← Book details Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 65

Sashe 6

Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin babu wasa a fuskar shi tace to yaya nadena basu jima sosai ba suka koma gida

Suna shiga suka tarar da daddy yadawo, Ameera tayi wajan daddy da sauri ta zauna a kasa kusa da kafarsa ta daura kanta akan cinyarshi tace; daddy wani gida mukaje nida yaya

Murmushi daddy yayi yana shafa kanta yace kennan yau kinga gari

tace a a fa gida daya mukaje shima yace abokin sa ne

Mom tace to kije ki shirya kutafi islamiya keda Fatima

Ameera tace to mom

tayi dakinsu basu jima ba suka fito cikin shirin islamiya sunyi kyau sosai" sukace mom muntafi

Mommy tace adawo lfy

Ameer yace mom kinsan kuwa muna zuwa wajan abokina Anass kawai ameera taganshi yayi sabon iska tace wai dama abokin nawa dan iska ne"

Dariya sukayi mom tace gaskiya bana gajiya da surutun ameera musamman ma "idan fatima tana nan

Daddy yace yar gidan inna su inna yanzu ko andena kewar jikar ta ta mom tace to kila

Kusan magarib su ameera suka dawo a gajiye dan yau ameera tilawa tayi kuma tayi sosai,, suna shigowa ko zama basuyi ba aka soma kiran salla nan sukayi daki domin yin salla bayan sun gaba fatima tace""Anty ameera yau zamu zo muyi magana hausa cikin hausa wato karin magana,

Ameera tace to shikenan "idan mun gama cin abinci muka zauna hira sai na miki tambaya kibani amsa tace to

,, Bayan sallar isha'i suka fito falo harda daddy da ameer sukkansu, mommy ce tafito daga kitchen rike da kular abinci tace "idan kun shirya abinci yayi ready

suka ce to,,nan sukayi darning suna cin abinci fatima na mintsinar ameera

ita kuwa sai hararar ta takeyi tana mata nuni da zama rama,

,Murmushi tayi bayan sun gama ne suka koma falo fauziya ta kwashe kwanukan tayi kitchen dasu "ta wanke itama ta dawo falon

,,Ameera tace to yaudai karin magana za'ayi nida fatima mom idan ta fadi ba daidai ba kice yati error mom tace to muna jinku.

Fatima tace to bari na lissafo miki questions kibani amsa gyara zama ameera tayi tace, ina jinki

fatima tace to gasu kamar haka

Abun da ka shuka?

Kowa ya deboda zafi?

Mutu ka raba?

Dan hakin daka rena?

Kowa yabar gida?

Fatima tace to bani amsa

Sudai su mom kallo ne nasu,

Ameera tace yarinya yanzu kuwa

Abin ka shuka =shi zaka ba shanunka

Kowa ya debo da zafi =yayi wanka da ruwan sanyi

Mutu karaba =akwatin karfe

Dan hakin daka rena =shi zaka kakkarya

Kowa yabar gida =gida ya rushe

Aikuwa me zasuyi inba dariya ba fauziya harda fadowa daga kan kujera tana dariya

,Fatima kuwa burgima take dariya ce taci karfinta

" Daddy kuma da ameer suma dariyar sukeyi,,

Aikuwa ameera ta shaka ta hade rai ta mike tace shine kuke min dariya tana bata fuska kamar zata yi kuka

wajan ameer tayi shima yana dariya yace to kece kika bamu dariyar "wannan amsa haka ,

Tace shine kaima kake min dariya ai haka naji kaka na fada

Fatima ce har yanzu bata dena dariyar ba

dama ameera haushinta take ji,,nan tayi kanta suka fara tsere

Mom nacewa kubari kunji kema zo ki mata tambaya ta baki amma basu kulata ba "

nan aka soma dambe ameera tace ni kike wa dariya saina lallasa ki a gidan nan

Ameer zai tashi daddy yace kyalesu tukun musha kallo

Fatima tasamu ta kwace daga rukon da ameera tayi mata tana mata gwalo

"Aikuwa suka ringa zagaya su mom fatima na dariya

Ameera kuwa har ta soma kuka tana cewa,,yarinya ki tsaya ko kuwa sai kinyi bacci na yanke miki gashin kanki irin na maza

