← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 73

Sashe 13

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anwar ya samu ya kammala karatunsa cikin wahala da dagiya da kuma taimakom anty husaina wadda ta sadaukar da dukkan wani abu nata don ci gabanshi,yayin da shahida ta zamo mutum na biyu data sadaukar da dukkan wani abu da take ganin ta mallaka saboda anwar din.

Bayan fitowar sakamakonsa wani yayan abokinsa ya kirasu yayi musu tallar aikin d'an sanda da za'a soma dauka,rimi rimi sukayi komai da karime karime da qarfafawar gwiwar shahida data dage kan sai yaje,sai kuma batun tafiya training ya taso,a nan ne ya sare saboda lissafen lissafen abubuwan da za'a buqata daga garesu,wanda kusan duka harka ce ta kudi,koda wasa bazai doshi anty husaina da wannan batun ba saboda yasan cewa wahala ce da nauyi kawai zai dora mata,saiya shiga neman kudi babu ji babu gani,sai lokacin da tafiyar ta matso sannan ya shaidawa anty usaina,ta masa addu'a sosai,ranar da zaiyi sallama da shahida ta dauko baqar ledar viva ta dire masa.

Sai daya gama kalla sannan ya dago yana dubanta,baisan ma da wanne baki zai mata magana ba,da wanne harshe zai gaya mata yadda take a wajensa?,kaya ne da tasan cewa zai iya buqata a ciki,wanda ko bata fada ba yasan a qalla zata kashe dubu biyar,Da hannu ta masa nuni dole yayi shuru,tamkar ba zasu rabu ba ranar,ji yake kaman idan yaje zaiyi shekara ne bai dawo ba.

Kwanansa uku acan shida wasu mutum biyar suna cin wuya saboda ance sam babu sunansu cikin list din,bawai kuma babu dinba,yanayin qasarmu ne kawai,an suba wadanda sukafi kowa rashin galihu an cire sunayensu daga list din an maida gurbinsu dana wasu,hakanan suka tattara suka dawo gida.

Randa shahida ta ganshi ya dawo ba qaramin jin takaici tayi ba,har kuka ta kusa yi,shi ya dinga lallabata yana bata haquri
"Duk randa Allah ya horemin abu na farko da zan fara ginawa shahida shine makaranta,zanyi irin makarantar da yaran masu kudi suke zuwa,irin makarantar da suke karatuna zuba yaran masu qaramin qarfi,su samu irin ilimin da yaran masu hannu da shuni suke samu,su samu gata da kulawa irin na yaran masu dashi"shuru shahida tayi tana karantarsa,har cikin zuciyarsa maganar take fitowa saboda yadda hakan ya bayyana saman fuskarsa
"Yaran marasa shi suna shan wahala,suna shan wahala matuqa wajen neman ilimi,bayan sun samu karatun da qyar ya zamana karatun ya kusa zama na banza,sakamakon yadda aiki ke musu wahala,wanda wasunsu daga qarshe sakamakon karatun nasu kusan dai dai yake da takardar tsire" nan ma dan shuru yayi yana hadiyar yawu,sosai lamarin ke sukar zuciyarshi,sun jima suna tattaunawa game da halin rayuwa sannan daga bisani sukayi sallama.

Anwar bai gajiya ba bai kuma sare ba yaci gaba da neman aiki baji ba gani,burikansa din nan guda biyu su yake fafutukar ganin ya cimmawa,yana tsoron shahida ta kammala secondry ba tare daya samu aiki ba,babban burinsa a duniya suyi aure sanda zata kammala makaranta,ya kuma tsaya mata tayi karatu kaman yadda takeso harsai tace ya isheta,yana da burin yi mata halacci kwatankwaci koma fiye da yadda tayi masa.

*BAYAN WATA HUDU*

Kallonshi take tamkar ta zabga masa mari haka takeji,saidai hakan ba maiyuwuwa bane tunda ba tarbiyyarta bace,dawowarta kenan daga gidan anty amina ya tsaidata,sam batasan yana biye da ita tun daga qofar gidan anty amina ba cikin motarsa saida ta iso layin nasu,ta shiga gida da niyyar ba zata saurareshi ba yadda yaketa zabga aike yasa umma tace ta fita ta saurareshi.

