← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 73

Sashe 19

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda suka shiga wajen gabanta ke faduwa,gaba daya jinta take a tsarge,har qasan zuciyarta takejin kaman tana aikata wani abu daba dai dai ba,wajene da yake kama da gida daki daki,kaman gidan masu zaman kansu,daya daga cikin dakunan suka nufa ba tare da sun kula kowa ba,saida fiddausi ta tura qofan suka shiga taga ashe falone babba,akwai maza wajen biyar ciki,ga kayan da sukazo nema zube a gabansu da alama ciniki ake,guri daya shahida ta samu ta zauna duk ta takura,sai taga fiddausin ma ta samu waje ta zauna bayan sun gama gaisawa da mutanen cikin sanayyar juna.

Ganin lokaci nata ja fiddausin bata sake cewa komai ba hakanan basuyi abinda ke gabansu ba ya sanya shahidan tabo fiddausin ta mata magana
"Sorry....sallamemu uban gayya...qawata na sauri zata koma gida ne"
"Kuxo ku xaba mana" ya fada ba tare daya dubesu ba yana ci gaba da lissafin uban kudin dake gabanshi,fiddausi ce ta soma zuwa wajen kayan dake tsakiyar mazan ta zazzaba kaloli daban daban sannan tacewa shahida taje ta zaba itama,a darare ta tashi ta nufin wajen,tana zuwa tsakiyarsu dab da zata isa wajen kayan wani santsi da batasan na meye ba ya kwasheta ta tafi zata fadi,daya daga cikin mazan wanda tunda sukazo yake tsaye a wajen yayi caraf da ita ta fada jikinsa.

Cikin wani irin hanzari da tashin hankali tayi yunqurin miqewa daga jikinsa saidai ya riqeta gam,ta tattara dukkan qarfinta ta hankadeshi ta miqe,harara ta dalla masa kana taja tsaki cikin bacin rai da dana sanin zuwanta wajen,ko fiddausi bata kalla ba ta fice a wajen,kanta take baiwa laifi tare da jin haushin kanta da kanta,me ya kaita zuwa iri wadan nan wuraren?,sam wannan ba tarbiyyarta bace.

Har taci rabin tafiya don bata tsaya taren abun hawa ba sannan ta biyota,gabanta tasha
"Matsamin na wuce,dama wajen wadan can watsattsun zaki kaini?" Kan fiddausin ta langabe tana share qwalla
"Wallahi na fiki baqincikin abinda yayi miki shahida,abinda ya tsaidani kenan ma yace na baki haquri shiba don wani abu yayi ba ganin zaki fadine" ta iya dadin baki da tsara kalamai,haka ta dinga baiwa shahida baki harta sauko
"Kin fasa daukan abun ne?,kinga ni gobe zanyi tafiya kuma zan dan kwana biyu ban dawo ba,shi yasa nace kizo ki dauki wanda zaki amfani dashi kafin na dawo"
"Inaso,amma bazan sake komawa gidan wadan can 'yan iskan ba" da haka tasha kan shahida tace gidan wata qawarta zasuje.

Gidan qawartata ne,wanda itama ta fito musu da kayan,fiddausi tace bari tayi testing,bayan tasha ta dubi shahida
"Kai wannan sunyi,kinji taste dinma daban da irin namu,don Allah sha kiji shahida" kai ta girgixa
"Ni bani da qarfin jini irin naku,bacci yake sakani sosai,kuma yau banason inyi baccin nan da wuri,saboda anwar zaizo" juna suka kalla suka tabe baki ba tare da shahidan ta kula ba sannan qawar fiddausin tace
"Lahhh,wannan na musamman ne baya saka komai,mai kyan ne,banda ma fiddausin da babu wadda zan bawa shi" qawar ita ta hada mata ta miqa mata kwalbar,ta karba ta dan sha,sai taji yayi dadin fiye da wanda suka saba sha kamar yadda fiddausin tace,saboda haka ta shanye duka.

Tun tana jin hirarsu sama sama har sai data fara ganinsu bibbiyu ta kuma kasa gane me suke fada,abu daya zata iya tunawa,sun dagata sun cire pant da pad din jikinta,taga jini na sake fitowa sosai daga jikinta,wanda batasan cewa cikin syrup din suka saka mata qwayar da zata sake sakata yin bleeding sosai ba.

