Sashe 53
Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba daya ta susuce cikin kwanakin ta fita hayyacinta,idan ka ganta saika dauka ba ita bace ba,gashi daga mummy har abban nata ba wanda ya sake bi ta kanta koya tanka mata dangane da hukuncin data yanke na ba zata auri anwar ba bare ta fadi abunda yake ranta ko zataji dadi,kullum kwanan duniya kamar ibada kuwa saita kira number mima sau babu adadi amma tana a kashe amsar kenan kullu yaumin,ko fita yanzu ba kasafai take ba,kishin anwar da sauran kwanakin daya rage ya zama mallakin shahida su take lissafi,sanda taga kwanakin na qaratowa kuma bata da madafa ko makoma saita soma dana sani da nadama tana tuhumar kanta anya kuwa batayi kuskure ba?,anya bata aikata ba dai dai ba?,da wannan tunanin ne a yau daya rage saura kwanaki hudu biki ta sake jan wayarta tana gwada lambar mima karo na wajen dari biyu da wani abu.
Kaman a mafarki taji ta shiga,saita miqe zumbur tana kaiwa da kowawa ita kadai tana fadin
"Ki daga mima,ki daga ki daga don Allah" gab da zata katse ta daga din kuwa
"Ina kika shiga don Allah?,ina kika tafi?,don Allah duk inda kike ki dawo a yau"
"Lafiya?"
"Ba lafiya ba mima,nace na fasa auren anwar saboda zai aureni nida shahida mima kina ina,ina buqatar taimakonki"
"Shahida kuma?" Ta tambaya cikin mamaki
"Eh ita dai" wani malalacin murmushi mima ta saki sannan tace
"To ai kinyi dai dai da kika ce kin fasa,hukuncinki shine dai dai"
"Kaman yaya mima,nifa ina qaunar anwar har yanzu ina jin soyayyarsa cikin raina,ina jin bazan iya rabuwa dashi ba" dan bata rai mima tayi sannan tace
"Duk da haka dole kiyi haquri ai yanzu bake ba shiga gidan saikin shirya,sabida haka kici gaba da walwalarki har zuwa sanda zan dawo karki damu komai zai gyaru yadda kikeso"
"Ina cikin damuwa mima,burina yanzu kawai shine na mallaki anwar,sai zuwa yaushe zaki dawo"
"A'ah fa,aikina kinsan babu gaggawa sai biyan buqata,saboda haka idan gaggawa kike kawai ki nemi wata mafitar bani ba"
"Shikenan saikin dawo"
"Yauwa...am idan ba damuwa kimin transfer mana,ina da buqatar wasu yan kudi"
"Babu damuwa,kaman nawa kike da buqatar?"
"Dubu dari uku ma sun isheni in jalauta"
"Ohk,accnt dina ya samu matsala bazaiyiwu inyi miki trasfer ba,amma zanje banki na tura miki"
"Shikenan saina jiki,karki wuce la'asar"
"Ba case" daga haka suka aje wayoyin,duk sai taji salama na shigarta tamkar matsalarta ma ta yanke kenan tunda sukayi magana da mina,saidai kuma har yanzu zuciyarta cike take da kishin anwar da tsanar shahida,da kuma jun babu dadi duk sanda ta tuna kwanaki qalilan ya rage su zama ma'aurata,amma idan ta tuna mima tasan cewa data dawo komai yazo qarshe,don so take kafin ita ta shiga gidan ta fara yin waje da shahida.
Kai tsaye ta sauqo qasa don zuwa kitchen ta samu wani abu da zata ci,yunwar data tarawa kanta tsahon satittika sai yanzu take taso mata,a falo taga mummyn tata,saita bi nafisan da kallo ba tare data ce mata komai ba harta shige kitchen din,lokaci daya ta fada ta rame,yarinyar Allah ya zuba mata taurin kai da kafiya,duk sunsan tana son anwar amma ba yadda suka iya sabida ta nuna ba zata aureshi ba,sun fita jin zafin rabuwarsu sabida sun shaida nagartarsa,basu da sauran abunyi bare su tursasata tunda basu zasuyi mata zaman auren ba.