Hakanan cikin jikinta takeji kamar akwai wanda yake kallonta,kamar anwar na wajen tare dasu,a hankali ta kalli damanta,shine kuwa sanye cikin jibgegiyar rigar sanyi da wandon jeans,kasancewar ana cikin yanayin sanyi,yayi kyau matuqa,kai kace wani ne ko dan gidan wani,kyansa ya sake fitowa,fitilun motar daya bari a kunne sun haskeshi sosai kaman yadda suka haskesu,idanunta cikin nashi saiya ja da baya ya juya ya soma barin wajen.

Wani tashin hankali ya ziyarceta,da wanne baki zata yi masa bayani?,ganin yadda hankalinta ya wajen ya sanya saurayin shima juyawa yana kallon wajen saidai baiga komai ba,bata sake bi ta kanshi ba ta shige gida da hanzari,wayarta ta laluba ta soma kiran layin anwar din,saidai harta qaraci ringing dinta ta gama bai daga ba,hakan ba qaramin daga mata hankali yayi ba,ba zata manta ba shekaran jiya suna hira yake ce mata
"Shahida tsoro nakeji,gani nake kaman zan rasaki,kaman kinfi qarfina" cikin mamaki tace
"Me kake fada anwar?" Murmushi yayi saidai ya taba har zuciyarsa
"Shahida...kina kallon kanki a mudubi kuwa?,irinki ba qananun mutane ke aurenki ba....ina tsoron kada wani mai motar yasha gaba na" sosai taji haushi harma ta shige gida ta barshi ko sallama basuyi ba,da qyar yasha kanta ya waya,to jiya bai samu zuwa ba kasancewar ya samu dan wani aiki yana kulawa wani da provision dinsa cikin anguwarsu,ladan da yake bashi ba wani mai yawa bane kasancewar kanti ba wani girma gareshi ba,amma ya karba yana yi saboda ba mutum ne shi mai raina sana'a ba komai qanqantarta.

Kusan ranar kwana tayi tana kiran layin nashi amma ko sau daya bai daga ba,daga nashi bangaren hankalinsa a tashe yake,hakanan zuciyarsa ke wani irin tafasa,kishi ne ki cinsa sosai,fargaba ta lullubeshi,fargabar kada ace zancansa ne zai tabbata zai rasa shahidansa,duk sanda ta kirashin bai daga ba sai yaji wani qunci na sake ziyartar zuciyarsa,bai iya daurewa yana jin kiranta na shigowa amma ya kasa dagawa,daga bisani tilas ya kashe wayar duka yana fatar ta haqura tayi bacci.

