← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 73

Sashe 38

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kofin kunun hannunshi ya aje yana duban anty usaina
"katsina zan wuce,ko kina da wani saqo wajensu inna?" Cikin mamaki take kallonshi
"Katsina kuma anwar?" Kai ya gyada yana murmushi
"Mamaki kikayi anty irin wannan kallo haka?"
"Ai dole nayi mamaki,idan zaka katsina ba haka muka saba yi dakai ba,hasalima saina tursasaka kafin kaje,wani lokaci ma saika zabi lokaci da kanka,baka taba cemin zaka katsina haka katsaham ba sai yau,kodai wani abu ya faru acan ne kake boyemin?" Sai ta bashi dariya ganin yadda duka ta damu,har yanzu bata daina damuwa dashi da lamuransa ba
"Anty na,babu wani daya faru,shikenan Allah baya shiryar da bayinsa duk sanda yaga dama,da da nake qin zuwa yanzu Allah ya shiryeni shikenan?" Kai ta kada
"Allah yasa"
"Yasa ma" ya amsa yana murmushi
"Atamfofi ne kawai zan baka ka kaiwa innan kayan sallarsu dana saba basu,sai kuma sannu da jiki da zakace ina yiwa basira"
"Gsky banjin zan samu zuwa gidansu basiran,saboda ayau nakeso na dawo"
"Shikenan,mayi waya" ta fadi tana miqewa don shiga ciki ta debo masa saqon.

Zuwa qarfe sha biyu na rana ya gama duk wata siyayya da yakanyi musu a sanda zaije katsinan waje kakanninsa wadda ta haifi mahaifinsa,kasancewarsu masu qaramin qarfi sosai,daya na raina ya dauki hanya,ya saki ajiyar zuciya yana qissima yadda abubuwan zasu kaya idan ya isa can.*zafafa biyar na kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqatar siya zaki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*Alqawarin Allah*
2️⃣5️⃣

Tafiyar awa biyu cif ta shigar dashi garin katsina,tuqi yayi lafiyayye cike da nutsuwa da kuma tunani kala kala,kai tsaye unguwar kakanninsa ya nufa.

Yana qoqarin parking motarsa kawunshi modu ya fito da alama masallaci zashi saboda yadda yake dan hanzari,bai ganshi ba hakan ya sanya anwar kirayenshi,saiya waiwayo yana dubanshi cikin murmushi
"Ikon Allah,yau kaine a garin da kanka?" Yana murmushi gami da kashe motar yace
"Wallahi kawu,mun sameku lafiya?"
"Lafiya qalau...mu shiga daga ciki"
"A'ah kawu,gwara na soma yin alwalar tukunna"
"To...to,shiga daga mana saika daura"
"Ah ah kawi,kar naje su tsaidani mu rasa jam'i,idan mun idar ma shuga tare" daya daga cikin yaran da sukazo wucewa kawu modu ya qwalawa kira ya sashi ya shuga ciki ya debo musu ruwa a buta
"Dan kuwa yau inna ta samu nayi,kazo yau zuwan ba zata sanda ba'a tsammaci ganinka ba" murmushu anwar yayi
"Wallahi kawu,Allah ne ya kawo tafiyar haka"mintuna kadan yaron yafito dauke da 'yar matsakaiciyar buta,anwar ya karba suna dan taba hira da kawu madun harya gama alwalar suka rankaya zuwa masallacin.

"kaine yau kuma?" Inna ta fada sanda yake qoqarin zama kan daya daga cikin kujerun dake falon,murmushi ya saki yana dubanta,sun riga da sun camfashi baisan dalili ba
"Nine inna,kaman wanda bai zuwa?,kodai rikicin tsufa ya soma samunki ne kike zaton na jima sosai banzo ba?" Baki ta tabe tana rufe kwanon shan data gama shan ruwa a ciki
"Idan ina rikicin tsufa na kasa lissafi ai kawunka ahmadu baiyi tsufan da zai kasa lissafi ba ko?" Dariya ta bashi sosai har sai daya danyi sannan yace
"To shikenan yanzu Allah ya shiryeni,saime kuma?" Harararshi ta danyi
"Allah yasa"
"Amin inna" gaisheta yayi cikin mutuntawa ta amsa tana tambayarshi su anty usaina
"Lafiya lau take,tana gaisheku dakyau"
"Muna amsawa" daidai lokacin rashida 'yar kawu ahmadu ta shigo da kwanon abinci guda biyu,cikin girmamawa ta isa gaban anwar ta aje tana gaidashi
"Duba cikin dakina ki dauko kwanon sha ki debo masa ruwan a randa idan zai iya sha" dariya ta sake bashi,ya fuskanci rikici yau take ji da gaske,saboda wancan zuwan da yayi tace ya zabi daya cikin yammatan 'yan uwa dake katsina ya hada da wdda zai aura a kano duka ya aura,yasan yau zai kashe bakin tsanya ne gaba daya shi yasa bai tada maganar ba ya barta take rikicinta
"Sha kuwa harda shaye shaye...amma ba yanzu zanci abincin bane,zanje wata unguwa ne na dawo,saqonku na tsaya saukewa don na ragewa motar nauyi" duban rashida yayi dake zaune gefe tana kallonshi,ji take daman a gidansu yake
"Inasu abdurrashid?"
"Suna qofar gidan malam"
"Maza jeki kiraminsu" da hanzari ta miqe ta fice kawu ahmadu ya sako kai hannunsa dauke da ruwan roba da lemon roba ya aje gaban anwar yana cewa
"Garin yau ana zuga rana da zafi,ko rashin saukar ruwan sama ne kwana biyu ya saka haka oho?"
"Ba mamaki kawu,kasan ko yaya hadari ua hadu ba ruwa sai gari ya bada zafi" daga haka kawun ya samu waje ya zauna suka shiga taba hira kan harkar noma da abinda ya shafi damina har yaran suka shigo.

