← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 73

Sashe 18

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin mintina qalilan bacci ya soma zuwa mata,kafin kace ta sheme a wajen,ba ita ta farka ba sao washegari da safe bayan gari yayi tarwai rana ta take,da hanzari ta miqe tana tariyo abinda ya farun,sosai taji dadi har ranta da Allah baisa taji qarshen masifar ba,don haka batasan ya aka qarke ba,ta bude sakatar dakinta ta fita tsakar gidan nasu,a share yaje fes saidai gidan nasu yayi tsit alamun ba kowa ko duka yaran basa nan,tasan da hakan don lokacin tafiya makaranta yayi,saita tari ruwa ta shiga bandaki,wanka tayi don tafijin qwarin jikinta sannan ta hado da alwala ta fito ta shiga dakinta ta sauya kaya ta tada sallar asuba da bata samu tayi ba,bayan ta kammala ta wuce dakin ummanta,ta sameta a zaune a falonta tana tsintar shinkafa,ta dago suka hafa idanu,kallo daya zaka mata kasan ranta a masifar bace yake,wanda tasan hakan bai rasa nasaba da kace nacen da sukayi jiya da babanta,gaidata tayi ta amsa sama sama
"Wato don wulaqanci da iskanci da asuba kina ji ana bugun qofarki ki tashi kiyi sallar asuba kikaqi ko?" Ita sam batasan anyi hakan ba,batasanma yaushe aka buga qofar tata ba,amma kawai sai tace
"Kiyi haquri umma,bacci ne yaci qarfina"
"Oho ke kika sani,naga alama kin fara goyawa mahaifinki baya,to wallahi kikace haka zakiyi wahala zakisha" ko kadan ranta bai baci ba sai tace
"Kiyi haquri" banza tayi da ita,sai bayan mintina wajen goma sha biyar sannan tace da ita
"Saikije ki dauki abun karyawarki a kitcheni,idan kin gama ki kunnan wuta na dora shinkafar nan"
"Toh" ta fada tana miqewa zuwa madafa.

Tana cin abincin tana tunanin abinda ya farun jiya,gaskiya baqaramin rage mata radadi maganin yayi ba,ko banza batasan qarshen abun ba,hakanan bata ji wani bacin rai ba,saita yanke kawai yau ta sake zuwa gidansu fiddausi ta gaya mata inda ake saida abun ta siya,duk sanda suka soma balahirarsu tasha ta samu bacci ta qyalesu.

To tun daga lokacin shahida ta shiga ruwa tsundum,batasan illa da giraman abinda takeyi ba,batasan yadda take rushe rayuwarta ba,kawai ita ta bada amanna ne tana shan maganin matsalarta,batasan tana sake qarawa rayuwarta matsala bane,tana tunanin maganin bacci kawai takesha,batasan ta fada shaye shaye bane tsundum,wanda ba wanda ya kula da sauyawarta banda anwar,lokaci zuwa lokaci idan yazo fira wajenta da zarar sun fara zata soma gyangyadi,haka zai mata sallama ya tafi,ya nazarceta sosai baiga wani abu daya sauya dangane da ita dinba bayaga yawan jin baccin,hakan ya sanya yayi tunanin ko shawara ce da ita?,baiyi qasa a gwiwa ba ya amso mata magungunan gargajiya harda na sanyi,ta amsa dai kawai ta jibge taci gaba da sha'aninta.

Zuwa sannan sam abinda ke faruwa tsakanin mamanta da bbanta ya daina damunta,wani lokaci takan iya shigowa gidan ma ta taddasu sunayi tayi wucewarta daki ta kwanta abinta tahau baccinta,dukkan wadan nan sauye sauyen basu ganshi ba,ga ummanta kawai tayi mata shaidar ta koyi nunqufurci tana goyon bayan babanta,yayin da abban nata yake ganin hankali tayi ta daina damuwa da al'amarin dake faruwa.

