← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 73

Sashe 30

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ya jikin naka?"anty usainar ta tambayeshi bayan sun gama gaisawa,dubanta yayi
"Waye yace bani da lafiya?"gajeran murmushi ta saki
"kana tunanin zaka iya boyemin ne,tun zuwan da kayi cikin wancan satin nasan baka jin dadi"
"Don dai karkice na musa miki ne...amma da nace lafiyata qalau,kawai stress ne na wajen aiki" kai ta kada kawai,tasan dama bazai taba yarda ba,baisan tsohon abu bane wannan a wajenta,ta karanceshi ciki da bai
"Hakane....Allah ya taimaka to"
"Amin" ya amsa yana ciro wayarsa da tayi qara alamun shigowar saqo,nafisa ce,ya karanta ya maida mata da thanks sannan ya maida wayar idonsa kan anty usainan
"Dama inason muyi wata magana ce da kai"
"Toh anty,Allah yasa ta samu"
"Eh to.....zancan nafisa,munyi magana da ita ta sanarmin kace rana ita yau kakesan suje su sami alhj abba,amma saga bangarenka banji kace komai ba har yanzu,ya kamata fa anwar ka maida hankalinka jikinka,da da yanzu ba daya bane,kullum shekaru qara yawa suke akan mutum,baya ga haka ma ya kamata mu fita kunyar yarinyar nan da iyayenta" shuru yayi yana saurarenra idanunsa na kallon carfet din da suke kai,har sai data kammala sannan ya dubeta cikin nutsuwa da jeranta kalamai
"Anty,har yanzu banji nutsuwa da gamsuwar nafisa ta zama mata agareni ba,har yanzu ina qoqari da tsarawa kaina yadda zan amshetq,bana son ayi abinda daga qarshe zai xama wani batu na daban,ina matuqar ganin qimar mama da abbanta,ina ganin mubi komai a sannu har zuwa sanda komai zai dai daita,zuciyata ta amshi abun dari bisa dari yadda ya dace"fuska anty usaina ta canza,har cikin ranta tana jin anwar din zai aikata ba dai dai bane kawai
"Anwar,idan ka sauya ra'ayi ne kawai ka furta,har xuwa yaushe kakeson yarinyar tayita zaman jiranka?,tun tana kara har takai ga tana takowa ta sameni da maganar,waishin ma idan bakayi aure ba yanzu sai yaushe xakayi anwar?" Ta jefa masa tambayar tana tsareshi da idanu
"Duka anty ba wannan maganar bace"
"To wacce ce gaya min?"
"Kamar yadda na gaya miki ne a baya,har yanzu zuciyata ta kasa nutsuwa da yadda da soyayyar kowacce yarinya,da nafisa zata haqura dani da nafi kowa murna,saboda zanso mata ta auri wanda yake sonta ba wanda takeso ba"
"Maganata ta tabbata kenan,kawai anwar ka fasa auren nafisa kakeson cewa,ka shirya butulci wa mahaifanta" cikin bacin rai ta qarashe maganar
"Banason ranki ya baci anty,za'ayi duk yadda kikeso,zanje da kaina na samu kawu abdulkarim na shaida musu,Allah yayi mana jagora" ajiyar zuciya ta sauke sannan tace amin Allah yasa ayi a sa'a,ko kadan batason iyayen nafisa su kallesu amatsayin butulu marasa cika alqawari,marasa kuma rama alkhairi da alkhairi,daga wannan magana ya miqe
"Har zaka wuce?"
"Eh...ina da aiki da yawa kwana uku ban samu shiga company ba"
"To Allah ya taimaka....amm dama inason gaya maka,cikin satin nan nakeso na shiga katsina mu gaisa dasu baba furai'ah,ya dace kaima ka ware lokaci kaje ku gaisa,don ba qaramin jimawa kayi rabonka dasu,tun suna qorafin kayi kudi ka watsar dasu sai aike har sun haqura ma sun daina" bawai zuwanne wajensu baya sonyi ba,katsinarce baya son shiga,shi duk wani abu daya jibanci tuna mishi da ita baya qaunarsa
"Zanyi qoqari in sha Allah" tana zaune daga nan har ya isa inda ya aje motarsa tana kallonsa,ya bude ya shiga ya tayar da ita yabar gidan.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan ya bacewa ganinta,ta fada dogon tunani,abinda yake dojewa dai yake nuna tsantsar qinsa shine ke wahalar dashi,lamarin da yake qaryatawa shike dawainiya dashi,itakam a duniya kaf bataga matar data dace dashi irin shahida ba,har yau yaqu furta nata meye sanadi?,meye dalilin rabuwarsu,har cikin zuciyarta tana qaunar yarinyar,ta zabi gida kusa dasu ne don tana saka ran wataran ta dawo mishi da ita cikin rayuwarshi,tarihin soyayyarsu,yadda tayi tambari ta kuma yi suna bai kyautu ace ta qare a haka a banza ba,ta sani cewa ko yaqi ko yaso koya nuna koya boye shahidan wani bangare ce na rayuwarshi,ta jima tsahon shekaru tana addu'a tare da fatan Allah ya shige mata gaba yasa taci galaba duk sanda ta tasamma tunkarar lamarin,domin cire qiyayya daga zuciyar da ada take cike da soyayya ba qanqanin abu bane,saidai a jikinta da xuciyarta duka tana jin lokaci yayi daya dace ta tashi ta gwada tabuka wani abu,koda zaiyi kuka da ita gaba tana da tabbacin zaya gode mata,duk da batasan meye yayi silar ruguxa wannan kyakkyawar alaqar da aka ginata cikin fahimtar juna ba.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Cikin lokaci kadan ta soma jin cewa zuciyarta ta karbi canjin da tazo mata dashi,ba'a dauki dogon lokaci ba uncle hisham yazo mata da upper ta daukan aiki a companyn *TRIPLE R GEM* kamfanin dake sarrafa duwatsu masu daraja da tsada zuwa kayan ado da qawa na mata ,irinsu sarqoqi,dan kunnaye,zobuna,abun hannu,munduwa da sauransu,mallakin *RAYYAN* miji ga *RUMANA DA RAIHANA* (DANGANTAKAR ZUCI).