Sai data ci ta qoshi sannan ta shiga tayi wanka,tayi 'yar kwalliya sama sama ta dauki muqullin motarta da kudaden da mummyn ce ta bata ajiya ta irga dai dai yadda mima keso ta fita bankin donta tura mata.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
File na qarshe ya qarasa dubawa ya rufe yana fadin wash gami da miqar da bayansa jikin makarin kujerarsa da yake kai yana cire agogon hannunsa gamida ajeshi gefa,duban muhsin yayi
"Uhmm ina jinka" ba tare daya ce komai ba ya ciro wata 'yar guntuwar takarda ya tura gaban anwar din,sannan ya aje wata a tsakiyarsu,wadda ya tura masan ya dauka yana dubawa,sai daya gama karantawa sannan ya kalli muhsin alamun yanason qarin bayani
"List na kudin dinkin kayan angwancinka ne,bazan biya wannan ba kai zaka biya" qaramin murmushi ya saki,gaba daya muhsin din ya hana kanshi sakat kaman shi zaiyi auren,hatta shi kansa sabbin kayan daya dinka saboda auren suna da yawa
"Ni malam dama bannce maka ina buqatar sabon kaya ba,saboda haka kayi sadaka" shima murmushin ya saki yana hararshi
"Baka isa ka sani sadakar da babu niyya ba,nadai ranta maka kuma zaka biyani" dariya ya dan saki yana daukar ruwan da muhsin din ya zuba baisha ba ya soma sha a hankali daidai sanda muhsin ya sake tura masa daya takardar daya aje a tsakiyarsu,aje ruwan da yakesha yayi yana sake dubanta
"Oh god,muhsin wai kana nufin da gaske dinner zakuyi?"a kaikaice ya kalleshi
"au...kai da kana nufin an buga katinne kawai saboda burga ko wani abu?,dinner ne na gama tsara komai ka duba gashinan ka gani,ka saka mana sunayen qawayen amarya" aje takardar yayi yana furzar da iska daga bakinsa
"Sai kaje ka tambayeta ai,nikam ban sani ba,ina zaman zamana lafiyar Allah zaka tayarmin da zaune tsaye ka tsiri hada dinner"
"Aikin banza aikin wofi,qaryar banza,ina cewa duka kwanakin nan saboda auren nan gaba daya ka canza,walwarka da fara'arka,duk wanda ka gani bakinka har qeya yake" tilas muhsin din ya sanyashi sakin dariyar da bai shirya ba
"Bakasan dawar garin ba muhsin,kasan auren dole?" Ya tambayeshi bayan fara'ar fuskarsa ta ragu
"Qwarai kuwa"
"Toshi zanma kaina" dariya sosai muhsin ya fashe da ita yana kallonsa
"Gayawa qaramin yaro da baisan abinda yakeyi ba...waima don Allah,ka gayamin meye ya hadaka haka da shahida,shahidan da a baya duk duniya baka da kamarta?"
"Tsarin Allah ne" ya bashi amsa ba tare daya dubeshi ba,fuskarsa na bayyana akwai radadi da ciwon dake cikin zuciyarsa,sai muhsin yayi shuru yana dan karantarsa kafin daga bisani yace
"Duk abinda zakayi kabishi a hankali anwar,ba dukka zatone yake zama gaskiya ba,daukan hukunci cikin zafi yana haifar da dana sani,ka dauki komai da sassauci karka yarda ka tsaurara dayawa,don tsauri bai har da komai sai cakudewar lamura da rashin samun gyara ko ci gaba" baice komai ba ya miqe yana rufe sauran takardun gabanshi sannan ya nufi toilet dake cikin office din.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Duk wani abu dake faruwa ganinsa take tamkar mafarki ne bawai gaske ba,tuni ta sare taci gaba da zubawa sarautar Allah idanu kawai,cikin kwana biyu da suka biyo baya gidan anty zubaida ya soma samun baqi 'yan biki,komai tana yinsa ne kan tsari da shirin anty xubaida,saura kwana biyu a fara biki akaje akayi mata jeranta,sanda su hasina suka dawo suna yaba kyan gidan tsarinsa da kyansa,itadai nata ido ne da kunne,shiri sukewa bikin sosai takowanne fanni,baga gidansu ba baga gidan anty zubaida ba,ba daga katsina ba,kaman dama kowanne jiran lokacin auren nata yake,hakan baya rasa nasaba da yadda take mutum mai kirki ga kowa,sannu a hankali kuzarinta ya dinga raguwa,karsashinta ya dinga raguwa,bata sake sallamawa ba sai ana ya gobe za'a fara gudanar da bikin sanda ta dawo daga qunshi,wani irin qunshi ne da aka shimfidawa hannu da qafarta kai kace zanene saboda kyau da haduwarsa,ba lallen ba gaba dayanta ta canza,duk wanda ya kalleta saiya kuma,gyaran kuma ya hadu da kwarjinin amarci saita zama kamar wata zara cikin wata,duk da yadda take fama da rashin kuxari da walwala.
