← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 73

Sashe 67

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Horn biyu maigadin ya dage masa gate din ya saka motar,ya qaraso suka gaisa da anwar din sanda yake fitowa daga motar,suka soma takawa zuwa cikin gidan,suna gab da valcony din da zata sadasu da qofar falon tana fitowa cikin doguwar riga da yalolon mayafi,hada idanu sukayi da anwar,saita kasa dauke idanunta daga kanshi,gabanta na faduwa qaunarshi na sake ratsa zuciyarta fiye dada,sai taga kaman an qara masa kyau da haske,ga wani kwarjini na musamman da gake fitarwa,shi ya soma janye nashi idanun ya soma yin gaba,suka hada idanu da shahida dake bayanshi,kowacce nata idon cikin na 'yar uwarta,sake kallon shahidan nafisa take sama da qasa,kishinta na ratsata,ta sake kyau da aji fiye da daa,duk da cewa ba zata taba mance fuskarba,duk da cewa ta ganeta amma saita janye idonta daga kanta ta rufawa anwar baya,tana jin wani abu na sukar zuciyarta,da kallo tabi bayan shahidan har suka wuce,sannan taja qwafa ta wuce,tanajin a zuciyarta wannan karan kam ba zatabi shawarar mima ba,zuciyarta takai maqurar da bazata iya jurewa ba.

Yana gaba tana binsa a baya cike da kunya har cikin babban falon anty usaina,gaba daya yaran suke miqe suna musu sannu da zuwa,sa'ida ta soma tare shahida ta rungumeta
"Oyoyo anty,uncle,amma bakacemin zakuzo da anty ba yau"
"To ai gata kin ganmu" ya bata amsa yana zama saman daya daga cikin kujerun,yayin da maibin sa'idan ta haura sama donta shaidawa anty usainan zuwan sun tana cewa
"Yanxu ma tahau saman,anty nafisa ce tazo dubata" cikin shi da shahidan ba wanda yace komai ba,itakam nunawa ma tayi kaman bata santa ba bare ta ganeta,sunata taba hira da sa'idan,yayin da shi kuma ya shiga tunanin me nafisan tazoyi gidan anty usainan?.

Dawowa tayi ta shaida musu tace su hau saman,shine dai a gaba tana binsa a baya har suka bayyana wani falon dake daman,anty usainan na zaune qasan carfet suka shiga da sallama,fuskar anty usaina wadace da fara'a takewa shahidan lale kota anwar ma bata biba,a kunyace ta zauna gefan anty usainan tana jin anwar na tambayar antyn fitilun harabar gidan da wasu suka mutu
"Ka qyalesu hakanan tunda dai gidan da haske ai shikenan" saita sake maida kanta ga shahida wanda kanta ke sunkuye a qasa,gaidata tayi a kunyace anty usainan ta amsa cikin kulawa,Shahidan ta mata sannu da jiki ta amsata
"Aina warware alhmdlh,shine sai daya tattagoki" qaramin murmushi ta saki kanta a qasa cike da jin kunya da nauyinta,daidai lokacin sa'ida ta shigo dauke da tray wanda ta cikashi da kayan ciye ciye,kai tsaye ta aje gaban shahidan,ta durqusa tana zuba mata duk abinda ke cikin farantin,qasa qasa shahidan ke kallonta tana dariya idanu a waje yadda su anty usaina bazasujiba tace
"Sa'idah,wannan duka?,aisai cikin antyn taki ya fashe"
"A'ah anty kici wallahi,yauke baquwarmuce ta musamman"
"Mu kuma aisai a koramu ko?,yauni aka yiwa danwaken zagaye saboda kin ganta ko?" Tana dariya sa'idan ta daga kai daga shiryawa shahida cake da take cikin plate ta kalleshi cikin dariya
"Ba haka bane uncle nina isa?,kawaidai nasan ka gayamin cewa kaida anty abu guda ne,kaga idan na bata kamar kai na baiwa" murmushi yayi yana daga mata hannu yana satar kallon shahidan,shi sam ya mance daya gaya mata hakan,ya fada ne a gaban anty usaina don sake kwantar mata da hankali da amintar mata tunaninta,saidai ya manta sa'idan bata mantuwa,ta kammala zubawa shahida komai ta miqe tana duban anty usaina
"Na gama ummi"
"Shikenan,idan kin sauka ki shiga kitchen ki tafasa min maganin nan,ki samu botiki mai murfi ki xuba a ciki kidan sabashi yasha iska kafin na sauko shi xansha"
"Tohm" tajuya ta dubi shahida
"Anty kici sosai don Allah ki cinye duka" murmushi kawai tayi tana dubanta,sosai yarinyar take sonta da burgeta.

