← Book details Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 65

Sashe 39

Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maman anty karima ce ta matso kunsan,, Ameera tace daughter kina nufin kece mana keba jenifer ta bace,, indai har hakan ne to gaskiya kuna mugun kamanni da jenifer ,, wanda ko dani bamu kai kama haka ba

Ameera tace mama ita jenifer ,, ina take ne wani waje ,, ta tafine bata dawo ba

Mama tace no daughter mutu wa tayi amma duk zuciyoyin mu,, basu aminta ta mutu ba

Nan mama ta bata tarishin su har zuwa lokacin da jenifer ta,, mutu

Runtse ido ameera tace to jenifer ,, a ina na taba jin sunan,, cen ta daga kai kamar ,, mai tunani " da sauri ta bude iko tace

Wace joshow a nan

Da sauri joshow yace nine joshow

Kallon shi tayi tace tabbas haka anty karima tayimin kwatancen shi

Kafin tace ina baby da boy suke

Cike da mamaki mama ta " fita waje ta dauko su she kuke sukeyi ganin maman nasu a shinfide ta shigo dasu

Da gudu sukayo kanta suna fadin mommy mu,, suna kara sautin kukan su

Kallon ameera takeyi ,, taga yadda suke kamannin da yaran ,a zuciyar ta tace lalle wannan babu,, wanda zaice bani na haifesu ba

Kasowa sukayi,, suna rungume ta beauty tace mommy , shine kika fadi yanzu aka shigo dake, daki kuka barmu awaje

Shafa kanta tayi tace am so baby kinji,, turo baki tayi, tace to bazamu je gidan granny ba ameera tace sai anjima zamuje,

Marus yace " mommy yaushe zaki haifa mana,, baby's dinmu

Waro ido ameera tayi tace ba yau ba yace to mommy sai yaushe tace ba lokaci boy

Ameera ta dago tana kallon su tace wannan,, ina ganin nasan ke maman " anty karima ce wanda kuke kira da jenifer

Kai kuma mijin tane,,

Wannan kuma maman ka,,

Duk suka amsa da eh

Ameera tace yanzu karfe nawa ne,,

Kallon agogon shi joshow yayi yace 1:30 PM ne

A daddafe, ameera ta mike tace kubari nayi sallar zan baku labari na,, da kuma yadda na hadu da jenifer din ,, da kuke kirana da ita

Joshow yace dama ke ubangiji daya kike bautawa,, Ameera tace eh , yanzu kubari nagama nadawo nabaku labarin komai

Nan suka zauna suna jiranta

Ameer ne yafito , cikin shirin sa na jallabi da alqur"ani dinsa,, a hannun sa , yana isowa falon yaga su mom nan ya gaishe su yana zama

Mom tace son sai ina haka,, da shiga mai burgewa," aikuwa kayi kyau

Shafa kanshi yayi yana aiyanawa a ranshi ina ma ace ameera ce ta fada mishi wannan kalamar da yasan sai tafi haka dadi

Tabashi mom tayi

Da sauri yadawo daga tunanin da yakeyi

Mommy tace son kake " rage tunanuka a ranka please na rokeka ' kaji son bana son kake wannan damuwar ,, kar kaje kasawa kanka cuta

Ajiyar zuciya yasauke, yace insha Allah mom zan dena na barwa Allah komai, nawa

Murmishi mom tayi ,, tace very good haka nakeson ji daga gareka tace ina zakaje ne haka

Yace mom wannan mlm Ahmed zanje so nake na kara yin hadda,, saboda zai ragemin zaman kadaicin da nake ciki

Mom tace to shikenan adawo lfy yace ameen mom

Harya juya yadawo yace am mom ina hajara ne

Mom tace tana daki ai tinda kuka dawo daga hospital tashiga " bata fitoba tana ciki

Ameer yace bari naje na ganta,, nan yayi dakin su Fatima

A zaune ya ganta ta juyawa, kofar dakin baya " a hankali yake tafiya harya karaso hannu yasa ya rufe mata,, idon

Da sauri ta rike " hannun tana fadin waye ne tana taba hannun shi amma, takasa gane wa , ai kawai saita saka kuka tana fadin , waiyo mommy " ga barawo yazo zai saceni " nima inna kuzo zai tafi dani

Dariya ce takama ,, Ameer jin yadda ta tsorata , shi mamaki ma tabashi " dama haka take da tsoro jin ta soma rawar jiki yasa shi sakinta yana dariya

Juyawa, tayi tana kallon shi tace dama kaine ka tsorata ni to wllh saina rama nan tayo kanshi , tana kara sautin kukan ta

Ko motsawa baiyi ba yana kallon yaga mai zata mishi

Tsalle tasoma yi wai zata kamo fuskar , shi itama ta rufe mishi idonshi sai faman haki takeyi, kamar tayi gudu

Tsayawa yayi yana kallon ikon Allah

Ganin dai bazata iyaba yasa, ta fada jikinsa tana kuka

Yar dariya yayi yana rungume ta yace ke yanzu in banda rigima , irin taki kanwata " kalle kifa yar guntuwa dake ko cikina baki kaiba,, amma kice zaki taba fuska ta

Duka takai mishi ya rike hannun ,, kiciniya, tasoma yi ta kwace hannun amma takasa" sai ta koma ta kwanta a jikinsa ,

Bayan ta yasoma bubbugawa alamar tayi shuru, jansu yayi suka zauna bakin gadon tana kara shigewa jikinsa saboda bacci da takeji , dan jiya dare ta raba tana kuka da nafila

Sai cen anjima yaji tayi bacci dagota yayi,, tana kallon fuskar ta kamar kace ameera ta amsa ,, ya kwantar da ita sake kallon yayi

