← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 73

Sashe 68

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Doguwar rigar bacci ce a jikinta mai sulbi wadda takai har qasa da dogon hannu,sai baby hijab data sanya wanda iyakarsa saman kafadunta,duk motsin datayi qamshi ne yake tashi harta iso matatattakalar qarshe wadda daga ita sai qaramar baranda da zata sadaka da falon samanshi,cak ta tsaya tana ajiyar numfashi,shida kanshi ya mata magana kafin su shigo gidan kanta taho samanshi saboda sa'ida kada ta karanci yanayin zamansu,baiso anty usaina ta fahimci komai,baisan yayi sara bane kan gaba,ta riga data gama shirinta dukda ciwo da takeji a qirjinta da nauyin alqawarin data dauka,anya zata iya saukewa?,takewa kanta wannan tambayar,duk sanda fuskar nafisa ta gilma mata a idanu,yadda ya cillota da girman kalaman daya sossoka mata saitaga gaba daya yayi mata baqi a ido,koren shaidan tayi sannan tayi bismillah taci gaba da takawa ta tura qofar falon ta shiga. *Alqawarin Allah*
43

Wani irin murdawa mararshi tayi wanda hakan ya sanyashi duqawa riqe da cikinsa,ya tako a haka a hankali zuwa gefan gadon,idanu ta zaro jikinta ya dauki rawa,ta tako ta tsaya daga bayanshi amma ta kasa cewa komai,da qyar cikin rawar murya tace
"Sannu,baka da lafiya" kallonta kawai da yayi da qwayar idanunsa da suka kada zuwa launin jaa ya tabbatar mata da bashi da lafiyar kenan,ta juya zata futa da niyyar ta kira anty usaina ta shaida mata,saiya dakatar da ita
"Jirani na shirya,zanje naga likita".

Hannu likitan ya saka ya cire abun abun awon jini daya sanya a dantsen anwar din yana kallonshi
"kamar yadda na tsammata ne,jininka yahau sosai,kamarma yahau fiye da kowanne lokaci,gaskiya anwar bazan boye maka ba,wani lokaci sai naga kamar kana wasa da lafiyarka ne,bansan meya hanaka kwantar da hankalinka ba ka samu jinin nan ya sauka gaba daya,sai yayi kaman ya sauka saiya sake hawa,bansan daga inda matsalar take ba" murmushin qarfin hali yasaki,ya lumshe idanunsa kana ya bude
"Share kawai khalid" likitan mai sunan khalid ya waiwaya ya dubi shahida wadda ke zaune wata kujerar daban,hannayenta rungume a qirjinta,ta zubawa anwar ido ba tare da yasani ba,kallon mamaki take masa na bayanan da taji daga bakin dr khalid,wanne irin hawan jini?,yaushe anwar din yasamu hawan jini?,iya saninta dashi kaf tarayyarsu anwar baida hawan jinin,yaushe ya gamu da wannan matsalar?
"Madam" ya kirata wanda hakan yaja hankalinta zuwa kanshi
"Bayan hawan jini gaskiya abokina na buqatar kulawa,don Allah ki kulamana dashi,nasan kinfi kowa sanin mutumin kirki ne,lalurarshi ba zata yiwa mutane da yawa dadi ba" kai ta gyada likitan ya miqe yana cewa
"Ruwa naso indan saka maka,amma nasan hali ba zaka taba yarda ka zauna ba,bari na rubuta maka wasu magungunan na bayar a karbo maka,madam sai a kula da bashi akan lokaci" kai ta sake gyadawa tana duban anwar din,saita kauda kai sanda taga ya waiwayo suna shirin hada idanu.