Ranar da za'a yi kamu da wuri anty zubaida tasa ta koma a qarasa gyaran jiki na qarshe,itada hasina da wata coursin dinta suka je,daga can suka biya gidansu saboda daada data sauka a can tace tana son ganinta.
Gidan nasu ma baqine kota ita kasancewar wannan shine karo na farko da ummantata zata aurat da diya,tun daga soro aka soma sakin mata guda,wanda hakan yasa taji kanta ya sara,tadan tsuke fuska suka wuce ciki,a rumfa suka samu dadan,duk da tsufarta ita dinma amma sai data lallaba jan lalle wanda yayi mata kyau,tana zaune cikin matan 'ya'yanta da jikokinta shahida da hasinan suka shiga,guri daya ta samu ta zauna don ba zata iya maida tsokanar da ake mata ba da kiranta amarya da ake faman yi,tana jinsu har sukayi suka gama suka qyaleta.
Da daya da daya kowa ya fice ya barta a rumfar daga ita sai dadan,ta dubeta sosai gami da gyara zamanta tana kallonta
"Abinda yasa nace a turomin ke tun yanzu saboda bani da tabbas din xamu samu zama kamar haka idan kuka fara wadan nan bidi'o'in naku" baki shahida ta tabe,su waye a gaba idan ba goshi ba da zata ce haka,duk basu suka tada aurenba,suka tayar da zaune tsaye,sosai daada ta zama cikim seriouse ta soma magana tana duban shahida
"Kafin rasuwar mahaifinki Allah shine shaida cewa ya baki tarbiyya bakin gwargwado ya baki duk kulawar data dace,hakanan mahaifiyarki itama ta baki tata tarbiyyar bakin gwargwado,abinda nakeson cewa shine,kinar gani ko karki duba cewa anwar mun lanqwasaki ne kan dole kin aureshi,ba ruwan Allah da wannan,yi masa biyayya ya zama miki wajibi,dole kiyi idan yace dole ki bari idan yace,sauke dukkan haqqinsa ki sani ya rataya a wuyanki babu fashi,ruwanki ne kije ki masa tsiya ruwanki ne ki kyautata,koma meye kikayi abinda za'a soma fada shine tarbiyyar gidanku ce ta uwa da uba kenan,idan kinso kija musu yabo,idan kuma kinso kija musu zagi,Kiyi biyayyawa mijinki sauda qafa,yi nayi bari na bari,anwar ya riga ya zama mijinki Alqawarin Allah ne wannan daya cikashi"a fakaice ta sake tabe baki sannan ta miqe tsam tana cewa
"To,na gode" ta soma yin gaba zata fice daga falon,a tsakar gida ta samu hasina tana tsakiyar mutane suka kwasar cafta,da hannu kawai tayi mata inkiya ta fice,hasinan ta tashi ta bita bayan ta yiwa su umma sallama.
Qarfe hudu na yammaci harabar gidan maqotan anty zubaida ta cika ta tumbatsa da jama'a,wanda shahida dake zaune cikin dakinta anty zubaida ta kasa ta tsare mai kwalliya na mata takejin surutun jama'a da hayaniyarsu har tsakiyar kanta,babbar harabar gida ce wadda aka qawata da decoration me kyau da tsari wanda ya dace da sutturar da amarya zata saka,kota ina mutane ne dangin shahidan na uwa dana uba,manya da yara da yammata,wajen a tsare yake duk da yawan mutanen da suka halacci kamun.