← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 73

Sashe 9

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tuni zunnurah ta hade rai,hakanan a duniya taji sam fiddausi bata yi mata ba,ko kadan jininsu ya kasa haduwa,shahida ta rasa dalili,tun tana sharewa har tazo tanawa zunnurah fadan ta daina haka,wulaqanta dan adam babu kyau,yarinyar na sonsu hakanan bata da wata matsala meye abun sha mata qamshi da take
"Hakanan wallahi nidai naji batayimin ba" amsar da zunnurah ta baiwa shahida kenan.

A tsakar gida fiddausi ta duqa ta gaida umma cikin ladabi,ta amsa ba tare data tsaya ta mata wani cikakken kallo ba taci gaba da sabgoginta(babban kuskure na biyu da ummanta ta sake tafkawa bayan fada da miji gaban 'ya'ya),fiddausi ta shige dakin shahida,cikin fara'a suka gaisa ita da shahida,yayin da xunnurah ta kauda kai ta amsawa fiddausin sama sama,dif zunnurah tayi sai shahidan da fiddausi dake hira sama sama,har shahida ta gama shiryawa suka fice daga gidan.

Suna gab da shiga gate din makarantar xunnurah ta kamo hannun shahida tayi baya da ita,duk sai suka tsaya ta hade gira tace da fiddausi
"Me kike jira?,magana zamuyi da ita" sum sum fiddausi ta juya ta wuce ciki
"Wai me yasa kikeson koyon halin daba naki ba zunnurah me fiddausi tayi miki?"
"Shahida,ba haka kawai naji banson yarinyar nan ba,an bani labari fiddausi tana taba shaye shaye..." Rufe bakinta shahida tayi da hannu tana kallon zunnurah gami da zaro ido
"Haba zunnurah,haba,zato fa ance zunubi ne,ya zaki jefeta da wannan mummunan kalmar don kawai tana son mu'amala damu?"
"Da gaske nake miki shahida,daga bakin namiji na samu wannan labarin,kinsan kuwa su basu fiye munafunci kosa ido ba bare kice,sannan kuma idan zaki lura da kyau zaki ga yanayin fiddausi ba irin namu bane,yawan bacci da kasala kawai alamune na mutum yana taba shaye shaye,zaman kadaici rashin so magana da yawa" zame hannunta shahida tayi daga na zunnurah,don sosai taji babu dadi ta kuma ji ranta ya baci
"Duk abinda kika fada zunnurah baki da tabbaci a kanshi,karki fadi abinda zaki jawo a tsaidaki a miki hisabi ran gobe qiyama,ni fiddausi ta gayamin bata da cikakkiyar lafiya,tana da sicklier shi yasa take yawan bacci" kada kai zunnurah tayi
"Shikenan shahida tunda baki yadda dani ba,kinfi kowa amma sanin halina,nidai ina baki shawara kibi a hankali,don bazanso abinda zai cutar dake ba"
"Babu abinda zai faru in sha Allahu" daga wannan suka rankaya suka shige cikin makarantar.

Washegari da wuri taje wajen bada sadaka ba kamar yadda ta saba zuwa ba,hakanan takejin wani nauyi da kunya tunda ta karanta kalaman da yarubuta mata jikin takarda,niyyarta tayi da wuri ta koma gida ba tare daya sameta ba,saidai abinda bata sani ba tuni ya rugata ma zuwa,saboda gaba daya ya rasa nutsuwarshi Allah Allah yake gari ya waye yamma tayi yaje ya ganta,bai taba tsintar kansa cikin irin wannan yanayin ba,duk yanayin rayuwa da yake ciki hakan bai hanashi bacci ba,sai gashi a karon farko saboda ita ya kasa bacci daren ranar gaba daya,duk juyin da zaiyi itace cikin ranshi.