Yana zancen zuci , yace yanzu da ameera ce shima zai kwanta a gefen ta ne " ya janyota jikinsa suyi bacci mai dadi da annashuwa ", saidai ba ita bace

Hawaye ne ya tarun mishi, a ido yana kallon hajara sai sauke ajiyar zuciya takeyi saboda kukan data ci

Bai ankare ba yaj,,hawayen na bin kuncinsa " goge wa yayi yana dafe satin zuciyar shi " a haka ya mike ya fita waje

Mom na zaune ganin ameer bai dawo yasa tayi tunanin ko , hira suka kama, saitaga ameer ya daura hannun shi akan saitin ", zuciyar shi da sauri mom tayo wajanshi " tana tambayar shi lfy

Baice mata komai ba " zaunar dashi tayi ruwa mai sanyi tabashi yasha sosai

Yana sha yaji , zuciyar shi tayi sanyi " tashi yayi yace mom zan fice

Cike da tausayi take kallon shi tace to son Allah yakiyaye hanya adawo lfy

Yace ameen ya Allah mom love you yayi murmishi zai fita

Har yakai bakin kofa tace son tsayawa yayi " ya juyo ya dawo

Zama yayi " kusan ta yace mom gani

Mom tace son a kullin ina kara fada maka ,, kayi hakuri , da duk abinda yasameka a rayuwa " ita rayuwa haka take yau kaji dadi gobe akasin hakan"" shi ba ruwansa yakan jarabceka akan " abinda kake so ,, yarabaka dashi yaga zaka mishi biyayya zaka jure rashin abinda " kakeso idan baya tare dakai , to ina mai maka nasiha " daka dage da addu'a,, ka mika lamuran ka, ga Allah komai zaizo daidai insha Allah

Numfashi ameen yaja kafin ya rungume mom ,, yace ina alfahari " dake mahaifiya ta ina yiwa Allah godiya daya bani ke a matsayin uwa mai share, mini kukana " mai nuna min hanyar Allah idan kuma,, kika ganni a damuwa kina " yimin nasiha mai ratsa zuciya da samun nutsuwa " lalle kin cika uwa ta gari,, wanda manzon Allah (s .a. w .) Ya fadi siffofinta,, da halayyar ta to Alhamdulillah mahaifiya ta kin kasance mai wannan halayyar da siffofin , Alhamdulillah Allah na gode maka " daka yoni musulmi dakuma samun family na gari , ya Allah ka bayyana min ameera ta " yana kai karshen maganar ya sunbaci koshin mom ya fice a falon

Murmishi mom tayi ,, itama taji dadin maganar dan nata tace Allah yamuku albarka yarana

Su joshow suna zaune " har ameera tayi sallar azuhar suna kallon ta kamar sunn,, samu tv tana gamawa tadawo wajan su

Zama tayi tana kallon su tace mama kuzauna zan baku labarina da kuma ya akayi nasan jenifer

Zama sukayi ,, mama tace muna jinki daughter "

Ameera tace ni sunana , Ameera Ahmed nan tabasu labarin ta har auren ta,,

Tadago,, tace dalilin dayasa " nasan jenifer ,, tin a mafarki " take zuwan mini tana kuka akan nazo na taimaki ahalinta,, na fiddasu daga duhu zuwa haske

Kuri suka mata da ido suna jin bayanin ta joshow yace to kin taba ganin ta a fili ne

Ameera tace eh na taba ganin ta sau daya ,, lokacin banida " lfy ne har suma nayi ina daga idona na ganta akusa dani,, da kayan likitoci,, a jikinta ita ta kira mijina ta fada mishi inda nake,, to daga nan ban sake ganin taba

Amma tace min insha Allah zanzo garinsu kuma zan ceceku " daga wannan halin,, amma tacemin batasan ta wacce hanya zanzo ba , kuma tace saina samu ciki zan rabu da mijina " ashe maganar ta gaskiya ne gashi narabu,, da ahalina kuma saida na samu cikin kamar yadda tace" gashi yanzu bata zuwan mini a mafarkin ma takai karshen maganar tana fashewa da kuka

A sanyaye, suke kallon ta cike da tausaya mata

Ameera tace,, yanzu ko kallona kukayi " ai kunsan bankai jenifer shekaru ba amma kun kasa gane hakan,, saboda son da kukewa jenifer

Joshow yace " tabbas nima jenifer ta taba zuwa min tace min bata mutu ba amma tana tsakanin " mutuwa da rayuwa amma akwai wadda zata zo ta fiddo ta, daga inda aka boyeta,, muma zata " fiddamu daga duhu zuwa haske

Ameera tace to nice wadda zan fidda ku tabbas jenifer bata mutu ba tana raye saidai " suna azabtar da gangar jikinta tana cikin ciwo

Ameera ta dago idonta " yayi kamar gauta,, saboda kukan da takeyi , ganin Allah yakawo ta cikin arna dole ne ta zama jaruma amma saita haihu zata yi wannan yakin " tace ko kunsan cewa jenifer tana bauwata Allah daya " dalilin addu'ar da takeyi yasa take samun " sassauci, da azabar da suke mata

A matukar razane " suke kallon ta joshow yace na tuna tace min malaman majami'a, ne suka yi tsafi da jinin ta,, na tuna yanzu

Zaman yan bori maman anty karima tayi tace yo jenifer wani abu kika yiwa malaman majami'a suka tsafemin ke ne , lalle na gama musu biyayya " tinda suka yimin tsafi dake kuma ko mai za'ayi saina" fiddoki

Suma su " mama sai jimami suke da al'ajabin wannan lamari ashe dama jenifer ba mutuwa tayi ba
Chapter 39 · 0% Book details