Ta bangaren fiddausi kuwa da akayi amfani da ita don cusa shahida cikin wannan harkar nasara ce a wajenta,don duk yadda aka tsara abun ya tafi dai dai,hakan yayi sanadiyyar samun kudade mai yawa daga wajen nafisa,plan dinsu na gaba shine cusa samari masu kudi 'yan duniya rayuwar shahidan,saidai duk yadda sukaso ga ganin hakan ya yiwu abun bai kasance ba,saboda sam shahidan tun asali a jininta yake,bata da kule kule,haka suka qaraci shirya plan din nasu suka gaji,hakan ya sanya suka sauya dabara,suka sake sabon shiri sabon taku da sabon tsari,wanda suke fatan shine mataki na qarshe da zai tarwatsa mu'amalar dake tsakanin anwar da shahida komai qarfinta.

*_SHARRI KAYAN KWALBA_*

Kusan a yanzu babu wata qawa kuma aminiya da shahida ke da ita data wuce fiddausi,kusan koda wanne lokaci suna tare,hudubar farko data soma yiwa shahida shine anwar ba son shahidan yake ba,yasha fada cewa mai zaiyi da yarinyar da iyayenta suka kasance tamkar karnuka saboda fada,sosai xancan ya daki shahida,saidai iya saninta anwar baisan badaqalar dake faruwa a gidansu ba,don tuni ta yanke yin zance dashi a gidansu bama gidansu kawai ba unguwar baki d'aya,yanzu kacokam gidan anty amina take tafiya su hadu a can,saidai kuma akace yau da gobe tafi qarfin wasa,sai maganar ta dinga tsayewa shahidan aranta,duk da cewa ko daya bata yarda ba bata gasgata ba,hakanan ba abinda ya ragu game da son anwar daga zuciyarta,duk sanda taso yin wani dogon nazari kan maganar fiddausi na kadar da hankalinta ta bata wani abun mayen sai zancan yasha ruwa.

Ta gefan anwar gaba daya hankalinsa ya ta'allaqa ne kan nemawa shahida gurbin karatu cikin daya daga cikin makarantun gaba da secondry dake jahar kano tunda aka yi musu qarin albashi,bai gaya mata ba saboda yana sonne yayi mata ba zata,yaci wahala ya kashe kudi kafin komai ya kammala.

Ana ya gobe zai shaida mata yana gurinta,ranar sun jima tare suna hira,sunyi hirar da suka jima basuyi irinta ba,kowanne yan jaddadawa d'an uwanshi yadda yake jinsa cikin jikinsa da zuciyarsa,sun tsokani juna sunyi raha wasa da dariya sosai,har anwar ta saka ranakun cikin daya daga cikin kundin ranakun farincikinsa da bazai taba mantawa dasu ba,ta bashi hotunan data dauka musamman sabodashi wanda ba qaramin kyau tayi cikin hotunan ba,kyanta ya fita muraran,ya qurawa hotunan idanu yaga kada kai
"Wannan hotunan bazan iya maidasu enlargment ba" dubansa tayi tana narke ido tana dubanshi
"Saboda banyi kyau ba ko?" Dariya ya saki yana cewa
"Dama akwai wani lokaci da zaki qiyin kyau a idanuna koda wankan kashi kikayi?" Dariya sosai ya bata har shima ya tayata darawa
"Dama ana wankan kashi ya anwar?" Girarsa ya dage
"Eh waikoda ace anayi din...kyan da kikayi ne shahida yayi yawa,ina kishin mai aikin budawarma ya ganki" baki ta bude tana dubanshi
"Ya anwar"
"Shahida....kaman har yau kina kokwanton yadda nake sonki da kishinki ko?" Kai ta girgiza tana dariya
"Xaki fahimta,sai ranar da aka kawoki dakina a matsayin matata" kunya ta sata sadda kai tana qiyasta ranar a ranta,gata ita dashi a matsayin miji da mata.

