Sashe 58
Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tin wannan lokacin yohun shike kula da maryame ,, sosai yake sonta hakan kuwa ba karamin dadi yawa su papa ba ,
Maryame nada shekara daya maman yohun ta haihu shima namiji ne ansha murna sosai shima , amma yohun yace shifa bazai koma gidansu ba anan, zai zauna ,, babansa yace , shikenan duka ai dayane,, aka kawo masa kayansa duka sosai anisha tayi murnan barin mata yohun da akayi ,, nan taci gaba da kula dasu
Bayan maryame takai shekara uku , anisha itama sake haifan wata mace ,aka saka mata suna ingozi wato maman karima
Haka suka tashi cikin so da kaunar iyayensu kamar yaran mutum daya haka suke
Yohun ya takura akan shifa saiyakai , Maryame sa school haka tasa papa yace ya saka maryame a school , hakan yayiwa yohun dadi ,,dan dama kullin idan yazo school sai kajun yana da kanwa ahima yar uwanshi mai kyau ce idan yafadi haka sai sumishi dariya , banza yakeyi dasu , yace to saiya kawota ,shiyasa ya nace sai ansaka maryame a school
A tare suke zuwa ,shi yake mata wanka ya shirya ta , Anisha batada damuwa da shirin su zuwa school shi yake shiryasu su tafi abinsu , shakuwa sosai tashiga tsakanin maryame da yohun , kamar ciki daya suka fito ba kowa na school din bane yasan ba, yaya da kanwa bane maryame da yohun ,,haka suke rayuwar su yohun nabawa maryame kulawa ta musammen
Bayan wani lokacin maman yohun tasake haifan wani namijin aka saka mishi suna papa wato sunan ma haifina ,, yanzu mun kasance mu biyar ne maza uku mata biyu
Hakan yasa ingozi ta koma wajan maman yohun nan muka dawo mu biyu a wajan anisha mahaifiya ta
Haka mukaci gaba da rayuwa har muka girma alokacin yohun nada 25years ni kuma ina da 18years , banju dana 17years , ingozi nada 15years papa shine karamin mu yanada shekara 12years , haka muke kanmu a hade sosai iyayenmu ke jin dadi ,, idan za'ayi taron wajan abin bauta yohun ne agaba ,tare dani duk inda yake nima ina nan ,,haka yasa sosai mai tsananin gaske tashiga tsakanin mu nida yohun
Alokacin nima nayo gadon mama tace anisha bana barin bashi,, kullin muna fada a school akwai wata wadda tace tanason yohun , aikuwa abin yabata min rai ,,dama yar ajinmu ce , dan haka na kudurta araina sainayi maganin ta ,, baa tabani bama inayi bare aka shiga gonata ai abin nema yasamu ,, nan na kira ingozi na fada mata ,, itama dake tana da fadan sosai taringa cika tana batsewa ,,saidai fa duk fadan ingozi batakai ni ba ,, ni har nafice maman mu ma a masifar fada
Mutanen gari sukance wanda ya auri maryame ya auri bala'i idan mutum yafada min haka toko yaro yaje gaban uwarsa saina bishi na, mishi duka ", idan kuma daidai nine sai mu yini muna dambe bana gajiya
Ingozi nazuwa muka nufi haryar da yarinyar take zuwa , muka zauna zaman jiranta tazo muyi mata duka ,, cen sagata tazo
Saida ta nufi wajan wani lungu na hanyar gidansu muka tare ta
Cike da masifa nace ke dan ubanki , ni zaki kalla kice wai kinason yohun ,, ni sa' arki kice ko kinga ina wasa dakene
Yarinyar tace oho so dai ina sonshi ,, kuma ko mutuwa zakiyi saina aureshi
Jin haka yasa ingozi balla mata wani zazzafan mari har biyu tace ke yar uwan tawa kike fadawa magana to yau zanga mai kwatarki ,,,a wannan wajan
Da sauri ta dago tanason ramawa ,, nima nakara mata biyu ai tuni ta gigice , nan tayo kan ingozi dambe aka kama ,, batasan munfi karfinta ba ,, nan muka mata duka har suma tayi amma bamu dena ,, dukanta ba dan alokacin raina daci nakejinsa idan ban karya mata kafa ba ,, saida mukagaji dan kanmu tukun muka barta mukayi harya gida
A hanya ne muka hadu da baban yarinyar ,, bamu kalleshi ba muka fice ,, sai kawai yace ku wannan mafadatan yaran , kuzo nan dan ubanku marar kunya
Wani bakin ciki ne yarufeni jin anzagi ubana ,,idan anason ganin zallar masifata to azagi papa nan ko kwana ,zaayi ana fada to bazan bari ba ,, dawowa mukayi kamar wasu na Allah ,, muna sumkuyar dakai mukace gamu
Kallon mu yayi yace , ku bakuda kunya ko kuna ganin mutane bazzaku ce good morning ba saiku wuce ,gaba koda yake ai dama gidanku ba tarbiya ce daku ba sargantattu , , ne ku
Ingozi ta yunkuro zata mishi rashin kunya na rike hannun ta ,, kaina a kasa nace kayi hakuri baba zamu gyara
Harara ya banka mana yace ta ina zaku gyara kuda kuka taso gidan rashin tarbiya nan yajuya tafice ,
Da sauri nacewa ingozi maza dauko mana duwatsu daidai jifa da gudu tayi gefen hanya ta kwaso dayawa bayanshi mukabi , ganin munkusan kamoshi ,, aikuwa kuma soma jifanshi ba saurarawa
