← Book details Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 65

Sashe 55

Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A razane yadago jin muryar da bazai taba ,, mantawa ba juyo da ita yayi , kawai ya rungume ta sosai yana fadin Alhamdulillah , Alhamdulillah , Alhamdulillah Allah abin godiya ,

Inna tace kai ameeru ,, bakada hankali ka rungume matar mutane kana ,, cewa Alhamdulillah , ko kasha giya ne

Dagota yayi ya juyo sa fuskar ta ta yadda zasu ganta idan yacire niqaf din , cire niqaf din yayi ,,yana dariya hade da kuka yace ,Inna kin ganta wife na ce tadawo garemu dama ,, nace ba mutuwa tayi ba

Da sauri ,inna yayo wajansu tana kuka sosai tace allahu akbar ,, yarinya ta dama kina raye bamu sani ba , Ameera ina kike duk wannan tsayin, lokacin ,, sakin ameer tayi ta rungume inna ,, suna kukan farin ciki ,, abin tausayi

Sakin inna tayi taje wajan daddy ta rungume shi tana kuka ,, tace daddy kun dauka na mutu ko , ,, rungume daddy yayi yana share hawaye ,, yace daughter ,, ai bamu yadda kin mutu , ba kawai , dai mun barwa Allah komai ne

Sakin daddy tayi ,,tazo wajan mommy ta rungume ,, kuka mommy tasa sosai tana fadin Alhamdulillah ,, Allah mungode maka daka dawo mana da yar garemu

Sakin mommy tayi da gudu hajara tazo ta rungume ameera ,,, tana kukan itama tace anty ameera ta ,, dama nasan yar uwata baki mutu ba kina nan " a raye Alhamdulillah

Ameera ta gaskiya ne kanwata gani ,, nadawo ahlina

Sakin hajara tayi taje ta rungume Fatima da fauziya a dare ,, sosai fatima ke kuka

Tace yar uwa ta dama kina raye ashe kai Alhamdulillah Allah nagode maka ,,

Maman anty karima ko , Inna ce tajuyo aikuwa da karfi tace maryame ,,, da sauri inna ta kalli inda aka kirata ,,, cike da al'ajabi tace , ingozi

Maman anty karima da sauri tazo ta rungume inna nan sabon kuka yatashi mama sai shafa inna takeyi tana fadin ,, yar uwa ta dama kina raye ashe nayi kuka harna gaji ,,da zubar da hawayen rashinki

Dagota inna tayi tace ingozi ina nan a raye ashe kema kina nan suka sake rungume juna suna kuka

Nan fa kallon yakoma kansu ,, Fatima ce takasa hakuri tace inna wannan din yar uwanki ce ,, naga kuna kama sosai

Dagowa inna tayi tana share hawaye tace " eh wannan labarine mai tsayi yar uwa ta ce uwa daya uba daya

Baban anty ma ganin yasashi zumar tsaye sai cen , yadawo daga hankalin yace maryame ,, ina shareef , ina dan uwana

Da sauri inna ta kalle shi tace papa , kaine

Baban karima yace eh maryame nine ,, yanzu duk mun cenja wannan sunan sunana, Usman ugozi kuwa,, sunanki gare ta ina shareef maryame,,

Share hawaye inna ,tayi tace ai ya dade ta rasuwa tin ameera tana yar shekara uku ya ,rasu ,, kullin zancen shi papa da gaye , harya mutu

Mama ce ta matso kusan Usman tace ,,wai usman kana nufin shareef ,dan uwanku ,, shine mijin maryame , kuma kakan ameera

Jinjina kai yayi yace sosai makuwa ,,

Su daddy kam abin al'ajabi ,, da mamaki da komai sukewa su inna

Daddy yace , wai ina kina nufin kice mana wannan duka dangin mune da , naki dana " baffa ne

Inna ta bace majina tace , eh muhammadu wannan sune ahalinmu nida bananku

Sai alokacin ameer ya kalli doctor aisha da suma ,, suke kallon ikon Allah ,, Ameer yace a a kakata wai dama harda ku akazo

Muhammed yace eh tare mukazo " ashe kaine mijin na ameera ,, a lokacin dazaka dawo kano kana tafiya sukazo " da alokacin zaku hadu

Doctor aisha tace kai masha Allah dama ameera matarka ce

Murmishi ameer yayi yace eh kakata kowa ya zauna tukun

Zazzanawa , sukayi farima tace wai ameera ,, ina cikin da kika tafi dashi

Kallon Fatima ameera tayi , sai kuma tayi murmishi ,,ta dago da muhammed,, ta kama hannun ikram tace ,, wannan sune ckin dana tafi dashi " yan biyu na haifa , sunan daddy da sunan momsy na ,, garesu

Ai kafin kowa ya taba su ameer , ya yace kuzo nan yaran albarka , Ikram dama ita so take yace tazo da dan gudun su suka nufi ameer
Saukowa yayi daga kan kujerar , y durkusa ,, bude musu hannu yayi suka shige jikin sa,, Ikram tace daddy cike da murna ameer yace na'am my daughter ,, na ashe dai ,, ke jinina ce shiyasa ganin farko " kika makale min , nima kamar na sace ta naji ,a lokacin ashe jinina ce

Doctor aisha tace ,, haba koda naji fa yarinya daga ganinka ,,taki yarda ku rabu ashe ita dumin babanta taji

Sakinsu yayi yace kuje mommy na kiranku ,, wajan mommy muhammed ,, yayi yana dariya ganin suma dariyar sukeyi , Ikram ko tana jikin ameer , ko matsi batayi ba " itadai ,daga anjima tace daddy shikuwa ,, Ameer yabiye mata sai yaketa amsawa