Yana biye da ita bata sani ba,baiyi mata magana ba saida suka gota wajen suka shiga wani layi
"Yanzu yau kuma haramiyar ladan rakiyar za'a yimin?,wanne irin laifi nayi haka?" Cak ta tsaya,farinciki da kuma faduwar gaba na cakuduwa cikin ranta,idanunta a waje har ya iso gabanta yasa hannu ya amshi botikin,ya jera kafada da ita
"Muje" ya fada cikin sassanyar muryarta da kullum take mamakin dad'in muryar da Allah ya bashi,idan yana magana dole sound dinshi yaja hankalin duk mai sauraro,yau saitakejin nauyin tafiya dashi,ta kasa yin gaba,ya sake dubanta
"Waiko amsar tambayata itace a'ah akemin irin hakane" wani wal tayi da ido,saiya dafe qirjinsa da hannunsa daya
"Kiyi haquri karki qarasa tarwatsamin zuciya,wannan zuciyar mai rauni ce akanki"

Fuskarta ta qunshe cikin hijabinta tana dariya qasa qasa,wawiyar ajiyar zuciya ya saki
"Wai Allah na,alhmdlh,ko iya haka aka tsaya na tabbatar da cewa ina da nasara...amma dai a gayamin ana sona?" Kai ta kada cike da tsananin kunyarsa,wani dan tsalle ya saka sannan yace
"Alhmdlh,alhmdlh" yana rungume da hannayensa.

A hankali suka ci gaba da takawa shida ita,saidai ita gaba daya nauyinsa takeji,yayin da shi kuma yake janta da hira jefi jefi,yau duk masu binsu da kallo mutanen cikin unguwarsu basu dameta ba,har sai taji ma batason su isa gida yace zai wuce.

"Kina son wanda bakisan sunanshi ba hakanan bakisan waye shi ba" ya fada bayan ya miqa mata botikinta,ita sam bata damu da wayeshi ba,sonsa takeji irin wanda bata taba zata ko tsammatar akwai irinsa ba a duniya,tanajin koma wayeshi yayi mata hakan
"Ni sunana muhammad anwar aminu,haifaffen kano ne kuma dan kusa da unguwarku ne ni,maraya ne ni bani da uwa bani da uba,sai 'yar uwata d'aya data ragemin anty usaina,ina karatu ne a fce kano...kefa?,shahida ko?" Murmushi ta saki tana dubanshi cikin tausayi jin cewa maraya ne,kai ta kada sannan tace
"Khadija amma shahida,nice ta farko wajen umma da abbana,ina da qanne hudu,nan ne gidanmu a nan aka haifeni,ina SS 2 yanzu" kai ya kada sannan yace
"Idan nazo anjima za'a barni na ganki" kai ta gyada da sauri,don tasan yadda zatawa ummanta bayani yadda zata fahimta
"Shikenan zanzo anjima in sha Allahu,inason mu soma mu'amala cikin fahimtar juna gaskiya da amana...ki shiga gida lokacin islamiyya ya kusa ko?"
"Na gode" ta furta cikin siririyar muryarta data dauki hankalinsa,kai kawai ya iya gyadawa ya bita da kallo harta shige.

"Waye a waje kuke tsaye dashi?" Tambayar da ummanta ta soma jefo mata kenan sanda ta aje botikin tana shirin zama,kunya ta d'anji ta kamata,saita kasa amsa mata da wuri har sai data maimaita
"Ba kowa umm,yadai taba rakoni gida sanda su ahmadi suka fasamin botiki,shine...shine...." Saita kasa qarasawa,murmushi kadan ummantata tayi,saboda burinta bai wuce su aurar da shahida ba da zarar ta kammala secondry schl,ita kanta tasan basa kyauta mata yadda koda yaushe suke cikin fada da juna suna sakata kuka qunci da baqinciki
"Shine me?" Ta sake tambayarta tana tura mata kwanon da tayi kwadon zogale ta rage mata saboda tasan tana sonshi,sai data sadda kai sannan tace
"Shine yace wai anjima zaizo idan za'a barni na fita"
"Allah ya kaimu" ta fada tana miqewa don ta wanko hannunta,cikin farinciki taja kwanon ta soma cin zogalenta,wanda tana gamawa ta shige bandaki ta sake watsa ruwa saboda ranar da ake,fitowarta kenan daga bandaki dauke kwandon wanka zunnurah ta iso,tana shiryawa tace
"Zunnu...akwai labari fa yau"bakin zunnnura a washe tace
" ta samu kenan?"kidai muje na baki kisha,ta fada tana zura plate shoes dinta,ta dauki jakarta suka leqa suka yiwa umma sallama suka wuce.

