← Book details Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 65

Sashe 26

Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan fitar,,Ameer, finsu minti Goma tukun bilal yace beauty yakike,, tana murmishi ta amsa mishi da lfy yagida yasu ammi,, murmishi yayi shima yace lfy lau nan suka sake yin shuru,, cen bilal yace

A gaskiya jiya, nafara ganinki amma naji kin kwanta min,, a zuciya naji ina sonki,, soyayya ta gaskiya ,, shiyasa " na matsawa abokina yakawoni,, na gabatar dakaina a wajanki da wajan " su baba,, ,, Jamila inason mukasance a cikin inuwa daya ma'ana muraya sunnar annabi Muhammad (S.A.W.) ,, jamila ta karasa fadin haka,,

Ajiyar zuciya tasauke tace,, na amince dakai,, dan nasan " yaya ameer bazai yimin abinda,,, zai cutar dani ba kuma yayimin, bayanin komai,, kuma na fashimta,, cike da farin ciki,, yace Alhamdulillah beauty inason ki,, rufe fuskar ta tayi,, tana yar dariya,, basu jima sosai ba " yace muje na kira ameer ki mana iso,, wajan su mama ko da to, ta amsa suka " fita ita tayi part din mama shi kuma ya fita waje

Yana fita yaga ameer shida dr. kabeer suna magana nan,,, yakarasa " wajansu suka gaisa da dr. kabeer tukun shiga gidan,, mama taji dadi,,da taga, abokin ameer ne yakeson jamila,, nan suka fito daga gidan, har bakin get ta rakosu " tana daga musu hannu dama sunyi,, masanyar member ita da bilal,, sai murna take tasamu saurayi hadadden gaye " kamar ameer

Bayan sallar isha"i zaune suke sunata dariya,, ikram tace waiku lfy kuke wani "gaman ido kuma dariya,, Fatima tace momsy ai munyi,, maganin yan iska ne,,

Ameera tace momsy,, ikram tace,, baby "wasu yan iska kuma,, suna dariya suka bata labarin komai,,, cike da al'ajabi da mamaki take, kallon, su tace haba koda najifa "" anty haleema bata amsa gaisuwa ta yau naga ta amsa,, ashe kune kuka,, rikita su " Ameera tace wllh momsy " munkasa bacci ne,, saboda rashin mutumcin da,, tayimiki ""shine muka mata kashedi tace har abada bazata sake yiwa uncle aureba "" dariya ikram tayi tace,, yaran nan gaskiya bakuda dama,, haka suka ringa hira har bacci yasoma daukar,, Fatima ikram tace, suje su kwanta,,

Yau zasu tafi gida duk sun hada kayansu suna jiran ameer,, Ikram tace zanyi kewar ku sukace muma haka momsy,,ai zamuke, zuwa duk week murmishi,, tayi tace to, ana yin la'asar saiga,, Ameer yazo daukar su,, da gudu suka karawa inda yake suka rungume shi a tare,,, yace iyee kaga yaran,, momsy " dariya sukayi tukun suka shiga,, ciki,, gaisawa sukayi suka taba yar hira tukun suka fito,, zuwa waje "da kayansu da tsarabar,, tuni ansaka musu,, ita a mota,, suna dagawa,, ikram hannu har suka fita

Ikram harda hawayen ta saboda sati dayan nan ba karamin sabo sunkayi, ba nan takoma ciki,,

NA GODE DA COMMENTS DINKU
[27/10, 22:39] MRS. MU'UTASIM: 🌟𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑 𝐃𝐀 𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑𝐀 🌟

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝙖𝙣𝙙 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮

𝐌𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐍𝐔𝐒𝐀𝐈𝐁𝐀 𝐂𝐄 ✍️

💫💫JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️

MARUBUTA MASU AIKI DA JARUMTA DOMIN WA'AZANTARWA ILIMANTARWA NISHAD'ANTARWA TARE DA FAD'AKARWA DA JAMA'A BISA HARSHEN HAUSA 💪

💫(J.W.A.)💫

41—42

Suna, isa gida da sauri su ameera suka,, fito daga motar " sukayi,, gidan , mommy , mommy suke cewa,, da sauri,, suka rungume,, ta suna dariya " sukace, i miss you mom,, kara rungume su tayi tace , miss you too,, sakinta,, sukayi sukayo,, wajan inna,, da take kallon su , kwanciya "" sukayi

