gaba da rayuwa me cike da k'unci

BABAN SHEKARA BIYU

Wata rana su papa da daddy suka tafi legos domin yin wani taro , nasu na manya

Kwana biyu basu dawo ba sosai abin yabawa maman mu mamaki ganin basu taba irin wannan abun ba

Muna gida munyi jugum jugum sai aka sanar wani nason ganin maman mu awaje fita mukayi tare

Tashin hankalin da muka shiga alokacin da mukaga gawar papa da daddy a kwance jini yanata kwarara a jikin su

Da gudu mukayi inda suke bude fuskar su papa maman mu tayi tana kuka sai jijjiga papa takeyi

Maman su yohun ne tazo itama aguje tana kiran sunan mijinta kafin wani lokaci gidanmu yacika da mutanen garin kowa kukan mutuwar su papa sukeyi saboda sune manya garin ragamar komai a wajansu take

Shiyasa suke ganinsu kamar iyayensu , haka munaji muna gani aka dauke, su papa aka binnesu

Sosai muka sake shiga damuwa mutuwar iyayenmu maza sai kowa yayi sanyi har mutanen garin

Bayan wata daya da mutuwar su papa aka rasa wadda zai gajesu ganin ga papa da banju sai akace su zasu maye gurbindu tinda su zama samari a lokacin
Haka kuwa akayi

Bayan cikar su papa shekara daya da mutuwa aka radasu , mai sunan papa shine ya maye gurbin papa banju ya maye gurbin daddy

Mutanen garin sukace dole suyi aure tinda an basu mulki

Hakan kuwa akayi dama muna soyayya da papa banju kuwa , lokacin bashida budurwa , sai wani dattijon garin namu yace ya bashi diyarshi ,,ai kuwa su maman mu sunji dadi sosai sukayi godiya har ya gida sukaje godiya

Aka saka ranar bikinmu sati biyu kadai kacal saboda bikin na gaggawa ne shiyasa aka saka sati biyu kacal

Banju da farko kin yarda yayi da auren yarinyar da aka bashi
Jin haka papa ya yaringa kwantar mishi da hankali yana nuna mishi idan sukayi aure zai so ta da haka aka shawo kanshi ya amince

Sati biyu nayi aka daura aurensu a majami'ar garin akayi shagali sosai harna kwana goma

Bayan biki aka kaimu gidanmu a lokacin gida daya aka bamu

Sosai nakejin dadin zama da kutta saboda tana hankali ga biyayya ta daukeni kamar yayar ta nima na dauketa kamar kanwata saboda banida yar uwa ,

Haka muke zuwa gidan su maman mu anan muke yini sosai sukejin dadin hadin kanmu

Auren da wata biyar kutta tasamu ciki aikuwa munsha murna sosai ba kamar ni dan ina son yara

Kutta takusa haihuwa surukar mu ta mutu wato maman su yohun munyi jimami sosai kafin mudawo nomal

Su papa ko sosai suke kawo mana cigaba a garin mu hakan yayiwa mutanen garin dadi sosai

Ranar asabar kutta ta haifi danta namiji ai kamar na maidashi cikina saboda tsananin son danakewa yaron

Sosai nake kuda da ita komai ninake mata dan ko mamanta saidai ta kallemu nida ita kuma tanajin dadin zaman mu

Ranar suna aka sakawa yaron suna joshow ,,sunan yayimin dadi sosai

Bayan suna aka ce za'a tafi kutta aikuwa na haukace musu nace bansan zancen ba , na ringa kuka nace babu inda zataje ta barni ni kadai ba sosai nake kuka

Gaban maman ta na zauna ina kama kafar ta nace tabarmin kutta zan kula da ita

Kallona tayi sai taga nabata tausayi tayi murmishi tace shikenan ta bari

Aikuwa da sauri naje na dauki joshow na goya na kama hannun kutta nace muje part dina acen zata zauna