Daukar muhammed mommy tayi , tana fadin mai gida oyoyo ,,nan kowa yayi ta daukarshi ,, Ikram kuwa ko kallon inda suke bata yiba ,, tayi kwanciyar ta , jikin babanta ,, duk wanda yace zo ikram "" bata fuska takeyi tace daddy ta dago ta kalli ameer ,, shafa kanta yake yace daughter ,,kwanta abinki " idan kika huta sun ganki

Hajara ko murna kamar tayi rawa haka takeji sai rungume ,ameera takeyi tana shafa fuskar ta

Murmishi ameera tayi tace , to mage ashe dai baki dena son jiki ba ,, yar dariya hajara tayi tace ,ai kinfini ingaya miki ,

Doctor aisha ce ta kalli ikram tace babyn mommy zo mutafi mana kinsan anbani rikonki " tin kina jaririya to yanzu munzo gun babanki ban saniba kozai banike

Murmishi ameer yayi , yace ai indai nine " bakida matsala ,,dago da ikram yayi yace daughter , maza jeki wajan kaka ,

Kallon shi tayi zatayi kuka muhammed ,, yace babyn mommy ,,zo nan juyowa tayi,, ganin muhammed ne yasa ta sauka daga kan ameer ta tafi inda muhammed yake,, tace daddy , daukarta yayi yace kinga mommy na kallon ki maza jeki wajan ta , mikawa doctor aisha hannu tayi " daukar tayi ta rungume tana shafa kanta har bacci ya dauketa ,

Baba laraba ce tashigo gidan ,da sallama daga,, kasuwa take ,niki niki da kaya ganin falon cike da mutane,, tace sannunku baki , ,, dagowa tayi zata wuce bazata ga ", da sauri ajiye kayan hannun ta ,, tace hajiya koda gizon ne dana saba yi ameera nake gani ", mommy tace babu gizo itace

Wulli baba laraba tayi da c, kayan hannun ta ta nufi ,Ameer tana kuka ,,, itama ameera mikewa " ta taro baba laraba , rungume ta sosai

Baba laraba tace ya'ta kece ashe , ba gizo bane ashe zan sake, ganinki yar lelen ameer ' waiyo Allah Alhamdulillah ,

Share hawaye ameera tayi , tace nice baba laraba " gani nadawo gareku ba mutuwa nayi ba ,,, ina raye

Sakinta baba laraba tayi, tana dariya sosai najin dadin dawowar " Ameera cikinsu ,, mommy tace baba laraba ki mana girki dayawa ga hajara ,nan zata tayaki da fauziya " Baba laraba tace to hajiya nan tayi kitchen din don , daura girkin

Daddy ne ya kalli ,, Inna yace inna ashe dai ameera tana wajan danginta ,, to amma daughter ya akayi suka tsince ki , keda kukayi accident ,a kan hanyar ku ta zuwa nan

Zama ameera ta gyara , tace daddy lokacin da motar mu , tashiga dajin dake gefen titi , kawai gangara wa nake ina daga kwance , wata bishiya " na buga daga bansan inda nake ba, ashe lokacin dana buga kaina cikin wani kogin dake " gindin bishiyar na fada yayi ta tafiya dani har kogin su yaya umar na bayan gari " anan ya tsinceni ,,,da farko sun dauka ni anty karima ce " saboda na manta komai na rayuwa ta na baya , shiyasa saida " nadawo haiyacina , tukun nace bani bace karima ,, nan ta kwashe labarin komai tabasu har cututtukan datashayi ,, da sokar ta da akayi da wuka " da mutanen garin da sunfi rabi duk sun musulinta ,

Su mommy sai kuka ,, suke jin abubuwan da ameera ta fuskanta , amma Alhamdulillah tinda har mutanen garin sun musulinta , kadan ne basu musulinta ba

Sake rungume ta , Inna tayi tace Alhamdulillah jikata Allah yakara daukaka musulinci akan kafirci , ashe kece hasken ahalina , Allahu akbar Allah mai girma Allah Allah yakarawa annabi daraja s.a.w. ,,,, yan falon sukace ameen

Mommy tace inna zamuso ,, kibamu tarishin ku na rayuwar ku dakukayi a baya kuma ya akayi kuka baro garinku kuka dawo jahar katsina ,,da zama

Zama inna ta gyara tace , kozan baku labarina ,, sai kowa yazo dan kowa yaji ni da babanku suwaye mu

Da sallama tashigo falon ,,hijab din a hannu har dan kwalinta ,, tana fadin babyn momsy baby ina kike

Kowa kallon ta yake cike da tausayin yadda take kuke

Da gudu ameera , ta nufi ikram tana " fadin waiyo momsy na ,, momsy na rungume juna sukayi ikram ta rungume ameera sosai ,, saida suka jima sosai , a haka kafin suka zauna

Ameera tace momsy na , waya fada miki ,, nazo " Ikram tace Fatima ta kirani , ta fadamin wai nazo kindawo , kamar almara " naji kawai nace bari nazo nasan fatima ,, bazata min wasa ba ashe da gaske ne,,, baby ina kike a wannan tsayin lokacin ,,,, Ameera ta bata labari bayan accident din su " sosai ikram tayi kukan tausayin ameera ,, ta kumayi madallah da Allah Allah yasa , mutane da dama sun musulinta , taji dadi sosai

Ameera tace , Momsy ina kannuwa na

Murmishi ikram tayi tace , gasunan a kusanki

Juyowa ameera tayi ,, tace kai momsy haka takwara da mijina suka girma " masha Allah kuzo nan kannuwa na ,, wajan ameera sukazo ta zauna dasu a gefenta ,, tace kusanni
Chapter 55 · 0% Book details