Cikin girmamawa suka gaidashi kowa na murnar ganinsa,ya amsa musu cikin kulawa ya dubi kawu da inna
"Kawu xanje wata unguwa na dawo,Allah yasa zan sameka idan na dawo din,akwai maganar da nakeso mu tattauna"
"Eh nima inason dan fita in duba shago na yau aike akemin,dalilin ma daya sanya ka ganni gida ban fita kasuwa ba kenan,amma ba jimawa zanyi ba,zan sallami yaranne na dawo"
"To ma sha Allah,kafin sannan na dawo,inna zanje na dawo"
"Allah ya tsare hanya" ta fada tana aje carbin hannunta sannan suka fita da yaran ya bude motarsa ya fito da duka kayan da yake nasu ne,yace sukai cikin gidan,sai daya tabbatar sun shige sannan ya tada motar ya fice daga layin.

Sassanyar ajiyad zuciya ya fitar sanda yake gab da isa unguwar,qwaqwalwarsa na masa bitar abinda xaije ya aiwatar din,jiki da zuciyarsa tana gaya masa abinda zaiyi din shine dai dai,a nutse ya kutsa motar cikin layin,bai tsaya ba sai daya rage daura gida daya ya isa qofar gidan sannan ya kashe motar,zamansa yayi ciki yana tunanin ta yadda zai soma shiga gidan,daada zata ganeshi kuwa?,zata karbi zancansa?,zata yarda da qudurinsa?.

Idonsa ya bude sosai sanda yaga saurayin daya saba aike zuwa gidan lokaci xuwa lokaci ya leqo ya koma da sauru,addu'a yake Allah yasa ya sake fitowa.

Da hanzari sulaiman ya koma zuwa cikin gida da sauri yana kiran
"Daada,daada" dattijuwar da ake kira da daadan wadda ke zaune cikin rumfarta tana daura busashshiyar kubewa ta daga kai kawai tana kallonshi har ya iso rumfar tata
"Haba sule,wannan wacce iriyar dabi'ar banza ce haka?"
"Daada wallahi saurayin nan da yake bani saqo lokaci lokaci nake kawo miki wanda kikace bakisan waye ba kema shi na gani a tsaye a qofar gida,kince duk randa ya sake zuwa na tsaidamiki shi shi yasa nake sauri na gaya miki kar yana bada saqon ya tafi"
"Miqo min mayafina....duk abinda ya baka kada ka amsa kace masa lallai lallai ya shigo inason ganinsa"
"To" sulaiman ya fada yana bata mayafin sannan ya sake fitowa da hanzari.

A nutse yake nufo motar anwar,wanda shima ganinsa yasanshi sauke glass dinsa har sanda sulaiman din ya qaraso bakin window bakinsa a washe,anwar ya miqa masa hannu kaman yadda suka saba,yana Murmushi sulaiman ya miqa masa hannu sukayi musabaha,yana bala'in son musabaha da anwar din,koba komai zai gogi qamshinsa dake burgeshi yaji laushin fata sannan kuma hannunsa ya shaqi sanyin acn dake cikin motar kamar yadda sulaiman din ke cewa
"Kwana biyu yallabai?" Sulaiman ya fada yana sosa kai,murmushi anwar din yayi sannan yace
"Ko zaka yimin iso gurin mutanen gidan?"
"Me zai hana?,dama daadan nason ganinka,ta roqeni ma kan don girman Allah yaudai ka shigo taga me mata aiken nan" murmushi ya kuma saki yana cire belt din jikinsa sannan ya maida glass din motar sama ya bude murfin ya fito,sai daya rufe motar sosai sannan sulaiman yayi gaba anwar din na biye dashi a baya.

A bakin qofar gidan anwar ya coge yana duban soron gidan yana tuna wani abu daya taba faruwa a wajen shekaru shida baya,a shekarun baya da suka wuce idan aka ce masa zai sake taka soron saiya qaryata,amma dattako mutunci da qaunar da dattijuwar ta nuna masa a baya ya dawo dashi yaci gaba da nuna mata nashi karamcin,sulaiman ya dubeshi
"Ka shigo mana,bismillah" kai ya kada
"Shiga tukunna ka gaya mata zan shigo" anwar din ya masa kwarjini da yawa don haka ya kasa musa masa,ya saka kai zuwa cikin gidan karo na biyu.

"Tace ayi maka iso" sulaiman din ya fada yana duban anwar,a nutse ya sanya qafafunsa soron yaci gaba da takawa bisa jagorancin sulaiman.

Qarqashin bishiyar dake gefe daya na tsakar gidan tabarma ke shimfide,nan sulaiman ya nuna ma anwar,ya sabule saucikin dake qafarsa ya ajesu sannan ya isa saman tabarmar ya zauna,dai dai lokacin da daada ke fitowa daga rumfarta hannunta dauke da kwanon sha wanda ke cike da ruwan randarta mai sanyi,idanunta akan anwar din harta qaraso,duk da ganinta dashi sau biyu ne tak a rayuwa,a lokacin da yafi haka qarancin shekaru da rashin cikar xati da kamala.
Chapter 38 · 0% Book details