Inda shahidan ke zaune ya sauko,ya zauna sosai a gabanta,farantin dake tsakiyarsu ne kawai ya raba tsakaninsu,idanunsu suka shiga cikin na jina,kowanne ya zare nashi idon daga cikin na dan uwanshi yana jin yarrr cikin jikinsa saboda kusancin da sukayi da juna yayi yawa,saiya sanya hannu ya dauki kofin gabanta yana cewa
"Tunda niba wanda yayimin tayi bari nayiwa kaina"
"A'ah..ban yarda da wannan juyin mallakar ba,aje mata,kaidin baqo ne da bazaka dauka da kanka ba?" Murmushi ya saki yana tsaida kofin da yayi nufin kaiwa bakinsa
"To ai anty itama ba zata sha ba idan bansha ba" ya qarshe maganar yana waiwayawa ya dubi shahidan yana kashe mata ido,sadda kanta qasa tayi saboda wani abu dataji ya saukar mata saman zuciyarta mau nauyi,yakai bakinsa ya kurba lemon ya miqa mata suna magana da anty usaina,qin amsa tayi har ya gama maganar ya juyo yana dubanta
"Karbi mana,kosai na baki da kaina?" Harara ta cilla masa a fakaice ta saka hannu takarba ganin yana kai kofin bakinta,ya xuba mata ido sanda takai kofin nata bakin,tana sane ta juya daga wajen daya sha ta sauya gurbi,murmushin mugunta ya saki ya waiwaya wajen anty usaina yana tambayarta
"Me yarinyarnan tazoyi gidan nan?,na ganta sanda muke shigowa"
"Nafisa?....waitaji banji dadiba shine tazo dubani,amma tazomin da wata magana da nace saikazo naji ta bakinka tukunna" ta fada tana dan dubam shahida,batason yin maganar a gabanta,amma kuma tana ganin yin maganar a gabantan kamar xai bada wani alfanu game da kawo gyara kan yanayin mu'amalarsu da anwar,don har yanzu bata gamsu da yanayin zaman nasu ba,tana ganin yadda suke abu kaman baqin juna
"Tace na baka haquri akan kuskuren datayi a baya,tana son idan da hali ka dawo ka....." Daga kai anty usaina tayi tana duban shahida wadda ta miqe tsaye
"A'ah,ki zamanki shahida mana?"murmushi tadan saki,don tunda aka ambaci sunan nafisa zuciyarta ta gaya mata ba kowa bace illa wannan wadda suka gani dai sanda zasu fita,fuskar da anwar ya aiko mata da ita cikin envalope din data baiwa suna da baqin saqo,hotunan da har yau ta kasa rabuwa dasu dukda yadda suke qona ruhi da zuciyarta duk sanda ta tuna dasu,ko kuma duk lokacin data kallo gefan da suke aje
"Zan saukane wajensu sa'ida"
"To shikenan,nima ganinan zuwa,ai bamu gama hirar ba"
"Toh anty" ta fada ta juya tana fice daga dakin,anty usaina ta bita da kallo farinciki na ratsa zuciyarta,tanason karanto wani abu game da shahidan,saita maida dubanta ga anwar,wannan karon shiya soma magana
"Don Allah anty karki shiga maganar nan,an riga da an wuce wajen tuni,na godewa Allah da bani na soma gudunta ba bare aga butulcina,ta ruga data gayamin manufarta tun rannan,kuma kullum kwanan duniya saita aikomin da saqo kan hakan" ajiyar zuciya anty usaina ta saki,itakam a duniya yanzu ba abinda ya rage mata illa taga kan shahida da anwar din ya hadu kawai,ta tabbatar idan hakan ta faru babu kuma sauran wata matsala
"Shikenan Allah ya zaba abinda yafi alkhairi,nikam yanzu bani da burin daya wuce naga kanku ya hadu yadda ya kamata kaida shahida,yarinyar tana da nagarta anwar,kayi qoqarin gyara zamanku,gashi kuna qoqarin cinye wata na biyu amma a karatuna banga hadin kan da nake buqata ba,ajiyar zuciya ya saki yana dan kashingida kadan,cikin zuciyarsa yana fadin antyn ba zata gane ba,shi kadai yasan me yakeji kullum kwanan duniya,a raye yake amma zuciyarsa matatta ce,ya gaza gano dalilin daya sanya shahidan aikata dukkan abinda ta aikata a rayuwarta,meye sila?,meya janyo haka?.