Tsahon wasu awanni wanda batasan awa nawa bane jikinta yayi danshin jini sosai,tanason tashi ta gyara kanta ta maida pant dinta ta kasa,sai malelekuwa take a tsakar dakin qawar,saita tashi saita koma yaraf,da qyar ta iya hada kalmar fiddausi ta kaita gida
"Yanzu kuwa" ta fada.

Tasan sanda ta kamata suka sata a motar wani saurayi gaban motarshi wanda ba zata iya tantace waye ba,suka rufe yaja motar.

Tun daga nesa ta hangi kaman anwar zaune saman dakalin da lokaci zuwa lokaci suke zama,kanshi a duqe wayarshi na hannunsa yana dannawa da alamu ita yaketa qoqarin kira,hankalinsa na a tashe saboda ya iske gida suna bulayin nemanta ne su dinma.

,tanaso tacewa drivern ya sauketa amma ta kasa bude bakinta bare ta furta komai,tana son ta yunqura ta sauka amma ta kasa,tanaji tana gani ya isa dab da anwar din,yayi parking din motar,ya fito daga mazauninsa ya bude mata qofa sannan ya kamata ya fito da ita yana cewa
"Saida nace miki kisha kadan kisha kadan amma da yake shegen hadamar tsiya ne dake,abu ya riga yabi jini saida kikayi tatul" lafazin daya sanya anwar dagowa daga danna wayarsa da yakeyi kenan,don tunda motar ta tsaya hankalinsa bai wajen saida yaji maganar dake fitowa daga bakinsa,yayi kuwa mummunan gani,yayi tozali da abu na farko daya ji kaman zuciyarsa zata tarwatse,shahida ce,shahida ce wani riqe da ita tana tangadi,wanda kana mata kallon farko kasan cewa cikin maye take,idanunta na cikin na anwar din,tana son qwace kanta,tana son yi masa magana,tanason qaryata abinda saurayin ke fada akanta,tanason tabbatar masa da meye ainihin abinda yake gani amma idan ta bude bakin shirme ne yake fita wanda shi kansa shirmen can qasan maqoshinta sautin ke fita,sakinta yayi daura da anwar wanda banda Allah yasa tayi hanzarin dafe bango zubewa zatayi a wajen,ya koma cikin motar ya riqo pant dinta da jakarta ya dawo inda take yana cewa
"Saiki kula wajen shiga gida,ga jini nan duk ya bataki,gaba kya sake bari ciki yayi qwari a jikinki kafin a cireshi" ya qarasa maganar yana sakin kayan hannunsa,jakar ta fadi dama zip din a zuge yake,take tarkacen ciki suka fado dai dai qafafun anwar,kwalaben syrup dinta ne da tarkacen qwayoyin da ba shansu ma take ba,bata taba kwatanta sha bama.

Anwar dake zaune daskare a wajen yaji kaman an jona mishi shociking,baisan ya akayi ba baisan kuma yaushe ya miqe ya kaiwa matashin kyakkyawan naushi a fuska ba,wanda karon farko yayi nasarar fasa masa baki da fitar haqorin bakinsa guda daya,sosai ya tsorata ya kuma razana da yadda yaga yanayin anwar ya juye ya zama,cikin hanzari ya juya don tseratar da kanshi,saida tuni anwar ya damqo kafadarsa ya juyo dashi ya watsa masa wani kyakkyawan mari,bai jira ya gama wartsakewa ba ya kwasa da gudu ya nufi motarsa,anwar ya rufa masa baya,kafin yakai wajen har ya shige motar ya kulle qofar,iya qarfinsa anwar ya saka ya dinga dukan glass din window din motar,wanda kafin yakai ga tasar motar anwar yayi nasarar fasa glass din motar dai dai da sanda matashin ya figi motarsa yabar layin a guje.