Yana tafiya kawai yaji ana mishi ruwan duwatsu ,, yana juyowa ingozi ta aika mishi jifa sai a goshinsa wani a bakinsa , nan da nan wajan yafashe , muna ganin yadda hakan muka gudu , Gida ingozi tashiga gidansu nima nashiga namu
Kamar babu abinda mukayi haka kowa tashiga gida ,, ina zuwa nasamu yohun yayi tagumi,,,da sauri na karasa cikin dakinsa na zauna a kusanshi tabashi nayi
Da sauri ya juyo yana ganin nice da sauri ya rungume ne yana sauke ajiyar zuciya ,, kamar wanda yaci kuka
Dagowa nayi nace yohun yamafaru kake wannan ajiyar zuciya ,, ko wani yabata maka rai naje na rama maka ne
Girgiza kai yayi yace naje school dinku daukarki banganki ba ance kintafo gida , nazo banga kowa ba mama ta tafi wajan biki sai ni daya a gida ,, banason naje gidansu papa duk shesu dameka da surutu
Murmishi nayi nace to ai gani nadawo ,, gidan wata kawata naje " sai yanzu nadawo
Mikar dani yayi yace ,, zomuje kici abinci kiyi wanka saimu kwanta nan muka fita ,
Abinci naci nan mukayi wanka ,, sai bacci
Baban budurwar ,, yohun ko da kyer ya kai gida yana dafe da goshi da baki , nan yasamu wani tashin hankalin ,, sosai abin yabashi haushi jin , wai su maryame ne suka mata duka ,, nan sukayi, asibiti bayan sundawo , gida yatafi yakai kashen mu wajan papa
Yana zuwa ya fadawa papa komai abinda muka mishi ,,hakuri sosai papa yabashi yadauko kudi masu yawa yabashi ,, tukun suka tafi
Papa nazuwa gida ya kirani zai zaneshi " yamin bulala daya na saka ihun ai da gudu , yohun yafito
Wajan papa yazo yace please am so sorry papa kadena dukar min kanwa
Papa yace kabari na zaneta ,, wannan yarinyar bata ji nan yafada mishi duk abinda sukayi ,, hakuri yohun yabawa papa da kyer ya hakura
Niko sai ihu nakeyi ina bayana shikenan sai jini yake ,, ganin hakan yohun ya dauke muka koma daki
Ruwan zafi yayimin ya gasamin bayan tukun na kyale
Haka mukaci gaba da rayuwa ,, duk yarinyar data ce tana son yohun tofa ,, zataji a jikin ta shiyasa yan mata ajinmu tsoron yiwa yohun magana sukeyi saboda namusu ,,iyaka dashi
A sabuwar shekara ne aka kawo mana sabon headmaster a school dinmu ,,malamin yana da nutsuwa sosai ga fara'a duk abinda baka gane ba zai maka bayani sosai yasamu karbuwa a wajan daliban
Saidai wani abu da bamu gane ba yana yin wani abu sai yake ta karanta wani littafin alokacin bamu ,san alqur"ani mai girma bane ,, saboda mu krista ne , hakan yasa inyana karanta wa nida yohun muke rakubewa muna jin karatun nashi
Kullin haka mukeyi , ida yana karatu ,, saimuke labewa munaji ,
Su papa ganin soyayyar dake tsakanin mu ,, yasa suka saka ranar bikin mu nida yohun sosai muke murna nidashi
Headmaster dinmu mukaje wajan sa fada mishi mukayi ,, ansaka mana ranar biki ,, sosai yataya mu murna tin daga wannan ranar , yazamana kullin sai munje hira wajan headmaster ,dinmu sosai muke jin dadin hirarsa ,, wani lokacin da dare ma muke zuwa yayi ta bamu labarai masu dadi da haka yasoma jan hankalin mu zuwa addinin sa
Kullin saiya yita mana wa'azi mai ratsa zuciya yace , mudena rungume juna nida yohun ,, inba aure mukayiba
Idan kuma munayin haka zanyi ciki
Ai nan da nan muka dena amma ba dukaba in wani abin farin ciki yasamemu ,to saimun rungume junan mu ,,da haka da haka imani , yake shigar mu nida yohun ,,, sosai muke tuna irin azabar da za'awa masu mugun ,, hali hakan yasa na nutsu nadena jan mutane fada ko anja ni bana tankawa ,, kowa sosai mutane " suke mamakin cenjawa ta har su papa suna mamaki maman mu kuwa farin ciki taringa yi ,, tace ai naji dadi dana dena , fada da mutane ,
Haka mukaci,, gaba da rayuwa muna kara jin tsoron Allah a zuciyar mu
Wata ranar wadda bazan taba manta wa da ita ba a tarishin rayuwar ta ,ta duniya ,, ranar dalilin rabuwar mu da iyayenmu ,, ranar shigarmu bakin ciki
Da dare mukaje,,wajan headmaster mukace, munason musulinta , sosai headmaster ,,, yaji dadi nan yabamu kalmar shahada , mukayi cikin sa'a nan yace muzabi , suna , yohun yace shi yana son asamishi , Shareef headmaster yace masha Allah
Kallona yayi yace yasunana nace maryame , murmishi yayi yace , ai ke kawai naki gyarawa zaayi ne yanzu kin koma maryam
Sosai naji dadin sunan , haka muka dawo gida muna ta farin ciki
Muke zuwa, muna daukar karatu sosai muke fashimta damu jin dadin karatun "
Papa shi yafara ganowa mun shiga addinin musulinci ,, aikuwa sosai ranshi yabace nan yazo ya samemu ,
Ranar munga bacin rai awajan papa yace saidai muzaba ko addinin musulinci ko su
Kallon juna mukeyi ,, nida shareef saida papa ya daka mana tsawa tukun muka dawo
A tare mukace , gaskiya papa addinin mu mukeso na gaskiya
Ran baba yayi mugun baci dan haka tashemu ya koramu ,, har waje yace mubar mishi gida