← Book details Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 65

Sashe 40

Amir Da Amira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ameera tace wannan yakin sai na haihu zamuyi shi amma fa sai kunyi abu daya idan kuna ra"ayinsa

Kallon ta sukayi joshow yace menene shi abun munason,, mujishi ya ake samunsa

Ameera tace idan kuna son mu yaki karya to saifa kun zama irin wato ma'ana kun musulunta" shine zai kara mana karfin yakar ,, wannan azzalumai" amma shi musulinci ,, baa tirsasa mutum,, ace dole saiya shiga ko dan wata bukatar shine yake son shiga " to baa haka a musulinci , kuma baa shiga a fita , daga cikinsa

Shi addini ne mai sauki , kuma ba kudi ake biya ba don a shigeshi , kawai kalma zaa fada maka ka maimaita "

Addinin Allah mai tsaki da samun nutsuwa da kwanciyar hankali , da zaman lfy

Ka so Allah da annabi Muhammad (S.A.W) son da baka taba yiwa wata,, halitta a duniya ba , ka nuna soyayyar ga manzon Allah (S.A.W) domin samun rabauta ranar gobe kiyama takai karshen maganar tana sauke numfashi

Kafin tace kuje kuyi tunani " kada waninku yace zai shiga musulinci dan wani abu idan zaka shiga kafara tsakake zuciyar ka, tukun kuma kasa aranka zaka " shiga musulinci da zuciya daya bada wata manufa ba nan ta kwanta ta juya musu baya

Duk jikinsu yayi sanyi da bayanin ta ,, dan haka maman anty karima ka tafi gida cike da tunanuka barkatai, koda taje gida dan ta ta fadawa,, shima dai mamaki da " al'ajabi yakeyi,,

Joshow da mama , kuwa suma zama sukayi,, suna ta tunani,, akan maganar ameera

Ameer ne zaune gaban malam Ahmed yana daukar karatu , sosai ya maida hankalimshi kan abinda ake koya mishi kuma yana jin dadi sosai bayan sun gama

Malam Ahmed yace masha Allah mlm ameer kana kokari sosai kuma naji dadi daka dawo domin yin hadda, Allah yakara basira da hadaza

Kan ameer a kasa, yace ai nine da jin dadi mlm saboda ina jin dadi sosai ina samun nutsuwa

Malam Ahmed yace to yayi kyau yanzu gyara ne za ake maka insha Allah kana kokari

Ameer yace to mlm Allah yasaka da alkhairi yajinkan magabata, ai dan mutum yayi sauka bashi yake nuni da cewa ya iya dukkan karatu cike ba ko ya karanta wani wajan baiyi kuskure ba shiyasa nazo hadda dan habaka karatu

Murmishi malam Ahmed yayi yace to Alhamdulillah yanzu kuma sai ranar lahadi, insha Allah

Ameer yace Allah yakaimu mlm nan sukayi sallama yatafi gida

Wani babban mutum " ne yana tsaye jikinsa da bakaken kaya " wani ne ya karaso " kamar an koroshi , yana fadin shugaba !shugaba ' shugaba , akwai matsala fa

Da sauri ya juyo, yace kamar yaya " raju kaxo kamar an tsorata ka

Wanda aka kira da raju yace shugaba wannan yarinyar mai kamar jenifer ta dawo nomal , yau da kwana biyu , kuma mai bautar ubangiji daya ce " tana yiwa yan gidan tayi shiga addinin ta " kuma yanzu sun san jenifer bata mutu ba mune muka saceta " tana wajan mu

A matukar razane " yake kallon shi yace wai kana nufin wannan yarinyar tadawo nomal kuma ba abu " daya muke bautawa ba "

Raju tace wannan haka yake kuma yanzu idan muka fadawa mutane wannan ba jenifer bace " bazasu yadda ba kuma zasu zarge mu ne

Shugaba yace" dole ne itama ta mutu ko muyi tsafi da ita mubawa dodo jinin ta bata isa tazo " ta tuguza mana cikar burukan mu ba dole musan abunyi

Raju yace ai takusa haihuwa sai mu mata irin na jenifer kaga shikenan mun gama da ita dan dole mucika burin mu na zaman manyan masu kudi a Nigeria

Shugaba yace wannan haka yake raju su sun dauka,, haka zamuke zama muna musu hidima a banza basusan duk muke kashe yaransu ba mubawa dodo jinin yabamu kudi,, ao dole ma mu kashe wannan bakuwa nan suka tafa suna dariyar keta suna shiga cikin majami'ar

Daddy ne da mommy suna zaune da ummi mufeeda suna hira,, ummi mufeeda tace yauwa yaya dama ina da wata magana

Daddy yace ina jinki mufeeda

Ummi mufeeda tace maizai hana a hada hajara da ameer aure tinda naga yanzu sun shaku kaga hakan zai sakashi dena tunanin ameera dayawa " tinda kaga suna kama koya kace

Numfashi dad yaja yace to banki takiba " wannan ma shawarar tayi kyau " zan fadawa yaya,, Ahmed wannan maganar da Abubakar

Mom tace hakane gyara amusu auren saboda kullin ameer cikin damuwa yake Allah ma yasa yanzu yana zuwa hadda

Ameer ne da hajara suka shigo, da sallama amsa musu sukayi suna kallon su

Karasowa sukayi zama sukayi,, mom sukace musu sannun ku da aiki

Hajara tace yauwa ta kalli, Ameer kamar zatayi kuka tace yaya nafa gaji wllh bazan rakaka ba wajan karatu anjima " tana hade rai

Yar dariya yayi yace to yarinya baki isaba dole muje dake " kona ki siyo min takalmin da kikace kina so

