← Book details Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 65

Sashe 16

Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dagowa, tayi tace "good morning my sweet yaya,, murmushi yayi, yana zama bakin gadon, yace morning wife na dafatan kintashi,, lafiya,, itama murmushin ta mayar mishi tace alhamdulillah, mungode wa Allah, yace to, zo mu kwanta,, kafin karfe,, goma tayi mutafi kotu, ,kayan, sallar tacire,, taje tasaka riga bakin gwiwa, tazo suka haye gadon,, nan yaja musu bargo,

A gidansu, Aliyu kuwa tin jiya Alhaji hashim baiyi bacci ba sabida tashin hankalin, dayake , ciki ganin dan gwal din nashi a hannun yan sanda, kuma gashi, D.P.O. , Anass yace, bazai bada belinsa, ba , yakasa koda cin abinci da, yunwa, ya kwana' yanzu ma yakira, lauyansa, ne yana fada, mishi komai "" bayan yagama ya dasa, aya, daga, cikin wayar aka ce ranka yadade karka, damu, ai, babu wanda ya isa yataba, aAliyu, yazauna lfy, murmushi alhaji hashim ya yi, yace ai nasan idan inadakai,, bazaka bari wani yaci galaba akaina ba yace haka ne yallabai,, nan sukayi sallama, itakuwa mama tana jinsa amma tayi, kamar, batajinsa,, taci gaba da karatun, ta, bayan " tagama ne, yace kishirya, "anjima zamuje,, kotu, wajan shri'ar su aAliyu fatiha ta shafa tace to Allah yakaimu anjima din nan tafice a , dakin tana jinjina, hali irin na mijin nata, shi baisan damuwar kowaba, inba tashiba, data dansa ba, haka tashige dakinta bayan ta gaisa da masu, aikin gidan tashige dakinta

A gidansu,, Ameer kowa yashirya sun fito, falon gidan harda, hajiya inna sai cika take tana, batsewa wai jiya Ameer ya zageta, shikuwa, ko, a" ajikinsa, dan babu wanda zai tafin masa da mata wani kauye,, su , abbane sukace zasutafi, nan daddy yace subari adawo daga kotu inyaso shesu tafi gidan, da haka suka fita zuwa kotun saboda,, 10AM za'a saurari kararsu,

Bangaren Anass ma da ,, Bilal suma cikin shiri suka, fito kamar hadin baki, atare sukayi fakin bakin,, felin kotun, nan suka shiga gaisawa, nan , suka shiga, ciki ,, kowa ya zauna kotun tacika bak'il, da mutane,, nan aka kawo Aliyu, duk jikinsa ya yi bak'i kamar bashi , bane Aliyu , dan gata maiji, da izza yayi zuru-zuru,, bayan alkali, ya zaune aka soma gabatar,, ta kara,, saboda akwai wani karar,, kafin nasu ,, bayan angama ne mai gabatar,, da kara yatashi yasoma, da

A yaune ranar alhamis zamu saurari karar,,Ameer Muhammed da kuma Aliyu Haidar alhj hashim, akan zarginsa,, dayake yasace masa mata yana kokarin keta mata haddi, ,nan kotun tayi shuru jin sunan dan wanda ake kara,, yaron da baya ganin mutumcin kowa agarin nan alkali, yace lauyoyin, masu kara da wanda ake kara,,nan, wani yatashi , yace"" ranka ya dade ni sunana ,, barrister mansoor usman, nine lauyen wanda yake kara,, tukun ya zauna,, wani yatashi,, yace ranka "yadad'e ni sunana,,, barrister mustapha kamal, nine lauyen wanda ake tuhuma ,, shima, yakoma ya zauna, alkali yayi rubutu kafin, yadago yace ko lauyen wanda yake kara, yana da magana barrister mansoor Usman, yamike yace eh, inadashi ranka yadade yamike nan yayi wajan Aliyu , ya gyara,, tsayuwarsa,, kafin yace,, kozaka fada, wanene kai, ,,Aliyu yasaita, kanshi yace,

Sunana Aliyu haidar alhj hashim, anhaifeni,, a karin kano anguwar, nasarawa, J R A , , barrister mansoor yace, masha Allah, kozamu iya sanin menene alak'arka da, Ameer, Mohammed , aliyu yace abokina ne munyi, karatu dashi, a London, anan muka daura, abota,,,barrister mansoor yace to menene yasa, kasace mishi yar, uwa kuma mata, , yace saboda, inasonta,