Shahida na qasa suna hirarsu dasu sa'ida anty usaina ta koro anwar qasan takuma ce ya turo mata shahidan,sanda taje kusan karatun xama da miji tayi mata sosai ba kunya ko nauyi tsakaninsu
"Shahida...kiyi haquri da yadda rayuwar aurenku taxo muku ahagunce kuma a kaikace,farinciki gamida walwalar gida a hannun matar gida take,tana da ikon maida gidanta aljannar duniya ko kuma akasin haka,duk yadda namiji keda taurin kai,taurin zuciya da kuma kafiya abune mai sauqi matarsa ta canzashi matuqar tayi karatu mai yawa akanshi da halayyarshi,kiyi haquri kiyi qoqarin canza gidanki,ki zama mace sosai,kiyi amfani da hikima da basirarki,kaf dinmu makusantanki dana anwar ba wanda yake fata ko burin rabuwarki dashi,kinga kenan babu ranar da zaku rabun,tome zayasa abinda babu ranar yankewarsa maimakon ka gyarashi kaji dadinsa ka amfaneshi saika zabi dawwama cikin karkatacciyar rayuwa maras dadi?,duk lokacin da rayuwar auratayya ta kacame ta lalace babu wanda yafi cutuwa a ciki,yafi quntata,yafi zama cikin wahala baqinciki da bacin rai irin MACE,namiji nada tarin hanyoyin da zai debewa kansa kewa ya ragewa kansa baqinciki da bacin rai,ba kamar ke mace ba da taki damar qwaya dayace wannan mijin da kike aure,kome anwar ya miki,duk da bansan girman cutarwar da yayi miki ba abaya,ina mai qasaqantar da kaina da roqa masa alfarmar ki yafe masa,ki tashi tsaye ki gyara gidanki,ki masa kyautatawar da girmanta zaisa yayi nadama yayi danasani,ya kuma ji kunyar aikata miki dukkan abinda ya aikata mikin,ita mace tana da wannan power,zuciyar namiji a wajenta ba komai bace horewa ce ta ubangiji,nasan zaki iya din ina kyautata miki wannan zaton,ina roqar alfarma zakiyimin shahida?"cikin jin kunya da nauyi gamida gasgata kalaman anty usaina ta gyada kai
"Xan miki anty,zanyi in sha Allahu" ajiyar zuciya ta saki tana lumshe idanu
"Na gode qwarai,amma kafin sannan,ki nutsu ki mu'amalanceshi ta yanayi da sigar da yake mu'amalantarki gudun kadda kisha wahala,ina fatan kin fahimceni?" Kai ta gyada mata alamun ta gane,hakan ya yiwa anty usaina dadi sosai,da kanta ta bude cupboard dinta ta ciro mata wasu rigunan bacci masu shegen kyau da sulbi guda shida,ta hada mata da turarukan bedroom suma guda hudu masu kyau da tsada,ta amsa tayi mata godiya sosai,saita danyi jim,anty usainam ta fuskanci akwai maganar da takesonyi,saboda haka tace da ita ta fada kada taji nauyi ko kunya
"Anty aron sa'ida zaki bani don Allah tayimin ko sati guda ne" baki anty usaina ta bude
"Keda zaki shiga yaqarmin tunanin dan uwa na hadaki da sa'ida ta hana ruwa gudu?" Kunya ta sata sadda kai tana dariya
"Shikenan,amma ba zata wuce kwana uku ba"
"Don Allah anty ki barta tayi sati" daqyar ta yadda da hakan,sa'ida murna kaman me ta hada kayanta ta bisu.

*11:30 pm*
Chapter 67 · 0% Book details