Fuskar tausayi tayi ta kalli mom tace mom kinga yaya ko kice mishi nagaji banzan iya fitaba " bacci zanyi

Murmishi mom tayi tace bazaki jeba kuma dole yasiya miki, tinda tare kuke aikin

Gwalo hajara tayiwa " Ameer harara ya aika mata yana mata nuni da zai kama ta tashi tayi ta shiga ciki dan tagajin da gaske

Shima ameer yace yayi sama sai ajima zai sauko yaci abinci

Ummi mufeeda tace wllh yaya gyara ayi hadin nan daddy yace to insha Allah ai naga sun shaku nan sukaci gaba da hira

Yau " tinda safe ameera ke jin ciwon baya da marar ta amma saita yu shuru

Mama na lura da ita data tambaye ta saita ce ba komai

Ciwo yaci karfinta saboda wani irin juyi da cikin yayi da karfi tace innalillahi wa inna ilaihin raju'un wai mama na mutu mama kizo

Da sauri mama tashiga tana fadin wannan haihuwa ce bari na dauki keys mutafi asibiti ,

Joshow ne yashigo gidan jin karar ameera yasa yayi dakin da gudu " mama tace maza dauko kayan baby mutafi asibiti haihuwa ne da gudu yafita ya kai kayan mota yakoma suka dauko ameera aka kaita cikin motar,, duk ya rikice ganin idon ameera na juyewa bakin idonta na sama "

Ameera kuwa tsananin azaba ne ya mata yawa tana fadin innalillahi wa inna ilaihin raju'un , la'ilaha' illallahu Muhammad rasulullahi , salallahu alaihi wasallam, " saita saki jiki ta duf

Cikin tashin hankali mama tace ameera ! Ameera ! Ameera ! Kada kitafi kibar mu irin na jenifer please karki mutu kitashi ki fidda mu daga duhun da jenifer tace

Joshow kam kusan haukacewa yayi da mugun gudu take dravin ,, kafin kace mai sunzo asibiti da sauri aka dauki ameera kamar dai ta mutu su mama ke gani......

*tofa tirkashi shin ameera ta mutu ne ko tana raye shin ameer zai aminta da auren hajara ko ita zata hajara zata yadda shin malaman majami'a zasu ci nasara akan ameera ko kuwa to wannan amsar saiku biyo (maman nusy ) domin jin yadda zata kaya*

Ina godiya da comments din Allah yabar kauna
[28/10, 14:22] MRS. MU'UTASIM: *🌟AMEER DA AMEERA 🌟*

*RUBUTAWA DA TSARAWA*

*MAMAN NUSAIBA CE ✍️*

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

*61—62*

Cikin sauri , aka yi emergency room da ameera " numfashin ta na sama da kasa kamar na fitar rai

Mama da joshow " kana ganinsu kasan suna cikin tsananin tashin hankali sai safa da marwa suke ,, duk hankalin su baya jikinsu

Marus da beauty kam,, sai kuka suke sun rungume suna beauty ta kwanta a jikin marus dukkansu suna rera kuka " gwanin ban tausayi " ba kamar beauty ma har shidewa,, takeyi ganin maman nasu kamar gawa

Mama ce ta karaso inda suke ta kallesu sai ta share hawaye " saboda mugun tausayin dasuke bata gashi ,, a haka ma basusan ameera ba ita ta haifesu ba

Tace kuyi shuru,, kunji maman ku zata samu lfy yanzu za'a fito da ita

Marus ne ya juya yana kallon mama " yace ,, mama please kice mommy tafito mutafi gida,, naga sun kaita daki sun rufeta,, in lefi ta musu mama ki basu hakuri " karsu yiwa mommy wani abun please mama yana kara sautin kukan shi

Danne kukan ta mama tayi,, tana rarrashin su tace marus kayi hakuri maman ku haihuwa ce zatayi ko bakuson babyn ne

Da sauri marus yace muna so kenan mommy brothers ko sisters zata haifa mana ,, muke zuwa school tare

Mama tayi ajiyar zuciya tace, eh anjima zaa fiddota

Beauty ta,, tashi daga jikin dan uwan nata tace mama sister mommy zata mini ko nida marus muke, masu wasa ko

Murmishin yake " tayi tace eh

Joshow kuwa ya kasa zama sai yayi wajan dakin ameera yadawo yazo wajan su mama,, duk ya rasa nutsuwar sa ko ganin, kirki baya yi saboda tashin hankalin

Jin ameera tana ihu tana kiran sunan Allah dana yayanta ,, hadda su inna " kowa dangin ta a wannan lokacin ameera saida ta kira shi saboda tsananin azaba

Ameer ne zaune shida hajara " tana bashi labarin dariya duk dan ta hanashi " tunanin da yakeyi

Dafe saitin zuciyar shi yayi da hannu " ya runtse idonshi saboda bugun da zuciyar shi keyi , da sauri ya mike tsaye

Itama hajara mikewa " tayi yana fadin yaya lfy ko wani abun yake damunka ne ,, bai amsa mata ba " kama hannun shi tayi ta zaunar dashi " akan kujerar tana fadin wai menene yafaru yaya kayi magana mana

Shuru baice, komai ba" kuma bai mude idonshi ba

Ganin yasa hajara fashewa da kuka tana fadin please yaya tell me what happened ne

Ganin bazai ce mata komai yasa ta kama hannun shi , ta nufi ciki dashi tana taimaka,, mishi suka shiga ciki " basu tarar da kowa ba, a falon nan sukayi sama

Cikin room din,, takai shi har bakin gado " har yanzu baiyi magana ba har ta zaunar dashi

Zama tayi gefenshi " tana share hawayen ta " tace yaya kamar zata sake sakin wani kukan " tana yin fuskar tausayi
Chapter 40 · 0% Book details