Daya tashi tafiya saita miqo masa dari biyar bayan wata baqar leda,wadda daya bude links ne da agogo guda biyu masu matuqar kyau irin wanda tasan yana masifar so,kallonta yayi itama shi take kallo
"Kada kacemin komai,na fuskanci yau miskini kake baka dako sisi(ta furta cikin sigar zolaya)"murmushi ya saki,gaskiya ta fada,don duka albashinsa ma na wajen wata uku ya qare ne wajen sama mata admission,dan abinda yaje riqewa bamai yawa bane,kudi ya dinga badawa don ta samu gurbin karatun,don yasan cikar burinta kenan shida ita,hakan bai dameshi ba ko kadan,yana jin zaiwa shahidan fiye da hakanma indai ita dince
" har saika fada?"ta katse masa tunaninsa
"Ina iya karantar zuciyarka ba tare daka furta abinda ke cikinta ba" ta fada cikin sanyi da taushi,sun riga da sun zama daya,sai ya saka hannu ya amsa yana murmushi
"Na gode matata" kalmar data yi mata dadi sosai,cikin farinciki walwala da qaunar juna suka rabu,yana tafe yana tariyar dukka kalamanta,saiyakejin kyautar data masa tayau din daban take,hakan ya sanya ya kasa fasa kudin ya hau mota,ya taka har zuwa gida da qafa yana juya ledar data bashi gift din a ciki,gift din data bashine da sunan tayashi murnar xagayowar ranar haihuwarsa,wanda sam shi ya mance ma da yaune ranar haihuwarsa.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Qarfe biyar na yammaci da 'yan mintuna ta sauke wayar daga kunneta tana sakin ajiyar zuciya,itakam har cikin zuciyarta sam batajin zuwa ko ina,haka kawai taji batason fita.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/video

*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata saiya tuntubi wadan nan lambobin*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*Alqawarin Allah*
1️⃣3️⃣

Fiddausi ce ta kirata tanason ta rakata wajen da take siyo musu kayan zaqi kamar yadda ta sawa syrup din da take baiwa shahidan suna,duk sanda shahidan ta buqata tana amsa ne kawai daga wajen fiddausin,wanda nafisa ce ta baiwa mima kudin da za'a siya a jibgewa shahidan,ita kuma mima ta baiwa fiddausi kudin ta saya ta aje din take bata,don ita bata harkar shaye shaye,barta da biye biyenta kawai,shahidan taso ta tirje don yau din anwar ya gaya mata zaizo akwai wata muhimmiyar magana da zasuyi,amma sai fiddausin taji haushi ta katse wayar sanda tace ba zata samu zuwa ba,ita dinma a karan kanta sai taga bai kamata taqi rakata ba,tunda abun nan tare suke amfana dashi,bugu da qari duk sanda takeso kyauta take bata shi ba tare dako sisinta ba.

Tilas ta shiga bandaki ta sake gyara jikinta kasancewar tana al'ada ne,kuma idan tanayi din tana bleeding ba laifi,hakan ya sanya duk sanda zata fita take saka always biyu ko kuma pant biyu,yau always din tata ta qare saura daya saboda haka ta saka pant biyu duk da tana tunanin Allah yasa ya riqeta.

Tsaf ta shirya ta shuga wajen umma
"Umma....zan raka fiddausi gaisuwa,baban wata 'yar ajinsu ya rasu"
"Ina ita fiddausin?"
"Ta gidansu zan biya ai umma yafi kan hanya"
"Saikun dawo" ta fada tana miqa mata dari biyu kudin mota,ta amsa ta miqe ta fice daga gidan.

A qofar gida suka hadu da fiddausi
"Amma karmu jima don Allah fiddausi saboda anwar kar yazo bai sameni ba,kinsan baison yawan fita" baki ta tabe cikin ranta tace
"Yau za'ayi mai gaba daya ma ai" amma a fili sai tace
"Sannu matar kulle,yaushe aka daura auren naku ban sani ba?" Harararta shahida tayi
"Kinga banason wulaqanci,kome zakiyi ki tsaya iyani,koda ba'a daura aurenmu ba ya isane dani"
"Allah ya baki haquri...shi yasa har na kira daddy A yazo ya kaimu saboda mufi sauri sai kuma nace ya barshi,don nasan halinki yanzu zakice ba zaki shiga motarsa ba" dan hade rai shahida tayi
"Kinfi kowa sani ai,nifa banason kina hada alaqarmu data wadan nan tarkacen samarin naki,tunda dai mu ba 'yan bariki bane"
"Iyee,wato samarina ne ma tarkacen,ba komai zan rama"
"Saidai ki rame" da haka suka qarasa wajen.
Chapter 18 · 0% Book details