,Ameera tace , Inna ta nayi kewarki,,, murmishi, Inna tace nima haka, yakuke, nan suka tashi ajikinta suka tafi wanka ameera tayi sama Fatima tayi dakinsu

Ameer ne yashigo da sallama ,, amsawa mom tayi, tace sannu, da zuwa yace yauwa,, mom sannu da gida, kayansu aka kawo mai gadi ya, yashigo,, dasu

Baki mom tarike tace wai, Ameer duk wannan kayan fa,, murmishi ameer yayi yace anty ikram ce fa mom, nace , sunyi yawa amma tace bata rageba " murmishi mom tayi, tace to Allah yayi albarka,, ameen yace nan ya zo wajan inna,, yace barka da warhaka inna ' dangware, mishi goshi tayi yace wash,, kai inna wllh akwai zafi fa, yar dariya inna tayi tace " sallamenme,, to ba yarda badai zanyi ka, kawo mana abokin ka bature gidan nan ba,

Dariya yayi, yace kefa inna baki mantuwa,, ai tinda, bakiso bazan kawoshi ba nan yamike yayi sama

Yana shiga,, tana fitowa daga wanka,, suna hada ido murmishi tasakar,, mishi shima murmishi,, ya mayar mata,, kusa da ita yazo " man ya amsa yace oyaa,, zauna nashafa miki, ba musu ta zauna, , tace yaya kallon ta " yayi ta cikin madubin tace nayi kewar ka, murmishi yayi yace,, aina fiki,, tace anya kuwa yaya,, yace sosai makuwa,, tace to shikenan ,,yagama shirya ta cikin doguwar riga suka sauko kasa,,

Su bilal soyayya ake zubawa shida jamila,, sosai suka saba da juna, hakan yasa, Bilal fadawa ammi ,, cike da farin ciki take saka mishi albarka,, tace da zarar babansa yadawo zata fada mishi don aje nema mishi auren ta sosai,, yaji dadi " da maganar ammin nashi,

Haka kuwa akayi, daddyn bilal,, daya dawowa ammi ta sanar dashi komai ,, shima da farin ciki yace,, zan kira Alhaji Muhammed,, sai muje da abban anass,, ammi tace to Allah yakaimu lokacin ,, yace ameen

Bayan kwana biyu, aka je tambaya wa bilal auren,, jamila baban jamila babu wani,, gardama " yabada ta,, aka saka biki, wata biyu masu zuwa ,, nan suka dawo " gidan cike da farin ciki , aka shedawa, dangi bikin bilal nan da wata biyu masu zuwa,, sosai kowa ke nuna farin cikin sa

Da sauri ameera, ke saukowa daga,, kan bainan,, Fatima ce tafito itada fauziya " suka gaisheda,, mom inna tana dakinta,, komai cikin sauri suke saboda yau islamiya ,, zasu tafi malamin su yace, kowacce zata,, amsa mishi tambayoyi dazai,, wa duk daliba,, acikin su,, basu ci na kirki ba suka tafi,, mom na musu addu'ar samun nasara ,, direba yakaisu yau saboda,, ameer shima tin da 6:30am yabar gidan

Kowa yazauna cikin aji suna,, yar hira nafeesa,, tacewa ameera besty, Allah yasa dai ayi mana tambaya,, marar wahala,, dariya ameera tayi tace to amen dai ke uwar " yan tsoro itama dariyar tayi tace bazaki ganeba bane besty shiyasa,, basu gama magana malamin yashigo cikin ajin kowa,, yayi shuru yana sauraron jawabinsa,,

Gyaran murya, malamin yayi yace " yau zamu bada tambayoyi daga cikin abinda ake muku,, zaku amsa yace ,,Ameera Ahmed ki fada mana shika—shikan musulinci guda nawa ne?? , muna jinki

Mikewa ameera tayi tace assalam alaikum yan uwa,, kamar yadda,, yake acikin littafin kawa'idi,,shika—shikan musulinci guda biyar ne gasu kamar haka