Fatima tace anki din,,

Ameer ne ya tashi yayi caraf da ameera sai ta rushe da kuka janyota yayi suka koma kan kujera ya soma rarrashin ta,,yace to kiyi shuru mana

Tace yaya ba ruwana da Fatima tinda take min dariya

Ameer yace kiyi hakuri kinsan fa kece babba,

daddy yace to shikenan ameera kuje ku kwanta gobe kuna da school,

,Ameera tace daddy nidai bazan kwana da Fatima ba wajan yaya zan Kwana

Mom tace daddyn su gyara taje cen ta kwana idan aka barsu hallau fadan zasuyi

Yace to shikenan kuje kowa yaje yayi bacci,,

Ameera da ameer suka yi sama su Fatima suka yi dakinsu .....

.Suna isa yace baki dauko kayan bacci ba tace bari nadauko, sanin halinta yasa yace no bari na dauko miki tace to yaya "nan yafita ita kuwa sai kallon dakin takeyi tsarin dakin ya burgeta sosai ahaka yadawo ya sameta ,

,yace cire na jikin naki ki saka wannan tace to" nan tasoma cirewa shi kuma yayi toilet dan yayi wanka dama ita tuni tayi nata

,,A kan gadon yaganta tace nima zanyi nafilar yace to dauro alwala ta mike tayi toilet tayo alwala suka tada iq'ama

Bayan sun idar ne sukayi addu'a suka koma gado"

Ameera tace yaya ?

yajuyo ya kalleta yace na'am

Tace, dama namiji da macce suna bacci a waje daya ?

Murmushi yayi yace sosai makuwa idan miji da mata ne

Kallon sa tayi tace to kaidin mijina ne ?

yace eh nine mijin ki

tace amma maiyasa bama kwana a gado daya?

yace ke kikace awajan su fauziya za kike kwana shiyasa na barki,,

Tace to daga yau zamuke kwana tare "

Yace eh idan kinaso ba

Tace inaso nan suka kwanta ya janyota jikinsa,a tare suka sauke ajiyar zuciya ita ta gajiyar gudun da tayi "

shi kuma saboda yaji dumin jiki ta saboda ba karamin so yake mata ba tin tana jaririya yake sonta,..

Haka sukaci gaba da rayuwar su cikin farin ciki kuma yanzu ameera tana fashimtar karatu sosai daga boko har islamiya, ta dena kwana a wajan su fatima tare suke kwana da ameer shikuwa haka yayi mishi dadi dan yana jin dadin dumin jikin ta "ita kuwa sarkin son jiki kullin ajikin shi take kwana shine katifar ta,

Yau sun dawo daga school ameera tace mommy munyi hutu akaini naga Inna ta

Ameer yace,ba yanzu ba aikuwa tasaka kuka tana zama a kusa dashi tace,, nidai akaini naga inna ta

Mom tace kyaleshi kinji daughter ni zan sa akaiki kokuwa shi yakaiki kuje cen kuyi hutun,,

Sai tadena kukan tace yauwa mommy na nagode "

Harara ameer yamata ta murguda mishi baki nan yace zan kama ki ai

Dariya tamishi

kyaleshi ta yayi

sama tayi zatayi wanka "dan ta jima da komawa wajan ameer har kayanta dukansu,..