Dariya suke min ganin nazama kamar wata zararriya maman mu tace a su ingozi badai son yara ba ,,,ficewa nayi na bansu ban kula suba

Haka naci gaba da kula dasu kutta da joshow , komai ninake mata

Banju da papa ko ba karamin dadi sukaji ba yadda nake kula da yaron da soyayyar danake nuna musu

Haka mukaci gaba da rayuwar mu mai dadi har kutta tayi wata uku tukun na mata lalle kitso duk mata saboda na iya sosai , na gyarata tukun papa yayo mata siyayya tashirya nida papa muka kaita part dinta ,muyi yar hira tukun muma muka dawo gidanmu

Kullin joshow na hannu na ina lalenshi , har yakai shekara daya da rabi , nina yaye shi yadawo wajena gaba daya , saboda lokacin banju aka kira daga kasar America donyin wani aiki haka suka hada kayansu muka kaisu legos nan muka jirginsu ya sauka ,

Sallama mukayi muna kuka nida kutta su papa na mana dariya

Jirgi yasoma kira nan muka rabu sai tafiya sukayi jirginsu ya daga zuwa America , nan muka dawo gida cike da kewarsu

Naci gaba da kula da joshow wasa wasa su banju suka shafe shekara uku a America sau daya suka zo ganin gida amma muna waya dasu

Da suka shirya dawowa nan banju ya kira papa yace zasu dawo gida gaba daya gashinan jirginsu zai tashi zuwa legos

Murna nasoma nace zanbi papa legos yace a a namusu girki kawai nan yatafi ni kuma nayi girki na gyara joshow

Papa na xuwa legos ya zauna jiran jirgin su banju yazo ,,, abu kamar wasa har yamma ba su zoba abin yabashi mamaki

Yana zaune nan yaji ana magana a spika da sauri ya nutsu dan yaji mai ake cewa nan mai magana yasoma da fadin

𝗝𝗶𝗿𝗴𝗶𝗻 𝗱𝗮𝘆𝗮 𝘁𝗮𝗳𝗼 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗮𝗺𝗲𝗿𝗶𝗰𝗮 𝘇𝘂𝘄𝗮 𝗹𝗲𝗴𝗼𝘀 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗮𝗰𝗰𝗶𝗱𝗲𝗻𝘁 𝗺𝘂𝘁𝗮𝗻𝗲𝗻 𝗰𝗶𝗸𝗶 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘄𝗼𝗻𝘀𝘂 𝘀𝘂𝗻 𝗺𝘂𝘁𝘂 𝘄𝗮𝘀𝘂 𝗴𝗮𝘀𝘂𝗻𝗮𝗻 𝗮𝗰𝗶𝗸𝗶 𝗮𝗻𝗮 𝗱𝘂𝗯𝗮𝘀𝘂 𝗱𝗮𝗻 𝘀𝘂𝗻 𝘀𝘂𝗺𝗮

A razane papa ya mike yanufi inda aka fada wajan gawawwakin ya ke budewa yana dubawa ,cen yaga gawar banju da sauri yamatso yana fadin kanina dubawa yayi baiga kutta ba

Wajan masu jinya yanufa yana dubawa nan yaganta tana kuka an nade mata kai da bandej da gudu yayo wajan ta

Tana ganin shi ta sauko tace ina banju kasa mata magana yayi sai ya kama hannun ta suka fito nan yakaita inda gawarshi take
Tana yin arba da shi yamutu nan ta yanke jiki ta fadi sumanmiya papa kusan haukacewa yayi saida ya dauko ruwa yazufa mata ta farfado , tana kuka sosai wani doctor yaxo yace kuna da wanda ya mutune papa yanuna mishi kanin sa

Daukar shi yayi agadon nan suka fito aka sakashi a mato ya saka mutta da kyer yake dravin saboda zafin da zuciya take mishi Allah ne kadai yakawosu gida

Suna shiga gida aguje na taresu ina oyoyo kanwata ga kanina ,turas nayi ganin kutta ta nufoni tana kuka sosai