باب قواعد ا لإسلام:
وأما قواعد ألإسلام فخمسة،أولها:
شهادة أن لا إله الا الله وحده لا شريك له و شهادة أن الحمدا أعبده و رسوله، وبعده ألصيلاة،والصيام، والزكاة،وحخ بيت الله لمن استطاع إليه سبيلا. ومن لا يعرف هذه ا لاشياء لا تجوز شهادته ولا إمامته ومن صل خلفه يعيد ابدا،هكذا روي عن سعبد بن المسيب ءاخر المتقدمين.::wato ma'ana

Babin shaka—shikan musulinci:
Amma shika-shikan musulinci guda biyar ne,,,na farkonsu:

Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai babu abokin tarayya a gare shi,

Da shaidawa cewa annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne

Bayansa sai sallah da azumi da zakka da ziyartar dakin Allah ga wanda yasami ikon zuwa duk wanda bai san wadannan abubuwan ba, to yin shaidarsa ba t halatta ba ko limancinsa, kuma duk wanda ya bi shi sallah ya sake sallar har abada haka aka rawaito an sa"iidi bnil musayyibi,aakhiril mutakaddimiinia.

Ameera takai karshen jawabin ta tana sauke,, ajiyar zuciya,

Murmishi malamin nasu yayi yace barakallahu fikii ya ameera Allah yakara basira da ilimi mai anfani ta ameen mlm nagode,,

Sauran yan ajin sukace allahu akbar ,,

Tukun aka soma, bin ko wanne ana tambayar sa, wani yafadi,, daidai wani yayi " ba daidai ba, ahaka har suka tashi, Ameer ne yazo yadauke su suka tafi gida

Haka rayuwa gidan ta kasance musu, cikin farin ciki ,, saidai yanzu ameera ta soma nutsuwa, amma ko yanzu shirman zancen yazo saita yi,, mijinta kuwa, basu da wata matsala da ameera duk abinda yakeso shi take mana,,

A bangaren gidansu Bilal, kuwa shirye shiryen biki suke yi sosai,, saura kwana goma yanzu bikinsu,, su ameer abokan ango suma , suna nasu shirin

Ameera kuwa duk week sai taje gidan ikram, ta yini sai yamma akawota gida har gidan su jamila take zuwa,, saboda bikin ya matso kusa su uku suke zuwa,, ameera fatima nafeesa, sosai suka shaku da juna

Yau anass yace shima zai fadawa,, dadyn sa ya tambayo mishi auren Fatima,, dariya su bilal ke mishi sucemishi mijin yarinya,, haushi yake kamashi ya kyalesu dan yagaji da wannan abun nasu yana zuwa gida yafadawa mom dinsa tafadawa dad dinsa , babu bata lokaci aka je gidan su fatima neman auren , ta bayan sunyiwa daddy bayani, murmishi yayi yace haba dai,, yanzu saboda,, wannan ne kuke neman izini na , ai kawai kusaka rana , dadyn anass yace ai dole, ne a matsayinka na mahaifi "" daddy yace to nabashi fatima nan suka tsaida ranar bikin fatima,, wata daya kadai,

Daddy daya, samu mom da maganar,, bataso hakan " ba tace yanzu dadyn su sai ayiwa fatima aure alhalin,, Fauziya batayi ba, murmishi daddy yayi yace fadila, kada kidamu ai shi aure lokaci gareshi ita nata lokacin ne bai zoba shiyasa kikaga, hakan ta kasance " tace hakane to Allah yakaimu yayi musu albarka,, yace ameen,

Ameera ce ta kalli,, mom tace mom kallon ta mom tayi " gwabe fuska tayi murmishi mom tayi tace to yau kuma yan rigimar ne my daughter,, turo baki gaba tayi tace to nima yaushe zaa saka ranar bikina ayi irin nasu fatima,, dariya tabasu,, daddy yace tare zaa muku ai daughter,, da murna tadawo wajan daddy tace da gaske dad gyada mata kai yayi,, yace insha Allah daughter,, Ameer na jinsu bacci a idonshi,, ya mike yace to saida safe

Mikewa ameera tayi,, tabishi suka yi sama, toilet yanufa,, ruwa ya hada musu "yazo yakama hanun ta suka shiga,, sukayo wanka " da alwala nafila sukayi kamar yadda suka saba,, tukun suka dawo,, gado,, " addu'a yayi musu sosai tukun,, yashafesu da ita suna,, kwanci ya janyota jikinsa,, da sauri ta kara rungume sa,, yaja musu bango
Chapter 26 · 0% Book details