← Book details Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 65

Sashe 4

Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana matsowa kusan su ameera ta kara kamkame yayan nata

ameer yace kai dakata cikin tsawa

Da sauri lado yaja birki ya tsaya

Ameer yace lfy ?

lado yace wannan yar iskan yarinya jiya saida suka yimin targade ita da kawar ta khadija yana nuna ameera data cakume ameer

Ameer yace to kayi hakuri nawa ne kudin gyara

......Lado yaji kudi saiya saki ransa yace raina dari biyar ne

Ameer ya ciro kudin a jakar sa yabasa yace karka sake koda ka ganta a wani wajan ka daketa

Cikin jindadi lado yace ai ranka ya dade bazan ma ko kallon taba bare duka

Ameer yace to shikenan tashi kaje nan yabar wajan

Ameer yace wai maiyasa ke bakijin magana ne kullin kina fada kamar baki gajiya

turo baki gaba tayi tace to yaya bashi bane yake zagina shine jiya muka rama

kunnan ta ya murde ta saki kara tace waiyo Allah yaya akwai zafi tana yarfa hannu

Harara ya aika mata yace ai daukeki zanyi mukoma birni kowa ma ya huta da wannan fadan naki

Da sauri ameera tace da gaske yaya tana tsalle

yace gobe kuwa zamu tafi nan ta kama murna suka yo gidan

Abba ne zaune shida umma yana fada mata shawarar dasuka yanke na hada auren ameer da ameera

Sosai umma tanuna farin cikin ta taji dadi dan ta gaji da wannan fitinar na ameera tace Allah yasa haka shine mafi alkhairi kaga idan ta kara girma saita tare kafin lokacin tayi hankali

Abba yace hakane kinga zataci gaba da karatun ta acen

Su Ibrahim ne suka shigo shida hajara na biye da shi suka haye kan cinyar abba

Ibrahim yace abba wai sai yaushe zan girma nima kamar yaya safiyan

Umma tayi dariya tace sai ka kara shekara ashirin

Ibrahim yace to umma yaushene gobe idan natashi daga bacci zanganni babba kamar malamin mu na school

Hajara tayi caraf tace hmmm dallah cen bakauye kawai waya cema gobe zaka girma kuma malamin school dinmu uncle mustapha kake hada kanka dashi wannan garjejen k'aton dashi ta karashe maganar tana cuno baki gaba

Ibrahim yace yarinya idan nazama babba jirgi zan siyawa umma da abba suke zuwa saudiya da Dubai

Hajara tace to sai kayi tayi ai yaro

Umma tace to ya isa haka kufice kuyi wanka duba kuga yadda kukayi da kayan jikinku

Ibrahim yace umma anty hajara ce tace muyi gini na kasa shine fa muka bata kayanmu

Hajara a masifance tace mai karya asaka mishi rigar fatalwa ya kwana yana bingel bingel

Abba yayi dariya sudai kullin sai shirme akama gardama nan suka fuce

Abbu ma gidan yanufa shima yafada ma mama cewa gobe za'a daura auren ameer da ameera

Itama ta nuna farin cikinta tace Allah yasanya alkhairi cikin farin ciki abbu yace ameen masoyiya

dariya tayi dan tasan mijin nata badai barkonci ba yace ni ina su rashida kuwa

Tace suna daki yace ok nan suka kama hirar su na miji da mata

Daddy masaukin su ya nufa nan ya tarda ameer da ameera suna ta zancen su yaji dadi dan kuwa yasan irin son da ameer yakewa kanwar tasa

Sallama yamusu suka amsa gaishe shi ameera tayi tace natafi

Daddy yace to yar gidan inna, nan ta fice abinta

Daddy yace ameer gobe zaa daura auren ka

A razane yadago yana kallon sa yace dad aure na kuma nidawa

Murmishi daddy yayi ganin yadda ya rude alokaci guda yace kaida ameera

Ai tuni ameer yasaki fuska yace to amma dad ai ameera karama ce dukafa 12 years gareta saidai tayi school acen kafin tagama tayi hankali

Daddy yace nima haka na yanke shawara nan ya kira mommy yafada mata itama ta nuna farin cikin ta dan tana son ameera nan sukayi sallama

Da dare bayan sallar isha'i ameera tayi d'amara a kugunta taci kwalliya kamar wata aljana tafito tace inna zanje dandali bazan jima ba

Inna ta dubaita tace a a hadda kwalliya haka
Ameera tace eh

Inna tace adawo lfy nan ta fita abinta tana wakar karo taci da ameer taja da baya tana dafe kirji tace sannu ban ganka bane yaya

shikuwa ameer k'uri yamata da ido dan yaga ta caba uwar kwalliya kamar aljana yace ina zakije

Cuno baki gaba tayi tace dandali

Ameer yace daukan magana dai ?

Sake turo baki tayi

Yace idan kika sake turomin baki saina cire miki shi

Da sauri ta mayar tana dariya tace to shikenan matsa na wuce

yace karfa ki jima

tace bazan jima ba

Yabata hanya tafice

Tana fitowa saiga khadija itama tasha kwalliyar irin na ameera taci damara a kugunta nan suka tafi dandali

wajan yan mata ne da samari wasu na hira wasu na wake wasu na kallon su.