Sun bata matsayin accountant na wajen gaba daya saboda yarda da amincin uncle hisham da rayyan yayi yasa ya bashi cigiyar wanda zai riqa masa wannan matsayin,matsayin da aka bata sai taji yayi mata girma,har taso tace ba zata amsa ba,uncle hisham ya zauna yayi mata bayani da kyau ya kuma nuna mata Allah ne ya bata,fatanshi kada ta bashi kunya ta kumayi aiki tuquru,tace in sha Allah.

Duk wani abu da ake baiwa sabon ma'aikaci mai matsayi irin nata sun bata,saidai taqi amsar gida da mota da suke bayarwa,tace bata da ra'ayinsu,ganin haka sai suka qara mata kudi kan wanda ya kamata a bata.

Uncle hisham da kanshi ya kaita gidan shugaba kuma mamallakin kamfanin gaba daya don tayi musu godiya,gida mai dauke da matan aure biyu kuma aminan juna,gida na farko data ji yanayin rayuwarsu ya burgeta bayan gidan anty zubaida,haduwar farko jininta ya hadu dana raihana,yanayin rayuwarta nutsuwarta da komai nata,haduwar farko ta karanci yadda ta iya tattalin miji cikin wani yanayi mai sanyi da kuma mu'amala,rumana uwargida,mace mai fara'a da saurin sabo itama sunsha hira da ita,wanda daga qarshe ta tattara kan yara tace zasuje siyayya ne ta barsu da raihana,yaran da shahida ta kasa tantance wanne ne yaran rumana wanne ne na raihana?.

Cikin qanqanin lokaci ta kama aikinta sosai,ta kama mutuncinta haka nan tsakaninta da ma'aikatan sai gaisuwar mutunci da girmama juna,ita kanta idan ka kalleta zakaga sauyi mai yawa tattare da ita sabanin baya,ta sake fresh hakan fatarta ta qara kyau da gogewa,kwanciyar hankali da nutsuwa sun samu tare da ita,ta soma shimfida sabuwar rayuwa,tayi wancakali da dukkan wani qalubale da bacin ran rayuwa.