Hannunsa na digar jini ya dawo inda shahida ke zube,duk da bata cikin cikakken hayyacinta amma tasan cewa babban tashin hankali ne ya sameta,dubanta yayi sosai wani abu mai tauri ya tsaye masa a wuya,ji yake kaman ya farka maqogaronsa zuwa qirjinsa ya cillar ya huta,yau shahidansa ce yashe a qofar gida?,ba hijabi ba dankwali?,cikin maye?,cikin jinin da aka kira da jinin cire ciki ne?.

Wasu mutum uku da sukazo wucewa ne suka dawo da baya don ganin me yake faruwa?,yaga sadda suka dawo din hakan ya sanyashi cikin hanzari ya damqi kafadar shahidan da kayanta ya turata soron gidansu sannan ya jawo qofar soron.

Koda suka dawo din suna tambayar ba'asi banza yayi dasu har suka qaraci tambayarsa sukaji haushi sukayi gaba.

Tamkar shima d'an mayen haka ya dinga takawa yana hada hanya,tun daga gidansu shahidan har zuwa nashi gidan,yana shiga ya danna sakata,bai ma tuna da abokansa da zasu zo kallon ball yau a sabuwar qaramar plasmar daya sakawa falonsa ba cikin salary dinsa.

Kan carfet din dake malale a falon ya zube,bai damu da ciwon hannunsa dake zubda jini ba,ciwon da yakeji cikin zuciyarsa ya ninka ciwon da yake hannunsa ninkin baninkin,wani irin suya qirjinsa da zuciyarsa suke masa,baisan me zai tuna ba,bansan me zaiyi tunani akai ba,baya gane komai,shahida kawai yake hangowa a yanayin daya ganta a gabanshi,sai kawai ya zame ya kwanta a wajen.

Ranar haka ya kwana nan wajen,kafin gari ya waye ya zubda jini mai yawa,takwas na safe abokinsa kuma babban amininsa yazo ya dinga bugun gidan bai tashi ya bude ba,yana da tabbacin yana ciki tunda gashi ba kwado a qofar gidan,daga qarshe dai da hankalinsa ya kasa kwanciya saiya haura gidan kawai.

A lokacin ya samu a daddafe yayi sallah yana zaune wajen xazzabi nason rufeshi
"Wannan wanne irin abune haka anwar?,ya zaka kulle kanka cikin gida ayita nemanka?" Ya fada yana son karantar yanayin da anwar din ke ciki,baikai ga bashi amsa ba sukaji ana buga gidan,miqewa muhsin yayi don ya duba mai bugun gidan.

Minti daya sai gashi ya shigo riqe da envalope ya ajiye gaban anwar yana cewa
"Hala ma dai baka da lafiya ko?"muhsin yayi tambayar yana qare masa kallo
"bani da lafiya muhsin"
"Subhanallahi,kasha magani?" Kai kawai ya iya kad'a masa
"Ya zaka zauna haka?,bari naje wajen sule mai shayi na samo maka ruwan zafi kasha sai ka samu magani kasha,ko na rakaka asibiti a dubaka" bazai iya magana ba saboda shi kadai yasan me yakeji,yana kallon muhsin har ya fice daga gidan.

Sai a sannan idanunsa suka sauka kan envalope din dake gabanshi *SAQON GAGGAWA MAI MATUQAR AMFANI GA WANDA SAQON YA SHAFA* ya gani rubuce baro baro a bayan envalope din bayan ya juyata,hakanan yaji hankalinsa ya karkata gason sanin meye a cikin envalope din.

Ta sama ya farketa saboda yadda ta mannu,ya zazzage duk abinda ke ciki,hotom farko ya kusa tafiya da numfashinsa,shahida ce rungume jikin wani qato,wanda hoton an daukeshi ne jiya da sukaje siyan syrup sanda ta kusa faduwa ya tareta,hoto na biyu sanda sukaje gidan qawar fiddausi ta daga syrup tana sha,sauran duka hotuna ne na tsiraici tare da wani saurayi haihuwar mahaifiyarsu,kaf numfashinsa ya dauke saboda wani abu daya tokare kafar numfashinsa,ya tafi daga zaune zai kifa luuu,abu na qarshe daya ji kiran sunanshi da muhsin yayi cikin qaraji da razana,daga haka komai ya tsaya mishi cak.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/video

*Alqawarin Allah*
1️⃣4️⃣
Chapter 19 · 0% Book details