Kowa na wajan sai kuskus, akeyi lauyan,, Aliyu ne zai tashi yin korafi, akaci sa'a Aliyu yana kallon shi yadaga mishi hannu, alama, bayason, lauyan, nasa yayi magana , saiya koma yazauna shikuwa Alhaji hashim sai zufa yake sharcewa, kamar, wanda yayi gudun tsere ita kuwa mom dinsa sadda,,kai tayi, saboda"" ciwon ta yanason tashi, barrister mansoor yace to daka saceta mai zaka mata,, ba tsoro aliyu yace , tin lokacin dana ganta nakamu da so da kaunarta, kullin sonta, kara shigata yake, gashi ,,afarkon haduwarmu,, abokina, yace matar sa ce ni kuma ban yadda ba da zancen sa danaga,, nakasa samun haduwa, da ita shine nasa, aka satomin ita amma sai taki yadda dani ,, shine nace tabani kanta,, amma ta kiya ina shiga inda take,, zata fara gudu ,, lokacin,"" da naso yimata fady ina kokarin mata, saiga police " sunzo shine suka kamani,, wannan shine abinda yafaru, yakai karshen zancen yana share hawayen fuskar shi saboda, yanajin, nadama "" na kara shigarshi, barrister mansoor, yace,

Dama kataba yiwa wata kokarin, fady ko kuwa Ameera ce farko, Aliyu yace, ba ita kadai bace wata yar aiki gidan mu harda, cikina ajikinta, amma yanzu bata gidan dan daddy na yakoreta,, saboda tace nine namata cikin shine daddy yakoreta, yace tana min sherri ,ita kuma dazata fita tace min insha Allah saika wulakanta saika tozarta a duniya kafin ka mutu, kuma sai duniya baki daya, tasan kai tantirin dan iska ne ,, banza namata saboda alokacin ko a jikina sbd daddy na shiya dauremin gindi nake duk abinda nakeso a garin mutum ko wayeshi, idan yashiga gonata, zan kafta mishi rashin mutumci, komin shekarun sa sbd babana ya nunamin cewa babu abinda ,zan nema na rasa, yanzu kuma naji tsoron Allah yashigeni, nayi nadamar abubuwan danake aikata mahaifiyata,, kullin cikin koka halina, take amma sainake cemata,, ita bata sona kamar daddy " sai tace aliyu wannan fa ba soyayya,, bace babanka yake nuna ma idan kaci gaba da wannan dabi'ar to wllh karshenka bazaiyi kyau , idan tabafadi haka daddy na zai rufeta da fada,, na fadawa kotu gaskiya ne saboda karna bata wahalar Shari'a alhalin nasan komai,, kuma nayi nadamar abinda na aikata,, yana kaiwa karshe ya rushe da kuka mai tsuma zuciyar mai karatu

Alkali yayi rubuce rubuce kafin ya dago yace ko lauyan wanda ake kara yana da magana,, saboda karfin hali,, barrister mustapha, yamike yace eh inada ita, alkali yace to zaka iya tambayar ka barrister mustapha yace inason kotu takira mana, 𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 𝙙𝙖 𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧𝙖 , juyawa akayi mai kira yace kotu tana neman ameer da ameera,, nan ameer yamike ameera, na manne ajikinsa, yace mata babu abinda aliyu zai mata tinda gashi amma taki yarda, sai kuka take, ahaka suka je kusa da aliyu sake kankame ameer tayi tace yaya kada kabari yataba,, ni please tsoron sa nake ji rungume ta, yayi yanajin kunyar mutanen dake wajan yace , babu komai please kinutsu, tambaya zaa miki,, tukun ta dena kukan