Suna tafe a hanya motar ta dauki shuru,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,tambayar ta yiwa shahida tsaye a rai na hawan jinin anwar,yayin data gefan anwar din maganganun dr khalil suka dinga kai kawo a qwaqwalwarsa,tabbas ba shakka shine mutum na farko da zaifi kowa son rabuwa da cutar,zaifi kowa son ganin ya cire kome cikin ransa,zaiso ace ya goge kome dake damunsa,amma saidai shi kansa yasan hakan bame yiwuwa bane,shahida ce,idan da wata macen ce daban ha tabbatar da tuni ya cireta daga rayuwarshi irin fitar da mai rai kanyi daga duniya wanda har abadan bazai dawo cikinta ba,amma akan shahidam hakan ya gaza,ya sani cewa koda zai fada a baki koda zai nuna a aikace shahidan bata dameshi ba yayiwa kanshi qarya,karon farko dayakejin inama inama,inama ace bai kalli hotunan ba,inama ace ranar baije gidansu zance ba bare yaga abinda ya gani,inama ace shahidan bata fada halin data fada ba a baya,da wannan tunanin suka isa gida,da kanshi wannan karon yasha maganin sannan ya shiga bedroom dinsa ya kwanta kozai samu relief.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

A kasalance yake shiryawa cikin farar shadda,riga iya gwiwa mai gajeran hannu da dogon wando,kana ganin yadda yake shiryawar kasan cewa ba wani dadin jikinsa yake ji sosai ba,yana daura agogon hannunshi ta turo qofar dakin da sallama,hannunta riqe wata butar shayi me kyau,da mamaki take dan dubanshi saidai bata tanka ba ta aje butar
"Ya jikin?" Ta tambaya a taqaice,daga kai yayi ya dubeta yadda ta juya baya ya maida kansa yaci gaba da daura agogonsa sannan yace
"Alhamdulillah" tadanyi taku biyu sannan ta sake tsaiwa,ya fuskanci akwai magana a bakinta saiya amsa
"Tun jiya akwai alqawari. Haduwarmu dashi,jiya banjin dadi,so yau nakeson nacika" yana gama fadi ta taka ta sauka daga saman,dama tanson jin fitar zaiyi amma tanajin nauyin tambaya.

Tun jiya take zuba idanun ganinsa,ta kasa zaune ta kasa tsaye,tun bakwai na dare take zirya tsakanin harabar gidan,falon abbansu zuwa nasu falon da dakinta ma gaba daya,ganin goma na dare tayi hankalinta yayi mummunan tashi,Allah yasa abba bai gane ba,Allah yasa anwar bai kira abba ba ya sanar masa yaji yana nemansa ba abba kuma yace bashi bane,daga daren zuwa safiyar ranar ji tayi kaman ta zare,duk motsin shiga da fitar mota a gidan yana kan idanunta,saida dare yayi ta tabbatar babu wani sauran wanda ka iya zuwa a wannan lokacin sannan ta haqura.

Da safema haka ta dasa abun zama cike da fata da kuma buri,qarfe goma da rabi da minti takwas aka saki horn mai gadi ya doshi qofar don ya bude,gabanta wani mugun faduwa yake haka tamiqe tsaye tana duban qofar gidan,kusan shidewa tayi sanda taga fitowarsa daga motar,idanunta qur akanshi yana sake burgeta duk wani motsi da yayi,tana kallon aka masa iso cikin falon daddyn,cikin wani mugun hanzari ta diba tayi cikin gida kai tsaye ta wuce dakinta,hijabi ta lalubo ta zira saman kanta sannanta sake fitowa da hanzari don kada lokaci ya qwace mata.

Sanda ta shiga mummynta na tare da daddyn,hakan yayi masifar yi mata dadi,sait tayi qoqarin daidaita nutsuwarta ta taka zuwa cikin falon da sallama.