_yanzu aka soma,muje zuwa masu karatu_

*Alqawarin Allah*
2️⃣1️⃣

*BAYAN SHEKARA DAYA*

Komai na duniya baya ga qaddara yana tafe ne da lokaci,wanda wannan lokacin shike qunshe da komai,yake tattare da faruwar komai,shike bayyana komai hakanan shike haifar da komai din,cikin shekara guda shaheedan ta samu sauyi da canje canje masu tarin yawa,tayi qoqarin binne duk wani qalubale data taba samu cikin rayuwarta,ta kaucewa dukkan wani abu da zai tuna mata dashi fiye da baya,ta fannin rayuwarta kuwa shahidan ta sake zama wata mace mai aji,irin macen da kana mata kallon farko zakasan ta goge,bawai gogewa ta budewar ido ba,gogewa ta kyau,gogewa ta iya ado da mu'amala sakamon mu'amala da take da mutane kala daban daban daga sashe daban daban na qasashen afrika,ta qara wani kyau da kwarjini,hakanan ta murje,ta gefe guda kuwa a yanzu nuraddeen ya samu kanta babu laifi,aduk sanda ya kirata zata daga su taba hira,hakanan duk sanda yazo wajenta a gida takanyi qoqarin fita,wani lokaci ma yakan bita wajen aiki da niyyar daukota,anan ta dakatar dashi,don babu abinda ta tsana a duniya a yanzu irin shiga motar wani d'a namiji,duk sanda ta saka kai zata shiga sai abun ya fado mata,wannan moments din ya kasa barin qwaqwalwarta,shine kuma abu mafi muni cikin dukkan abinda ya faru da ita,tana mamakin me ta yiwa wannan mutumin daya watsota qofar gidansu cikin cin mutunci da wulaqanci?,me ta yiwa fiddausi wadda har yau bata bi ta kanta ba ko neman inda take,hasalima bata sake ganinta ba,to me zatayi mata?,me zata buqata daga gareta?,koma meye tana roqon Allah yayi hukuncin daya dace.

To ko cikin company ma da baqin dakanzo siyayya kamfanin masoyane suka mata rubdugu,wani lokaci har haushi kan kamata na yadda ba'a cikakken kwananki uku wani bai ganta yace yana so ba,ta rasa meye a jikinta haka?,me take dashi wanda yake jan hankalinsu?,da tasan wannan abun ba shakka data cireshi ta jefar kota huta da shegen binbinin da suke ma rayuwarta
"Kin hadu ne shahida,kina da komai Allah ya miki baiwar komai,ba zaki gane abinda nake nufi ba shahida,amma kinyi tako ina,ki bani dama don Allah" ta tuno kalaman wani alhj wanda tunda yazo kamfanin siyawa matarsa sarqoqi gift na birthday dinta ya dafewa shahidan,a sannan ta sauko zata je cin abinci,baima san ma'aikaciyarsu bace.

Gefe daya ta sake yalwata rayuwar ummanta da qannenta,hakan ta yiwa gidansu gyara ta sake qawatashi,ita kanta a yanzu jin dadin rayuwarta take,abu daya ne data fuskanci umman nata ta tsiro dashi shine son shahidan tayi aure,don zancan da ake mubina na ss two ne,kuma ta samu wanda yake sonta,dama yakeso a bashi yaje can wajen dangin mahaifinsu dake katsina ya gabatar da kanshi.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Qarfe hudu suka tashi daga aiki yau,cikin sauri saboda kar lokaci ya qwace mata ta shiga adaidaita sahun da yake nata ne yake kaita aiki ko wata unguwa da takeson zuwa,a sanda kuma ya ajeta yaje yayi haya dashi.

Saloon din da take zuwa kitso ya sauketa,ta dubeshi
"Ka dan jirani yau ba dadewa zanyi ba"
"To hajiya" ya fadi yana kashe adaidaitan,ta juya cikin takun nutsuwa zuwa bakin saloon din.

Yanayin wajen kaman tsarin ciki da falo aka yi masa,duk da qofar cikin mai fadi ce sai aka saka labule mai shara shara,falon kuma kujerun zaman custumers ne da kuma kayayyakin siyarwa na kwalliya kamansu ribbom,man kitso man shamfo,beads da sauransu.
Chapter 30 · 0% Book details