← Book details Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 65

Sashe 41

Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bude idon shi yayi " yana kallon hajara

Hajara tace maiya faru kafada min kaji yaya

Numfashi ya sauke kafin yaji wasu zafafan hawaye na bin kuncinsa " sai kallon hajara, yakeyi

Girgiza kai takeyi , kafin tasa hannu " tana share mishi hawayen fuskar shi tace, wai menene yaya maiyasa kake kuka na maka tambaya tafi biyar " amma kaki bani amsa haba so kake nima nayi kukan

Janyota yayi jikinsa ,, ya rungume ta yana sauke ajiyar zuciya , wasu hawayen na fitowa ,, yace kiyi hakuri kanwata wllh nakasa magana ne ina jin ajikina ameera ta bata lfy " kodai haihuwa ne zatayi ko kuma wani abun ne yasameta marar kyau ina jin ajikina nabani,, tabbas tana cikin mawuyacin hali yana kara rungume ta

Itama rungume shin tayi ,, tace kayi hakuri yaya ba kuka ya kamata kayiba,, addu'a take bukata, shine gatan da zamuyi mata,, kaji yaya

Dagowa yayi yana kallon hajara yace nagode kanwata,, Allah yamiki albarka ina alfahari dake kanwata

Murmishi, Hajara tayi "tace ba komai yanzu tashi kayi alwala nima sainayi muyi,, Sallar tare

Sakinta yayi yana murmishi ya shiga toilet din yayo alwala nan itama tashiga tayo suka tada nafila suna tokawa ,,Ameera kariyar Allah aduk inda, ta tsinci kanta

Kusan awa daya suka shafe ana abu daya ,, sai kan baby tafo kamar zai fito saya koma ", su kansu sun tausaya wa ameera saboda karfinta yagama karewa gabaki daya tayi lakwas bata iya komai ,, dan haka babbar doctor din , ta fita waje domin tacewa,, su mama ", Ameera bazata iya haihuwa da kanta ba sai an bata c.s. nan tafito waje tana tunkarar wajansu mas

Da sauri sukayo wajan ta suna daha baki wajan fadin , doctor ya jikin nata ta haihu '

Numfasawa,,, Doctor din tayi tace a a gaskiya bazata iya haihuwa da kanta ba sai an mata c.s . Dan yaran sun girma a cikinta

Da sauri joshow yace in akayi c.s din babu abinda zai faru

Doctor tace gaskiya ban saniba muje kasa,, hannu saboda tana jin jiki

Har sun juya zasu tafi wata nosee , tafito da sauri tace ma kizo sauri baby yatafo

Da gudu gudu doctor din tayo room din " ta rufe kofar

Joshow kam ya tsorata sosai sai,, kashe kunne yakeyi " yaji kukan baby

A cikin room din kuwa ameera tana hada sauran kafinta tana kiran sunan Allah ya kawo mata dauki

Daidai lokacin kuma umma,, tagama nafila tana addu'a wa ameera Allah ya kareta ya taimake ta aduk halin da take ciki ta shafa fatiha

Suma su ameer da hajara a lokacin suna mata addu'a hajara hadda kukan ta suka shafa fatiha

A lokacin kuma ameera ta haifo danta qato dashi tana haifoshi aka , daukeshi " suka bawa wata nosee ta gyara shi

Wani sabon ciwon ya zowa" Ameera wannan karan da karfi a jikinta tana addu'a suna fadin ta yi nishi

Da karfi tayi nishi sai ga yarta mace ta fado suka dauke itama aka gyara ta

Su mama na daga waje sukejin kukan baby's murna suka kama yi sosai suna jiran a fito musu da baby's din

Saida aka gyara ameera,, suka mata wanka sosai suka gasata " saboda taji dadin jikinta,, kafin suka gyara wajan tsam kamar " baa yi wani ,, abu ba a wajan " nan suka fiddo ameera da yaran ta

Da sauri joshow ya karaso " wajansu mika mishi babyn akayi aka bawa mama daya , nan akayi gaba da ameera zuwa,, dakin hutu

Kukan baby's dinne ya tashi su marus da beauty ,, aikuwa suna hada ido da baby's din,, da gudu kowa yayi wajan daya suna dariya

Marus yace yauwa,, naji dadi mommy ta haifo min brother ,, mai kama dani

Beauty ma tace,, nima kaga sister na sai nake mata kwalliya , mai kyau nima mai kama dani

Kallon baby's din mama da joshow sukayi " suna ta al'ajabin wannan kamanni,, haka

Joshow ya kalli macen yana kura mata ido babu abinda yaraba ta da jenifer har farar fatar,, kamar jenifer ce tayi kaki yana shafa fuskar babyn , yace beautiful ,, kina kamar jenifer na

Mama , ma kallon su tayi tace kamar ma ,, harta baci sosai suke kamanni da jenifer

Wata nosee ce tafito,, daga inda aka kai ameera nan sukayi wajan ta sukace doctor zamu iya ganinta", tace eh kushiga ta kusa tashima nan suka nufi dakin

A kwance ", suka sameta karasawa sukayi beauty zata tasheta, joshow yace no kibari zata farka ne nan tayi baya ta zauna suna jiran tashin ameera

Baa fi minti goma ba " tasoma motsa hannun ta mama,, tadawo kusa da ita , ta rike hannun ta

Bude idon ta tayi akan mama, tana kallon kowa

Murmishi ta wa su marus nan sukayo wajan ta suna fadin mommy sannu kintashi saimu tafi gida,, ko