...Kafin su ameera su iso wajan wani saurayi ya tare ta yace a a su ameera kune sai yanzu

Kallon tara saura kwata tayi mishi tace eh mune ya akayi , yace dama jiranki nakeyi gashi kuma kinzo
Khadija tace buba kabamu waje mu fice

Wanda aka kira da buba Yace ke dallah cen danma kunga ana kulaku waye baisan halinku ba hatsabibai yana aikawa harar

Ameera tace khadija kyaleshi ai yaya yacemin kar nayi fada bata idarba ya buge mata baki aikuwa taji zafi

khadija tace aikuwa sai mun rama yana hararar su yace mugani mana, ameera ta jumke kasa a hannun ta tace inka isa juyo yana juyowa ta watsa mishi kasar a idonsa
Ihu ya saki ka yana dafin kin makauta ni, sukuwa dariya suke Dan su ganima sukayi kadan suka mishi sai gobe zasuje gidansu da dare sumishi balle balle da reza nan suka wuce

Yau dai basuyi fada sosai ba suka dawo gida ameera tafara shiga gida tukun khadija

Washe gari

Misalin karfe 3:pm bayan sallar jumma'a aka daura auren 𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 𝙙𝙖 𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧𝙖 akan sadaki raina dubu hamsin bayan angama su daddy suka iso gida ameer sai washe baki yakeyi

Ameera da aka fada mata an daura mata aure da ameer dinta aikuwa tahau tsalle tana taka rawa ita ala dole tayi aure kuma da ameer dinta duk wanda tagani sai tace anyimin aure tana dariya baruwan ta da damuwa ita ko ajikinta

Babu bata lokaci aka soma shirya musu kayansu na tafiya kano daga kauyen karkara

Inna na kuka tace ameera shikenan zan dena ganin ki , Ameera na dariya tace to kekuwa inna meye na kuka idan naje birni zanzo ina ganin ki kinji innata

Kowa na wajan dariya yayi dan ita batasan mai ake nufi da aure ba nan aka rakasu bakin kofa

Ameera ta soma gada musu hannu tana fadin sai wata rana umma da abbana natafi kano wajan mommy nake kwalliyar yan gayu ina kashe dauri ina hawa lilo tana ta surutun ta aka ja mota

Daddy ne ke jan su kuma suna baya shida ameera suna hirar su

MUHADU A GOBE INSHA ALLAH KUYI COMMENTS DA SHARE DIN NOVEL YAWAN COMMENTS DINKU SHINE KARFAFA MANA GWIWA NGD
[23/10, 23:12] MRS. MU'UTASIM: 🌟𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑 𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑𝐀🌟

𝙎𝙏𝙤𝙧𝙮 𝙖𝙣𝙙 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮

𝐌𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐍𝐔𝐒𝐀𝐈𝐁𝐀 𝐂𝐄✍🏻

4

Tin kafin suyi nisa ameera ta fara bacci nan ameer ya gyara mata kwanciya sukaci gaba da tafiya basu Jima ba suka kawo kano ta dabo tumbin giwa anguwar nasarawa J R A wani gida mai kyau daidai misali naga sun nufa nan aka bude musu suka shiga gidan ameer ne yasoma tashin ameera bude idonta tayi akanshi yace my ameera munzo kano

Ameera tace da gaske?

yayi murmushi yace tashi kigani

tashi tayi akan shi taga dai ashe dai da gaske yake yi sunzo cikin murna ta rungume shi tace yanzu zan ga mommy ko

Ameer yace sosai makuwa keda zaki zauna tare da mu

Ameera tace to amma zan ke lilo irin na gida ko

Yace zanke kaiki wajan wasa nan suka fita

Fauziya ce ta fito daga wata kofa ita da fatima suka yo inda ameer yake suna oyoyo yaya nan suka rungume sa suna murna

Fati ta juya gefen ta kawai sai taga ameera tana cika sai hura hanci sama take ta rike k'ugu ita wai an share ta taga basu ganta ba

Fatima tace la anty ameera fuskar ta dauke da farin cikin ganin ameera

fauziya ta juya itama nan suka rungume ta suna cewa dama dake za'a zo mommy bata fada mana ba

Sai alokacin ta saki fuska tace eh ai tare daku zan zauna tana yar dariya

Fatima tace aikuwa munji dadi

Ameer yace to iyayen surutu sai kuzo mu shiga daga ciki ko yayi gaba suna binshi abaya wata kofa naga sunbi wadda zata sadasu da falon gidan da sallama suka shiga mommy ta mike tana musu oyoyo yarana

Da gudu ameera taje ta rungume mommy tana dariya tace mommy na munzo

Murmishi mommy tayi tace to sannunku da zuwa ya kauye yasu inna da umman ki da sauran yan gidan

Ameera na dariya tace ai in gaya miki mommy harfa kofar gida suka rakomu , kinga kuwa yadda inna take sharce hawaye kamar fa ance mata bazan dawoba kuma ma kin me mommy

Yar dariya mommy tayi tace a a saikin fada

Ameera tace nifa banyi kuka ba yayana yacemin zaike kaini wajan lilo shiyasa banyi kuka ba

Mommy tace to masha Allah mu zauna ko , zama suka mommy tayima su ameer barka da hanya

gidan yana da part uku

daya a sama

biyu a kasa
na saman shine na ameer
kasa kuma daya nasu mommy daya na Fauziya da fatima

Mommy ce ke jera abinci akan danner da

Suna zauna a falo fatima na bakale da ameera sbd itama indai surutu ne ba'a bayaba

Tace anty ameera a dakin mu zaki zauna ko

Ameera tace eh

Ameer ne ya harari Fatima yace kedai yarinyar nan kin cika magana

dariya fatima tayi tace yaya ai zamuke hira idan mun shiga daki

Ameer yace to naji

...Mommy tace "idan kungama surutun kikai ameera tayi wanka sai kuzo muci abinci

Da murnanr ta tace to mommy

Fauziya ta rakata da kayan ta a jaka nan ta nuna mata yadda zata yi wanka da ruwan dumi tace "idan kin gama ina jiranki
Chapter 4 · 0% Book details