← Book details Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 65

Sashe 50

Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwabe fuska tayi tace , cikin nan yahanani zama irin nakowa, ko bacci ban iyayi na kirki ,ga bayana namin mugun ciwo ,, dana fadawa mom cemin tayi wai idan mace ' ta kusan haihuwa haka take fama da wannan ciwon bayan " har ta haihu ,, nidai wllh nagaji da ciwo nan please ka amsa nima nahuta,, kona sati biyu ne kayi sweetheart yana kai karshen maganar tana dagowa daga kafadarshi

Danne dariyar shi yayi tana rarrashin ta,, har bacci yayi gaba da ita yace fatima rigima kenan inbanda abinki ina maza ke daukar ciki, ai sai mata Allah Allah yasaukeki lfy,, nan yaringa matsa mata kafafunta dasukayi,, kumburi yana murmishi,, yakusa zama daddy

Alhamdulillah yau ameera takoma islamiya,, kuma taji dadi makotansun nan suma suna zuwa sosai , lokacin da aka ce musu an doki ameera ,, mai gidan saida yakai reported wajan sanda amma aka kasa gano mutumin " haka suka hakura amma yace duk lokacin da suka ganoshi, su fada mishi ' shiyasa yau da umar yace musu zatazo suke ta murna

Assalam alaikum ameera tace lokacin datazo bakin kofar shiga

Amin wa'alaikum salam suka amsa mata matan da sauri sukayo wajan ameera ' suna nuna farin cikin su da ganinta

Murmishi tayi tace, kuna lfy daiko ,, a tare suka amsa mata da lfy lau,, ya saukin naki '' Ameera tace Alhamdulillah,, nan suka zauna aka kama karatu

Bayan antashi kowa yatafi gida,, Ameera ta dauko jakarta, har taje bakin kofa saita dawo,, wajan muhammed

Kallon ta muhammed yayi , yace kanwata yadai,,, ko kewar ikram kike ne

Yar dariya tayi,,tace tab kewa fa aiko shekara zatayi bazanyi kewarta ba haba yarinya sai rashin jin tsiya

Murmishi yayi yace to shikenan kibamu ita kyauta " dama bamuda mace agidanmu , shikenan

Ameera tace to nabaku ai inda ikram ce gata gaku, asha zama lfy

Tace am dama inason muyi wata magana ne

Muhammed yace ina jinki kanwata

Numfashi ameera taja tace wllh yayana wani mafarki nayi mai ban tsoro kuma nakasa samun nutsuwa

Muhammed yace subhanallah to mai kikagani acikin mafarkin naki kanwata

Tuni har ameera tasoma kuka tace matar yaya umar nagani acikin wani hali tana kirana amma wasu suka bugeni nafadi nakasa manta abinne

Muhammed yace ban ganeba ameera dama umar yana da mata shin dama su abubakar sadeeq da mufeeda ba ke kika haifesuba ,, kaina fa yakulle kanwata kiyimin bayani ta yadda zan gane

Ciki kuka ameera tace,, yayana niba matar sa bace bakaga sai wannan shekarar suka musulinta ba su din kaddarar rayuwa tane,, shiyasa Allah yajefoni cikinsu bansan suba anty karima kadai nasani itama a mafarki nake ganin ta sau daya naganta afili sanye da kayan likitoci

Zama muhammed yayi yana dafe kai yace to kanwata " kince su kaddarar rayuwar kine to kuma naga su abubakar suna tsananin kama dake " babu wanda zaice bakece mamansu " ba duk da ana samun masu kamanni amma basuda,, hadin dangi haka Allah yakeyinsu kama daya " amma naga shakuwar da kukayi da yaran abin yana bani mamaki ,, kanwata shin ke wacece daga ina kikazo nan " da ciki ajikinki ina baban yaran da kika haifa please kiyimin bayani