Kwana biyu ba anwar din ba dalilinsa,hakan ya daga hankalinta don har wajen kai sadaka bata ganinsa,da yammacin kwana na ukun bayan ta dawo daga kai abinci wanda yanzu ajewa kawai take wajen baba ado dake wajen ya raba a aiko da botikin don fir anwar yace ta daina kaiwa,shiryawa tayi ta tadda ummanta zaune tana jan carbi bayan ta idar sallar la'asar
"Umma....zanje gidan anty amina"kai ta daga ta dubeta sannan ta shafa addu'arta
"gidan amina kuma?,makarantar fa?"kanta tadan sunkuyar tana wasa da farcenta
"hadda ake karba,kuma ni na bada tawa tun jiya" dan jim tayi sannan tace
"Shikenan,ki gaisheta....yauwa....kice mata yaushe za'a fitar da ankon umaiman,ki gaya mata lokaci yana qurewa fa"
"Tohm umma....saina dawo"
"Zan rakaki yayaa" cewar mubina wada ke shirin islamiyya ta fada bayan ta watsar da hijabinta wajen
"Babu inda zaki,makaranta zakije" cewar ummanta,tana jiyo ihunta ta saka kai zata fice tana dariyar rikici irin na mubinan,dai dai lokacin abbanta ya shigo,saita koma da baya tana masa sannu da zuwa yayin da yake tambayar abinda aka yiwa mubinan
"Wai gidan anty amina tace zata bini,kuma islamiyya zata"
"Ke ina taki islamiyyar?"
"Hadda ake amsa abba kuma na bada tawa tuni..."
"To ma sha Allahu,dama inason ganinki"
"To abba gani" ta dawo tana dawowa saman kujera 'yar tsuguno ta zauna,
"Shahida....ina fatan ba wani abune ya shiga tsakaninki da yaron nan ba anwar?"
"Abba meka gani?" Ta tambaya a sanyaye
"Kwana biyu bana ganinsa yana zuwa" shuru tayi tana tunanin amsar da zata bashi,dukkaninsu ummanta da abbanta wani irinso sukewa anwar din,halayen anwar abun sone,nagarta gareshi wadda ta zama tilas ko waye kai ya burgeka
"Uhmmm...bakice komai ba"
"Abba in gaya maka?" Mubina dake goge hawayenta ta fada,harararta shahida tayi amma hakan baisa ta fasa magana ba
"Wanine mai mota yazo...umma tace taje ta sallameshi,shine yaya anwar ya ganshi ya tafi"
"Ubanki mai shegiyar magana" umman ta fada tana kai mata duka
"A'ah hadiza barta ta fada....kice kawai kin soma shanshano wani ne....ke shahida tashi ki tafi,kema zamu gamu dake"
"Duk abinda kaga dama ka fada,tunda dai ba zuciyata ka shiga ka hangi haka ba shikenan na gode Allah" tun kan ta fice daga soron nasu ranta ya soma baci,saboda taji suna gab da kaurewa da halayyar tasu da suka saba,saitayi maza maza ta ficema don kada ta jiyo abinda wunin yau zai sa ta kasa walwala,sam bata iya daurewa duk sanda wani sabani ya hasu tafi kowa jin zafin abun,tqfi kowa shiga qunci,ta rasa me yasa dukkansu basu haquri da juna,kowa kaman jiran kowa yake,kamar wadanda aka sakawa hannu cikin mu'amalarsu.

Ba dadewa ta isa gidan anty amina,ta taddata tana wanki ta saka mata hannu suka gama tare,tanata tambayarta anwar kwana biyu bai leqo ba batace komai ba,har sai da suka gama suka zauna dakinta suna ninke wasu kayan da suka soma bushewa
"Anty....nifa zuwa nayi ki mana sasanci da anwar"
"Sasanci kuma,me ya hadaku kenan?,yau kwana uku kuwa da zuwanshi ya gaidani"ana ya gobe abun zai faru kenan?,shahida ta raya a ranta,batasan ma yazo din ba,jininsu ya hadu da anty amina,gashi kuma ba wani nisa sosai tsakanin gidanta dana anty usaina,don har zumunci ma suke yanzu ta sanadinsu,tsaf ta kwashe komai ta gayawa anty aminan,a take tasa shahidan ta kirashi,saidai harta gama ringing bai daga ba
"kin gani ko anty?"shahidan ta fada idanunta na cikowa da qwalla
"Bari na kirashi da wayata" anty amina ta fada tana daukan wayarta,ringin biyu ya daga cikin girmamawa
"Anty amina...da kanki?" Ya fara fada cikin girmamawa
"To ya zanyi?,diyata ta dagamin hankali?"dariya ya danyi
"Shahida ko?"
"Ita mana"
"Karki qona katinki anty bari nazo"
"Da kuwa ka taimakeni karta fashemin gata nan ta cika fam" da haka sukayi sallama tana duban shahidan
"Shima a muryarshi kadai ya isa kasan cewa yana cikin damuwa da kewarki,wanne irin so kukewa juna shahida?" Kunyace ta kamata saita soma sinne kai.

Ba'ayi minti talatin ba cikakke d'aya daga cikin yaran anty amina suka shigo suna cewa ga uncle da yake haka suke kiranshi,anty amina ta saka hijabinta tace suce mishi ya shigo.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*Alqawarin Allah*
1️⃣0️⃣
Chapter 13 · 0% Book details