Barrister mustapha yazo kusa dasu yace kozamu iya sanin cikekken sunanka, , Ameer yace sunana ameer Muhammed,, an haifeni a garin kano a anguwar nasarawa J R A,, amma babana dan asalin jahar katsina ne barrister mustapha yace menene alak'arka da Aliyu ,, Ameer yace abokina ne shi munhadu a London wajan karatu ,, barrister mustapha, yacewa, ameera yarinya, ko zamuji cikekken sunanki "" dagowa, dayi,, daga jikin ameer tace sunana ameera Ahmed,, anhaifeni a garin kankara jahar katsina, , barrister mustapha yace kokinsan,, wannan yanuna mata aliyu ,, da sauri takoma jikin ameer kamar zata koma cikinsa ,, tana kuka tace shine, yasa aka, saceni"" zai ketamin mutumci na danaki yarda, shine yace zaisa akashemin, yaya ranar, da yazo yafi karfina har rigata ya yagamin,, da hijab dina, alokacin harna saddakar mutuwa zanyi saiga, yaya bilal ya banko kofa nan naje wajan sa shine suka kamashi,, ta dago ,tana kallon aliyu tace azzalumi macuci dan iska fasik'i, ,, sai Allah yasaka min raunikan, daka min da kataba jikina ban yafe makaba ,, shine, bayan nadawo gida yaya yace ayimin wankin ciwon har akamin allura,, yanzu ma hannuna ciwo yake,, duk kai kasa yaya yace sumin allura to wllh kaci wuta balbal,, ta kai karshen magana tana murguda,, baki mutanen wajan sai dariya suke saboda ameera tabasu dariya,

Nan akace sukoma sukoma wajan zamansu suka. zauna ,, alkali yayi gyaran murya, yace bisaga yadda wannan kara yakaya kuma wanda, ake zargi yace, ya aikata, kuma yafadi gaskiya,, batare daya baiwa kotu wahala ba,, alkali yace,, kotu ta,, yanke,, mishi hukuncin ,,, aliyu yayi kasa dakai,, yana sonjin wani hukunci zaa yanke mishi ,, alkali yace anyanke mishi hukunci shekara biyar agidan yari,,tareda aikin horo mai tsanani, nan alkali yabuka, gudumarsa aka mike kowa yafita, waje mahaifiyar aliyu ce taje wajan su mommy,, da sallama takarasa, nan suka amsa, mata, tashiga basu hakuri tana kuka mommy,, tace babu komai sun yafe mata tukun ta fice aliyu kuwa yana ganin babansa na mishi magana amma yayi saurin shigewa, motar police kowa yabar wajan

Suna zuwa gida,, daddy yakira su Anass yayita saka musu albarka shida Bilal, tukun yakashe, wayar su abba sunci yanzu, zasu wuce gida , bayan sallar azuhar, su daddy suka musu, rakiya, abbu yace, yar gidan, Inna bakice, agaishe miki dasu umman kiba rufe fuska tayi tace abbu kace,, ina gaishesu " idan aka bamu hutu zanje musu,, Abbu yace to shikenan, tukun suka fice agidan, kowa yazo falo,, yazauna " ita kuwa ameera tana nan manne da ameer dinta,, Inna ce tajuyo taga ameer yana saka kanshi tsakanin wuyar ameera da kafadunta,,

Salati inna tayi tana tafa, hannu, tace a ni maryama,, wannan iskanci, dame yayi kama kai, ameeru,, haka dama kake ban saniba,, banza yayi da ita su fatima kuwa sai dariya,, suke kasa kasa,, dankar inna taji tasauke musu ruwan masifa,, Inna tace to wllh gobe zan tafi da ameera,, itakuwa""" Ameera ta lafe ajikin shi sai shakar kamshi mai sanyin dadi take,, tace yaya, dagowa yayi yana kallon ta yace,, my wife,, menene, shagwabe fuska tayi, tace nidai bacci nakeji mutafi,, daki,, murmushi yamata yace to shikenan,, muje na kwantarki,,, kuka inna tasaka tace yau naga takaina shikenan ya asircemin jika, su mommy tuni, sukabar falon, shesu ameer bai kula taba ya dauki ameera kamar,, jariri yayi sama da ita yabar inna na fada tana zaginsa,,, wai ya iskanta ameera,,

NAGODE DA COMMENTS AND SHARE DINKU FANS INAYINKU, SOSAI
[26/10, 22:57] MRS. MU'UTASIM: 🌟𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑 𝐃𝐀 𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑𝐀🌟

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝙖𝙣𝙙 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮

𝐌𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐍𝐔𝐒𝐀𝐈𝐁𝐀 𝐂𝐄✍🏻

💫💫
JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️

https://chat.whatsapp.com/Gu2Mxr0SRlx8Da4tv0J2AR

MARUBUTA MASU AIKI DA JARUMTA DOMIN WA'AZANTARWA ILIMANTARWA NISHAD'ANTARWA TARE DA FAD'AKARWA DA JAMA'A BISA HARSHEN HAUSA 💪

💫(J. W.A)💫

Follow this link to join my WhatsApp group::https://chat.whatsapp.com/Gu2Mxr0SRlx8Da4tv0J2AR

25—26
Chapter 16 · 0% Book details