Share hawaye tayi " tace hakane yaya muhammed nima abin yana bani mamaki sosai yadda muke kama da yaran har mamansu , ita munfi kama sosai.
Nan tabashi tarishin rayuwar ta da yadda akayi aurenta da lokacin da anty karima " take zuwar mata a mafarki, da kalaman datake mata har zuwa rabuwar dasukayi ita da ameer din ta da yadda " tayi luzing din memory dinta " har zuwa yanzu tana saka kuka mai taba zuciya " saboda ta tuna yadda ameer ke sonta na riritata kamar jaririya da kulawar shi,, amma yanzu gashi kaddarar rayuwa ta rabasu.
Tace ninasan yanzu sun dauka na mutu kawai yanzu shekara biyu da rabi ,,kenan rabona da family na

Baki da hanci muhammed yasaki yana kallon ameera " da tagama bashi tarishin wannan rikitaccen,, lamarin ,share zufar dake karyo mishi yayi yace kai amma kanwata na tausaya miki " insha Allah kinkusa komawa wajan mijinki,, wannan mafarkin yana nunin ,, muje cen gidan abin bautar tasu,, mu bincika mu fiddota " kisamu ki koma ahalinki " ki kara hakuri kinji kuma kici gaba da addu'a zan tayaki,, dani zamuje amma mubari sai dare mutafi muduba

Dagowa, tayi tana kallon shi tana dariya da kuka a hade, tace nagode sosai yaya Allah yasaka da alkhairi

Ameen sukaji ance daga bakin kofar " da sauri suka juya ,, Umar suka gani yana share hawaye karasowa " yayi ciki

Zama yayi yace tabbas hakane nima nayi wannan mafarkin jiya ashe kema kinyi to mubari gobe insha Allah da dare lokacin babu kowa agidan abin bauta " saimu je amma fa muje da shirinmu dan akwai masu tsaro

Jinjina kai sukayi ameera tace insha Allah hakan zamuyi nan sukafito daga cikin islamiyar,, Muhammed yayi gida suma suka shiga gida

Fatima tafito daga daki tayi fayawo,, abinta , sai k'aton cikin dake rinjayar ta a hankali take tafiya harta karaso cikin falon ,, Anass ne ya kamata ta zauna

Wayar tace tayi kara dubawa tayi ganin sunan yasa tayi murmishi tace momsy,, Allah yasa su ameer ne, dagawa tayi tana fadin assalam alaikum

Daga cen bangaren ikram sai taji,, su ameera ne ameer yace hello anty fati ", mommy mu tace zaki haifa mata baby ni mace nakeso sai muke kwana tare " anty fati aidai mace zaki haifamin muke wasa ko

Dariya fatima tayi tace ,, kai dama nasan kune kuka kira yan rigima kawai , to nima dai ban san mai zan haifaba idan na haifa saina kai muku shi gidanku,

Kwace wayar ameer yayi yace anty fatima brother " nake so ki haifa mini kinji sai muke zuwa wajan wasa dashi daddy,, zaike kaimu ko ???

Fatima dai dariya take musu jin ansoma fada tsakanin ameer da ameera " yasa tayi saurin fadin ameer ameera ku tsaya ,, kuji yan uku zan haifa muku kunji saina dauki daya nabaku biyu

Ihun murna sukasa suna fadin yee muma zamuyi sister and brother , mommy zoga anty fatima kuyi magana tace uku zata haifa tabamu biyu tadau guda

Dariya ikram tayi tace , to naji iyayen surutu maza kuje kuci abinci saimu gaisa da fatima , wayar ta dauka tana fadin hello fatima

Fatima tace ina yini momsy yagida ya uncle dinmu

Murmishi ikram tayi tace lfy lau ya jan kafa uncle dinki bayanan, yafita sai anjima zai dawo

Fatima tace to Allah yakawosu lfy suna hira fatima " tasoma jin ciwo, da sauri tace momsy , sai anjima nan sukayi sallama

Duk abinda takeyi anass na kula da motsinta , matsowa yayi yace , yadai fatima wani wajan yake miki ciwo ne kifadamin