A hanya ta labartawa zunnurah komai,dariya ta dinga
"Kai amma wannan gayen yayi addu'a tuquru kafin yazo,shahida da babu wanda ya isheta kallo?,da kinga wata da saurayi ma zakice wannan ai iskamci ne dududu shekarunmu nawa?,ashe harkin girma" dundu ta dumawa zunnurah
"Banason iskanci qawa,wallahi nayi mamaki nima sosai,dama haka abun yake?,kinji kuwa yadda nakejinsa a raina?,har banason mu rabu,idan yana kallona wlh zunnurah ni kadai nasan me nake ji a zuciyata,ban taba tsammanin akwai wani da zanji haka a kansa ba" dariya zunnurah taketa tiqawa
"Na shiga uku ni zunnu,sati daya kacal amma shine kika zare haka?,Allah yasa to nan gaba kar ya haukatamin qawa ya cuceni"
"Ba komai idan ya haukataninma zunnu" ta fada tana tayata dariyar,gab da zasu shiga makarantar sukayi kacibus da fiddausi,da fara'arta take musu magana amma shahida ce kawai ta amsa suka rankaya suka shige makarantar tare.

Tunda ta dawo daga islamiyya ta kasa zaune ta kasa tsaye,qiyasta da qimanta yadda haduwarsu zata kasance take,wannan ne karon farko data soma son wani a rayuwarta,kuma karon farko da zata fara tsayawa zance da wani.

Tuni ummanta ta yiwa babanta bayani,bai kuma ce komai ba,illa ya kirata ya masa tambayoyi game da shi,ta bashi amsa gwargwadon abinda ta sani game dashi,yace ta kula kuma idan sun fahimci juna zaiyi magana da yaron.

Ba wani kwalliya tayi ba,tadai saka kayanta masu kyau atamfa riga da skert,ta kuma yafa wadataccen mayafinta,sanda ya aiko kiranta tare da mubina suka fita,yana zaune saman yalwataccen dakalin qofar gidansu,daga soron ta tsaya tana qare masa kallo,yayi kyau sosai fiye da dazun cikin qananun kaya,iya kwanakin kadai da tayi tana ganinsa ya tabbatar da cewa shi din dan gayune kuma mutum mai son tsafta,bata taba ganin kayanshi babu guga ba,hakanan bata taba ganinsa da datti ko wani abu makamancin haka ba
"Daure ki fito princess...saiki kallenin da kyau" habawa,wata iriyar kunya ta taso ta lullubeta,bata taba tsammanin yana kallonta ba,saita sake lafewa ta kasa fitowa,tashi yayi yana murmushi ya tsaya a qofar soron nasu yana kallon mubina dake gaidashi,ya amsa yana shafa kanta gami da yi mata wasu tambayoyi tana amsa masa,rabi duk a kan shahidan ne,kunya duk ta sake kamata ganin yadda mubina ba abinda ya shalleta,komai ya tambayeta gaya mishi take,saida suka gama hirarsu sannan yace
"ALLAH YA TAIMAKEKI...kona koma ne yau ba za'a samu ganina ba?" Dole ta fito ta saka musu tabarma daga soron nasu,da yake yana da yalwa sosai masu wucewa ba zasu takurasu ba.

Gaisheshi ta sakeyi ya amsa yana tambayarta gida kaman ba dazu suka rabu ba,cikin wani shauqi da yake fusgarsu gaba dayansu.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

ALQAWARIN ALLAH 08
Chapter 9 · 0% Book details