Abin yabani mamaki sosai kasa daurewa nayi nace kutta lfy kike kuka , ai murna zakiyi da kuka dawo gida lfy

Papa ne yafito shima kukan yake sosai

Hankali na yatashi ganin suna min kuka kuma bamai min magana nima na ringa yin kuka bamai rarrashin wani

Papa ne yayi karfi hali yadena yace ingozi banju ya mutu accident sukayi na jirgi sai itace bata mutu ba

A zabure nake kallon shi da dauri na bude motar nan na ganshi a shimfide

Ihu na kurma ina shikenan family mu sai karewa sukeyi yanzu kaka da maman mu ne suka rage mana

Aikuwa yan unguwa suka shigo dan ganin mai nakewa kuka ,mugun ganin da sukayi suma nan suka ringa kuka

Kama kutta nayi muka shiga ciki akayi majami'a da banju cen suka binneshi

Maman mu naji mutuwar banju ciwonta na zuciya ya tashi itama tace ga garinku nan

Wannan lokacin hauka ma nayi nida kutta har kullemu ake a daki saboda da gudu muke fita kamar sabbin shiga hauka ,,haka muke

Bayan sati daya na zauna saiga kutta da joshow suka shiga zama sukayi na share hawayen fuskar ta ina kallon su

Kutta tace haba yakamata kidena kukan nan ya isa haka

Kallon ta nayi sosai kafin nace taya bazanyi kuka ba kutta yanzu fa kaka kadai ta ragemin duk duniya sai ita duk suntafi sun barni

Rungume juna mukayi muna kuka

Haka mukaci gaba da rayuwa ba dadi amma har yanzu ban haihu ba , ban damu ba saboda mamanmu tace itama tadau shekaru bata haihuba shiyasa ban damu ba

Joshow saida yacika shekara 12years tukun nasamu ciki ,, aikuwa sosai muke murna zamu karu

Kutta ke aikin komai ta hanani koda daukar cop ne nakai kitchen haka nake zama na nida joshow idan yadawo daga school

Wata rana na haihu ya' mace zo kuga murna wajan papa sosai yake farin ciki harmu da kaka

Papa yace asa mata sunan mama na ,nace a a yasa duk wanda yakeso

Papa sai yace to asa mata jenifer sunan kaka aikuwa kaka hadda kukan ta jin taji takwara

Haka mukaci gaba da kula da yaranmu jenifer da joshow

Jenifer shekara ta daya da rabi na haifi kaninta daga nan haihuwar ta tsaya , nan suka zama su uku sosai muke kula dasu

Bayan wata shida kaka itama ta mutu munyi jimami kafin mudawo nomal

Haka muke tare har yaran suka kai aure muka hada jenifer da joshow aure ganin suna son junansu

*WANNAN SHINE ABINDA YA FARU LOKACIN DA KUKA. BAR GARIN DAJI*

Inna ko kuka take sosai tace Allah sarki papa na su mamana duk sun rasu ashe

Mama tace eh yaya maryame sunfa rasu sai gashi dalilin jikar mu ta hada familyn masha Allah kuma mundazama musulmai Alhamdulillah zamuce

Daddy da abba da ubbu suka amsa da ameen gaskiya munji dadin haduwar wannan family ashe batan ameera alkhairi garemu masha Allah

Muhammed ne ya mike yace to daddy zan tafi gida ga ikram nan bayan kwana biyu zanzo daukar ta

Daddy yace baka tsayawa akira la'asar da yamma sanyin marece saika tafi

Murmishi muhammed yayi yace a a zanje gida nayi wanka ne ko wanka banyiba nazo to zan wuce

Inna tace dan kan uba shiyasa ashe nakejin falon yana tsami ashe kaine kazami , shiyasa ka kasa samun matar aure , yowama zai auri miji kazami ,saidai irinka kalle ka kamar wani dodo duk kayi baki kamar kayi birgima a toka tana banka mishi harara
Chapter 61 · 0% Book details