Bayan kwana biyu yau ne kuma su AMEER DA AMEERA zasuje kauyen su ameera sai murna take dan so take taga inna,,nan mutanen gidan suka zo har bakin mota

Fatima na kuka tace itama dole sai an kaita ameer kuma yace bata bisuba, daddy ne yace saita je

Ta dauko kayanta suka tafi,,

Suna hanya Fatima da ameer sai surutu suke kafin wani lokaci sunyi bacci,

Ameer yajuya dan yaji sunyi shuru kawai saiya ga sunyi bacci murmushi yayi yace iyayen zance surutu anyi bacci

ANAN ZAN TAKATA KUYI COMMENTS DA SHARE DIN SA NGD
[24/10, 01:45] MRS. MU'UTASIM: 🌟𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑 𝐃𝐀 𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑𝐀 🌟

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝙖𝙣𝙙 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮

𝐌𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐍𝐔𝐒𝐀𝐈𝐁𝐀 𝐂𝐄✍🏻

7-8

Suna isowa kauyen su Ameera yayi anguwar su nan yashiga gidan,,

Yaran gidan suka yo wajan su "suna ga ameera ga ameera

Zantukan yaran ne ya tayar dasu ameera bude marfin motar sukayi suka fito,

Aikuwa kafin su yo kanta tayi sashen inna da gudu tana cewa,,Inna ta gani nazo

Inna na zaune jita kamar a mafarki takejin muryar ameera
bata yadda ba saboda ta saba jin murya ameera na mata gizo "dan kullun sai ta takurawa abba tana cewa yakaita kano gidan muhammadu sai ansha fama ake shawo kanta,, tace "idan ma siyar mata da ameera sukayi to wllh bazata yadda ba su koma inda suka siyar da ita su basu kudin su akawo mata ameera ta kullin haka takeyi bata idar da zancen zucin da takeyi ba taji mutum ya jikin ta da sauri tadawo,,takai dubanta da wanda ya rungume ta wazata gani ameera ce "ta murza idon ta dan tabbatar wa tagadai ba gizo bane ita din cedai aikuwa ta rungume jikar ta 'ta tana cewa dama ai nace musu babu wanda zaiyi min mafiya da jikata yazauna lafiya ya akayi kika gudo,

,dariya ameera tayi tace to inna yan mafiya kuma nida nake gidan daddy maiya hadani dasu

,,Ajiyar zuciya inna ta sauke tace a ni maryam Allah na gode maka daba siyar min da jika aka yi "

Ameer ne yashigo da sallama jin inna na zantuka kamar an jonata yace,,Hajiya inna ikon Allah kaga kakar, 𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑 𝐃𝐀 𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑𝐀 yana zama kusanta

Dariya fatima tayi tace to inna mu baki ganmu bane '?

'kallon su tayi da mamaki tace a a harda ke aka zo ashe kuna tare

Tashi tayi kawo musu tabarma suka zauna nan aka gaisa, take tambayar yasu mommy suka ce sunce ma a gaisheku

...Inna tace ina amsawa

Su Ibrahim ne suka shigo hajara tace anty ameera sannunku yaya ameer la hadda fatima tana tsallen murna

Ibrahim ya zauna kusa da ameer ita kuma Hajara tayi wajan su ameera suka kama hira.

....Bayan sallar azuhar suka yi sashen umma suna zuwa ameera ta zauna ta kwanta kan ciyar umma tace,,umma na nayi kewarku

Murmushi umma tayi kuma taji dadi sosai ganin yar ta, ta takara girma tayi kyau sosai

""Ameer ne ya durkusa har kasa yake gaishe da umma cikin jin kunya yake gaisheta

Umma ta amsa tace ya maman naku yace lfy,,umma tace to su fatima ne a garin namu zo kusa na kizauna

,,ta matso kusa da umma ta saki jiki aka suka soma bawa umma labari dan fatima babu ruwan ta da bakunta

,,Yaya safiyan ne yashigo yaga su ameer yace a a yau mutanen kano ne a garin namu

Ameer yace mune dan uwa jan ameer yayi sukayi dakin yaya safiyan yabar su ameera anan ,,

Umma tace kuje ki gaishe da mama nana tace to umma na

Nan suka fita sukayi sashen mama ,,da sallama suka shiga kausar ce da Usman zaune suna wasa, suka amsa sallamar kausar tace ga anty ameera da Fatima oyoyo
Chapter 6 · 0% Book details