Kafin ma yataba ta cikin ta yayi mata wani mugun murdawa,, kara tasaka tana fadin innalillahi wa inna ilaihin raju'un " yaya mutuwa zanyi

A rikice yafauketa yasaka mata hijab ya yi waje da ita " a mato yasaka ta ya koma yadauko bakullin " motar har zai shiga saiga bilal da jamila zasu fita

Da sauri sukayo " kansu suna fadin lfy anass ganinshi a rikice da sauri yace fatima batada lfy "

Da sauri jamila tashiga baya bilal da anass suka shiga gaba ,, nan sukabar gidan

Tin kafin suje bilal yakira ameer a waya

Ameer yafito yasha kyau sosai sajan fuskar shi yakara mishi kyau " yana fadin kanwata maza kizo mutafi karmuyi last ,,

Da gudu gudu tafito tana fadin ganifa yaya hijab zansa

Kallon ta yayi yace kinyi kyau ,

Harara ta aika mishi , tace eh dama nayi kyau kasan ko a family dinmu nida yaya jalal da munfiku kyau,,

Dariya yayi yace tab " kaji zubaida jalal din ne mai kyau tab, jin wayarshi na kara yasa duba wa ganin bilal ne dahar bazai daga ba zai maida aljihunsa

Hajara tace ka daga mana yaya

Dauka yayi yana fadin ,, hello bilal yadai

Da sauri Bilal yace, ,bro maza maza idan baka zo hospital ba kayi sauri kazo

Hankali a tashe yace lfy bilal jamila ce ba lfy kowa

Bilal yace fatima ce kafadawa, su mommy kayi sauri kazo mun kusa zuwa

Da sauri yace gamu nan

Hajara tace yadai yaya

Cike da damuwa yace fatima ce ba lfy maza muje

Da karfi yace mommy

Fitowa mommy tayi tace lfy kakemin wannan kira haka

Ameer yace maza muje asibiti ankai fatima

Da sauri tasaka mayafi ta kira inna suka tafi

Da sauri bilal ke gudu Allah ne kawai yagansu " da gudu Bilal yashiga ciki " yana kiran nosee da sauri sukayo waje suka dauki fatima ,, akayi ciki da ita

Su ameer ne suka karaso ko gaisawa basuyi ba " Ameer yayi sauri yashiga office dinsa ya saka safar hannu yafito ya shiga inda fatima, take

Tin bayan isha"i , Ameera takasa bacci ta q'agu gobe tayi dare yayi ,, su tafi gidan ,, bauta
Su fidda anty karima ,, addu'a taringa yi

Umar ma hakan take agareshi ,, addu'a yakewa " Karima Allah yasa goben insunje su ganta , harda kukan shi

Muhammed ma, haka yakeyi sosai suka dukufa da addu'a

Kusan awa uku fatima na cikin dakin " babu Wanda yafito a likitocin ,tinda suka rufe kofar

Cen anjima saiga ameer yafito fuskar shi na nuna damuwa sosai

Da sauri mommy , da mama sukace ameer yadai ta haihu ne

Kallon su yayi yace gaskiya bazata iya haihuwa da kanta ba sai an mata c s , karfinta yakare " kusa hannu amata,

Anass yace maza kuje kuyi ,, basai nasa hannu please ameer

Ameer yace dole ne saika sa hannun nan yamika mishi takarda " yasa hannu kafin ameer yakoma ciki

Bayan minti hamsin " wata nosee ta fito da baby tana murmishi

Da sauri ,,Bilal ya amsa yana fadin Alhamdulillah " masha Allah mai aka samu , Nosee din tace ansamu baby girl

Kowa sai murna suke shi kuwa anass ko kallon babyn baiyiba, shi ta fatima yakeyi ,, yace ya ita uwar , tace mishi yanzu zaa fiddota zuwa wani dakin
Chapter 50 · 0% Book details