Dukkaninsu suka amsa mata,ta isa gefan daddyn inda anwar ke zaune qasan carfet saboda girmamawa suna gaisawa,nan ta duqa kan duka gwiwoyinta,ta saki kuka sosai wanda ya karade ilahirin falon,duka sakin baki sukayi suna kallonta,mummy ce cikin hade rai tace
"Kewai meye haka?,wanne irin shashancine wannan kawai zaki shigo kisa mutane a gaba da kuka?" Cikin muryar kuka tace
"Don girman Allah mummy ku yafemin,ku yafemin,ku roqamin ya anwar shima ya yafemin"
"Me ya dawo da wannan maganar data riga tawuce kuma nafi?"
"Gafarar ya anwar nake nema" gaba daya kanshi ya kunce,shi sam.bai dauki abunda tayi a matsayin wata matsala ko abun bacin rai ba,tuni ya riga daya wuce wajen,tun a lokacin da abun ya faru shiya tattara komai daya shafi wannan fannin ya ajeshi a gefe,baison zancan yayi tsaho saboda haka yace
"Ya riga ya wuce har abada" ranta taji yayi,wani mugun sanyi,alamun nasara na tabbata kenan a gareta,saita sake sunkuyar da kanta qasa sosai sannan tace
"Bansan cewa nayi wauta ba kuma nayi kwaba saida na rabu dakai,nakai kukana ga abba da mummy amma kowannensu yaqi mara min baya ka dawo cikin rayuwata,sunce idan ka amince suna murna da hakan,saboda sunsan cewa idan sukayi maka magana ko bakaso zakace eh,gani a gabanka anwar don girman Allah inason ka sake dawowa rayuwata karo na biyu,ka yiwa iyayena dake shauqin son ganin haka alfarma wanda alkunya da kawaici yasa suka kasa gaya maka"
"Ke nafi!" Abbanta ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsaw,a,bataji komai ba don idanunta da zuciyarta sunyi nisa wajen son ganin cikar muradi da burinta,saita daga kai ta dubi abban sannan ta sake sunkuyarwa
"Abba na fadi masa gaskiyar abinda yake faruwa ne,na tabbatar da zaka iya da kaine xaka nemi ya aureni karo na biyu....anwar,ka duba wannan alkunya da kara ta iyayena gami da girman soyayyar da nake maka" baqinciki ya kama mummy na yadda sam halayen nafisan suke wadansu irin mabanbanta daban,ta kawo mata duka anwar ya dakatar da mummyn cikin sauri
"Rabu dani na mata duka,baki da kunya nafisa ko kadan?,a gabanmu kice kin fasa aurensa,sannan ki dawo a gaban namu dai kice ya aureki?,wace iriyar yarinya ce ke?" Cikin kuka sosai nafisan tace
"Kuskure ne mummy yanzu kuma na gane kuskuren da nayi,wallahi idan babu anwar rayuwata ba zata taba dai daita ba,mummy ku tayani bashi baki"
"Ce miki akayi baida zuciya da zaki gujeshi yanzu ki dawo masa saboda rashin ta ido?,kema kinsan bazai taba yiwuwa ba" mummy ta amsa mata tana jifanta da harara,so take kawai ta samu dama ta daki bakin nafisan ya fashe ko zata samu sassauci takaicin dake cikata
"Na amince zan aureta" anwar ya furta,lafazin daya girgizasu dukka su ukun,basu taba zata ba sam ko a mafarki,sunyi tsammanin bazai taba yarda ba,cikin hikima yake karantar yanayin fuskar alhj abba da munny bilkisu,ko basu fada masa ba ya gama karantar yanayin da zukatansu suka shiga,alhj abba da mummyn suna da daraja a idanunshi,ya sani cewa tsantsar kara kawaici da alkunya ne dasu,amma da qauna kowa ya sani suna matuqar qaunar nafisa,me yasa shi bazai iya musu kara ba ya auri diyar su wanda yasan shine cikon muradinsu,ba shakka da nafisan diyar wani ce da ya barta kenan har abada,amma ko a lahirama wani yana cin albarkacin wani bare nan gidan duniya.
Chapter 68 · 0% Book details