Mama ta taimaka mata " ta zauna tana kallon su

Joshow ma murmishi yakewa ameera ganin yaran data haifo amma lfy lau take

Mama ta mike ta hado mata tea mai zafi ta matso kusan ameera tace,, amshi kisha wannan kinji daughter ,, zakiji " dadin jikinki ma muso ta amsa tashanye duka sai zufa take hadawa"

Joshow ne yakaro wa A.C. karfi dan taji sanyi sosai

Yaran mama ta mika mata,, suna jin hannun mahaifiyar su suka tashi , nan suka soma kuka kallon ameera keyi,, itama tana hawayen , tana ganin yadda namijin ke kama da ameer rai da rai

Su mama kam mamaki ne yakamasu, ganin tana kuka

Mama tace daughter lfy daiko kike kuka keda, zakiyi farin ciki da samun kyawawan diya haka gasu , kamar ba twins ba

Ameera tace mama kuna da ruwan zam zam ne

Mama tace a kasuwa dai naga suna siyarwa masu irin addinin ki

Ameera tace a kira min doctor din

Nan joshow yafita kiran doctor babu bata lokaci suka shigo tare,

Ameera ta kalli matar ta mika mata hannu alamar ta karaso ,, matsowa tayi ameera tace,, anty kina da waya

Doctor din tace eh tace please bani zan duba wani abu ne

Ba muso ta bata

Nan ameera ta tubuta sunan zamzam nan yafito gasu nan a jere kafin ta kuma rubuta dabino nanma,,, yafito ta nuna mata tace tana son akawo,, mata su

Doctor din tace muna dashi anan kafin tace amma ke Muslim ce

Ameera tace eh ni musulma, ce inason bawa wannan yaran kafin susha nono

Doctor din tace nima Muslim ce har mijina da yarana bari,, na kira yarona yazo dasu saiya " rada musu suna ya misu kiran salla

Cikin jin dadi ameera ta rungume doctor tace thank you nagode sosai

Nan doctor ta kira yaronta yazo dasu aka bashi yaran

Kiran salla ya fara musu a ko wani kunen kafin ya tauna dabinon nan ya diga musu " a baki aikuwa suka tsotse tas dan yunwa sukeji " kafin yabasu zamzam din sukasha

Dagowa yayi yana murmishi yace wani suna za'a saka musu

Ameera tace macen inason a kasa ,, mata ikram

Namiji sai kuma tace ya sunan ka kai

Yace ni sunana Muhammed

Ameera tace to kasa mishi Muhammed sunanka,, dama sunan kakansu ne

Cike da farin ciki yace to sister godiya nake nan ya rada musu nan , Muhammed da ikram yana jin dadi an mishi takwara,

Su kuwa su mama kallon ikon Allah sukeyi dama idan musulmi ya haihu haka ake saka suna ,, lalle kam musulinci da ban yake

Doctor din tace kina da waya kibani nember ki

Ameera tace eh amma yana gida kawo nasa miki nember ,, idan na je gida zanga kiran

Mika mata tayi " sata mata kafin ta mike sukabar dakin

Mama ta matso kusan ameera tace daughter haka ake saka suna idan mai addinin ku ya haihu

Murmishi ameera tayi tace haka akeyi mama

Mama tace mu sai anje wajan abin bauta ankai yaron , yayi kwana biyu acen ana mishi addu'a tukun sai asa mishi suna

Da mamaki ameera ke kallon mama tace tab lalle kuna, wahalar da kanku mama

Sallama aka basu suka yo gida

Haka aka yita hidima da ameera da yaran ta sosai takajin dadi ,, ganin yadda dangin joshow dana anty karima suke kaunar yara

Gasu lafiyayyu masha Allah da kuzarinsu gwanin burgewa , a haka har akayi suna

Joshow ya tambayi ameera yaya akeyin sunan a garinsu nan tafada mishi komai ,, ya nemo Muhammed ,, suka kai kayan suna gidan su Muhammed su uku suka yi fatihar sunan twins , kafin joshow yadawo gida

Kayan baby's kam ameera tashasu sosai dangi ko kawo kyautar,, shi ta kaya ko kudi

Su ameera baki yaki rufuwa tana jin dadi sai ta kuma yi tunani wai wannan a cikin bare ne take,, ake mata wannan hidimar ,, to inda a wajan dangin tane ya zai kasance " girgiza kai tayi ta maida hawayen ta,, tana fadin ke zuciya ki nutsuwa " wannan ameera bata da,,, bace kizama " jaruma dan akwai aiki ja agaban ki,

Cikin wannan satin, Ameer cikin farin ciki yake duk inda yayi sai murmishi ita kanta hajara , taji tana cikin,, farin ciki sai godiya sukewa Allah ameer kam "dayaje wajan mlm Ahmed har,, kudi yaringa yarabawa mutane,, sosai sukaji dadin ganinshi haka

Dan kullin cikin damuwa yake shiyasa suka tayashi farin ciki duk da basusan meyasaka shi farin ciki

Mom ma taga ameer na farin cikin hankalin ta yasoma kwanciya ganin dan nata na cikin fara'a

Suna zaune da daddy da mom daddy yace gobe zaije kauye, saboda a saka ranar bikin hajara da ameer sai an saka zasu fada mishi nan mom tayi na'am da shawarar da daddy ya yanke

Raju, ne shida shugaban nasa,, suna tsafinsu " so sukeyi a daren nan su aikawa ameera bakaken aljanu su zuke mata jini daga baya kuma su dauketa " su maidata irin na anty karima ",

Sai hado kan aljanun suke suna fada musu yadda zasu kamar yadda sukabi suka dauka na anty karima ana gama musu jawabi nan suka bace,, sai gidan su joshow

Ameera na zaune tana bawa ikram nono ganin gilmawar,, wani bakin abu tayi
Chapter 41 · 0% Book details